_BM_
_08_
_NA:_
_NANA HAFSATU_
_______
Ahankali ta shiga bude manyan idanun ta tubarkAllahbda ke mata nauyi saboda baccin da ke neman rinjayar ta.
Dai dai lokacin da liman ya fara kirayen assalatu. Ta tashi da addua a bakin ta tana mai mike hannuwan ta sama.
Mikewa tayi ta shiga bandaki ta yo tsarki hade da dauro alwala. Tun da safe da aka kammala gyaran gidan aka kintsa ko'ina..don hatta sallayar da zatayi sallar akai an shimfida an ninke hijabi an ajiye shi daga gefe. Ga kuma charbi da wasu littafai na islama. Sai Qur'ani akan abun ajiyewar sa
Ta hau kan sallayar bayan ta zura hijabin ajikin ta. Nan da nan ta dau niyya ta da sallar.
Ko bayan data idar bata tashi ba tana zaune akan sallayar tana azkhar. Cikin haka aka kwankwasa kofar dakin
Tana daga zaunen ta mike ta bude kofar.. mahaifiyar tache ta shigo ciki.Ta tsugunna har kasa cikin girmamawa ta shiga gayshe da mahaifiyar ta ta.
"Alhamdulillah Amaal. Da fatan kin kwana lafiya?"
"Alhamdulillah..."
"Ma shaa ALLAHU! Ai inata sauri nache ko baki farka ba."
"Ah na tashi.. Na ma ruga alarm din tashi."
"Ma shaa ALLAHU... Allah yayi albarka"
"Amin Hayateey. "
"Kin kai kayan naki ne?"
"Ina?" Saboda baki daya ta manta .
"Dakin ku mana..."
Nan da nan fuskar ta ta sauya. Har ga Allah batasan kasancewar ta a dakin nan. Tasan kullu yaumin ranta ne zasu dinga bataa mata shi.
"Ina miki magana kinyi shiru..."
"Yi hakuri Hayateey. Wallahi banason zama tare da su."
Hajiya jamila ta sauke ajiyar zuciya. Ta sanya hannun ta kamo amaal suka zauna akan gado.
"Ya sunan ki na ainihi?"
"Maryaam."
"Sunan wa kika chi?"
"Sunan Hajiya.."
"Wacece Hajiya?"
"Mahaifiyar su abbiey..."
Haj jameelah ta kada kai kafin ta cigaba da cewa,
"Lokacin da abbieyn ku ya yanke dawowar mu Nigeria gaba daya. Da zama acikin kandem estate wayace ya roke shi alfarma daya hade kan kawunan iyalin sa ko dawowa akayi kada a rarraba kan yara. Son samu a hadesu waje daya don samun jituwa da wanzuwar zaman lafiya a tsakani. Waya ba abbieyn ku shawara ya amince batare da ya musa ba ko sau daya? Uhm waya bashi shawara?"
"Hajiya ce ta bashi shawarar."
"Ma shaa Allah! Hajiyar nan mahaifiyar sa ce, Kuma mafi soyuwa awajen abbieyn na ku. Abu na biyu kin manta biyayya ga bin nagaba da kai musanmam ma iyaye ? Iyayen ma mahaifi agare ki. Don haka kar ki kuskura kice ke a'a ko da kuwa zaki halaka sai ki hakura ki fawwalawa Allah lamuran ki.. Domin komai nisan dare gari zai waye Allah zai bayyana mai gaskia. Bugu da kari kada ki manta ma sunan Hajiya kikachi... Banason na sake jin cewar bakyasan kasancewar ki atare da su. In shaa Allah alkhairi ne zaman na ku. Kuma da yardar Allah Allah zai kare ki ki cigaba da addua. Kinji?"
Daga kai tayi. Hawaye daya na bin daya. Ta dubi dakin da take ciki wanda yake da a matsayin nata ita kadai yanzu kuma zata koma su dinga kwana tare da yan uwanta da suke uba daya
Hawa na uku agidan aka gyara akayi wani irin katafaren hadadden babban daki me girma sosai da babban parlorn sa aciki. Da bandakuna har biyu. Da kitchen da store da balcony.
Gadaje ne a jere kowa da nasa da durowar sa. Da kujera da computer ta aiki akan desk sai mini fridge karami a gefen gadaje biyu. Sai bookshelves guda uku manya a jere dauke da littafai.
Daga gabas kuma makekiyar tv ce plasma ta bango da setin kayan kallon. Kitchen dinsu ma babu abunda babu harda kayan abinci bayan kuma cikin agidah zaa dafo a kawo musu. Nasun kuma an ajiye musu ko saboda gaba zasu bukache su dafa dan wani abun
Sai wani daki daga gangaren bene, Shi kuma kayan motsa jiki ne kala kala acikin sa.
Sai wani babban daki daga hanyar fita an rubuta study agaban kofar dakin. Kana shiga zaka dora idanun ka akan kujeru kowanne da benchin sa agaban sa. Ga Qur'anai nan a ajiye da sauran littattafai na addinin islama.
Da makekiyar dispenser da disposable cups a gefe. Da manyan sallayoyi masu matukar laushi da carbi suma a gefe.
Gwanin ban shaawa dai ko'ina a tsare a kuma killace. Dakin gaban sa kuma babban daki ne shi ma da manyan katifu biyu da tv ta zaune da karamin firji a gefe. Da babbar fanka ta tsaye.
Dakin manyan masu aikin su ne da aka dakko musanmam saboda sa ido akan su da kuma tayasu ayyukan wasu abubuwan. Su uku ne. Manya biyu sai budurwa guda daya.
Su kuma bangaren mazan yana daga can baya idan an fita daga kofar sashen na iyayen su matan da na su Amaal.Anan akayi musu nasu bangaren suma kamar yadda na su amaal din yake.
Sai da su dakunan su kowanne daki mutane biyu ne aciki. Dakin da ya zamana a bangaren su Amaal din maaikatane aciki su kuma dakin ya zamana na Yaya babba wato sadeeq . Babban da ga amb. Junaid..
°°Bayan wayewar gari sosai ainun. Amb. Junaid da kansa ya kikkira matan na sa awaya ya sanar musu shi fa tun asubah ya koma bangaren Hajiya. Dan haka achan zai karya kumallo zai kumayi wanka.
Ya nanata musu cewar idan sun ci abindin safen su hanzarta su yiyyi wanka su shrya don zasu zagaya gidajen yan uwa da basu shisshiga ba. Kasancewar daren jiya yaja sosai shysa basu shiga ko'ina ba.
Maaikata ne suka kakkai musu abincin karin kumallon. Duk abunda zasu bukata an tanadar musu. Wani abincin ma ko tabashi ba suyi ba.
Tuni kowannen su ya fara shiri. Masu shiga bandaki nayo wanka. Masu rage ciki nayi. Masu saka kaya da sauran su. Kowanne dai ya zama cikin shiri.
Hajiya. J ta shiga wajen Amaal dake tsaye tana bottling din buttons din doguwar rigar da ke jikin ta. Tundaga saman rigar har zuwa kasanta wasu manyan botira ne masu girma da kyakyali. Sai kananan botiran a hannun rigar ta da ake maqale su. Mayafin rigar ma ya sha adon botiran gefe da gefe.
"Wai baki gama ba amaal? Ni meyasa ne kike da shiririta? Kinfi so kullum dai ache keche da lefi? Sarkin makara. Kullum ke ake bari a karshe a shirin komai. Sanyin jikin ki yayi yawa. Matso nan ni na karasa saka miki."
"Hayateey kiyi hakuri." Ta fada hade da matsawa wajen mahaifiyar ta ta. Ta kama hannun rigar ta na sakala mata botiran
"Gyara sanyin jikin nan zaki Amaal.. Kinga dai abbiey din ku yace sai kun maimaita ss2-ss3 anan saboda university. Don haka doke ki zama mai shirya wa da wuri. Yanzun kin ga makaranta daya zai saka ku. Ba kamar can ba ne da makaranar ki daban. Nan yana cewa ba zakuyi karatu waje daya ba zaa fara sukar sa. Duk kuwa da su ne kecin zalin ki. Kinji ko?"
"Tohm Hayateey in shaa Allah. "
"Allah ya miki albarka. "
"Aamin Hayateey tare da ke."
"Yauwa muje naga sun fiffito su ma."
"Tohm."
Takalmi ta zura, kafafunta sanye cikin safa baka. Tana gaba mahaifiyar ta ta na biye da ita a baya sanye take ita cikin doguwar rigar leshi dinkin bubu ta rufa babban mayafi.
Suna fita harabar gidan da harararrakin haj hadiza da ruwaida suka fara cin karo. Sunata doka musu ita. Ciki harda tagomashin ta yaran su dake gefe suma sun dakko halin.
Haj hadiza tayi gaba tana jan dogan tsaki. Badan amb junaid yace lalle su tafi a ayari dukan su ba kar wanda yayi gaba yabar wani da tuni sun dade da tafiya.
"Shafaffy da mai." Ta fada hadi da waiwayawa baya ta sake bankama haj jameelah harara da amaal.
A haka suka karasa sashen Hajiya Maryam mahaifiyar su Amb. Junaid.
Tuni har wasu yan uwan sun sun zo wajen hajiyar dubada motoci dake faffake na alfarma...
___
_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_
_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*
_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥