💖💖 *NIHAAD* 💖💖
Page 27
By Khaleesat Haiydar📖✍🏻
A hankali Nihad ta bude idonta ta dalilin sanyin da take ji, at first sai da tayi imagining cewar ai fa kauyen nan take, a firgice ta tashi xaune tana tattaba daya side din gadon don wutan dakin a kashe yake, amma taji ba kowa wajen, jin laushin duvet yasa ta tuna ashe a hotel suke, wani boyayyen ajiyar xuciya ta sauke, ta sauka daga kan gadon tunda hotel din ba bakonta bane ta san inda switch yake, tana tafiya a hankali ta xagoya xata kunna wutan taci tuntube da mutum ta fada kansa duk da a zaune yake, da farko tayi mugun tsorata amma tana jin kamshin turarensa ta gane shi ne, tashi tayi ta dafa bango ta kunna wutan, zaune ta gansa saman darduma alamar sallah yake, ta zaga daya side din ta kalli agogon dakin ta ga karfe biyu da minti goma, komawa tayi gefen gado ta zauna tayi tagumi, sai kuma ta tuna bata yi isha'i ba ta tashi da sauri ta shiga bandaki. Har ta idar da isha'i sallah yake shima, ta ɗan yi jim kamar xata tashi ta koma ta kwanta can dai kuma kawai ta mike ta hau sallan nafila, har ta mance rabon da tayi qiyamul lail, sai dai in mistakenly ta kwana dakin Nihal shine Mumy ke tashinsu su yi sallan dare, don dare daddaye ne Mumy bata sallan dare, a wannan daren kuma tayi addu'a sosai a kan Allah ya toni asirin duk wanda yayi ruining happiness dinta cikin gaggawa, abinda bata ta6a yi ba tun da abun ya faru, daga karshe tayi addu'ar Allah ya sa khalil ya rabu da ita na har abada don ita ba class dinsa bace, sannan baxata ta6a zama da shi a matsayin mijinta ba, ta kuma yi addu'an bayan Khalil ya rabu da ita Allah ya mallaka mata Aliyu, wajajen karfe Uku da rabi ta fara jin bacci, ta ɗan saci kallon side dinsa, yana zaune saman darduma shi ma da alamar ya idar, amma kana kallonsa xaka san yayi nisa tunanin da yake, and he look so distressing, dauke idonta tayi daga kansa tayi kwanciyarta saman inda tayi sallan, har dai bacci ya dauke wajen karfe hudu bata ga alamar Khalil xai kwanta ba. Da asuba loudspeaker din masallacin dake hotel ne ya tasheta, bata gansa a dakin ba alamar ya tafi masallaci, bayan ta idar tana zaune saman darduma tana azkar ya shigo dakin, ba tare da ya kalleta ba ya shiga bandaki, tana ta zaune kan darduma taji ring din wayarsa kallon gaban madubin tayi da sauri don bata san wayar na nan ba, kuma bata ta6a jin wayarsa na ring ba sai da vibrate, ta mike tana tafiya a hankali ta tafi gaban madubin, Mami ta gani gaban screen din karamar wayar, ta dauka kenan kawai ya bude bandakin ya fito da sauri ya nufota yace "Keee" Ba karamin rikicewa tayi ba ta juyo wayar na hannunta, zaro ido tayi ta saki wata er kara ganinsa daure da towel ta durkushe kasa ta rufe fuskarta da gwiwanta a tsorace, yana isa inda ta durkusa ya warce wayarsa a hannunta ya koma bandakin, duk da taji rufewar kofar bandakin taki dago kanta, bayan kusan minti daya ta dago a hankali tana kallon kumfan da ya sa mata a hannu wajen warce wayarsa, turo baki tayi ta mike jiki a sanyaye ta koma can daya side din gadon ta kwanta tare da juya ma kofar bandakin baya. Tana ji ya fito daga bandaki bayan kusan minti sha biyar sai kuma ta ji ya fita daga dakin gaba daya. Wajen karfe takwas ta gaji da kwanciya ta tashi ta zaga ta shiga bandakin, wanka tayi ta fito bayan ta goge jikinta ta maida kayan da ta cire, tana zaune gefen gado ta jinginar da kanta da gadon tana kallon Tv duk da hankalinta baya kan kallon ya bude kofa ya shigo dakin, tunda ta kallesa sau daya bata yarda ta sake kallonsa ba, ta dai ga ya canxa kaya, shi kam bai kalli inda take ba ya dau towel din da ta yasar saman gado ya shigar da shi bandaki ya fito, ya dauko magungunan da ya siyo mata jiya dake yashe kasan dakin ya jefa mata gefenta ya hade rai yace "Wato dama lafiyarki qlau kika sa naje chemist nayi asaran kudina ko?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Kudin babana dai" kallonta kawai yake ba ko kiftawa, can yace "Gaskiya ne, kudin babanki ne, sai ki taso mu koma can garin kiyi kumallo a can gidanmu, kinga can ai kudin babana ne ba na baban wani ba" Kallonsa tayi da sauri, ganin hada abubuwansa dake dakin kawai yake, tayi karfin halin cewa "Wani garin xan je in yi kumallo?" Ba tare da ya kalleta ba ya nufi kofa yace "Ina jiranki a waje" Ta fashe da matsanancin kuka tace "Ni wallahi baxa ka maida ni wannan garin ba, wai kai baka tsoron Allah ne?" Juyowa yayi ya rungume hannu ya jingina da kofa yace "Sai ke" Cikin kuka tace "Allah baxan je ba, kaji har na rantse, dama ba kwana biyu kawai xa mu yi ba? To wllh baka isa ka maida ni ba" Yace "Ohk, xan nuna maki kuwa na isa, sannan in mun koma sai mun yi wata daya kafin mu bar garin, kinga baxa ki kara min gorin kudin babanki nake ci ba" Cikin tashin hankali tace "Kaga don girman Allah kayi hakuri ka daina ce min haka, wallahi in ka sake maida ni kauyen nan xan iya mutuwa kawai" Khalil yace "Toh mu je a ga adadin kwanakin da xaki iya a can din kafin ki mutu" Cikin kuka tace "Don girman Allah kayi hakuri ka rufa min asiri" Shiru yayi na few seconds, sai kuma yace "Ohk, baxan maida ki garin ba amma da sharadi" Tana goge idonta tace "Ina ji" Ya fi second talatin yana kallonta kafin yace "Nasan komin daren dadewa xa mu rabu... Don haka idan Allah ya kai mu lokacin ina son ko me xai faru baxa ki fasa nuna ma iyayenki cewar ke kika bukaci mu rabu ba ni ba....." Nihad dake ta kallonsa da mamaki tace "Toh me yasa yanxun baxa mu rabu ba kawai, kuma wallahi babu wanda xan gaya ma, kaga babu wanda xai sani sae mu biyu" Yana kallonta yace "Ohk ta yaya kike tunanin xa mu rabun yanxu?" Ta gyara xama tace "Kawai kace ka sakeni, babu me sani sai ni da kai" Yace "Toh idan aka yi hakan sai me xai faru?" Ta daga kafada tace "Ba komai, kawai kayi rayuwarka inyi ta wa, ni xan ma iya bar maka gidan gaba daya kawai sai dai in dinga xuwa diban kayana, idan kana so ma sai ka saka yan haya ka dinga karban kudin kana xubawa a aljihu" Khalil ya ɗan yi murmushi ya gyara tsayuwarsa yace "Ohk, sai ki ci gaba da iskancinki daga inda kika tsaya kenan ko?" Tayi masa wani kallo tace "Me kake nufi? Ni nake yin iskanci? Kana nufin ni yar iska ce?" Yayi wani murmushin takaici yace "Toh baxan yi abinda kike so yanxu ba, kawai dai ki sa a ranki lokacin hakan na zuwa, nan ba da dadewa ba" Ta kyabe baki tace "Ni fa lokacin da kake nufi da yanxu duk daya ne ni a wajena" Ya daga kafada yace "Gwara dai a jira lokacin" Ita dai bata kuma cewa komai ba amma a ranta tunani take ashe ma ba wani babban sharadi bane, dama ita ai babban burinta su rabu na har abada, Ta kallesa tace "Ka dai yi alkawarin rabuwa da ni??" Yace "In sha Allah" Wani farin ciki taji ya rufeta tace "Toh nima in sha Allah ko ma me xai faru xan ce nice nace mu rabu babu ruwanka" Yace "Toh" Tace "Toh nima ina da deal dina in har kana son inyi abinda kace nima sae kayi abinda nake so" Yace "Ina sauraronki" tana gyara zama tace "Na farko ina son ka bar ni in ci gaba da xuwa makaranta na, na biyu baxa ka hana duk wanda xai zo wajena xuwa ba, like kawayena infact everybody, na uku xaka bani spare key na gida nima, sannan na karshe ina son ka bar ni da wayata..." Kallonta kawai khalil yake, ta langwabar da kai ta wara ido tace "Ehh, ni gwara nawa minor request ne, babu abinda xai ragu a jikinka idan kayi accepting, naka request din kuwa kilan har tsine min xa a iya yi a gida amma kuma ban damu da hakan ba na amince xanyi yanda kace" Khalil yace "Abu biyu kadai xan iya maki a abubuwan da kika ce, idan kuma kinga hakan bai maki ba kawai a bari, mu ci gaba da zaman mu yanda muke, kuma dole a titi ace maki matar drivern gidanku" Ta marairaice sai kuma tace "Toh ina ji, ka gaya min abu biyun" Yace "Babu xancen xuwa makaranta sannan baxa ki rike waya ba!!!" Shiru Nihad tayi tana nazari, wato kawayenta xa su iya xuwa gidan sannan xai bata makullin gida, daga kai tayi ta kallesa taga kallonta yake yana jiran jin me xata ce, tace "Toh ai shikenan, na amince" Yace "Sannan abu na karshe wanda muhimmancinsa kusan daya da sharadin farko...." Tace "Ina jin sa" Yace "Babu ke babu kallon inda wayata take balle ki ta6a, a takaice babu ruwanki da wayana har xuwa lokacin da xa mu rabu" Nihad ta kyabe baki tace "Toh dama ni meye ruwana da torchlight phone dinka bawan Allah??" Ya gyada kai yace "Toh" Juyawa yayi ya fita daga dakin, ta mike ta dau ledan magungunanta ta saka Hijab sannan ta bi bayansa. A reception ta tarar da shi ya bada makullin dakin ya fita compound din hotel din ta bi bayansa, wani ma'aikacin hotel din ne irin masu share share ya ganta yace "Ahh Hajiya kwana biyu kin buya, ya kawayenki" Nihad ta juya ta kallesa, murmushi tayi tace "Lafiya lau ya aiki?" Yace "Alhamdulillah, yau baku zo da kawayen naki ba kenan? Naga kullum tare ku ke" Sai kuma ya kalli Khalil dake tafiya yace "Au ashe da oga ku ke...." Katse sa Nihad tayi da sauri tace "Aa, drivern gidanmu ne, ya kawo ni in amshi sako wajen wani" Murmushi kawai Khalil dake tafiya xuwa inda ya ajiye mota yayi ba tare da ya juyo ya kallesu ba, Ma'aikacin ya fasa gaida Khalil da yayi niyyar gaidawa, sai kuma yace "Allah sarki ni na zata oga ne ae nagansa kalarki, to na gaisheki Hajiya" Bude jakarta tayi taga dari biyar ta zaro ta mika masa, ya amsa da ladabi yana mata godiya, tuni Khalil har ya kai gun mota ya bude driver seat ya shiga, Nihad ta karasa ta bude back seat ta shiga ta kulle, har suka isa gida bai ce mata ba bata ce masa ba, bayan yayi parking ya sauka ya tafi ya kulle gate, sannan ya nufi entrance din gidan ya bude kofar main parlor, Nihad dake ta tsaye tana jiran ya xo ya bude ta kyabe baki ta bi bayansa suka shiga parlon, wani ajiyar xuciya ta sauke direct ta nufi dakinta. Bacci sosai Nihad tayi bayan ta shiga dakinta, wajen karfe sha daya da rabi ta farka ta dalilin yunwan da take ji, a hankali ta mike ta shiga banɗaki tayi wanka ta wanke baki sannan ta fito, bata gansa a parlor ba har ta nufi dakinsa sai kuma ta fasa bude kofar ta dawo parlor ta zauna tana jiran ganin fitowarsa bude kofar parlor aka yi ta juya da sauri, taga ya shigo parlon rike da leda kallo daya yayi mata ya dauke kai ya karaso cikin parlon, a takaice tace "Makulli xaka bani xan fita in siyo kayan miya, sannan anjima xan je kasuwa siyo atamfofi don na kyautar da duk kayana a can garinku" Ya girgiza kai yace "Baya daga cikin sharadinmu, duk me kike bukata xa a siyo a ajiye maki" Ta kyabe baki tace "Toh a fita a siyo min kayan miya" Cike da isa tayi maganan, yace "Sai sanda nayi niyya" Yana gama fadin haka ya ajiye ledan hannunsa ya nufi kitchen don dauko plate, bin sa tayi da kallo yana shiga tayi saurin dauke ledan abincin nasa ta shige daki da sauri ta sa makulli, shinkafa ne da miyya da yaji uban nama sannan ga coslow a wani karamin takeaway din, ga ruwan roba me sanyi da drink, tayi er dariya ta gyara zamanta ta dau cokali ta fara cin abincin. Wajajen karfe uku Nihal ta kira Khalil, bayan sun gaisa yace "Kin dawo lafiya?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Maa sha daya, yaushe xa ki zo ganin er uwar taki?" Nihal tace "Shine dama nake son in ce mata xan zo yau, ka kai mata wayar pls" Yace "Xan gaya mata, Allah ya kawo ki lafiya" Tace "Ameen" daga haka ya katse wayar, tun da Nihad ta shige masa da abinci daki bata sake fitowa ba, don bayan ta ci ta koshi ma ramuwan baccin da bata yi a kauye ba ta ci gaba da yi. Wajen karfe biyar Nihal ta iso gidan, Khalil ne ya bude mata gate bayan ta kirasa a waya ta sanar masa tana bakin gate, ta sunkuyar da kai ta gaishesa ya amsa da murmushi yace "How are you Nihal?" Ta daga kai ta kallesa tace "Alhamdulillah" Yace "Maa sha Allah" Tana biye da shi suka shiga parlon gidan, ganin ta zauna a parlon ya daga kafada yace "Tana can daki, ki shiga" Nihal tace "Ko zaka dan mata magana ta fito" Yace "Aa, just go in" Mikewa tayi ta nufi kofar dakin da ya nuna mata, a hankali ta kwankwasa kofar, Nihad ta juya tana kallon kofar, to me xai ce mata yake mata Knocking, can dai ta mike ta nufi kofar ta bude a hankali, ido hudu suka yi da Nihal, wara ido tayi ta rungumeta tace "Yaushe kika dawo Nihal?" Nihal na Murmushi tace "3 days ago" Sai kuma Nihad ta hade rai ta koma cikin dakin, Nihal ta bi ta da kallo sai kuma ta bi ta cikin dakin ta kulle kofar, Nihad tace "Wato ke har xa a iya hada baki dake a cuceni ko Nihal? Ni nasan babu yanda xa ayi kice baki san komai a kan abin nan da Abba yayi min ba" Innocently Nihal tace "Wallahi ban san komai ba Nihad, kiji har na rantse" Nihad tace "Toh sai aka ce maki yarda xan yi da ke? Bayan nasan har tadi ku ke yi da drivern nan a waya amma kice baki sani ba?" A hankali Nihal tace "Allah ne shaida na, amma meye ribata idan nayi maki karya?" Nihad ta tabe baki tace "We have already sort out things da shi daxu da safe, and we are okay with our plan" Nihal tace "What plan?" Nihad tace "Ba sai kin ji ba, ina umma?" Nihal ta mika mata wayarta tace "Tace in na xo ki kirata" Murmushi Nihad tayi ta amshi wayar ta tafi can karshen gado ta hau kiran Umma, Umma na dagawa tace "Auta har kin je gidan ne?" Nihad tace "Umma ni ce" Umma tace "Aa Nihad, wato dai wannan matsiyacin duk wayar da aka baki sai ya karbe ga shi tatattce ko?" Nihad ta tabe baki tace "Wallahi Umma" Umma tace "Toh xa mu xuba da shi kuwa, xan kawo maki waya sannan in mika masa a gabana ya damka maki wayar da hannunsa" Nihad tace "Kin ma san abinda yayi min Umma?" Umma ta zaro ido tace "Me yayi maki?" Nan Nihad ta labarta ma Umma garinsu da ya kai ta ta kusa mutuwa, Umma tace "Ikon Allah, amma shine matsiyacin nan ya samu waje yake nuna ma mutane isa daga an aura maki shi? Asha ɗan kauyen kayau ne" Nihad tace "Wllh Umma ban gama rainasa ba sai da naje garinsu, yanxu 100% na rainasa wallah, Umma ko wuta fa babu a garin, sannan rafi suke xuwa debo ruwa, kai ni baxan ma iya baki labarin garin nan da baki ba, sai da nayi rashin lafiya kamar xan mutu sannan ya dawo da ni cikin gari" Umma da ke ta sauraronta tace "Ikon Allah, dama ance talaka da matsiyaci basu iya samun waje ba, ki ga yanda ya dawo birni ya kile yake daddaga ma mutane kai alhalin ko mage me gata baxata iya rayuwa a kauyen ba" Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace "Na sha mamaki Umma, ɗan kauyen kayau ne wllh, kuma yanda kika gansa fari haka family dinsa suke da haske a kauyen" Umma tace "Toh Allah ya kyauta, in sha Allah gobe ko jibi ina nan shigowa daughter" Nihad tace "Toh Umma kar ki manta wayar, idan ya so kamar yanda kika ce sai ki basa ya bani a gabanki sannan ki ja masa kunne sosai kar yace xai amshe" Umma tace "Kar ki damu sai dai na zo" Daga haka suka yi sallama, Nihal na kallon Nihad tace "kinsan Mumy bata da lafiya kuwa Nihad?" Nihad ta kalleta tace "Haba? To ai ni ba a gaya min ba" Nihal tace "Ai kam bata da lafiya, in kirata ku gaisa?" Nihad ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Ki bari anjima da daddare xan kirata" Nihal tace "Toh shkkn" Nihad tace "Idan xa ki ci abinci ga indomie can kitchen ki dafa fa" Nihal ta mike ta fita daga dakin, tana shiga kitchen taga kayan miya kawai tayi deciding ta dafa jollof rice, tana cikin grating kayan miyan taji muryar khalil yace "Sannu da aiki" Ta kalli kofar da sauri sai kuma tayi murmushi tace "Nagode" Yace "Yaushe xa ku kare hutun?" Tace "Nan da sati biyu" Yace "Ohk nan xaki gama hutun ko?" Tace "Aa ni da gobe xan tafi, i don't want to over stay my welcome" Murmushi yayi yace "Aa kiyi hutunki kawai a nan" Ita dai bata ce komai ba tana ci gaba da aikinta, juyawa yayi daga karshe ya bar kitchen din. Bayan Magriba yana xaune a parlor Nihal ta fito daga daki xata je kitchen ta xuba ma ita da Nihad abinci, ganin khalil zaune parlon ta koma daki wajen Nihad tace "Ki fito ki zuba masa abinci, ban fa xuba masa ba tun daxu" Da mamaki Nihad ke kallonta, sai kuma tace "A saboda me xan xo in xuba masa abinci? Dama da shi kika dafa abincin ne?" Nihal dai bata ce mata komai ba ta juya ta fita, Nihad ta rike ha6a tace "Ji wani iyayi wai in xuba masa abinci kamar wani mijina, ashe xai tsufa bai ci abincin ba" Tsaki ta ja ta jawo wayar Nihal for the 10th time ta sake kiran layin Aliyu amma a kashe, kwantar da kanta tayi saman pillow kamar xata yi kuka don har ta gaji da trying layin nasa, tun xuwan Nihal take abu daya, Nihal na komawa kitchen ta fara xuba masa abincin a plate sannan ta dauka ta fito parlor ta nufesa ta durkusa tace "Ga abinci" Yana kallonta yace "Thank you Nihal" Ta mike ta koma kitchen din ta xuba ma ita da Nihad a tare, kadan Nihad ta ci abinci duk hankalinta a tashe yake bata samu Aliyu ba, Nihal ta ci abinda xata ci ta bar mata ta koma saman gado ta dau wayarta tana dannawa, Daga karshe wajen karfe goma da taga Nihad ba ci xata yi ba ta dau plate din ta fita, Bayan ta kai kitchen ta fito khalil na kallonta yace "Wani level kike a makaranta?" Ta tsaya tace "Level daya muke da Nihad" Yace "But in tambayeki" Ta ɗan tsaya sai kuma ta dawo parlon ta xauna tana kallonsa yace "Ke kika ce ma Abba Ahmadu Bello University kike so?" Nihal tayi murmushi tace "Aa, kawai cewa yayi can xan je ni" Yace "Ita kuma er uwarki fa?" Ta sunkuyar da kanta tace "He gave her option" Khalil dake ta kallonta yace "Ohk ke daga baya baki ce masa makaranta daya kike son xuwa da er uwar taki ba?" Nihal tace "Ya Usman da Mumy sun masa magana a lkcn, Mumy tace masa tunda har Nihad ta zaba Maryam Abatcha nima ya biya mun Maryam Abatcha din mu tafi tare ko kuma duk mu tafi ABU, amma sai yace Nihad kawai xata je ni in tafi ABU, he can't afford the fee of Maryam Abatcha for the two of us" Shiru Khalil yayi yana kallonta, can yace "Kuma Ummanku bata ce komai ba?" Nihal ta girgiza kai tace "Kawai ce min tayi inyi hakuri in tafi ABU din" Khalil ya gyada kai yace "Amma secondary daya ku ka yi ko?" Nihal ta girgiza kai tace "Shi ma ba daya muka yi ba, ita Nigerian Turkish tayi, ni kuma Yan dutse nayi" Khalil ya gyada kai yace "Ohk, yan dutsen kamar su Amina da Sudais nan suke xuwa ko?" Nihal tace "Har Aunty Kamila da Ya Usman da ya farooq ma can suka yi, Nihad kadai ce tayi Nigerian turkish" Khalil yace "Amma kamar er uwartaki tafi sabawa da Ummanki akan mamanta ko" Nihal tace "To ai a bangaren Umma take, ni kuma ina side din Mum dinta, though I don't know for her" Shiru Khalil yayi yana kallonta, can yace "Maa sha Allah, hakan yayi.... amma wani saurayinta da ya zo can gida ranan, sun dade tare ne?" Nihal tace "Wai Aliyu? Yea definitely shi, don ita bata kula wani saurayi idan ba shi ba, shekaran da ta shiga Maryam Abatcha suka hadu, shekara uku kenan" Yace "Ohk, kinsan saurayin sosai kenan?" Nihal ta bude ido tace "Nasan shi mana, he is the son of General Jikamshi..." Muryan Nihad dake labe jikin pillar din corridor tum daxu ya katse Nihal, cike da bacin rai Nihad tace "A gidan uwar wa kika san shi? Shi Aliyun kike tunani kinsani? Har da wani gaya masa sunan babansa salon yayi masa mugun abu irin nasu na kauye? To wallahi baki san shi ba kuma baxa ki ta6a saninsa ba, dama don ki zo ki hadu da wannan mutumin ku kafa munafurcina ya sa kika zo gidan nan ashe ban sani ba? To wallahi ni dai ki tashi ki tafi baxa ki kwanan min a gida ba, ai dai mun ga juna, har da wani ce masa ni kadai nayi Nigerian turkish, to wani yace kar kema kice ma Abba can kike so? Naga dai choice dina ne kuma Abba yayi accepting, sannan Maryam Abatcha ma wani yace kar ki sakar ma Abba kuka kice ke baxa ki je ABU ba sai dai Maryam Abatcha? Wallahi kin ban mamaki har xaki zauna da bare kuna cakalkalar namana ko tausayina baki ji ba, to Allah ya isa wannan gulman nawa da kika yi" Nihal dai bata ce mata komai ba, Banda kallon Nihad babu abinda khalil ke yi, tana huci tace "Shi kuma saboda gulma har da wani cewa nafi son Umma, dama ashe maza na gulma ban sani ba? Kuma ai Umma da Mumy duk daya suke a wajena babu wani bambanci, to tunda dai mun ga juna zo ki dau handbag dinki kiyi tafiyarki" Mikewa Nihal tayi ta nufi daki, Nihad ta bi ta da harara, sai ga ta ta fito sanye da hijab tana rike da handbag dinta ganin xata nufi kofa Nihad ta rikota tace "Ina xa ki tafi da daddaren nan" Nihal ta fizge Hijab dinta hawaye cike idonta ta nufi kofa, Nihad ta bi bayanta da sauri tace "Ke ni fa wasa nake maki ina zaki da daddaren nan" Tuni Nihal ta fice daga parlon, Nihad ta marairaice tana kallon Khalil tace "Don Allah kayi mata magana, ni wallahi ba haka nake nufi ba" Ko kallonta Khalil bai yi ba, hakan yasa ta fita da sauri, can ta tarar da Nihal zaune bakin gate dake kulle tana rera kuka, kukan ta ita ma ta fara ta durkusa gabanta tace "Don Allah kiyi hakuri wallahi i didn't mean it, ni ba da ke nake ba, da shi nake"
TWINS NEEE.....