Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 14

Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 14

Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 14

 _BM_

_NA:_

_NANA HAFSATU_

_PAGE: 14_

_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._

___

  Bakin sa dauke da sallama ya shiga sashen.  Duk suna zazzau ne a babban sashen parlorn. 

Ya yin da likitan ke a tsaye, kafadar sa rike da jakar sa baka da wasu littafai aciki da laptop dake zip din jakar abude yake ana hango kayan ta na ciki.


Likitan yana ganin sa ya bashi hannu suka gaysa. Kafin daga bisani Amb junaid ya babbasu hannu suka gaysa ya kuma durkusa har akasa ya gayshe da su cikin girmamawa.


Sallamar sa kadai alhaji jalaluddeen ya amsa, itama a kasan mak’oshi bata fito da sauti sosai ba.


Amb junaid sam bayajin dadin hakan da yayan nasa yake masa ya rasa dalilin da ya saka babbar tsana me tsanani tsakanin su da wasu daga cikin yayyun nasa.


Ya nemi waje ya zauna daga can wata kujera dake gefe wadda ke fuskantar dakin da mahaifin na su ke acikin sa.


Likitan ya shiga dakin da aka kwantar da Alhaji Muhammd. Ya dan jima aciki kafin ya fito yana mai zare takunkumi/face mask daya saka,


"Zaku iya shiga.... Amma banda hayaniya"


"Doctor to ya jikin na sa?"


"To Alhamdulillah zamu ce... Tunda shi sauki ai na Allah ne... Ciwo lokaci daya yake shiga, Fitar sa kume sai ta jima"


"To Allah ya tashi kafadun sa.."


"Aamin doctor."


Amb junaid sai daya bari dukkanin su sun kammala tanbayar likitan. Har yayi kofar fita zai futa. Yace da shi,


"Yanzu menene cigaba?"


"Cigaba?" Likitan ya tambaye shi yana binsa da kallon karin bayani


"Ina nufin ba wani cigaba a bangaren farfadowa haka ko da motsinne na wani gabba na jikin sa?"


Likitan ya girgiza kai yana mai sauke nannauyar ajiyar zuciya,


"Muna kokari iyakar iyawar mu ambassador. Za kuma mu cigaba da dagewa Allah ya amince mana"


"Aamin. Godia muke."


Ya bashi hannu sukayi musabaha ya fuce shi kuma ya nufi kofar dakin mahaifin nasa zai murda kenan Alhaji jalaludden har yana gugar sa yayi hanzarin budewa ya shiga saura sukabi bayan sa..


"Ka shigo mana junaidu." Cewar Kawu Adamu da ya rike handle din kofar bai rufe ba. 


Amb Junaid ya shiga ciki yana mai yin sallama a hankali saboda likita yace kar ayi magana da karfi.


Duk sunyiwa gadon da mahaifin na su yake kai rumfa.. Alhaji jalaludden ya rankwafa kan mahaifin nasa yana gyara masa wuyar rigar sa daya harda waje daya..


Amb jumaid ya tsaya daga can gege yana hango fuskar mahaifin tasa da tayi fayau duk ya rame. 


Wasu hawaye suka zurara daga idanun sa masu dumi. Ya tuno tarin shekarun da yayi wanda basu hadu da mahaifin nasa ba. Alokacin daya dawo don kasancewa da shi sai ga abunda ya faru kuma na lalura. 


Daya bayan daya kowanne dayaje gaban gadon ya ganshi zai fita. Tunda yana kwance ne kaman marar rai. Numfashin nasa can can kasan ciki yake yin sa. Zama ka dauka ba rayayye bane... Wata na'ura dake gefen gadon ce ke nuna numfashin nasa yana tafiya ahankali.. Haka zalika jijiyoyin a hankali sike harbawa. Yayinda idanuwan sa ke a rufe ruf. Tamkar wanda ya shiga coma. Don bai farfado ba tun ranar da suka dawo ko abinci ma ta drip aka saka masa. 


Dakyar ya iya jan kafafun sa ya isa ga bakin gadon alokacin da suka fita. Hawayen da yake ta faman rikesu ne suka gaza hakuri suka fara kwaranya daga manyan idanuwan sa tubarkallah. Tuni kansa ya fara cuwo ya yinda gabansa ke bugawa sosai.. tamkar wani dan karamun yaro haka ya zube agaban gadon.


Gangar jikinnsa a jikin gadon yayinda kansa ke kan gadon ya kifar da shi yana hawaye mara sauti. 


Alhaji jalaludden dake daga bakin kofa ta waje a tsaye ya girgiza kai kawai ya juya yayi hanyar fita..


Wayar sache tayi karar agajin dauka. Bai dauka din ba har ta katse. Yayi hanyar motar sa ya shiga baya bayan direba ya bude masa ya zauna.


Wayar tasa ta sake yin ringing. Private number ce ta ke kiran sa. Yaja tsaki ya mayar ta cikin aljihu. Aka cigaba da kira ba kakkautawa


"Ranka ya dade Ina zamu je?"


"Sashen Hajiya (mahaifiyar su)"


Direban yaja motar daga nan zuwa bangaren mahaifiyar ta su kasancewar gidan babban estate ne daya fi wani kauyen a girma. Gefe daya kuma ya kawaatu fiye da kalamai.


"Yallabai ko na amsa ne?" Direban ya fada yana mai nuni masa da wayar bayan ya bude masa murfin motar ya sauka.


"Ba damwua zan dauka. number ce private ba suna ba number."


Daukar wayar yayi cike da kosawa ya kara a kunnen sa,


"Wa'alykm Salam.... Speak."


Shiru yayi yana sauraron maganganun da ake gaya masa ta wayar. Yaja tsaki yana girgiza kansa, cike da kosawa yace


"Wannan shine warning na karshe... Banason private number. Sannan turo account details yanzu ta wannan number.  What? Yanzu? "


Kit ya katse kiran. Ya zare wayar daga kunnen sa yana mai bin ta da kallo. 


Da sauri ya mayar da ita ya zura a aljihun sa. Kai tsaye ya koma mota ya shiga direba ya ja shi,


"Sir sai Ina?"


"Maidani bangaren daka dakko ni."


Direban ya kai shi ya sauke shi, da sauri ya shige ciki. 


Hankalin sa ya matukar tashi a lokacin daya gansu gaba daya a tsaye sun tsattsaya akan mahaifin na su. Yayinda wasu likioci biyu suke bashi temakon gaggawa


Wani irin bakin jini ne ke b'ulb'ulowa daga hancin sa da bakin sa. Harda guda guda. 


Alhaji jalaludden ya sauke ganin sa akan Amb junaidu dake tsaye wayar sa hannu ya zarota a aljihu yana duban screen din..


"Meya faru dashi haka?" Jalaludden ya tambaya yana daga tsaye a bakin kofa


"Wallahi ambassador ne yake gaya mana lokaci daya jini yana zubowa daga hancin sa. Badan yagani ba ma da abin ya zama worst tunda rufe kofar za'ai"


Idanun jalaludden ya kada kai jajir lalle ta tabbata junaidu kanin su so yake ya kashe mahaifin su.


Shi kuma a lokacin Amb junaid wayar sa daya zaro message ne ya shjgo masa da akayi amsa da rubutun ajami na hausa,


"Yanzu wasan zai fara......Barka da dawowa cikin zuriyar kandemi...."


Alhaji jalaludden ya kaj makura tamkar matashin zaki haka ya zabura ya rarumo kwalar rigar ambassador Junaid ya cacume shi yana jijjiga shi,


"Ba zaka ga bayan Alhaji ba... Azzalumi sai dai muga bayan ka......."


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Yaya kasan me kake cewa kuwa?" Amb Junaid ya fada cikin tsantsar tashin hankali mai tattare da kidimewa. 


Yan uwan suka tashi baki daya sukayi kansu suna kokarin raba tsakanin su.....       -_-_-_-_-_-_-_-__ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


 _INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k  _MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post