💖💖 *NIHAAD*💖💖
29
Suna fitowa parlor Nihad na kallon khalil cikin kuka tace "Don Allah ni ka barni in je in gaida Umma" Juyowa yayi yana kallonta yace "Akwai wata Umma bayan warce kike gaida da muka shigo daxu?" Muryarta na rawa tace "Toh kawai a parlor xan gaisheta?" Yace "Eh" Kuka kawai take tana kallonsa ta wuce sa kamar xata tashi sama ta nufi kofar fita parlon, bin bayanta yayi ya sameta jikin mota tana kuka kamar ranta xai fita, ya zaga driver seat ya bude ya shiga, bude bayan motar tayi ta shiga don ita har yanzu Drivern gidansu ne shi, Aminu ya marairaice bayan Khalil ya fito da mota waje yace "Ina ta rokon Saminu ya jira min gate in kawo maka ziyara amma ya ki..." Khalil na kallonsa yace "Wataran ma baxa kayi gadin ba gaba daya, sannan matsayinka xai dawo dai dai da na kowa a duniya" Aminu ya daga hannu biyu sama yace "Allah Ubangiji ya amsa bakinka, Allah ya dubemu yanda ya dubeka lkci daya, wannan gagarumin ci gaban da ka samu Allah ya sa mu a danshinka, wayyo wa yaga Aminu ya daina gadi, duk basur ya cinye ni sbda zama kan benchi daga safe har dare, na ma ji Alhaji yace xa a dubo sabon driver tunda kai yanxu ai ba batun tuki kuma" Murmushi kawai khalil yayi ya sa hannu a aljihu ya ciro dubu daya ya mika masa yace "Ga wannan ka sha kankana" Aminu ya karba hannu bibbiyu yana cewa "Allah ya taimakeka oga" Wani shegen kallo Nihad ke ma daga Khalil din har Aminu tana jin kamar ta hadiye zuciya don takaici, nan ta kara jin wani sabon tsanar Khalil ya dirar mata, wato fafa yake yi sbda Abba ya aura masa ita, ji yake babu ya shi a duniya, Bayan sun bar layin tana kallonsa ta madubi tace "Kai yanzu kawai jin kanka kake saboda Abbana ya daukeni ya aura maka ko? Gani kake ka fi kowa sa'a a duniya tunda yanxu kudin da Abbana ke baka ya ninku linkin ba linkin har da su kyautar dubu daya, shkkn xaka dinga amfani da ni kana cin kudin Abbana" Khalil yayi wani murmushi bai tanka ta ba, ta murguda baki tace "Ai shi dama talaka bai iya samun waje ba, nasan yanxu alfahari kake yau gani matarka ko?" Yace "Ohk" Ta kara murguda baki bata kuma ce masa komai ba har suka isa gida, sauka tayi daga motar bayan ya bude gate tayi shigewarta ciki kamar xata tashi ciki, yayi wani murmushi kawai ya motar ya shigar da shi compound din. Bayan Nihad ta idar da magrib ta fito parlor ta samesa kwance saman dogon kujera yana waya, ganin bai lura da fitowarta ba duka a hankali ta rarrafa har bayan kujeran ta kasa kunne tana sauraron wayar da yake yi, A hankali taji yace "Nan da wata daya in sha Allah xan dawo, idan kuma na dawo baxan sake fita ba sai bayan aurenmu" Yana fadin haka babu sunan da ya fado ran Nihad sai Nadeeyah don har ta haddace sunan nata a xuciyarta, ta ɗan kyabe baki tana tsugunne bayan kujeran tana kara kasa kunne, Taji yace "Aa, akwai dalilin da ya sa na dade wannan karan Nadeeyah, ba wai da son raina bane, amma in sha Allah na kusa gama abinda nake yi, ni kaina na gaji da USA haka" Buda baki Nihad tayi hangangan jin sunan kasar da ya kira, Tunda aka haifeta bata ta6a ganin me lafta karya kamar wannan mutumin ba, wato USA?? Mutumin da ko ruwa ta kasa sha a garinsu balle ta ci abinci shine yake karyan yana USA, ya ma san full meaning din USA din kuwa?? Taji yayi dariya ya mike zaune yace "Wai da gaske??" Magana yake amma bin parlon kawai yake da idanuwansa don banda kamshin Nihad babu abinda yake ji a parlon, amma kuma bai ga alamarta ba, don haka ya koma ya kwanta a hankali yace "Ke ce farko kece karshe Nadeeyah, in sha Allah baxan hada ki da kowace mace ba, don kin min hallacin da baxan manta ba, in dai kuma ba baturiya kike son in auro mu dawo Naija tare in hada ku gida daya ku zauna ba, kinga ai nasan baxa kiyi kishiya da ita ba" bayan few seconds yayi murmushi yace "Ya na ji kin yi shiru?" Mikewa Nihad tayi tana tafe hannu tace "Ni wallahi ban ta6a ganin inda babba yake karya ba sai kai..." tuni Khalil ya katse wayar, ya mike tsaye yana kallonta, da mamaki Nihad tace "Kasan ma'anar USA kuwa? Kasan ina ne Usa? Me yasa baka tsoron yin karya a rayuwarka?" Yace "Kin karya daya daga sharadinmu don haka nima dole xan karya daya...." Yana gama fadin haka ya bar parlon ta marairaice ta bi sa da kallo har ya shige dakinsa, ta fi minti biyar tsaye parlon can dai ta bi bayansa, a hankali ta murda kofar dakinsa, tsaye ta gansa yana unbuttoning shirt dinsa, ta turo baki tace "Toh kayi hakuri" Ya juyo ya jefa mata wani kallo yace "Baxan yi" Ta marairaice tace "Don Allah mana" Bai sake kulata ba ya shige bandaki, ta ɗan kyabe baki, sai kuma ta dinga kallon wayar tasa dake gefen gado, tana tafiya a hankali kamar munafuka ta karasa gadon ta dau wayar, number Nadeeyah ta shiga tana kallon number tana ta6e baki, wai ba ma tayi blocking din number nan ba, wato unblocking yayi, tana dai ta kallon number, can ta ja tsaki kasa kasa ta kara blocking number tayi deleting ta ajiye wayar ta fita da sauri. Fitowa Nihad tayi dai dai sanda Khalil ma ya fito daga dakinsa, ta 6ata fuska tace "To ai cikin deal dinmu baka ce idan ana kwankwasa gate kai kadai ne xaka dinga xuwa budewa ba, nima xan iya fita in bude tunda ba kai kadai bane cikin gidan" Ba abinda yace mata ya nufi kofar parlor xai je bude gate din da ake ta bubbugawa kamar xa a cire, Nihad ta tafi jikin window dake parlon tana kallonsa har ya isa gate din, Yana tsaye bakin gate din yace "Waye?" A mugun fusace Umma tace "Uban me tambaya, nace uban me tambaya, halan gidan na ubanka ne idan ka ji an kwankwasa gate sai ka tambayi waye sannan ka bude?" Kawar Umma dake gefenta tace "Wai kaddai Dreban ne ke maki wannan tambayar?" Umma tace "Atoh ba matsiyaci bane? Kuma kin mance matsiyata basu iya samun waje ba?" Hajiya Turai tace "Aa ga alama" Umma tace "Ai kinsan gidan Ardo ko Nenne dake kauye ne shi yasa yake tambayar waye" Hajiya Turai ta kwashe da dariya tace "Sai dai haka kam" A mugun fusace Umma tace "Au, baxa ka bude min gate din ba??" Khalil yace "Me gyara yana hanya don tun jiya gate din ya samu matsala, mu ma bamu samu fita ba duk yau, don haka sai ku jira" Buda baki Umma da kawarta suka yi jin abinda yace, shi kam yana gama fadin haka ya juya ya bar bakin gate din ya koma ciki, Nihad na masa wani kallo tace "Waye a gate din da kaki budewa?" Yana kallonta da kyau yace "Warce kika yaudari kanki kika bai ma matsayin mahaifiyarki" Nihad ta zaro ido tace "Umma?? Shine kaki bude mata gate din?" Bata tsaya jin abinda xai ce ba a fusace ta taho xata fita daga parlon ta je ta bude ya fixgota, tana tsaye dab da shi yana kallonta da kyau yace "In har kina son mu rabu cikin salama ba tare da iyayenki sun yi fushi da ke ba ko an ga laifinki to kar ki tsallake umarnina ko daya, datse alqarki da warce kike kira da Umma yana daga cikin umarnina gare ki, bayan mun rabu xaki iya ci gaba da mu'amala da ita wannan ba matsalata bace, amma muddin muna tare babu ke babu ita" Nihad was shocked and lost of words at first, can dai tana girgiza tace "Amma kasan abinda kake cewa kuwa? Kasan warce kake cewa xaka datse alaqata da ita?? Kasan wacece Umma kuwa ko dai duk zamanka gidanmu baka san matsayinta ba? Matar Abbana ce fa? First wife din Abbana ce, She is my step mother, kuma duk duniya babu wanda ke sona baya ga ita, ban san dai ko Mumy da ta haifeni ba ba tunda ita bata ta6a nuna min son da take min a fili ba na Umma kawai na sani, Umma tun tasowata ban ta6a cewa ga abinda nake so a duniya an hanani a gidanmu ba, kome nake so shi nake samu, yanda Umma taga Abbana ke ji da ni haka ita ma tafi sa ji da ni, kuma bata ta6a hanani yin duk abinda nake so in yi ba tunda a ɓangarenta ma na taso, she is 100% in support of me always, ta daukeni kamar er da ta haifa a cikinta, dai dai da second daya bata ta6a banbanta ni da Nihal ba, don sai taki goyon bayan Nihal amma ni ta goyi bayana, ba kuma ta son bacin rai na ko na second daya, yanda na shaku da Umma ko Mahaifiyata ban shaku da ita haka ba wllh, don dama tun ina karama ta maidoni dakinta, ita ce komai na, amma shine yau xaka bude baki kace min xaka datse alakata da Umma?? Kana da hankali ma kuwa?" Kallon cikin ido kawai khalil ke mata, bai kuma ta6a jin tausayin rayuwarta ba sai a wannan lokacin, Ta fashe da kuka tace "In har a sharadin rabuwar mu har da datse alakata da Umma to kar mu rabu din, kai xaka wahala ba ni ba" Tana gama fadin haka ta kwace hannunta daga rikon da yayi mata ta shige dakinta, zaunawa khalil yayi saman kujera deep in his thought yana sake digesting duk abubuwan da Nihad ta gama fada masa..... Ana magrib Nihad taji fitar Khalil, tun da rana take kuka duk idanuwanta sun kumbura saboda ya hana Umma shigowa gidan, tana jin fitarsa ta fito bakin gate din sai taji ya sa makulli, ji tayi kamar ta kwanta wajen tayi ta birgima, ta dinga rera kuka kamar ranta xai fita a wajen. Khalil na zaune parlon Abba, ya gaishesa kansa a kasa, kallonsa kawai Abba yake yana son jin me ke tafe da shi, hoping ba wani abun Nihad tayi masa ba, Khalil yayi kasa da murya yace "Alhaji dama na zo neman alfarma ne gun ka" Abba na kallonsa yace "Ina jin ka Ibrahim, fadi koma meye kanka tsaye" Khalil yace "Ina son xan koma garin mahaifiyata can Zaria tare da ita... Saboda xan ɗan yi noma a can tunda damuna ya fadi" Abba yace "Yanzu ai karkashin ikon ka take Ibrahim, ba sai ka tambayeni izini ba don xaka canza wajen zama da ita, iyaka ka sanar min don in maku fatan alkhairi sannan idan da tallafawan da xan maku sai a maku" Khalil dai ya sunkuyar da kansa, Abba yace "Maa sha Allah naji dadin noma da kace zaka yi, don noma ai shine tushen arziki dama, Allah Ubangiji ya baka nasara Ibrahim" Khalil yace "Ameen Alhaji, nagode" Abba yace "Yanzu dai ka sa a bincika maka nawa ake bada hayan gida a garin" Khalil yace "Ina da wani aboki a can na tambayesa jiya" Abba yace "Nawa yace maka?" Khalil yace "Dubu dari yace min" Kallonsa Abba yake ba ko kiftawa, can yace "Aa da dai a samo na sama da hakan Ibrahim, ni ko nawa ne ba matsala bane xan bada" Khalil na kallon Abba yace "Gidan a kusa da kauyen da xan yi noman yake, shi sa nace xan amsa" Abba yace "Dubu dari nawa kace?" Khalil yace "Dubu dari daya" Abba ya kasa cewa komai yana kallonsa, Gaba daya tunaninsa na kan Nihad duk da haushinta da yake kwana yake tashi da shi a ransa yasan baxai ta6a son ta zama uncomfortable a rayuwarta ba, deep down him yasan he still love his daughter" Abba ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace "Shikenan zan sa maka kudin" Khalil yayi noticing change a muryar Abba hakan ya sa bai dago kansa ba, Abba yayi breaking few second silence da ya biyo baya yace "Yaushe xa ku tafi?" Khalil yace "Ko zuwa satin da xa mu shiga in sha Allah" Abba yace "Ohk to amma ka sa abokin naka ya ɗan bincika min ko za a samu filaye a nan arean" Khalil ya daga kai ya kalli Abba yace "Toh Alhaji" Abba yace "Ina sauraronka zuwa gobe da safe" Khalil yace "Toh in sha Allah" Daga haka yayi ma Abba sallama ya mike ya fita, ɗan murmushi yayi kawai ya fice daga main parlor. Yana fita parlon Umma ta shigo da sallama, bayan ta zauna tace "Bako kayi ne halan" Abba ya girgiza kai yace "Ibrahim ne" Umma tace "Allah sarki, haka dai kawai ka hanani zuwa gun 'ya ta in dinga duba halin da take ciki, yau kusan sati biyu kenan rabona da ita, wallahi kullum da ita nake kwana nake tashi a raina, in ji dai suna lafiya?" Abba yace "Lafiya lau, zuwa yayi min da wani batu" Umma ta gyara zama tace "Wani batu kuma, to Allah ya sa dai lafiya" Abba yace "Lafiya lau, wai zai je noma garinsu xai tafi da ita" Umma ta zaro ido tace "Ya tafi da ita ina?? Yaushe Nihad xata wani iya zama a garinsu? To sai kace masa me Alhaji?" Abba yace "Toh ai a yanzu dai ya fi mu iko da ita, babu ta yanda xan iya hanasa tafiya da matarsa Sumayya" Umma na girgiza kai tace "Aa Yallabai wannan ba magana bace, to ko dai ka sallama ma duniya er nan ne bamu da masaniya? Duk wannan punishment din da kayi mata na aura mata dreba bai isheka ba sai ka ba dreba goyon bayan tafiya da ita kauyensu da sunan noma? Haba Alhaji ko ba kai ka haifi er nan ba kaddarar nan ya fada mata ai ka ji tausayinta ka raga mata balle er cikinka ce kuma masoyiyarka, ina laifin kace ya kawota nan gida ta zauna har sanda xai gama nomar tasa ya dawo daga kauyen nasu?" Abba yace "Aa, ai mu ba kananun mutane bane da zance ya bar ta gida Sumayya, tunda har ya girmama ni ya zo neman izinin tafiya da ita ni kuma baxan yi karanta ba a matsayina na mutum me kamala a gunsa, yanxu dai nace ya sa a bincika min fili a inda xa su zauna din, ko nawa ne xan siya, idan ya so ko 3 bedroom flat ne in sa a gina babu bata lkci, don yana min maganan sun samu gidan dubu dari, dama akwai gidan dubu dari a zamanin nan?" Shiru Umma tayi tana kallonsa babu ko kiftawa, Abba ya daga kai ya kalleta jin tayi shiru, tayi murmushi tace "Maa sha Allah, gida xaka gina ma Nihad din a can kenan?" Abba yace "Hakan xai fi gaskiya, idan ma babu wuta garin a saka masu solar 24/7, sannan ayi borehole a gidan, ayi furnishing yanda ya kamata" Umma ta gyara zama tana Murmushi tace "Hakan yayi kyau kam gaskiya, Allah ya saka maka da alkhairi ya kara budi, kaga zata zauna comfortably baxata takura ba, har ma ta sake a gidan ta ji kamar a cikin gari take" Abba yace "Yeah!! So i think duka duka da filin da ginin ai baxai ci miliyan goma ko sha biyu ba ko?" Umma tace "Ehh to, xai iya zama hakan tunda ai ba cikin gari bane kila, balle ace filin xai yi tsada sosai" Abba yace "In sha Allah, ko zuwa gobe aka samu filin xa a daura gini kawai" Umma na Murmushi tace "Madallah, Allah ya kai mu goben, bari in je in gama abinda nake a sama" Abba yace "Alright" mikewa tayi ta fita daga parlon. Yau ma kamar jiya ana kwankwasa gate Nihad da Khalil suka fito a tare, bai ko kalleta ba har ya fita, ta bi bayansa don wannan karan sai dai duk abinda xa ayi ayi a bakin gate din in dai Umma ce sai ta bude mata, Ya hade rai ya juya yana kallonta yace "Meye kike bi na?" Ita ma ta hade rai tace "Kayi tafiyarka inyi tawa mana" ya ci gaba da tafiya tana bin sa har suka iso gate din, yace "Wanene?" Husnah tace "Assalamu alaikum" Ya wani hade rai yace "Nace waye?" A hankali tace "Husnah ce" Nihad ta hade tafin hannunta kamar xata yi kuka tace "Don girman Allah kayi hakuri ka bude mata, ni kenan sai inyi ta zama babu wanda ke xuwa wajena kamar mayya,x kuma ai a sharadinmu nace baxa ka ki barin kawayena su zo wajena ba kuma ka yarda" Kallonta kawai yake, nan da nan hawaye ya cika idonta tace "Don Allah fa nace maka" Duk Husnah na jin su ita kanta addu'a take Allah ya ta6a zuciyar Khalil ya bude mata gate din, Juyawa khalil yayi ya bar wajen, Nihad ta wara ido cike da farin ciki ta bude gate din, tayi tsalle ta rungume Husnah tace "Wallahi nayi missing dinki kawata, ina su Naf da zully?" Husnah tace "Ba su ma san xan zo nan ba wallahi, tun shekaranjiya kike raina in gaya maki, shine kawai nayi tahowata ban gaya masu ba" Nihad ta kulle gate din tana Murmushin jin dadi ta kama hannun Husnah da ta bi khalil da kallo har ya shige parlor, suna isa balcony Husnah tayi kasa da murya tace "Amma dai kawai in gaida mutumin nan don gobe ma ya barni in shigo, kinsan abun sai da siyasa kawata, barin ma shi da yake ɗan kauye gaishesan da xanyi yanxu xa ki ga farin cikin da zai yi kansa yayi kato, kinsan bakauye akwai son girma" Nihad ta kyabe baki tace "Kar ki wani gaishesa, meye hadinki da shi ko ina ruwanki da shi bayan ba wajensa kika zo ba, ni kaina da nake gidan ban ta6a gaishesa ba saboda bai isa ba balle ke" Nihad na gama fadin haka ta ja hannun Husnah suka shiga parlon, Husnah na hada ido da shi ta janye hannunta daga na Nihad dake jan ta zuwa daki, ta dan yi murmushin yake tace "Ina wuninmu?" A fusace Nihad ta ja Husnah fuuu suka wuce daki ta kulle kofar tace "Amma ba nace kar ki gaishesa ba? Meye amfanin gaishesa yanzu?" Husnah ta yatsine fuska tace "Ni kaina wllh sai bayan da na gaishesa naga rashin dacewan hakan, baki ga ma wani shan kamshi da yake shi a dole ya aureki ba, yanzu fa ji yake shi wani shege ne ya auri er mai kudi" Nihad tace "Ke mu fa mun riga mun ajiye deal kan cewa xai sakeni, na amince shi ma kuma ya amince ya kuma yarda ni ba class dinsa bace" Husnah ta zaro ido tace "Haba??" Nihad tace "Wallahi in gaya maki, ai yaga tsanar da nake masa tayi yawa baxan kuma ta6a raga masa ba shi yasa yaga gwara mu rabu..." Husnah tace "Yanzu yaushe yace xai sake kin?" Nihad tace "Ku dai kawai ku zuba ido ku ga ikon Allah" Husnah tace "Kai amma na tayaki murna wallahi, ashe shegen ya san abinda yake yasan ke ba class dinsa bace cikin ruwan sanyi xai rabu da ke" Nihad ta tuntsire da dariya tace "Wallahi fa in gaya maki" Husnah ta cire Hijab din jikinta ta jefar kan gado, Nihad tace "Yaushe kika dinka hijab ke da baki da ko guda daya" Husnah tace "Wannan ma a hostel na aro shi, ke akwai abinci yunwa nake ji" Nihad tace "Ehh daxu nayi stew, kawai spaghetti xan yi boiling" Husnah tace "Toh bari in yi boiling dinsa, akwai a kitchen ai?" Nihad tace "Ehh akwai" Mikewa Husnah tayi ta bude handbag dinta ta fiddo after dress ta daura a kan riga da wandon jikinta ta fita, Nihad ta jawo jakarta bayan ta fita ta bude, as usual kayan maye iri iri ta ga a jakar da Prophylactics dinta, Nihad ta mayar mata da kayanta ta dau wayarta da ta gani ta bude password don tasan password din nata, har tayi dialing number Aliyu sai ta tuna ba shi da number Husnah don haka baxata samesa ba, lkci daya jikinta yayi sanyi, sai dai kawai tayi dialing number Umma, Umma na jin muryata tace "Daughter, ina ta tunanin ta yanda xanyi waya dake tun jiya wllh, har cewa Nihal ta kai maki waya gida nayi amma er nan taki, Amina kuma kinga tunda ana hutu islamiyya take safe da yamma ita ma baxata yarda tayi fashi ba don in aikota wajenki" Nihad ta marairaice tace "Nima babu ta inda xan kira ki Umma" Umma tace "Kina ji na?" Nihad tace "Ina ji Umma" Umma tace "Kullum nayi sallah ina saka wannan tsinannen dreban a addu'a kan cewa Allah Ubangiji ya rabaki da shi cikin aminci, to sunansa kawai na sani ban san sunan mahaifinsa ba ko uwarsa" Nihad tayi shiru, sai kuma tace "Nima wallahi ban sani ba Umma" Umma tace "Yo ai nasan baki sani ba, ke baxa ki iya dubara irin na mace ba ki tambayesa sunan ya gaya maki, sai kace ba wayayyar Nihad dita ba, ai cikin salo irin na wayayyun mata zaki bi masa har ya gaya maki" Nihad tayi Murmushi tace "Toh shikenan Umma" Umma tace "Yauwa zuwa yaushe xan saurareki?" Nihad tace "Gobe" Umma tace "Amma number waye wannan?" Nihad tace "Na Husnah ne" Umma tace "Au tana can shegen ya bar ta ta shiga kenan" Nihad tace "Wallahi kuwa Umma" Umma tace "To yaushe xata tafi?" Nihad tace "Kamar fa kwana xata yi naga kaya kala biyu a jakarta" Umma tace "Madallah dai dai kenan, kinga gobe sai ki kirani kawai ta wayar nata" Nihad tace "Toh Umma" Daga haka Umma tayi mata sallama Nihad ta katse wayar, dai dai nan taji Husnah tayi wani kara, ta mike da sauri ta fice daga dakinta, Tana fita parlor Khalil na shiga kitchen din, ita ma ta nufi kitchen din da sauri.
TWINS NEEE
BIYU TA FI DAYA