Nihaad page 13 by Khaleesat Haiydar complete

Nihaad page 13 by Khaleesat Haiydar complete

Nihaad page 13 by Khaleesat Haiydar complete

 💖💖 *NIHAAD*💖💖

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

13.....

Zaunawa Nihad tayi ta dau wayarta ta bude, nan ta ga miss calls da ya wuce misali, ta shiga call logs ta ga kiran Aliyu guda daya wanda yayi mata tun da safe, bata san sanda ta sauke wani ajiyar xuciya ba, so he did call her, wani Murmushi tayi, tayi dialing number sae da ya kusa katsewa ya daga, tayi kasa da murya tayi masa sallama ya amsa, jin yayi shiru a hankali tace "Can you hear me?" Yace "Yea ina ji" tace "You called da safe, bani da lafiya shi yasa ban samu dagawa ba" Yace "Baki da lafiya? Me ya sameki?" Ta langwabar da murya tace "Na tashi da xaxxabi ne" Yace "Subhanallah, how are u feeling now?" Tace "Da sauki shi yasa har na samu na kiraka" Yace "Since when were u sick?" Tace "2 days ago" Ya dan yi shiru, sai kuma yace "I am sorry, Allah Ubangiji ya baki lafiya" Ta lumshe ido tace "Ameen" Yace "Hope kina iya cin abinci?" Tace "Ehh daxu na samu na ci" Yace "Get well soon dear" Ta dan yi shiru sai kuma tace "Kayi hakuri da abinda ya faru few days back" Yace "Nihad" Tace "Na'am" yace "Daga ina akayi employing driver din nan?" Tace "Wllh ban sani ba i just saw him over night a gidan" Yace "Ya sunansa?" Ta gyara xama tace "Halilu" Yace "Good, yana gidan har yanxu ko?" Tace "Yana nan wllh, rashin mutunci kuwa sae abinda yayi gaba, i have just decided in dinga hawa adaidaita from henceforth idan xan je makaranta" yace "You don't worry, i will bring an end to everything" tayi wani Murmushi tace "Trust u dear" Yace "A gidan yake permanently ko yana xuwa ya tafi ne?" Tace "Aa a nan yake permanently ba inda yake xuwa" Yace "Ohk, gobe xan shigo kano in sha Allah" tace "Toh Allah ya kai mu" Yace "Ameen, i will call u back later" Tana Murmushi tace "Alright dear" daga haka ya katse wayar ta lumshe ido ta bude cike da farin ciki, at last they will bring an end to this forsaken driver, tasan tun da har ya shiga trap din Aliyu kuma ya shiga uku. Nihal na ta xaune parlor a dining area har kusan karfe tara na dare, she her self don't even know what exactly she is sitting down there for, har Umma sai da tayi mata magana ta tafi ta kwanta ita da xata yi tafiya gobe, amma bata bar wajen ba, Farooq ya shigo parlon ganin ita kadai yace "Me kike yi a nan?" Ta kirkiri murmushi tace "Ba komai kawai ina duba waya ne" Yace "Ohk, xo ki amshi sako ki ba Aminu" Tace "Toh" Mikewa tayi ta bi bayansa har xuwa bedroom dinsa ya dauko wani takalminsa ya mika mata yace "ki kai masa" Ta amsa tace "Toh" Yace "Gobe da yaushe xa ki tafi?" Tace "Da safe in sha Allah" Yace "Ohk" Juyawa tayi ta bar wajen, tana fitowa compound ta tafi bakin gate inda Aminu yake, Bata ga Aminu a wajen ba sai khalil, yana ganinta yace "Barka da yamma Hajiya" Ta gyada kai kawai tace "Ina Aminu?" Yace "Ya ɗan fita xai dawo yanxu" Tace "Ohk, ba nisa yayi ba?" Yace "Ehh ban san ko yyi nisa ba" Ta koma gefe ta tsaya tace "Ok i will wait" shi dai Khalil bai ce komai ba, but from all indication he was uncomfortable with her by his side, bayan kusan minti daya tayi breaking silent din tace "Daxu na maka tambaya baka ce min komai ba" ya ki kallonta yace "Ohh, yi hakuri Hajiya wani tambaya kenan?" Tace "Kawai cewa nayi, xan iya sanin ko kai waye?" Yayi shiru na few seconds, sai kuma yace "Ohk amma ina son ya kasance tsakanina da ke, don ba kowa nake ba labarina ba" Nihal tace "In sha Allah nayi alkawarin rike maka sirrin ka" Murmushi yayi ya gyara xama yace "Kinyi alkawari har yar uwarki baxa ki gaya ma" Nihal tace "Nayi alkawari" Yayi kasa da murya yace "Kamar yanda na sanar maki a baya, ni sunana Ibrahim, amma a kan kirani da Khalil, ni haifaffen garin getso ne...." Ta katse sa tace "Garinsu Malam Habibu?" Yace "Ehh, garinmu daya, har kuma yanxu iyayena na garin duk da baabata yar Nijar ce, don ta kan daukeni da kannena mu je Nijar a shekarun baya" Nihal dai tayi shiru bata ce komai ba tana ta kallonsa, ya sosa kansa yace "Nayi karatun primary, daga bisanni na daura da na sakandari inda na dakata a aji na uku ban ci gaba ba har yau, Baabata ta saka ni gareji a wancan lkcn, amma Allah bai yi xan maida hankali in koyi gyaran motar ba, kawai na koma aikin plumbing tare da wani d'an kanin babana a garin, sai dai ban dau lkci ina aikin plumber ba kasancewar na iya karatu da rubutu dai dai gwargwado ya sa wani a garin namu me suna Alhaji Mu'azu ya ajiyeni shagon chemist dinsa ina jire masa shagon, na kuma fi shekara takwas ina xama a shagon har daga bisanni Allah yayi masa rasuwa, da farko na samu wani aikin wanki da guga a gidan wani commissioner nan cikin garin kano, wani yaron me chemist din yayi min hanyar aiki a gidan, to yarinyar gidan ta kan xauna tare da ni mu yi hira, idan xata yi fita ba me nisa ba ni take sa in rakata, duk wani aike nata ni ke xuwa, kuma duk abinda aka girka a gidan da kanta take debo min ta kawo min, tana da kirki ainun, kuma baxan ta6a mance alkhairinta gareni ba, ita ta karfafa min gwiwa muke turanci tare, wanda banyi dai dai ba ta gyara min, bata kiran sunana kai tsaye sae dai ta ce min Kay... Wannan kusancin namu ya sa mahaifiyarta warce 'yar daya daga kasashen larabawa ce ta tilasta mai gidan sai da ya sallameni, a nata tunanin soyayya muke da yarinyarta, wanda kuma ba haka bane, sunan yarinyar Nadeeyah... da ita muka hadu a Supermarket daxu..." Nihal dae kallonsa take ko kiftawa babu, ya shafa kansa yace "Yauwa abinda na mance ban gaya maki ba shine ina da iyali da yaro daya wanda Allah yayi ma rasuwa ko wata biyu ba ayi ba yanxu, kuma shekarunsa biyar a duniya ya rasu" Nihal ta buda ido sosai tana kallonsa with shock, ya sauke kansa daga kallonta, he was looking sad, a hankali tace "Hasbunallah, Allah ya gafarta masa" Yace "Ameen, sunan matata Jiddah, wannan dalilin ya sa Nadeeyah kan kirani da Kay... Wani lkcn kuma ta kirani da KJay, har garinmu na kai ta wajen matata Jiddah" Nihal dai bata ce komai ba, Khalil yace "Bayan kusan sati uku da sallamata da aka yi daga gidansu Nadeeyah, shine Habibu yayi min hanyar wannan aikin a nan gidan, kin ji takaitaccen tarihi na...." Ta daga kai ta kallesa, kallonta yyi jin bata ce komai ba, a hankali tace "Allah ya taimake mu baki daya" Yace "Ameen" Aminu ne ya shigo compound din rike da leda, yana ganinta da farko sae da gabansa ya fadi don a xatonsa Nihad ce, sae ya ga ba ita bace, Aminu ya washe baki yace "Barka da dare Hajjaju" yana fadin hakan ya shige dakinsa da ledan hannunsa, Khalil yace "Karfe nawa xa kiyi tafiyar gobe?" Tace "Da safe in sha Allah" Yace "Ohk, ke kadai ce ai ko?" Ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Aa yawanci tare da Nihad muke tafiya, idan sun ajiyeni sai su juya" Yace "Ohk" ajiye takalmin hannunta tayi tace "Idan Aminu ya fito ka basa inji ya Farooq" Yace "To" Tace "Sai da safe" Yace "Allah ya tashe mu lfya" Juyawa tayi ta nufi cikin gidan ya bi ta da ido letting out a Sigh. Washegari da safe Khalil ya fito ta dalilin aika Aminu da Abba yayi ya kirasa, A balcony ya tadda Abba ya gaishesa da ladabi Abba yace "Xaka ajiye Nihal a Zaria, tare xa su tafi da yar uwarta sai ku dawo tare" Khalil ya sunkuyar da kai yace "Na gane... Amma sai dai na tashi yau bana jin dadi ranka shi dade" Abba yace "Me ke damunka?" Khalil yace "Ina jin ko malaria" Abba yace "Ya salam, Allah ya sauwake, baka da net ne?" Khalil ya girgiza kai yace "Aa bani da" Abba yace "Toh anjima xan baka kudi kaje ka siya" Khalil yace "Toh nagode Abba" Abba yace "Madallah, Amma ko kai da Saminu ne ku je asibiti a duba ka yanxu" Khalil yace "Toh in sha Allah" Abba yace "Kafin ku tafi ka sanar da ni" Yace "Toh nagode" Abba yace "Ba damuwa tunda farooq na nan sai yaje ya ajiyeta, kaje kawai" Khalil ya sakema Abba godiya sannan ya bar wajen, da Nihal kadai ce xai kai ta, but kasancewa tare da Nihad ne shi yasa ya gwammace yace bashi da lafiya, dalilin da yasa ma ya tambayu Nihal jiya kenan ta sanar masa tare da Nihad ne, tun jiyan kuma yayi deciding he won't be going shi yasa ya tashi da wannan plan din, he just can't withstand driving that far with Nihad in the car... Abba na shiga parlor ya ga Nihal har ta fito da jakunkunan kayanta, yace "Nihal ki jira in yi magana da Farooq ya kai ki, driver yace baya jin dadi" Shiru Nihal tayi tana kallon Abba, sai kuma ta nemi kujera ta xauna, Abba kuma ya tafi dakin Farooq, sai ga Nihad ta fito rike da handbag dinta tana kallon Nihal tace "Ke wai wannan yaron ne xai kai mu har Zaria? Ni gaskiya i can't withstand seating that long in the car with him, in har da shi ne gwara in fasa kawai, kar ma yaje da gangan ya kasheni a hanya idan muna dawowa" ko kallonta Nihal bata yi ba balle ta tanka ta, sai ga Abba ya fito yana kallonsu yace "Ku fita da kayan Farooq xai kai ku yanxu" Nihad ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Better" Trolly din Nihal daya ta dauka ta fita waje, tana ta tsaye a bakin motar har Nihal ta fito tare da Amina dake rike da wani Trolly din, Bayan farooq ya fito duk suka shiga motar, Mumy na tsaye balcony bayan tayi ma Nihal addu'ar Allah ya kai ta lafiya Allah ya tsare, Ummu ma na balcony din a tsaye, a duk sanda Nihal xata koma makaranta sai ta ji kamar xata yi xaxxabi, duk cikin yaranta babu wanda take ji har ranta kamar Nihal, a haka har farooq ya gama warming motar ya fita, Aminu ya daga masu hannu yana cewa "Allah ya bada sa'ar karatu, ku kuma Allah ya maido ku gida lafiya" Nihad da ke xaune back seat ita da Nihal ko kallonsa bata yi ba, Farooq da Nihal kadai suka amsa da Ameen.... Bayan sun dau hanya wayar Nihal dake jakarta ya fara ring, Nihad ta juya tana kallonta, bude jakar tayi ta fiddo wayar tana kallon screen din ta ga Khalil, Nihad ta kikkifta ido don ta kara tabbatar da sunan da ta gani a jiki, bata san sanda ta bude baki ba don mamaki, Nihal ta daga kiran ta kai kunne, Dubara Nihad tayi ta matsa dab da ita ko xata ji abinda xai ce, daga daya bangaren Khalil yace "Kin tashi lafiya Hajiya?" Nihal tace "Alhmdlh, ina kwana?" Yace "Lafiya, ban samu damar kai ki ba, kuma kin tafi ba mu yi sallama ba, Allah Ubangiji ya tsare hanya, ya kai ku lafiya, ya baki sa'ar abinda aka je nema" Ta sauke idonta kasa tace "Ameen nagode" Yace "Sai anjima" Tace "Nagode" Katse wayar yayi, Nihad ta matsa tana kallonta da kyau tace "Nihal ba driver din nan bane ya kira ki?" Nihal ta ki cewa komai, Nihad ta saki baki tana kallonta, Farooq dake jin su yace "Wani Driver?" Da sauri Nihad tace "Ji fa yaya, driver din gida fa, meye hadinta da shi har ma zai kirata yanxu??" Farooq dai sai kallon Nihal yake ta madubi, Nihal ta hade rai tace "You have problem Nihad, komai ke sai kin san yanda kika yi kika canxa masa ma'ana, what's wrong with me having the drivers number, naga har number Saminu ina da shi me yasa be xama laifi ba? Ke lkcn da Habibu yake nan baki da numbersa? Waye yafi communicate da Habibu a gidan banda ke?" Nihad tace "Noo, ae Habibu daban wannan daban, kuma Habibu sai ta kama muke magana da shi a waya...." A fusace Nihal tace "Toh wannan din ma kamawa yayi muka yi maganar a waya" Farooq yace "Toh wai ke Nihad ina ruwanki??" Kallonsa Nihad tayi, lkci daya ta hade rai bata ce komai ba, yace "Ke ce ai kika dau girman kai kika daura ma kanki but there is nothing wrong to have people that are under you phone number" All through the journey Nihad bata sake cewa komai ba amma fuskarta a daure yake. Satan kallon Nihal take taga tana bacci, a hankali ta dauke wayarta dake kafarta ta bude don ita bata sa password, ta shiga call logs tayi blocking number Khalil sannan tayi deleting ta mayar mata da wayar ta ajiye. Har Nihad suka kai Nihal Zaria bata ce ma kowa komai a motar ba, Farooq ya kalleta yace "Sauka ki kama mata kaya ku shiga hostel" Ta ɗan daure fuska ta bude motar ta sauka, nan ta taya Nihal suka kwashe kayanta xuwa hostel din, bayan Nihad ta ajiye jakar karshe ta juya xata wuce Nihal tace "Are u still angry? Toh kiyi hakuri" Nihad ta kalleta tace "Baxan yi ba, ba dai driver ya fi ni ba" Nihal tayi Murmushi tace "Ya xa ayi driver ya fi ki, kema kinsan babu wanda ya fi ki a wajena, kiyi hakuri i didn't mean to make u angry" Nihad ta harareta tace "Kamar da gaske" Rungumeta Nihal tayi tace "Wllh kema kinsan da gaske nake blood" Nihad tace "Toh shkkn na hkura" Nihal tace "Toh nagode" a tare suka koma gun mota inda Farooq ke jiran Nihad, Nihad ta bude jakarta jin wayarta na vibrate, ganin Aliyu ke kiranta ta daga, bayan sun gaisa yace "Xan shigo kano in the evening, ki turo min address din gidanku" Nihad ta wara ido tace "Are u coming to our house" Yace "Ki turo ina jira" daga haka ya katse wayar, Farin ciki ne ya lullubeta, bai ta6a cewa xai je gidansu ba sai yau, a baya babu yanda bata yi da shi a kan ya xo gidan nasu ba amma sai ya ki, har ta kagu ta gansu a gida ta tambayi Umma abubuwan da xata dafa masa, nazari ta shiga yi... or is he coming because of that useless driver?? Ohh God that will be very great.

07087865788✍🏻


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post