Nihaad page 40 by Khaleesat Haiydar complete

Nihaad page 40 by Khaleesat Haiydar complete

 

Nihaad page 40 by Khaleesat Haiydar complete

πŸ’–πŸ’– NIHAAD πŸ’–πŸ’–

40

NIHAAD

Umma ta shigo dakin da taga Nihal ta shiga for almost ten minutes bata fito ba, wato dakin Nihad, dube dube ta sameta take yi a dakin, tun da Nihal taga shigowar Umma ta dakatar da abinda take ta zauna gefen gado, da mamaki Umma tace "Me kike nemar mata a daki tun daxu?" Nihal dai bata ce komai ba, Umma ta kyabe baki tace "Ke idan fa kika ce xaki tafi makaranta a haka ba tare da kin saki ranki kin dawo yanda kike harkokinki da ba to ina me tabbatar maki zaki samu matsala a makaranta wannan time din, abinda baki ta6a ba, eh ansan er uwarki ce kuma ba dadi to amma so kike ki targada naki future din ne? Ko damuwar nan ne xai dawo maki da Nihad, to ma ta dawo ta maki me? yarinyar da ke can kauyen mijinta" Ita dai Nihal bata ce komai ba still kuma bata kalli Umma ba, Umma ta kara kyabe baki ta karaso ta zauna gefen gado tace "Ba kwanaki can kina da number shi dreban ba, ni da ma kin kirasa in ji ko kauyen nasu na nan garin suka tafi ko Zarian ya tafi kauyen uwarsa da yace" Nihal dai bata ce komai ba, Umma tace "Ba da ke nake ba kika min shiru Nihal?" Nihal ta daga kai ta kalleta, sai kuma tace "Bani da number sa" Umma tace "Toh amma ai farooq bazai rasa ba tunda shi ma Allah ya zuba masa shisshigi kira min shi ki tambayesa yanzu ina jira" Nihal ta dau wayarta tayi dialing number Ya Farooq ta sa handsfree, yana fara ringing ya daga bayan ta gaishesa tace "Yaya wai kana da number Khalil?" Farooq yace "Wa ke tambayar numbersa?" Duk da alamar da Umma ta dinga yi mata kan cewar kar tace ita ce ke tambaya amma Nihal bata kalleta ba tace "Umma ce" Farooq yace "Noo bani da shi, sai anjima" Tace "Toh sai anjima" Katse wayarsa yayi, Umma ta hade rai tace "Akan meyasa xaki ce masa ni ce ke nema?" Nihal tace "Nima na tambayesa Shekaranjiya yace bashi da, don ki tabbatar da hakan yasa na sake kiransa amma ni nasan bashi da number" Umma tace "Toh ai shikenan, dama wai da sai mu ji kauyen da suke, in ya kama mu je sai mu je kafin ki koma makaranta" Daga haka ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin, Nihal ta mike ta ci gaba da duba takardun da take. Ranan asabar da rana khalil na zaune parlon Mami sai ga kiran ya Farooq gaba daya ya mance sun yi waya few days ago yace masa xai shigo zaria, Ya Ι—an kalli Mami dake parlon, bai daga wayar ba har ya katse, Ya farooq ya sake kira, mikewa yayi ya nufi kofa yace "Mami sai later" Daga haka ya fita daga part din gaba daya sannan ya kira Ya farooq, ya farooq na dagawa bayan sun gaisa ya sanar masa zai taho zaria from kaduna, Khalil yace "Ohk amma kaga muna gidan wata kanwar Baabata mun je gaisheta" Farooq yace "A ina kenan?" Khalil yace "A Abuja take" Farooq yace "Ohk, babu damuwa Usman na Abuja, so xai je inda ku ke in sha Allah" Khalil bai iya yace masa komai ba da farko, can kuma yayi saurin cewa "Toh Allah ya kai mu" Farooq yace "Zan tura maka numbersa yanzu ko da xai kiraka" Khalil yace "Ba damuwa" Daga haka suka yi sallama, kamar ance ya daga kansa ya ga Farhana a tsaye tana sauraron wayar da yake, ya hade rai yace "Ke ya kika tsaya min a kai?" Bata ce masa komai ba tana rungume da laptop dinta ta wuce tana ta6e baki, ya bi ta da wani mugun harara. Khalil na shirin xai fita da yamma sai ga kiran number da Farooq ya turo masa daxu, wato number Usman, yayi jim yana kallon wayar, can ya daga ya kai kunne, gaisawa suka yi, Usman yace "Yauwa wani anguwan ne a Abuja?" Khalil ya Ι—an buda ido sai kuma yayi saurin cewa "Bari in tambaye Kanwar Baabar tawa" Usman yace "Ohk ina jira" Katse wayar yayi yana tunanin abinda xai yi next, bayan ya gama shiryawa ya fito zuwa bangaren Mami sannan ya kira Usman, yana dagawa yace "Tace Suleja ne" Usman yace "Ohk, akwai tazara sosai tsakaninmu, amma idan na shirya zuwa zan kiraka" Khalil ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Toh Allah ya kai mu" Usman yace "Ba Nihad din wayar mu gaisa" Khalil yace "Idan na shiga gida xan kiraka yanzu ina waje" Usman yace "Alright" Daga haka ya katse wayar, Mami da ta fito parlon tana kallonsa tace "Waye a Suleja?" Yace "Wasu ne" Tace "Ohk" Sannan ta zauna saman kujera a hankali tace "Ina son za mu yi wata magana da ke damuna Khalil" Ya kalleta yace "Toh ina ji Mami" Tayi kasa da murya tace "It's High time kayi settling down son, tun baka bar gidan nan ba almost 2 years ago Abbanka ke maka magana har Allah ya kaddara tafiyarka, babban burina a rayuwa a yanzu shine in ga kayi aure...." Khalil ya sauke ajiyar xuciya yace "Mami kinsan fa she aure lokaci ne, idan time din yayi sai kika nayi Mami...." Tace "I am not talking about you settling down wai saboda ina son ka auri Nadeeyah, No son, idan da wata warce kake so daban fine, present her to us xa mu yi accepting as far as tana da tarbiyya, i can never force u on marriage son, kar kaga ko Nadeeyah yar aminiyata ce shi sa nake so ka aureta, a'a idan dai kasan da wata warce kake so da aure go ahead ka nemi aurenta just make sure yar gidan mutunci ce me tarbiyya ce like i said, sannan she should be from a reputable family, ka dai san halin Abbanka ai" Khalil yayi murmushi yace "Toh Mami ai ba ke kika hada mu da Nadeeyah ba, i met her abroad without knowing she is ur friends daughter, ba ta dalilin ke da Mumy muka san juna da ita ba, kawai Allah ne ya hadamu..." Mami tace "Haka ne, amma kaga ai yan sa ido gani suke mu muke cusa maka ita ka aura, don ta Hajiya Safeenah ma ta fi son Nadeeyah tayi aure a can Yemen tunda danginta suna can, kuma dama ita a can din ta tashi" Khalil yace "In sha Allah, as soon as i come back from this business trip xan kai ma Abba batun Mami.... Nima ina son settling down" Mami tace "Toh Allah ya nuna mana, amma kwana nawa xaka yi a can?" Yace "It depends, but nasan baxan wuce wata daya ba, but duk sati xan dinga shigowa Nigeria" Da mamaki Mami tace "Duk sati kuma? Me xaka dawo yi kai da ya kamata ka zauna can har ka gama abinda ya kai ka" Khalil yace "Bana son xama can har na wata daya, duk weekend xan dinga dawowa" Mami tace "Toh shkkn, amma ka sanar ma Abban naka?" Ya girgiza kai yace "He said i should do what suite me" Mami tace "Toh Allah ya tsare ya baka nasara" Yace "And one more thing Mami, ki amsar min Cv's dina and my assets that he clutch" Mami tayi kasa da murya tace "No, kai ya kamata kayi masa maganan wannan idan ka dawo, kuma ina ga ko ka dawo din ma kar ka masa magana kawai ka zuba masa ido ka gani" Khalil yace "Aa i am asking him Mami" Shiru tayi bata ce komai ba, ganin ya mike tace "Toh shikenan son, Allah ya daura ka a kansa, Allah kuma ya kai ka lafiya ya dawo min da kai lafiya" Yace "Ameen" Daga haka yayi mata sallama ya fita daga parlon. Khalil na fita gidan Aunty Maryam ya nufa, can sama ya tafi ganin babu kowa a parlon kasa, ta fito daga bedroom dinta ta shigo parlor ta zauna ya gaisheta ta amsa tace "Ya su Mami?" Yace "Lafiya lau" Tace "Toh maa sha Allah, ya ake ciki?" Yace "Gobe ne zanyi tafiyar Aunty" Aunty Maryam tace "Toh Allah ya kai mu, sai ka dawo yaushe?" Yace "Nan da wata daya xan gama komai" Tace "Waii, ai ba lallai xaka dawo ka tarar da ni kilan a kasar nan ba, yanzu ya ake ciki maganar admission din?" Yace "In sha Allah an fara processing tun jiya" Sai kuma a hankali yace "But Aunty ya za mu yi da Mami yanzu? Kinsan halinta fa, and i don't want her to be angry with me as a result of this issue" Aunty Maryam tace "I will think about that khalil, in sha Allah xan san yanda xa ayi, har yanzu nima tunanin ta inda xa a billo nake wallahi, da ina nan babu abinda xai hanani riketa a gidan nan" Bai kuma cewa komai ba, amma tunani yake, how will Mami be convinced, shi kuma he will neva let her stay in the hostel.... Bai wani jima ba yayi ma Aunty Maryam sallama kan zai je gidansu Nadeeyah, yana sauka parlor ya ga Nihad a parlon da mai aikin Aunty Maryam dake ta bata labari, ita dai tayi tagumi tana kallonta don ta gaji da surutunta gashi ko gane labarin bata yi, tun suna girki a kitchen take bata wannan boring  labarin, wannan yasa ta tuna nasu mai aikin a can gida, warce ko magana bata son ya hadasu da ita ba kuma ta zama inda take saboda tana ganin ta fi karfin hakan kamar yanda Umma ta ke yawan sanar mata, and for the first time Nihad felt bad at the way she treated Hafsah back then, yau dai ga ta ita ma a gidan mutane ba gidansu ba tana cin arziki.... Khalil ya sauko downstairs yana danna wayarsa, yayi dialing number Usman, yana fara ring Usman ya daga, ya nufeta ya mika mata wayar, tuni Murja ta gaishesa ta bar parlon da sauri, Nihad ta amshi wayar ba tare da ta kallesa ba tana kallon screen din amma bata gane number waye ba, ta kai kunne, jin muryarsa a hankali tace "Ya Usman" Yace "Ya kike Nihad?" Tace "Lafiya lau, ina yini" yace "Alhamdulillah, hope you are doing fine, babu matsala dai ko?" Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace "Eh" yace "Ohk are you still using ur account?" Tace "Bani da atm card ne" yace "Toh ya kaiki banki ki amsa wani" Tace "Toh" Yace "Xan maki transfer a ciki yanzu" a sanyaye tace "To yaya Nagode" Katse wayar yayi, hawaye ya cika idonta ta rufe fuskarta jikin kujera hawayen na zubo mata, bata son taji tana jin haushinsu a rai sbda Umma because she love all of them, basu ta6a nuna mata ubansu ne kawai daya ba, shi dai Khalil na tsaye don bata basa wayarsa ba, bayan few minutes ta dago tana goge idonta ta mika masa wayar ba tare da ta kallesa ba, kallonta yake, zata ajiye masa kan kujera ganin yaki amsa yace "Kee" Sai a sannan ta kallesa babu yabo babu fallasa, yace "Da xan baki wayar saman kujera na ajiye maki?" Ita dai bata ce masa komai ba, ya amshi wayar ta mike ta bar wajen, ya bi ta da kallo har ta bace sannan ya fita daga parlon, washegari kuma ya bar Nigeria for Zanzibar in the morning. Ranan Talata Mami ta kira Aunty Maryam, bayan sun gaisa Mami tace "Maryam bakuwar nan ta tafi kuwa?" Aunty Maryam tace "Ehh ta tafi jiya" Mami tace "Toh maa sha Allah, banda dai yace a gidansu ya zauna ai yarinyar nan bai kamata a gansu tare ba balle har ya kawota nan gidan" Aunty Maryam dake sauraronta tace "Saboda me Mami?" Mami tace "Kika ce saboda me?" Aunty Maryam tace "Au... Toh Allah dai ya kyauta, Allah ya tsare mana zuri'a" Mami tace "Ameen" Aunty Maryam tace "Ai ko yan gidansu suna ta godiya" Mami tace "Allah sarki, yanzu hostel din zasu kama mata ta zauna kenan?" Aunty Maryam tace "Toh ban dai sani ba" Mami tace "Toh idan ba nan din ba suna da yan uwa a Abuja ne? In basu da kowa ai sai dai hostel din dama" Aunty Maryam tace "Haka ne" sallama Mami tayi ma Aunty Maryam ta katse wayar, Aunty Maryam ta fara tunanin ta ina za a fara convincing Mami?? Tun bayan tafiyar Khalil Zanzibar duk sanda Mami taje gidan Aunty Maryam a daki Aunty Maryam ke sa Nihad ta zauna har sai Mami ta bar gidan, idan kuma ita ke son xuwa gidan yayartata ita kadai take xuwa da Mus'ab ta bar Nihad da mai aikinta a gida, unlike before da har da mai aikinta take zuwa gidan, a cikin wannan kwanakin kuma mijinta ya sanar mata nan da kwana biyar xa su taho kasar da yake, ta rasa ta inda xata billo ma yar uwarta a kan Nihad. Ranan friday ta shirya taje can gidan, bayan sun gaisa da Mami a bedroom dinta, it took her like five minutes kafin ta samu kwarin gwiwan yi ma yayartata magana, Mami tace "Wani magana kuma ke tafe da ke? To Allah ya sa lafiya, ina jin ki" Aunty Maryam tace "Mami dama iyayen yarinyar nan ne suka kira jiya, suna neman alfarman ta zauna wajenmu don basu son xamanta a hostel, and i think lectures will be commencing in 2 weeks time" Mami dai kallon Aunty Maryam kawai take, Aunty Maryam tace "Toh ni kuma gashi nan da kwana biyar xa mu yi tafiya" Mami tace "Ikon Allah, to Maryam ke ko da ba tafiya xa kiyi ba ina ke ina rike yarinyar nan dama? Kuma ma da suka gaya maki haka ai sai kice barin kasar ma xa ki yi, sannan ni kuma da kika zo nan kika gaya min me kike son ince maki? Meye nawa a ciki?" Aunty Maryam tace "Amma Mami ke kam ba me mance alkhairi bace, bansan ki da manta alkhairi ba komin kankantarsa, ko albarkacin xama da suka yarda Khalil yayi a gidansu har na shekara daya ai bakya ce haka ba" Mami tace "Yanzu ya kike son ayi Maryam, ni dai kinsan baxai ta6a yiwuwa ince yarinyar nan ta zo gidan nan ta zauna ba, tsangwama da hantaran yan gidan ma kadai ya isheta balle aje ga shi matsalar da Khalil din xai shiga in har Abbansa ya samu labarin shi ya kawota gidan nan, a ina ya santa da har xai kawota gidansa, ku na lura yin abu ku ke kanku tsaye duk wani abun magana bakwa gudunsa, ke kinga da sararin zamanta nan gidan, kwana daya kadai da tayi kina ganin abinda ya faru" Aunty Maryam tace "Ni wallahi idan kina nuna shakkan matsiyatan gidan nan a fili abun kona min rai yake yaya, ita tsinanniyar Hasanar kike tsoro ko kuma Aminar? Haba Mami ko sau daya ke baxa ki kwatar ma kanki yanci ba, ke kenan baki son fitina ke kenan gudun abun magana, A haka rayuwar xai ci gaba? Yo Abun magana na nawa? Dubi tuggun da suka hada ma danki suka sa ya bar gidan nan kina ji kina gani baki iya buda baki kin tsaya kinyi defending dinsa ba shi da gidan ubansa, nima kika hanani magana a sannan, wannan wace irin rayuwace? Toh wallahi mu ba butulu bane, kuma ba mu mance alkhairi komin kankantarsa, in sha Allahu yarinyar nan bata da wajen zama tayi karatunta da ya wuce nan gidan, kuma wajenki tunda har iyayenta suka nuna mu ma sun yarda damu, sannan da iyayen nata basu rike shi khalil din ba Allah kadai yasan depression din da xai fada a lokacin, kana ji kana gani a kwace duk wani abu naka da ka mallaka, a amshe takardunka akan laifin da baka aikata ba, a toshe duk wani hanyar samun kudinka, sannan ace ka bar gidanku ba a son ganinka, infact garin ma gaba daya kada a samu information din kana ciki, ka tafi duk inda xaka tafi, me kike tunanin zai samu mutumin da aka ma hakan idan bai fada hannun na gari ba? Ni nasan zamansa gidansu really contributed wajen rage masa damuwarsa banda haka da baki gansa a yanda kika gansa ba yanzu, ai Allah ya tsine ma Hasana da Amina, ya walakanta su dai dai gwargwado, wato tunda ta kashe aurenta yau shekara kusan ashirin to bari naki ma ta kashe maki, ga agololinta ta cika gida da su suna ta baza mulki son ransu, wani abun ma sae ayi masu ba ayi ma naki yaran ba, to ai ni da xata burgeni ta auri Janar din kawai mana mu ga, for 20 good years kina daukan cin kashin matan nan kin kasa ta6uka komai, don dai kawai ni xamana ba steady bane a Nigeria amma wani abun da ba ayi ba wallahi, to gaskiya it's high time kema ki kwaci kanki ki daina shirun nan Mami, yarinya kuma duk shegiyar da tace Khalil ne ya kawota gidan nan kice karya take, bai santa ba bai ma ta6a ganinta ba, babu sa hannunsa a zuwanta gidan, dama ai kowa ya sanki da taimako to wannan ma duk cikin taimakon da kika saba yi ne, amma babu ta inda khalil ya santa, kawai haka za ki ce masu, sannan hantara da tsangwama da kika ce baxa ma su ganta ba balle su yi mata, dakin baki na nan bangaren xata zauna, da safe ta tashi ta tafi makarantar ta, ta dawo da yamma to a ina za su ganta? Duk sanda na shigo Nigeria yin wani abu ta dawo wajena har sanda xan koma, ba shikenan ba?" Mami dai kallon Aunty Maryam kawai take ta kasa cewa komai, sallama aka yi a parlon duk suka daga kai.


Kuyi min afuwa wlh Whatsapp dina ne ya saki matsala,still Ina kokarin ganin na gyara Amma haryanxu dai be gyaru ba


TWINS NEEE

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post