💖💖 *NIHAAD*💖💖
22
Husnah ta kalli su Naf jin abinda Umma tace, Naf tace "Aa Umma bamu zo da kaya ba, mu ma kawai yanzu xa mu wuce, idan ya so ko gobe ne ma dawo" Umma tace "Toh shkkn, hakan ma yayi, Allah yayi maku albarka, tunda ba da mota na zo ba mu je kawai ku ajiye ni" Duk jikin Nihad yayi sanyi ganin xa su tafi su bar ta, babu yanda ta iya haka ta rakasu har bakin gate suka wuce sannan ta dawo cikin gidan tana ta kumbure kumbure. Sai da su Naf suka kai Umma har kofar gida tayi masu godiya tana sa masu albarka, sannan suka juya ita kuma ta shiga gate, Aminu na gaisheta ko bin ta kansa bata yi ba ganin Abba a tsaye balcony, karasawa balcony din tayi da sauri tace "Har ka dawo daga gidan Baffan?" Abba na kallonta daga sama har kasa yace "Daga ina kike?" Ta sauke ajiyar xuciya tace "Kayi hakuri ban ce maka xan fita ba, na fita babu izinu, wallahi Yallabai Nihad ce kira ba dare ba rana ko da yaushe cikin kuka, to shine yau da abun ya isheni nace bari dai in je in ga wani hali take ciki a gidan, kasan tun da muka kai ta ai ban koma ba" Abba dake ta sauraronta har ta kai aya yace "Toh daga yau kada ki sake xuwa gidan...." Da mamaki Umma tace "Kamar yaya fa Alhaji? Shikenan saboda iftilai ya fada ma yarinya sai ka sallama ma duniya ita, mu ma kuma ka nemi mu sallama ma duniya ita? duka duka nawa Nihad din take fisabilillahi Yallabai? Yarinyar da ko shekara ashirin bata yi ba a duniya, me ta sani akan rayuwa at this her early stage? so kake wani cutar yaje ya kamata a banza mu shiga uku? Kai kanka kasan wannan yaron tun zuwansa gidan nan ba shiri suke ba, jininsu bai ta6a haduwa ba amma ka rasa wanda zaka hadata aure da sai shi? Me yasa ma idan hadin ne baxa ka hadata da wanda bata sani ba bai santa ba, sai Dreban gidansu? Haba wannan ai babu adalaci yallabai, baka kyauta mata, wannan fa kaddararta ce, sannan ace duk soyayyar da kake mata amma ka rufe ido ka saka rayuwarta a garari kawai don an samu wasu shegu sun hada mata makirci?" Abba yayi shiru yana kallonta, can yace "Yanzu shawara kike bani a warware auren kenan?" Umma ta kalli Abba, ganin how sincerely he spoke, tayi kasa da kai tace "Ni ba haka nake nufi ba, kuma ai kai ba karamin mutum bane aji an daura aure kuma an warware sa, mutuncin da kimarka ya wuce haka, kawai dai ina jimamin abun ne, amma don Allah kar ka hanani zuwa wajenta ko ba komai zan dinga kwantar mata da hankali har ta hakura da wannan auren" Abba yace "Sumayya" Ta yi shiru tana sauraronsa, on a serious note yace "In har kina son zaman lafiya da ni toh na haneki da kara taka kafarki zuwa gidan nan, idan da wani abu xai kawota gida ba sai kin je, ina kara ja maki kunne babu ke babu gidansu, sannan ko mutuwa take ke kina tunanin zan sa a warware auren? Ai sai dai ta mutu a dakinta" Umma tace "Tabdi, to yallabai kamar yanda baxan yi shiru ba idan Nihal ce aka ma haka to Nihad ma baxan yi shiru ba don duk daya suke a wajena babu banbanci, don haka hanani zuwa gidan 'ya ta bai taso ba...." Abba yace "Good! Don Allah gobe ma ki shirya ki kara komawa gidan, ina me tabbatar maki a nan xaki ga the other side of me" Yana kai wa nan ya juya ya shige cikin gida, Umma ta bi sa da kallo sai kuma ta kyabe baki ta bi bayansa. Su Husnah na komawa hostel duk suka shantake a saman gado babu zancen sallah balle salati, Naf ta sauke wani ajiyar xuciya tayi kasa da murya tace "Amma don Allah ku ya ku ka ga wannan drivern? Isn't this strange?" Zully ta riƙe ha6a tace "Not as i expected, anya kuwa da gaske shine drivern? Ni fa har muka dawo ina kokwanto a raina gaskiya" Husnah tace "Kun ji ku, idan fa an bibiya irin shuwan nan ne fa wanda ba shi da galihu, farin fatarsa ce tasa ku ke kokwanto ko driver ne shi ko ba driver ba?" Zully ta kalleta tace "Aa maganar gaskiya duk da Umma ta tabbatar mana da shi din ne har xuciyata na kasa yarda, ta yaya wannan cikakken mutumin xa ace driver ne? His skin... Ko ku baku lura da shi ba, no plss he is so fresh abeg" Naf tace "Ohhhhoo ashe dai bani kadai ma lura da skin dinsa ba, ni wallahi da ba don kar inyi karya ba ma sai nake ganin kamar na ta6a ganinsa, ko me kama da shine oho" Husnah ta kyabe baki tace "Kanku ake ji" Zully tace "Kai amma gayen nan Allah ya xuba masa kyau frankly speaking, kawai mu fadi gaskiya, duk inda me kyau xai shiga shi ma xai shiga, kuma ina tabbatar maku Nihad haukan ta bai taba barin ta nutsu ta kare masa kallo ba" Husnah tayi wani dariya tace "Kai kuma da da wani zance, Ina amfanin kyau ba nera? kina jin mutum na tukin mota for a living, kun ishe ni da wani yana da kyau? kawai Nihad din ma kadai ya raina dan ya ganta er karamar yarinya ne, mu kuwa da muka kusa talatin a duniya baki ga da muka masa wankin soso da sabulu bai iya yace mana komai ba sai sissine kai da yake, ni fa baxan yi mamaki ba idan aka ce shege ne mutumin nan, kilan uwarsa a titi ta haifesa ta yarda shi shine yake ta garari har ya samu driving gidansu Nihad" Zully ta kwashe da dariya ita dai Naf bata ce komai ba, Husnah ta kalleta tace "Ya dai... Kin yi shiru" Naf ta ɗan tabe baki tace "No kawai ni dai i am not comfortable cewar shi din mere driver ne, he might definitely have a mission, haba u girls should think deep mana, sai kace ba big babes ba, ko kayan jikinsa idan kuka lura ai ba na banza bane, ni fa har takalminsa sai da na kalla, wallahi da kyar idan mutumin nan ba wani mission garesa ba" Husnah da Zully suka kwashe da dariya har da kyakyatawa, Husnah tace "Wllh shi ba kowa bane don ma ki ji in gaya maki, a wannan zamanin babu wanda xai bata lkcnsa ya zo gidan mutane for almost a year now wai da sunan mission, sai kace wani film ko novel, mission for almost one year ace ba ayi accomplishing dinsa ba har yanxu? Ke dai ki yarda ɗan talakawa ne mukus me shegen girman kai, don yaga fatarsa ja ce sannan gashinsa irin na halfcast shine yake wani feeling, ba ga ire irensa ba a can Ibadan da Lagos suna bara bakin titi, kilan shi ma daga can ya gudo arewa bayan ya girma" Zully tace "Kuma haka ne wallahi, gasu can a karkashin gadan lagos har Ibadan" Zully ta kyabe baki ta mike tace "Ni dai bari in je in yi wanka in zo in kira babyna, ba ruwana da wani batun shegen dreba can" Naf tace "Yanxu yaushe za mu je mata can din, kun san fa mun sa mata rai" Husnah tace "Mu bari kawai jibi don gobe kinga xa mu je minjibir park" Naf tace "Ehh haka ne kuma, Allah ya kai mu" Washegari tuesday da safe Nihad ta shirya tsaf xata makaranta abunta tunda ga makulli a hannunta, mayafinta ta yafa ta dau jakarta bayan ta feshe turare kusan kala biyar a jikinta ta fito daga dakin, yana jin fitowarta yayi saurain mayar da wayarsa dake hannunsa xuwa bayan kujeran da yake zaune, bata ko kallesa ba ta nufi kofa ta fita abun ta, da ido ya bi ta imagining if tsallake gate din xata yi, rabonsa da ita tun jiya bayan ya bude ma Umma gate da suka zo, can dai ya mike ya fita parlon ya tsaya bakin kofa yana kallon ikon Allah, tana isa gate ta bude jakarta ta ciro makullin tana kokarin bude gate din taji yace "Keee" bata fasa bude gate din ba ta juya ta kallesa bayan ta bude tace "Saboda baka yi karatu ba baka san muhimmancin karatu ba kana tunanin ka isa ka hana ni zuwa makaranta ko, to baka isa ba, ba a kuma haifeka ba" Tana gama fadin haka ta fice daga gate din, mamaki ne ya cika sa yayi saurin ciro makullin aljihunsa yana kallo yaga it's intact, then where did she get a space key?? bai yi attempting bin ta ba balle har tayi showcasing altitude dinta a bakin titi, ya juya ya koma parlor filled with surprise. Ba karamin mamaki su Husnah suka yi ba ganin Nihad a school, Nihad ta zauna aji jikinta duk a sanyaye don tun da ta shigo schl ake nunata, wai ga warce ke cikin video din nan, har ta iso ajin da suke lectures idon jama'a na kanta, bata kara jin damuwan video dinta da ya bazu duniya ba sai a yanzu, dama haka abun ya tafi viral, a ajin ma sai satan kallonta ake ana kuskus, kai har ma da masu shigowa duk da ba department dinsu ba don kawai a zo a ganta, sai a sannan tayi da ta sanin fitowa, kuma fitowar ma da ɗan karamin mayafi, daga karshe dole su Naf suka dauketa suka fita makarantar xuwa hostel dinsu, Nihad ta zauna gefen gado lkci daya hawaye ya kawo idonta, Husnah tace "Kin ji ki, meye abun damuwa, abinda ba kanki farau ba kuma ba kanki za a kare ba, duk dan iskan da ya isa ya tinkare mu yace ai kece a video yaga yanda xa mu ci ubansa, ni ai baki ce min xaki taho makaranta yau ba da na hanaki don su yanxu ma suke tashen labarin, kuma ana ta jira aga kin shigo makaranta sai ga ki yau, ni ban ta6a ganin munafukai yan sa ido marasa aikin yi kamar yan makarantar nan namu ba, abu kusan sati daya amma kullum maimaita zancen ake kamar yau ya faru" Nihad ta hade kanta da gwiwa tana shessheka tace "Da na sani ban fito ba" Naf tace "Surutun mutane zai sa ki fasa rayuwarki yanda kike so? Ai ba a biye ma mutane, gwara su yi ta ganinki din har su gaji su yi shiru zancen ya mutu, yanzu dai ina kika baro ɗan rainin wayon Drivern can?" Nihad na goge idonta cikin sanyin murya tace "Toh meye hadina da wannan kuma kike tambayata" Naf tace "Aa babu hadinki da shi kam, ni ai na ga kokarinki ma da kike iya kwana gida daya da shi, da ni ce kwasan kayana xan yi in bar gidan iyaka Abba yayi bambami a wuce wajen" Nihad ta kalleta tace "Abbanmu yace xai yi disowning dina if i try anything of such" sai kuma ta fashe da kuka sosai, Naf tace "Aa ba kuka xa kiyi ba, nema ma kanki mafita xa ki yi" Nihad tace "Don Allah ku dawo gidan mu zauna gaba daya a can" Naf tace "Dama gobe muka yi ai za mu je can din" Nihad tace "Tunda na fito yau don Allah ku dau kayanku kawai mu koma can gaba-daya, the house is nothing but a living hell for me" Naf ta kalli Husnah dake ta danna wayarta bata ce komai ba tace "Husnah ya kika ga" Husnah tace "Duk yanda ku ka yi" Naf tace "Toh kawai duk mu dau kaya ko kala biyar biyar ne mu tafi can din gaba daya" Nihad tayi murmushin jin dadi tace "Amma naji dadi Nagode wllh" Zully tace "What are friends for, ai amfaninmu kenan" Nihad tayi kasa da murya tana kallon Naf tace "How about Aliyu?" Naf tace "Hmm, kinsan he is off social media tun da abun nan ya faru, to in gaya maki 3 days ago mun yi chatting da wani frnd dinsa yake ce min ai ba shi da lafiya ma" Nihad tayi narai narai da ido tace "Da gaske?" Naf tace "Wllh kuwa bari ma in nuna maki chatting din" Jawo wayarta tayi ta bude ta shiga chatting dinta da wani abokin Aliyu ta mika ma Nihad wayar, Nihad ta amshi wayar jiki a sanyaye ta dinga bin chat din, abokin gaya ma Naf halin da Aliyun ya shiga bayan faruwan lamarin yake, ya kuma ce mata har su abokanansa yayi isolating din kansa daga cikinsu ba ma social media ba kadai, abokin ya dinga nuna yanda Nihad ta kwafsa ga shi Aliyu yayi trusting dinta sosai kuma ya sa ran zai aureta duk da tulin manya manyan babes dinsa, Nihad ta hade kai da gwiwa tana shesshekar kuka tace "I don't know who did this to me, i don't know who is this that ruined my happiness" Husnah ta sauke ajiyar xuciya tace "Na fi ki son mu gano wanda yayi maki haka Nihad, amma abun akwai rikitarwa ni wallahi kawai zuciyata ta kasa yarda cewar ke ce a video din, ke baki zama da undies haka kamar yanda mu muke yi, sannan duk party tare muke zuwa balle ace wani partyn kika je aka maki haka, abun dai akwai confusion sosai wallahi, wanda ya sanki sosai sosai ne yayi maki wannan abun, i wish Abba xai ajiye duk wani fushi ya tsananta binciken ta ina wannan video din ya fito" Zully ta sauke ajiyar xuciya tace "Ai na dau darasi ni kam, ko daga ni sai singlet da skin tide baxan sake xama a waje ba balle undies, na saka kaina a shoes din Nihad ya fi a kirga but luckily the shoe did not even size me, waiii ai ni kashe ni kawai xa ayi a gida wallahi" Naf ta tabe baki tace "Koma waye da kansa zai tona ma kansa asiri nan ba da dadewa ba" Nihad ta share hawayen da ya ki tsaya mata tace "Pls Naf try calling Aliyu ki ga ko zai daga" Naf tace "Toh Allah ya sa ya daga, ko kuma ma dai Allah ya sa ya shiga" Contacts dinta ta shiga tayi dialing number Aliyu, ai ko ya fara ringing, gaban Nihad ya dinga faduwa tana kallon wayar, su kansu gaba daya kallon wayar suke, sai gashi kuwa ya daga, sai da Nihad taji xuciyarta ya kusa shigewa cikinta, Naf tace "Hello Aliyu what's up?" Daga daya bangaren cikin cool voice yace "Fine Nafisah, how are you doing" Tace "Cool, ya garin" Yayi shiru, tace "Are u there?" Yayi kasa da murya yace "U saw how ur frnd played with my heart right?" Nihad ta kauda kanta hawaye sai zarya yake a fuskarta, Naf tace "Calm down Aliyu, duk wannan abun set up ne ba wani abu ba, ka fi kowa sanin halin Nihad, sannan mu da muke tare da ita always xa mu shaideta, wllh wllh Nihad bata tsayawa a cikinmu daga ita singlet balle undies, wannan lamarin da rikitarwa yake, wa ya sani ko anyi hakan ne don a raba ku tunda anji xaka turo gidansu" Aliyu yace "But i have warned her severally Nafisah, na sha ja mata kunne duk yawace yawacen zuwa party ta daina, but unfortunately bata daina ba, and ga abinda ya faru daga karshe" Naf tace "Kai wai wa yace maka a wajen party aka yi mata haka? Ko a gida baxa ayi iya yi ma mutum haka ba sai wajen party kawai? Kai dai kawai ka kyale makiyi Ali" Aliyu yace "I am so heartbroken Nafisah" Naf tace "So is she also" Yace "Tana ina yanxu?" Naf ta kalli Nihad sai kuma ta ɗan yi murmushi tace "Mun zo gidansu ne daxu ganin halin da take ciki shine nace bari dai kawai in kiraka" Yayi shiru, tace "In kai mata wayar pls?" Nan ma dai shirun yayi, tace "Don Allah kar kace A'a, ko sai kaji ta mutu xaka fara da ka sani an kai mata wayar? Wallahi she is seriously sick" Yace "Kai mata" tace "Yauwa my guy" kallon Nihad tayi tana Murmushi, ita dai Nihad ta sunkuyar da kanta kawai, Naf ta kamo hannunta ta saka mata wayar a ciki, a hankali ta kai kunne tayi sallama. Aliyu yace "Now u get the reason why nake rabaki xuwa party?" Bata iya ta ce masa komai ba ta a goge idonta, yayi kasa da murya yace "Why Nihad, why?" Cikin rawan murya tace "I don't know how everything happened, kayi hakuri don girman Allah" yace "In yi hakuri Nihad? Ta yaya iyayena xa su amince da aurenmu bayan duk sisters dina babu warce bata ga wannan video din naki ba, hatta mum dita ta gani, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Nihad dai bata ce komai ba, Yace "How will we mend this damage?" Nihad tace "Abbana yace min wai ya min aure" Aliyu yace "Ban gane yayi maki aure ba, kina nufin aure Abba xai maki?" Cikin kuka tace "Ehh har ya min" Aliyu yace "Stop it Nihad, yaushe yace maki haka" A raunane Nihad ta sanar masa yanzu ita da khalil suke zama gida daya, kuma Abba ya sanar mata wai yayi mata aure da shi, lkci daya ya birkice mata yace "Baby yanxu kina nufin aure aka maki, aure da drivern nan na gidanku?" Nihad ta girgiza kai da sauri tace "Ni ba a min aure da shi ba, kawai Abba ne ke fadan hakan, ni ban yarda an min aure da shi ba" Aliyu yace "Nooo, it can never be, not when i am alive, hakan baxai ta6a yiwuwa ba, na yi isolating kaina from everything na kwana biyu ne but nasan baxan ta6a iya rabuwa dake ko da nayi attempting din yin hakan ba, i know i will come back to you, kuma ko iyayena bana jin xa su hanani in aureki don sun san ina son ki, ko da nude video dinki ne yayi yawo i stil love u Nihad, and i will still marry u" Nihad dai ta yi kasa da kanta ta kasa cewa komai yace "Ki kulan min da kanki Nihad, do not break my heart for the second time pls, sannan ta ina xan dinga samunki ko 2 days ago i tried ur number naji switch off" a hankali tace "Xan kiraka da sabon line dina idan na koma gida" Yace "I will be expecting pls" Sallama suka yi, Naf ta amshi Wayarta tace "Alhamdulillah" Nihad ta ɗan yi murmushi, Husnah tace "Gaskiya Aliyu ya san kaddara, yanxu ke kuma sai ki san duk yanda xa kiyi ku raba jaha da wancan driver din, koma yaya xa ayi kawai ya sake ki tunda Aliyu is still willing to marry u" Nihad ta kalleta tace "Ya sakeni?? To da aurena yayi da xai sakeni? Ai kawai xama muke gida daya bisa umarnin Abba, but i am for Aliyu alone" Zully tace "Atoh, kunsan akwai wani aure da xaka ji sa kamar wasan yara, to irin auren nan naku da drivern kenan, ko ni bana kallonsa a matsayin mijin Nihad wallahi, kilan kawai Abba is playing u, amma ta yaya ma xai ce ya maki aure da dreba" Nihad tace "Toh kun ga lkci na wucewa mu tafi pls" Naf tace "Bari in kara watsa ruwa" Zully ta mike tace "Ina zuwa in kwaso kayana" daga haka ta fita daga parlon, Husnah ta kalli Nihad tayi kasa da murya tace "In baki shawara? Toh wallahi kar ki yarda su wani bi ki, gwara kiyi tafiyarki ke kadai daga baya ni kadai sai in biyoki gidan, idan ba haka ba akwai matsala" Nihad tace "Matsalar me fa?" Husnah tace "Toh shkkn ki tsaya tambayar ta me, naga dai ni kika fara sani kafin su, kuma ta dalilina kika san su, don haka kawai yanxu kice masu gidanku xa ki daga can ne xaki wuce gida kina komawa gida kuma xaki kira kice mu taho gaba daya" Nihad tace "Toh shkkn" Mikewa Husnah tayi ta fita daga dakin. Khalil ya fito compound jin ana Knocking gate, yana bude gate din ya ga Farooq a tsaye, welcoming dinsa Khalil yayi with smile all over his face, Khalil ya rufe gidan suka koma can parlor tare, Farooq na cewa "Gobe xan koma aiki shine nace bari in shigo yau dai" khalil yace "Allah sarki" Suna shiga parlon Farooq na bin ko ina da kallo yace "Ina take?" Khalil bai basa amsa ba kawai ya tafi kitchen don ya dauko masa ruwa, Farooq ya dau throw pillow da ke kan kujeran da yake kokarin zama sai ya ga Iphone, duk tunaninsa na Nihad ne duk da a gabansa Abba ya kwace Iphone din nata, Farooq ya zauna yana jujjuya wayar amma sai ya ga ba na Nihad bane, dai dai nan khalil ya fito daga kitchen with bottle water and glass cup, still yayi yana kallon Farooq.....