💖💖 NIHAAD 💖💖
35
Khalil na isa hotel din ya nufi dakin direct ya bude kofar, sosai ya ji gabansa ya fadi ganin babu kowa cikin dakin, da sauri ya karasa ciki yana kallon abincin da ya ajiye mata yaga ko ta6awa bata yi ba, lkci daya yaji zufa na keto masa, kallon kofar bandaki yayi nufi can da sauri ya bude kofar nan ma babu ita a ciki, nan yaji hankalinsa ya kara tashi ya fice daga dakin ya sauka kasa yana kallon receptionist din wajen yace "Don Allah yarinyar da muka shigo dazu..." Kafin ya karasa receptionist din tace "Ta fita ai" kasa daina kallonta yayi, yayi karfin halin cewa "Ta fita? When pls?" Matar tace "Some minutes ago" juyawa yayi da sauri ya nufi kofar fita daga cikin hotel din, receptionist din ta bi sa da kallo, Khalil na fita bakin titi yana waiga gefensa ya ganta can zaune daga jikin hotel din kamar marainiya, lokaci daya ya hade rai ya nufeta, ita bata ma lura da shi ba tayi nisa cikin tunanin da take, yana isa dai dai inda take yace "Baki da hankali ne zaki fito nan bayan kinsan jakata na dakin?" Ta daga kai ta kallesa, sae kuma a hankali tace "To ba kai nake nema ba" yace "Me yasa zaki nemeni? Saboda me?" Ita dai bata ce komai ba, sai a sannan ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, ya juya ya bar ta wajen, ordering wani bolt din ya mayar da wayarsa a aljihu ya juyo yana kallonta yace "Ki jira ni a nan" Daga haka ya koma dakin don dauko jakarsa, yana fitowa sai ga motar, bayan sun gaisa da drivern ya sa jakarsa a booth, ya juya ya kalli Nihad dake kallonsa, ai bata ma jira yace ta taso ba ta taso ta nufosa, ya zaga ta daya side din ya shiga motar, tana dai ta tsaye, jin bai ce mata komai ba ta bude bangaren da take tsaye ta shiga ta jawo kofar motar a hankali. Kamar me Bolt din dazu wannan ma sae da ya tambayi khalil ko zai iya shiga ciki ganin unguwan da suka zo, Khalil ya sauke glass din side dinsa ya daga ma securities din wajen hannu sannan suka wuce, Nihad dai tun da suka shigo anguwan nan take kalle kalle uwa idanuwanta za su fito, she is wondering where he is taking her to, duk inda suka wuce sai taga securities, very tight security, bata ta6a jin tsoron kasancewa da Khalil ba sai wannan moment din, she looked at him looking very afraid, to ko dai inda ake yankan kai ma zai kaita, sosai gabanta ya dinga faduwa hankalinta yayi mugun tashi, ta dinga kallon Mad houses din da suke ta wucewa na masu kudi da suka amsa sunan su kudi a kasar, hakurin Nihad ya soma karewa ta juya a hankali ta sake kallon Khalil for the 5th time, gabansa kawai yake kallo fuskarsa babu yabo babu fallasa, Ai bata san sanda ta marairaice masa ba cikin rawan tace "Don girman Allah ina zaka kai ni? Don Allah kayi hakuri ka rufa min asiri, ina ne nan ka kawo ni?" Sai ta sakar masa kuka a hankali jin ya ki ce mata komai, shi dai ko kallonta baya yi, ko ma wanene yanda Khalil yayi keeping serious and straight face sai ya tsorata balle Nihad da dama can matsoraciya ce, Shi kam drivern bolt din slowly yake tafiya sbda Securities that are everywhere don zuwa lkcn gari yayi duhu, amma sai kayi tunanin rana ce don ko ta ina haske ne tarr, har dai suka isa dai dai gidansu Khalil, sai dai ba ta inda ya shigo dazu bane, wannan second gate din gidan ne dake ta baya, drivern ya tsaya yana duban ma'aikatan da suka nufo motar gadan gadan, Khalil ya bude motar ya sauka, suna ganinsa suka gaishesa suna komawa baya, Ganin Nihad taki saukowa daga motar ya zaga ta inda take ya bude motar yana kallonta babu yabo babu fallasa yace "Malama kina bata masa lokaci" Ta marairaice tana kallonsa cikin rawan murya tace "Don girman Allah ina ne nan din ka kawoni, kayi hakuri ka gaya min" Gaba daya tayi zuru zuru da ita kamar ba Nihad ba, shi dai kallonta kawai yake, can yace "Neman taimako na zo yi nan din, tunda kin ga bamu da inda za mu je" Ta gwalo ido sosai tana kallonsa da mamaki, can tayi karfin halin cewa "Taimako kuma? Unguwar masu kudi ne sosai fa, ba kowa ne ke shigowa nan ba wallahi, kuma ko kallonmu baxa su yi ba sai ma su kore mu ko su sakar mana karnuka, wllh ka shigo idan ba haka ba securities din nan za su iya sa mu tsallan kwado yanzun nan" ya dafa motar yana kallonta da kyau yace "Sa'armu za mu gwada, kuma ni nasan ina da sa'a sai in ke ce baki da, Malama ki sakko kina bata ma me mota lokaci" Da sauri Nihad ta kalli me tukin motar dake jiranta ta sauka patiently, can ta kalli khalil pleadingly tace "Ni dai don Allah ka zo ka shiga mu koma, babu abinda za su mana a nan" Yace "Idan muka koma kina da kudin da za mu ci abinci gobe? Ko kina da kudin da zaki sake biya mana daki a hotel din?" Kallonsa ta dinga yi, lkci daya jikinta yayi sanyi, hawaye ya kawo idonta, sai kuma ta sa hannu ta share idon nata a hankali tace "Sai ka bani waya in kira ya Farooq nasan zai turo mana kudi" Yana kallonta yace "Aa, wannan gidan dai nake son shiga in gwada sa'a ta" Ta kallesa zata yi magana ya hade rai yace "Kina bata masa lokaci malama" a hankali ta sauko daga motar tana kallon Khalil hawaye na bin kuncinta, ya daga ma mai bolt din hannu ya ja motarsa ya bar wajen, cikin kuka tace "Toh ni dai da kace ya maida ni in jiraka a can hotel din, in ya so kai kadai sai ka shiga gidan" Wani kallo yayi mata ya nufi gate din gidan da tuni aka bude masa, Ta gefen ido take kallon securities din gabanta na faduwa don wasu dirka dirkan bayin Allah ne, can dai tana ganin Khalil ya shiga cikin gidan ta bi bayansa da sauri, ga mamakinta basu kulle ba suka jira har ta shiga sannan suka rufe gate din, Nihad ta dinga bin makeken compound din me dauke da wani ubansun mansion da kallo, kai kana ganin gidan nan kawai kasan ba karya malam, Compound din kuwa yayi ukun nasu ga parking lot kaca kaca, ko wanne da ride lafiyayye a parke, ita bata ma san ta bayan gidan suka shigo ba, don ta can ne zata ga ainahin kyan gidan, chalet da aka yi can gefe da ta hango kuwa ya kusa nasu main building din, tafiya kawai yake tana binsa zuciyarta na bugawa, but how comes yana ta tafiya kansa tsaye and nobody is even stopping him, taga sun zaga ta baya ya shiga wani stairs wanda aka shimfida ma carpet grass, shi kansa tsakar gidan wajen duk malale yake da Carpet grass din, bude wani kofa yayi bayan sun haura sama sun mike wani babban corridor, ya bude wata kofar duk tana biye da shi a baya a tsorace, ko nisa bata son yayi mata, gaba daya she is really confused at how he is just badging in babu shakka ba komai, ita tsoronta kada a kama su ayi masu dukan tsiya, da ido ta dinga bin parlon da ya shiga tana makale bakin kofa ta kasa shiga zuciyarta na bugawa, Can taga ya shiga wata kofar da sauri ta bi bayansa ko kulle kofa bata yi ba, nan taga kofar da ya shiga wani parlon ne wanda ya fi wanda suka baro haduwa, at this point, she is super confuse, bayan ya isa kofar dakin Maminsa ya juyo yana kallonta, ya fi second goma yana kallonta wanda hakan ne ya kara mugun tsoratata, can kuma babu yabo babu fallasa yace "Zauna nan" Ta kasa zama har taga ya shiga wani kofar, Mami na nan zaune yanda khaleel ya bar ta don ta kasa samun nutsuwa, gani kawai take shikenan kuma baxai sake dawowa ba, gaba daya jikinta a sanyaye yake har zuwa yanzu da ya shigo dakin nata, da sauri ta mike ganinsa with happiness written all over her face ta nufesa kace "U kept to ur promise son, baka wuce awa dayan ba, i was so worried ina ga kamar tafiya ka kara yi...." Yayi Murmushi ya kamo hannunta a hankali yace "Amma bana son ki saka rai da yawa ki sakankance a kan cewar na dawo in zauna Mami, kar ki manta ban san kiran me Abba ke min ba, he might still not be needing me in his house, kilan idan ya gama fada min abinda zai fada xai iya cewa in bar masa gidansa and i don't have choice...." Hawaye ya shiga sakkowa idon Mami tana girgiza kai tace "Baxan yarda da hakan ba this time around son, sai dai duk abinda zai faru ya faru, shirun da nake masu ya zo karshe, baxan sake shiru ba in har yace ka bar masa gidansa for the second time" Shi dai khaleel bai ce komai ba sai kallon mahaifiyar tasa yake cike da tausayinta, kamar yanda take ganin ya rame, shi ma haka yaga ta rame saboda damuwa, Can Mami ta share idonta da sauri tace "Where is the young gal?" Ya kalli kofa yace "She is at the parlor" Mami tace "Ohk" Daga haka ta nufi kofar ta fita ya bi ta da kallo, zaunawa yayi gefen gado ya rike kansa, yasan ko me zai faru baxai samu courage din sanar masu ai Nihad yarinya ce da babanta ya aura masa ba, shi kuma ya amshi auren nata ba don ransa ya so ba sai don ganin girma da mutuncin mahaifinta sannan baxai iya turning down din offer din mahaifinta ba, yasan baxai ta6a fara masu wannan bayanin ba, fadawa saman gadon yayi ya kwanta ya lumshe ido yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mami na fitowa parlor taga Nihad a tsaye bakin kofa tana shesshekan kuka, tun bayan da taga khaleel ya mata wannan kallon sannan ga shiga kofar ya kulle tayi saurin komawa bakin kofar fita parlon ta tsaya zuciyarta na raya mata shikenan babu wani tantama ya kawota ne kawai a gille mata kai ayi kudi da ita, dama masu kudin nan wasun su kowa yasan ai suna yankan kai, to kila mai gidan ya ba khaleel contract din samo masa kan da za a gille shi yasa har ya shigo gidan tare da ita babu wanda ya hanasa, sai ma bude masa kofa da securities din suka yi har da masu gaishesa, irin dai ya saba shigowa gidan kenan, sannan gashi taga kansa tsaye ya taho bangaren nan da ita, wato in da za a gille mata kan kenan, uwa uba tun da suka shigo gidan bata ga ko wani mutumin ba sai securities, Da mamaki Mami ke kallon Nihad ganin yanda take hawaye tace "Subhanallah, Baby are you okay? why are you crying?" Kallon matar kawai Nihad take hawaye na sauka idonta kuma taki ce mata komai, wannan ba ita ce ta gani a hoto ranan a dakinsa ba? Mami tace "C'mon, come in dear...." Nihad taki karasowa sai kallonta take, Mami na ganin haka ta juya ta koma dakinta ta shiga tana kallon Khalil dake kwance saman gadonta da mamaki tace "Khaleel na ganta tsaye bakin kofa tana kuka, is she okay? Nace ta shigo kuma ta ki" Mikewa Khalil yayi ya fita parlon Mami ta bi bayansa, yana kallon Nihad, ya dake yace "Shigo ciki" Mami ta karasa inda take tsaye ta kamo hannunta ta shigo da ita parlon tana kallon Khalil murya can kasa tace "Doesn't she understands English?" Bai ce komai ba ya juya ya koma dakin, Mami ta zauna gefen Nihad da ta zaunar edge din kujera kamar me shirin fillawa da gudu, tace "Ya kike yan mata?" Nihad ta goge idonta tana kallonta a hankali tace "Ina yini" Mami na Murmushi tace "Alhamdulillah, ya su mamanki?" Nihad ta sauke idonta kasa cikin sanyi tace "Lafiya lau" Haka kawai Nihad taji hankalinta ya ɗan kwanta ganin Mami, Mami ta kwantar da murya tace "Ki saki jikinki kinji, nan ma duk gida ne" Nihad ta kasa ce mata komai, Mami tace "Kin yi sallan magariba?" Nihad ta girgiza mata kai, Mami tace "To ga banɗaki kije kiyi alwala, bari in kawo maki darduma a bedroom yanzu" Nihad ta mike ta tafi kofar da Mami ta nuna mata a parlon ta bude a hankali tana kallon ciki, bandakin ya kusa girman dakinta, ta karanto addu'ar shiga banɗaki a ranta sannan ta shiga, Mami ta mike ta tafi daki ta ga Khalil ya dauro alwala ya fito, area din da Mami tayi demarcating a dakin don yin sallah ya nufa, Mami ta dau ma Nihad darduma daya ta kai parlor ta shimfida mata, sannan ta koma dakin ta shiga bandaki ita ma ta dauro alwalan, Khalil na zaune saman darduma yana azkar bayan ya idar da sallah, Mami ta mike bayan ita ma ta idar tana kallon side din da yake tace "Yanzu abincin xan dauka in kai can parlon, ko ta shigo nan kawai ku ci?" Yace "Ki deba kawai ki kai mata can parlon Mami" Mami tace "Ai ban san abinda tafi son ci ba, kawai bari ta shigo ta yi serving kanta ko?" Mami na fadan haka ta fita zuwa parlor tana kallon Nihad dake saman darduma tayi kuri da ido tace "Baby shigo ki ci abinci" Nihad ta mike a hankali ta tafi kofar dakin ganin taki shigowa Mami tace "Shigo mana" Cikin sanyin murya tayi sallama ta shiga dakin, ta dinga bin abincin dake jibge a kasa da kallo kamar za ayi party, Mami tace "Ki duba duk abinda kike so ki diba" Mami na fadan haka ta fita daga dakin, Nihad ta durkusa tana kallon Khalil, murya can kasa tace "Don Allah ina ne nan ka kawo ni?" Sai a sannan Khalil ya kalleta tun da ta shigo dakin yace "Inda za a mana alfarma ba tare da an walakanta mu ko an ci zarafinmu ba, ba kuma tare da an damu da mu talaka ne ko masu arziki ba" Shiru tayi tana kallonsa, ya mike ya zauna gefen gadon yace "Debi abinda zaki deba ki fita" Ita dai ta kasa cewa komai kuma ta kasa bude ko warmer daya balle ta zuba abincin, Mami ta dawo dakin rike da teapot da cups dinsa biyu a tray, da mamaki ta ke kallon Nihad bayan ta ajiye tray din hannunta tace "Baki debi abincin ba" Sai kuma ta kalli khalil kafin tace komai ya kirkiri murmushi yace "Haka take Mami" Nihad ta daga kai ta kallesa, Mami tace "But why? pls tell her to feel free" Khalil ya maida idonsa kan tv dake aiki silently bai ce komai ba, Mami ta dau plate ta debar ma Nihad shinkafa da miya ta ajiye mata, ta debar mata duk wani abu da xata dibar mata sannan ta mike, Nihad dai bata ta6a jin she is confuse kamar yanda take ji yanzu ba, gaba daga kanta ya kulle ta kasa fahimtar komai, lkci lkci sai ta kalli khalil sannan ta kalli Mami, Mami na kallon Khalil a hankali bayan ta gama zuba ma Nihad abinci tace "When did you say he called you?" Khalil ya kalleta duk da ya gane wanda take nufi yace "Ke baxa ki ci abincin ba Mami? Ki zuba mana tare mu ci" Mami tace "Talk to me son, he is back now" Sai da gaban khalil ya fadi ya mike yace "Really? But hope you didn't...." Sai kuma yayi shiru, ta gefen ido ya kalli Nihad da ta kafesa da ido babu ko kiftawa, sai kuma ya fice daga dakin, Mami na kallon Nihad da murmushi fuskarta tace "Ki ci abinci kin ji Baby" Daga haka ta juya ta bi bayansa, Nihad ta bi su da kallo bata kwakkwaran numfashi, bayan kusan minti sha biyar Khalil ya dawo dakin shi kadai, har sannan Nihad na zaune position din da take kamar warce ruwa ya cinye, gaba daya jikinta yayi sanyi qlau kana mata kallo daya zaka gane hakan, Ta bi sa da kallo har ya dau teapot da cup zai fita, cikin sanyin murya tace "Ka gaya min, wanene kai?" Bai yarda ya kalleta ba yace "Driver!!" Daga haka ya fice daga dakin, ta bi sa da ido babu ko kiftawa, abinda ya fada dazu da turanci ne ke kai komo a ƙwaƙwalwarta, lokaci daya ta runtse ido ko zata samu saukin sara mata da kanta ke yi. Khalil na zaune parlor sai ga Mami ta shigo tana kallonsa, shi ma kallonta yake, a hankali tace "Kaje wajen Abbanka, yana kiranka parlonsa" Khalil ya kalleta looking so worried yace "Mami da baki ce masa na dawo yau ba" Mami ta girgiza kai tace "I never told him, tun daga gate ya tambaya securities, su suka sanar masa kana gidan nan....." Yayi kasa da murya yace "But bana son kowa ya san am around Mami" Mami tace "Zaka iya zagawa ta baya ai, har yanzu babu wanda yasan kana gidan nan" Mikewa yayi ya nufi kofa yana tafiya a hankali ta bi sa da kallo har ya fita.
TWINS NEEE.....