Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 10

Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 10

 

Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 10

_BM_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE:10_


_BM vip arewabook👇: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___


   _ARDO KANDEMI INT.. AIRPORT_


   *Ardo* kandemi international airport ne dake birnin Nukaa a kasar najeriya. Yana daya daya cikin manyan airports din da ake ji dasu a fadin najeriya da ketare..


Airport ne daya ci sunan marigayi me garin kandemi wato Ardo kandemi wanda daga yankinsa ne gwamnati ta tsakura ta saka sunan birnin Nukaa. Nukaa state kenan..


  Jirgi ne samfurin private jet wato ba mallakin gwamnati bane ko na kasa,  jirgi ne wanda masu hannu da shuni ke mallakar su, ko manyan siyasa, Yan kasuwa, Manyan malamai da ake damawa dasu. Da ma masu babban matsayi na jam'iyu ta kasa da ketare


Sosai mutane sukayi dafifi wajen son ganin sa. Masu gadin da masu tsaro sun sha mamaki kwarai matuka na ganin mutanen duk kuwa da baa sanar da dawowar sa ba. Haka zalika ko a ya uwa ba kowane yasan da waiwayowar tasa gidah ban amman masoyan sa sun cika airport din don tarbar sa..


Face mask yaja ya lullube hancin sa har wajen idanun sa, gaba da bayan sa kuwa dakaru ne dake zagaye da shi suna kare shi.


Kafafuwan sa ne lokaci daya suka shiga yi masa rawa, Gabansa ya tsananta bugawa. Kansa ma ya shiga masa ciwon. Jikinsa take ya hau rawa, Wani abu ya fara masa yawo kaman tafiyar kiyashi a jikin sa.


Jikin sa ne ya tsananta har ya kasa wani takun. Masu tsaron sa suka yi kansa


"Ranka ya dade..."


"Sir"


"Yallabai"


"Alhaji"


"Boss."


Haka dai sukai ta kiran sunan sa. Tuni ya yanke jiki ya fadi akan wani me 

tsaron sa. Suka rike da sauri duka suna kiran kawun sa dake bayan su yana cike wasu takardu.


Da sauri ya karaso wajen shima yana gyaran zaman gilashin idanun sa. Cike da tsantsar firgici ya shiga taba jikin dan uwan na sa.


"Karami... Karami? Karami?"


Girgiza shi ya shiga yi da iyakar karfin sa amman ba wani canji. 


"Ku temaka mun."


A tare suka tallabo shi sosai suka yi waje dashi ta wata kofa da take kebantacciya ce ba kowane ya santa ba sai kana da babban mukami ko kai wani ne a kasar ... Ko kuma idan emergency ya faru na gaggawa to ana amfani da ita...


Kai tsaye suka yi wajen mota da shi suka saka shi acikin wata motar yan kwana kwana (ambulance). Dandazon mutane har sun fara taruwa amman ina tuni suka ja motocin su suka fita daga cikin airport din.


Duk na'urar air conditioner din dake tirara motar da sanyi.. Hakan be hana jikin Alhaji Muhammad yin gumi ba. Wani irin gumi ne ke tsattsaga daga jikinsa mai tsananin kuna da yauki.


"Sir kaga ruwan da yake fita daga jikin sa."


Wani dan sanda ya fada yana mai nunawa Alhaji Adamu jikin Alhaji Muhammad.


Kasa magana Alhaji Adamu yayi .ya janyo wayar sa dakyar yana duba lokaci. Gefe daya yana duban yadda ma'aikatan lefiyan kwana kwanan ke bashi temakon gaggawa


Gashi ba tare suka taho gaba daya ba da sauran wanda suka tafin. 


Wani abu ya taho ya tokare masa a wuya. WhatsApp ya shiga. Da saqon amb junaid ya fara cin karo yana masa ya jikin mahaifin na su?


Nan da nan ya sanar masa ai sun dawo ma ga abunda ya faru. Alokacin amb junaid ya mike daga zaunen da yake don dama yana online wayar sa na hannun sa..


"Meya faru?" Cewar Hajiya Maryam


"Ba bakomai Hajiya Ina zuwa."


Futa yayi da saurin sa har yana cin tuntube yayi kofar gidan tsabar tashin hankali kafar sa daya da warin takalmi daya baby.


Ma'aikatan na ganin sa suka tashi


"Yallabai lafiya?"


"Ina sarkin mota?"


"Ya fita da su Hajiyan Makama"


"Ba wani direba a kasa?"


"An tafi dakko tara makaranta. Su hambali sunje cikin gari."


Yaja dogon tsaki yana dartse idanun sa. 


Yana juyawa ya hangi su Alhaji jalaludden zasu shiga motar su, Dama yaga sun futo daga parlorn dazu ba dadewa, da sauri ya karasa wajen su,


"Wajen su baba zaku?"


Alhaji jalaludden bai amsa shi ba. Sai Alhaji Nuraddeen.


"Eh ... Shigo muje."


Ya bude gidan gaba ya zauna. Alhaji jalaludden na owners coner sai Alhaji Nuraddeen a gefen sa direban Alhaji jalaludden na tukawa a gaba, sai amb junaid a kujerar gefe,


"Suna wani asibiti? Yaya?"


"Bansanj ba Junaid .... Kawu yace kai ya fara fadawa. Kafin ya mana forwarding."


"Bana online ne sai da na hau, Amma...Ai"


Bai karasa fada ba Alhaji jalaludden dake jinsu ya ja dogon tsaki, ya dubi Alhaji Nuraddeen cike da bacin rai yace,


"Bansan meyasa zaka ce mu taho da mutumin nan ba. Ko dai yayi shiru ko na futa na bar masa motar."


Amb Junaid ya juya ya kalle shi. Direban ma dik sai jikin sa yayi sanyi kansa a akan titi.


"Menene haka jalaludden?"


"No Yaya ai gaskia ne....Duk wannan shekarun sai daya tabbatar ya gama kitsa komai sannan zai waiwayo kandemi? Wanene yasa jikin baba a wannan matsanancin ciwon idan ba shi ba."


"Subhanallahi yaya jajaludden me kake fada haka? Wallahi wallahi bansan me kake nufi ba. Menayi? Meya faru? Wane ciwo na saka baba? Yaya Nuraddeen ka wayar dani me Yaya jalaludden yake nufi?"


Alhaji Nuraddeen ya girgiza kai kawai yama rasa me zai ce..


"Kuyi hakuri dan Allah. Hakan duk bata taso ba. Yanzu dai duka zukatan mu na cikin damuwar ciwon mahaifin mu. Shine agaban mu. Koma menene sai ya biyo bayan samuwar lafiyar mahaifin mu.."


Amb Junaid daya juya yana kallon su sai ya mayar da jikin sa ya koma kallon titi kawai.


Tarun damuwar dake cinsa ta sake masa tasiri. Baki daya maganganun Yayan su jalaludden ce ke masa yawo a kwanyar kansa. 


Dai dai lokacin da saqo ya shigo wayar sa da unknown number. Tamkar ba zai bude ba sai kuma ya bude sakon daya kunshi,


"Barka da dawowa zuri'ar kandemi. Ambasada mai murabus. Na haneka da kada ka soma sanya kafa ka dawo amman kayi fatali da magana ka dawo. To abunda ya faru yau wasa ne farin girki. Sannu da zuwa ne ka fara cin karo da shi kafin asalin babban wasan ya fara.... Ka tattara iyalin ka ku koma inda kuka fito. Idan ba haka ba......"


Runtse idanun sa yayi da sauri . Dai dai lokacin da suka shiga babban asibitin da ke na kudi kuma shine wanda yake na babban likitan estate din..


Nan motar yan kwana kwanan ta kunna kai ciki itama . 


Ma'aikatan kafiyan suka kai musu temako kan wani gado suka dora shi da sauri sukayi ciki da shi da gudu...


Suka furfuto daga cikin motar bayan direba ya faka motar awajen adana motoci da ke farfajiyar asibitin. 


Dukkanin su wayoyin su na hannun su. Ya dube su na dan wani lokaci ya kauda kansa da sauri don zuciyar sa ta fara kiyasta masa wani zato na daban a kan su. Don haka da sauri ya fara kamo addu'oi yana yi kasan makoshi... Don bayasan kyautata zato. Don zato zunubi ne ko da ya zamanto gaskiya. 


Cikin asibitin suka shiga da sauri kowanne hankalin sa a tashe. Sukayi bangaren emergency unit da akayi da shi.....


_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


 _INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k  _MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post