Tabarmar Ƙashi page 13 by H U G U M A

Tabarmar Ƙashi page 13 by H U G U M A

Tabarmar Ƙashi page 13 by H U G U M A

*H U G U M A*

_*TABARMAR ƘASHI*_💔

*Arewabooks: huguma*

https://arewabooks.com/u/huguma

Page 13

           Wani Parlor din ya tarar wanda baikai wannan girma ba,duk da dama abinda ya rabasu da wannan din babbar qofar glass ne da zaka turata,sai kuma labulaye na alfarma da aka zubawa qofofin duka,saidai wannan Parlor din nashi kalar daban da wancan,don komai da aka shirya a cikinsa minty blue green ne da ratsin creamy white. Dan matsaici ne da bai cika girma sosai kamar wancan ba,amma ya tsaru yadda jiki da zuciya zasu samu hutu yadda ya kamata. Shima shuru yake babu kowa,saiya taka zuwa hannun damansa,ya yaye labulen daya sadashi da wani tsararrren corridor wanda ya qawatu da wasu gold leaf picture frames,fentinsa olive green ne saboda qarawa idanu qarfin gani,kalar kuma ta dace da wajen sosai daya qawatau da fitilu masu haske tarwai,sai flowers a maqale a kowacce corner daga jikin bango,wanda suke bada qamshi na musamman da kuma samun kyakkyawar iska fiye da iskar da na'urar bature dake kafe a wajen zata bayar.


             Qofofin dakunan bacci ne guda hudu a wajen,kowacce da dan taqi kadan daga qofar dake kusa da ita,biyu na kallon guda biyun,sai yaci gaba da takawa a nutse kamar mai nufar full length mirror din dake maqale a bangon qarshe na wajen,ya isa qofa ta qarshen dake daura da madubin daga hannun damansa,yasa hannu ya murda ya tura sannan ya shiga.


           A nutse yake qarewa dakin dake a tsaftace kallo,yana watsa idanunsa tare da laluben daga inda zai hangota.


           . Daga saman gadonta ya hangi tattausan bargonta milk color me matuqar taushi cure waje daya,ya zubawa gurin ido sosai,alamun motsin da ya gani shi yaja hankalinsa,ya daga qafa da wani irin hanzari ya isa bakin gadon,bai tsaya jiran komai ba ya sanya hannu ya yaye bargon take ta bayyana.


             Kyakkyawar yarinya ce da duka duka shekarunta ba zasu haura biyar zuwa shida ba,fara ce qal siririya sosai,gashinta me tsaho da sulbi yana daure tsakiyar kanta da wani siririn ribbon pink color,kalar riga da wandon dake jikinta kenan. Cure take waje daya,ta qanqame ilahirin jikinta kamar wadda taga wani mummunan abun tsoro,saidai yadda bakinta yake rawa kawai ya isa gaya maka ta hadu ne da mummunan zazzabi.


          Da hanzari ya haura gadon gaba daya,jikinta na rawa,lokaci daya tashin hankali da rudewa suka bayyana qarara saman fuskarsa tamkar ba ingarman namijin nan da yanzu yanzu yake shigowa cikin gidan ba,cikin takun dake cike da karsashi ba.


"Ya salam......ya salam" ya fada fuskarsa na wani irin sauyawa,tare da rungumota gaba daya zuwa jikinsa yana fadin


"Zazzabi ne a jikinki fadeela?,ina baaba rabi?" Ya fada yana lullubeta cikin jikinsa tamkar yana shirin maida ciwon jikinsa ne. Bude qofar dakin sai ya zama kamar amsar tambayarsa,kamilalliyar matar tayi sallama,wankan tarwada ce,sanye take da atamfa riga da zani,sai kakkauran mayafi data yane kanta dashi,hannunta dauke da carbi


"A'ah lafiya?,me ya sameta?" Ta fada cikin nuna tsantsar kulawa,itama fuskarta na nuna zallar alhini tana matsowa zuwa bakin gadon


"Yanzu yanzu na fita nayi sallah,na barta tare da julia tana qoqarin bata kayan bacci ta saka" baaba Rabi ta fada cikin tsantsar alhini tana qoqarin karbar fadeela daga jikinsa,saidai yaqi sakar mata ita


"Itace sabuwar nanny din da aka kawo?" Ya jefawa baaba rabin tambaya yana kallonta da idanunsa da suka kada suka canza launi,cike fal da wani irin zazzafan bacin rai


"Itace" ta amsa masa dukka hankalinta yana kan yarinyar,kafin yace komai aka buda qofar dakin aka shigo.


           Matashiyar budurwa ce 'yar qabilar yoruba,sanye da uniform irin na ma'aikatan kamar kowanne ma'aikaci dake aiki cikin gidan. Cikin mugun razana taja da baya tana sauke idanunta qasa,gabanta yayi masifar faduwa,dukka jikinta ya dauki rawa,cikin matuqar kaduwa ta sulale ta duqa a wajen


"You are welcome sir" Idanunsa fal da masifa da kuma tashin hankali yake kallonta,ya zare yarinyar daga jikinsa ya miqawa baaba rabi ita,cikin harshen turanci ya fara magana cikin masifa tamkar zai bugeta,saika dauka bai cikin hayyacinsa


"Kin fadi adadin abinda kike da buqata na kudi,nasa an biyaki amma hakan bai hanaki kiyimin sakaci da rayuwar yarinya ba?,zaki barmin ita har zazzabi irin wannan ya sauka a jikinta ba tare da kin sani ba,banga amfaninki ba,ki tattara komai naki kibar gidan nan,na sallameki" ba ita kadai ba data rasa aikin da tayi mugun saka a rai kanshi ba,hatta baaba rabi tayi mugun kaduwa da hukuncin nasa,julia itace me aiki ta goma sha daya daya kora cikin qanqanin lokaci,kwata kwata baya daukan sakaci akan yarinyar,komai qanqantarsa shi ganganci ne a wajensa,duka masu aikin basa wuce sati daya suke rasa ayyukansu,masu nisan zango ne sukeyin sati biyu.


            Yana da mugun kwarjini da haibar da bazaka iya tsaiwa roqonsa ba,don haka tana share hawaye cike da baqinciki rasa aiki me gwabi da tarin albashi me tsoka,da kuma fita daga daular wannan gidan,wanda iya cima da AC din dake karakaina a lungu da saqo na gidan kawai ta isa sanyaka ka mallaki lafiyayyar fata me sheqi,ba tare da kana amfani da mai ko sabulu ba.


            Wayarsa ya ciro a aljihunsa cikin hanzari yayi kira na wasu sakanni,sannan ya matsa da sauri ya dauke yarinyar cak daga cinyar baaba rabi ya rungumeta cikin jikinsa,ya juya cikin kamewarsa da fushi ya bayyana a tsakiyarta yana fita a dakin.


             A nutse yake takawa da ita zuwa sashensa,yana jin kamar ya maido ciwon jikinsa,tana ruqunqume dashi itama duk da zafin zazzabin jikinta,yana takawa idanunsa na sauya launi,wani abu da yafi kama da bacin rai yana motsa zuciyarsa,yana jin wata qaqqarfar tsana ta wata halitta na sake haifuwar sabuwar yabanya a zuciyarsa.


             Da hannu daya ya bude qofar bayan ya ratsa wani hadadden balcony da aka qawatashi matuqa fiye da tunani,kyakkyawan falo ne na alfarma wanda ya kerewa dukka falukan gidan,komai da komai na cikin falon,hatta da door mat dinsa kalar creamy white ne me matuqar daukan hankali da burgewa,fararen fitilu qal da suka haska falon tarwai kamar safiyar da aka tashi da tsananin hasken rana sun taka rawar gani wajen qawata falon,tako ina qyalli yake,komai fes qal kamar rai bata rayuwa a ciki,duk inda ka waiwaya sai kaga kamar zaka ga fuskarka. Ba abinda falon yake bayarwa sai Wani irin ni'imtaccen qamshi dake cakude da qamshin air conditioner din dake tsaitsaye a kusurwoyin falon yadda zata wadaceshi tako ina saboda girman da yake dashi. Tsaf ya laqume saitin kujeru biyu na alfarma,iya wanzuwarka cikin falon ya isa ya baka wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali,saidai banda taufeeq wanda babu abinda ya sauya daga abinda yakeji cikin zuciyarsa.


"Welcome sir" ma'aikatan dake aiki a sassansa mutum biyar dukka maza suka fada cikin rusunawa da kuma girmamawa,baiko amsawa kowa daga cikinsu ba,sai hannu daya daga musu alamun ya sallamesu,suka juya da daya da daya suka fice a parlor din bayan kowa ya tabbatar aikinsa ya kammala,jibril ne qarshe,ya zube files din hannunsa da komai da komai ya juya shima ya fice.


            Ta hannun damansa ya bulla wani matsakaicin hallway da aka qawatashi sosai shigen na daya sashen,ya tura qofar dake a wajen,babban bedroom ne shima da komai na cikinsa creamy white ne kamar falon,tsararrren gado dan qasar italia da yasha shimfidu da lallausan farin zanin gado saqar qasar dubai,qarasawa yayi ya kwantar da ita akai cikin tsananin tausayawa,shi da itan duka yana jinsu shi da ita tamkar marayan da mahaifinsa ya rasu kafin haihuwarsa,mahaifiyarsa kuma ta rasu ta barshi yayin haihuwarsa,yakanji duniyarsu tayi musu fadi kamar babu wani me jibantar lamarinsu,bawai don sun rasa masoyan dake nuna kulawa da soyayya mara iyaka a kansu shi da ita ba,a'ah.....akwai wani boyayyen abu,wani internal love da dukka su biyun suke buqata,wanda suka rasashi,kuma shine sila sannan musabbabiyyar jin wannan kadaicin dake lasar zukatansu ta can ciki.


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post