Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 11

Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 11

Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 11

_BM_

_NA:_

_NANA HAFSATU_

_PAGE:11_

_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._

___

*Dakin* gaggawa na marasa lafiya magashiyan aka nufa da shi. Manyan likitocin suka shiga ciki suna bashi temako.


Ya yin da su Amb junaid ke daga wajen kofar dakin gaggawar a tsaitsaye. Kawu Adamu yanata kaikawo daga kofar dakin zuwa karshen corridor.


Kana ganin fuskokin su kasan suna cikin madaukakiyar damuwa marar misaltuwa. 


Ba a wani dau tsawon lokaci ba likitocin su biyu sika fito daga cikin dakin. Daya ya zare safar hannun sa ya jefar daya kuma ya nufi wajen wani famfo yana wanke hannun sa.


"Barkan ku da yammaci." Daya daga ya fada..


"Barka kadai."


"Barkan mu.,"


"Sannu ku da kokari doctor."


Suka shiga amsa masa daya bayan daya..


"Dr gwanzam zai muku bayani game da komai. Muna fatan Allah yabashi lafiya ya tashi kafadunsa cikin gaggawa ya kuma sa kankarar zunubai ce Amin. zan je rounds ne."


"Aamin Aameen Dr. Faysal."


Ya karasa fada yana mai basu hannu daya bayan daya suka gaisa sannan ya tafi.


"Makusancin Alhaji nake son magana da shi." Dr gwanzam ya fada.


"Ai duka nan likita, kowanne daga cikin mu makusancin sa ne. Wadannan 'yayan sa ne.. Sannan ni dan uwa ne kuma makusanci matuka agare shi." 


Kawu Adamu ya fada cike da damuwa marar misaltuwa.


"Alright...Ku zo muje ko?" Dr gwanzam ya fada yayi gaba suna biye dashi ta baya.


Wani daki ya shiga suka bi bayan sa. Dauke yake da kujeru da kayan kallo gefedaya kuma da drwer ta cika fal da littafai a jajjere. 


Sai wasu hotuna dake dauke a kusuruwoyin dakin.. Hotunan sikelaton ne dana hanjin ciki. Sai wani dake nuni da sassan jikin dan Adam da wasu rubutu a jere da manyan baki


"Bismillah ku zazzauna."


Ya nufi kujerar sa ya zauna. Suma suka zazzauna a kujerun gefen sa.


"Likita Allah ya saka da alkhairi..."


"Aamin... Allah yabashi lafiya yasa kaffarane."


"Aameen"

Suka hada baki wajen amsa shi.


"Ai kafin zuwan ku prof (Babban likitan mai asibitin) ya sanar mana komai."


"Allah sarki.... Yana can Ashe bai dawo ba."


"Ya kusa in shaa ALLAHU."


"Ma shaa Allah.. Allah ya temaka Amin"


"Aamin Aamen.."


"Allah ya biyaku da irin dawainiya da kokarin da kuke ga marasa lafiya." Cewar amb junaid.


"Allahumma Aameen..mahaifin ka ne amman ko kamar ta baci?" Dr gwanzam ya tambaye shi


"Mahaifin mu ne." Ya amsa shi yana murmushi.


Alhaji jalaludden ya daga kai ya masa wani kallo yana yamutsa fuska. Cikin hasalewa yace,


"Likita muna son sanin halin da mahaifin mu yake ciki...."


"Ko zan iya sanin matsayin ku awajen sa saboda magana ce mai matukar muhumman ci. Sannan zatafi dacewa idan da na kusa da shi mukai."


"Baka che Dr. Nogan ya fada muku ba?"


"Eh ya gaya mana cewar vvip patients zasu zo. Tunda mu ba mu wani dade a asibitin nan da fara aikin mu ba kusan ni daga baya na dawo kasar ma a Paris nake. Yace mu baku duk wata kulawa data dache.. already akwai history na ciwon ma mun duba sosai munyi nazari akai.  To Amma dai ko wani fanni abunda nakeson fada yana da sirri da kuma amana. Don haka asibiti na da tilashen lullube sirrin cutukan marasa lafiya da ke karkashin sa inde ba sanin hakan ne ya zama tilashe ba gaskia baa futar wa wanin wani yanayin ciwon sa..shi yasa muke son sanin ku din su wannene ya yan uwantakat taku ta ke? Tunda akwai 'yayan kanne ai suma na jini ne, akwai kuma 'ya'yan da aka haifa na ciki.. Kuyi hakuri da ni"


Alhaji jalaludden yaja dogon tsaki yana cije baki. Duk sukai shiru. Dr gwanzam ya sake cewa,


"Ku gafarce ni dan Allah yanayin aikin ne yazo da haka."


Alhaji Adamu ya sauke katuwar bahaguwar zuciya ya nisaa ainun kafin yace,


"Mun fada muku na lura kaman baku amintaa ba...."


"Ba haka bane ranka ya dade... Kawai munason tabbatarwa ne..."


"Wadannan duka su ukun 'yayan sa ne na cikin sa. Uwar su daya uban su daya, shine mahaifin su... Wannan shine na fari awajen sa Alhaji Nuraddeen. Wannan ma dan sane jalaludden, wannan shine karamin dan sa gaba daya. Ambasada Junaid.. Nasan zaka iya sanin su duka ba bakin fuska bane."


"Nasan wannan dai minister  ne..wannan ma na san ya rike jakada a akasashen waje. Wannan ne dai ne dai bansani ba." Dr gwanzam ya fada yana dan murmusa fuska..


"Kanne na ne duka...ni ne babban su kamar yadda Kawu ya fada..."


"Ma shaa ALLAHU.... To a zahirin gaskia Alhaji Muhammad idan muka che ga abubuwan da sike damunsa gaba daya min san su gaskia munyi karya. "


"Doctor wata babbar cutar ce dashi?"


"A'a ka kwantar da hankalin ka Kawu.... Ina nufin abubuwan dake faruwa dashi na rashin lafiya suna da yawa bazaar iya cewa ai abu daya be ko biyuu sike damun sa ba. Sannan kada kusa damuwar hakan a ranku. Shi ciwo dama lokaci daya yake shiga. Fitar sa ce ke daukar tsawon lokaci."


"Haka zancen ka yake."


"Tabbas hakane."


"Yauwa! Dan Allah ku kwantar da hankulan ku"


"To ai likita dole ne mu saka tsoro da farbaba azukatan mu. musanman da kache abubuwan da ke damun sa da yawa.,"


"Masana suka ce, Allah bai sauki kowane cuta ba fyace sai da  maganinta ko?"


"Hakane"


"Wannan gaskia ne"


"Sannan Allah baya dorawa dan Adam abunda yafu karfin sa."


"Tabbas."


"To sai mu cigaba da addua. Mu kuma dora da magunguna da sauran bincike..in shaa ALLAHU komai yazo karshe. Zai samu waraka da yardar Allah. Cuta ai kankarar zunubai ce. "


"Allahu ya sa likita."


"In shaa ALLAHU."


"Yauwa.... Magana ta farko dai nasan kunsani kuuma.. Alhaji yana dauke da cutar ciwon zuciya da hawan jini.. sai kuma bayan nann nasa da ke masa physiotherapy na lumbar sacral spine..shima da sauki Alhamdulillah. Ba kuma shi da calcium yayi kasa sosai. Sai kansa da mukai CT scan akwai jini daga gefe da zamu cire. Kusan wannan sune abubuwan da muka Gano a bincikemu na yau. Kuma aikin da zamuyi na zuke jinin anjima kadan zamiyi da ya farfado don mun masa allurar bacci mai karfi..sai kuma in shaa ALLAHU daga nan zamu shiga wadansu nazarin saboda yadda jikin nasa yake mana nuni akwai wadansu cututtukan a akasa wala Allah sai an kammala duka tasa tasan zaa karasa gano su.. sai Wani Kaho a wajen zuciyar sa... Aina akai masa? Sannan wacce iriyar lalura ya  gamu da ita da har sai da aka masa kaho na hausa.?"


"To Alhamdulillah likita duk munji bayanan ka Allah ya saka da alkhairi Allah kuma yasa karshen warakar ne yazo.  Kaho kuma duka kusan agaban yaran sa ne da wadansu jikoki daga ciki domin yayi gamu ne da wani matsanancin ciwon kirji. Ya sha magunguna dan har India mikaje ba saukin, Astagfirullah shine bayan mun dawo kasa Nigeria manya suka bada shawara akayi masa kaho. Allah da kkon sa kuma bayan anyin sai waraka tazo masa ciwon kirji ya lafa."


Likitan ya kada kai alamat gamsuwa,


"To Allah yasa karshen wahalar kenan ."


"Allahumma Aameen.."


"Toh zamu lura da nazartar jikin nasa dama duk abubuwan da sika dache sai ayi masa."


"Yayi! Allah ya saka da alkhairi lkkita."


"Allahumma Ameen."


"Yanzu wani acikin ku zai saka mana hannu a wadannan takardun. Muna san a lamunce mana me mu cigaba da tasatasan da aikin da za'ai da ma sauran mataki da zamu dauka akan lalurorin nasa. "


Alhaji Adamu ya juya yana kallen su Amb junaid. Alhaji jalaludden ya girgiza kai,


"A kira su Aisha suzo tukunna."


"Tabbas munsamman da ita ma likita ce. Sannan suma 'yayan sa ne suna da hakki akan komai na sa.."


"Ba damuwa ku kira su...." 


Cikin kankanin lokaci kuwa bayan an kira su a waya sai gasu sun iso,


Dr Aisha (gwaggo indo)

Professor Abdullahi (ballsj na Istanbul )

Attorney general of the federation. (Gwaggon court)


Bayan sun gaysa harda likitan ne. Dr Aisha suka sake gaisawa sosai ashe sun taba haduwa a wani taro da dadewa..


Yamasu bayani sosai. Musanmam ita da itama tanada ilimin bangaren likitanci amma ta wani fannin daban. 


Sun yi matukar mamaki da ma da mahaifin na su da tawagar su basu dawo ba. Sannan su junaidu ma kuma an duba basanan, Ashe abunda ya faru kenan.. Gwaggon court da gwaggo indo har kukayi sukayi kan jikin mahaifin na su...Dakyar aka lallashe su sukayi shiru,


Sun tattauna tsawon lokaci gaba dayan su. Har suka tashi gaba daya suka shiga wajen mahaifin nasu yana kwance yana bacci. Sika masa adduoin fatan samun nasara.


Kafin daga bisani su cike takardun sika saka hannu.  Sai tsakiyar dare suka bar asibitin.. Alhaji Adamu ne zai yi jinyar sa.


    Washegari da safe kuwa tun asubah wasu daga cikin yan uwa sika fara dafifin zuwa dubiya duk kuwa da baa fada ba anyi abun alullube amman sai da wasu sika ji. 


Dukkanin yaran sa da jikokin sa haka sika rika turereniya a aisibiyin nan suna dubiya.


Tsawon kwanaki uku kenan amman Alhaji Muhammd bai farfado ba. Since ya shiga coma wai. Baya iya bude idanun sa. Numfashin sa ya tsaya iya karshen ciki kawai.


Daga karshe dai a kwana na biyar babban liktan ya bada shawara kan mayar da Alhajin cikin kandemi estate. Ya kuma saka lokktici har uku da zasu dinga dawainiya dashi suna bashi kulawa har ranar da Allah zai tashe shi. 


A kuma kwanakin ne su Amaal sika fara zuwa makarajyar da aka sanya su. Idan sun dawo daga bokon kuma akwai islamiya ta hadda dake cikin estate din malamai masu ilimi da nagarta ke koyar da su....


 


_

_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


 _INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k  _MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post