Nihaad page 44 by Khaleesat Haiydar complete


Health College

Nihaad page 44 by Khaleesat Haiydar complete

 

Nihaad page 44 by Khaleesat Haiydar complete

💖💖NIHAAD💖💖

44

Da daddare Mimi na parlon Mami tana ta danna wayarta bayan sun gama cin abinci da Nihad, kallo daya zaka ma Nihad ka gane she is moody, gaba daya she is uncomfortable da zaman gidan, Noor ta shigo parlon tana kallon Mimi tace "Hey Madam Dad yana kiranki..." Mimi tace "Ohk" Daga haka ta mike ta kalli Nihad tace "I am coming" Nihad ta gyada mata kai, ta nufi kofa Noor na biye da ita, Nihad ta bi su da kallo, a hankali ta kwantar da kanta jikin kujera tana jin kewar nata Abban, bayan sun fita Noor na kallon Mimi tace "I don't like her" Mimi ta buda ido tace "Why?" Noor tace "Baki ga wani kallo da take ma mutane ba, beside bata iya gaisuwa ba sai bin mutum da ido, who does that" Mimi tayi murmushi tace "But she is nice, kawai bata son magana ne" Noor tace "Toh wa xata nuna ma rashin son magana, what's even the reason of her staying here? Na zata kwana biyu xata yi ta wuce" Mimi ta buda hannu bata ce komai ba tana ci gaba da tafiya. Mikewa Nihad tayi daga karshe ta nufi kofa xata bar parlon, kafin ta bude kofar aka riga ta budewa, suna hada ido ta koma gefe without looking at him tana jiran ya wuce, ya shigo yana kallonta, tayi ficewarta ta bar wajen ba tare da ta kallesa ba, ya bi ta da kallo... Nihad ta shiga dakin da take ta dau wayar da ya bata daxu, maganganunsa ne suka dinga dawo mata, ta tabe baki, kawai advice din Mimi ta dauka banda haka da tace masa to ya saketa din mana what is he even waiting for, though it's better that she kept silent, miss call ta gani da foreign number, ta dinga kallon number, xata mayar da wayar ta ajiye sai ga wani kiran da same number, dagawa tayi ta kai kunne tayi shiru, sallama taji ya mata da accent dinsa na larabci, ta amsa yace "Is this Nihad pls?" Tace "Who am i speaking to?" Yace "I am Ayman Fadlullah, i got ur digit from Ukhti Maryam" Nihad tace "Ohk" Yace "So how are you?" Tace "I am fine" Yace "Can we chat on WhatsApp plss?" Tace "Ohk" Yace "Thank you, i appreciate" Daga haka ya katse wayar, ita bata ma san ko da WhatsApp a wayar ba, ta dai shiga ta duba taga an ma bude WhatsApp din da number, but ba a fara chatting ba, sai shi kadai da yayi mata sallama few hours ago, tayi replying sallaman, with pure English ya shiga yi mata introducing kansa as the first son to his parent, yana da kanni maza biyu, sai autansu mace, ya kara mata da cewa he is from Yemen but now resides in America inda yayi studying Accounting... Ita dai Nihad karanta chat din nasa kawai take bata cewa komai, har ta mance rabonta da chatting almost 5 weeks now, ganin she is not replying yace "Are you der Nihad?" Tace "Yeah... " Yace "Ohk good, tell me more abou you" Kamar dai baxata ce komai ba sai kuma tayi masa introducing kanta a takaice a chatting din, yace "Waow, that's nice... I will be flying to Nigeria soon to meet with you in sha Allah, i have already beginning to feel comfortable with you" duk hiran yawanci shi yake yi, sai dai tayi masa reply da ok ko kuma tayi shiru har sai ya tambayeta is she there, and she noticed he is jovial and very friendly sannan wayayye ne sosai, he chatted her for almost an hour, babu abinda ya boye mata game da kansa, ya tura mata hotansa da iyayensa with his siblings, ta gansu kyawawan larabawa kamar su suka yi kansu, da yayi requesting ta tura masa nata hoton bata ta6a fuskantar low self esteem a kanta ba sai yan kwanakin nan da suka gabata, da kuma yanzu da Ayman ya bukaci hotonta, jin bata ce komai ba yace "Nihad" ajiye wayar tayi ta koma a hankali ta kwanta, bayan kusan minti sha biyar sai ga wayar ya fara ring daukan wayar tayi tana kallon screen din, sai kuma ta daga ta kai kunne tayi shiru, yace "Did i hurt you in anyway pls?" Tace "Not at all" Yace "Ohk sorry about me asking of ur picture" Tace "Ohk" Ya ɗan yi shiru sai kuma yace "I won't be asking u anymore" Tace "Good" Hiransa kawai ya ci gaba da yi mata, ta kalli agogo dake nuna sha daya da wani abu tace "I will be going to bed now" Nan yayi mata sallama ya kuma yi mata godiyan basa lokacinta da tayi, ta jira har ya katse wayar sannan ta kwanta ta lumshe ido, nan da nan bacci ya dauketa. Washegari da safe Mimi na dakinta ta fito wanka tana shiryawa gaban mirror aka yi Knocking kofar dakin tare da budewa, ta daga kai tana kallon kofar ya shigo tace "Yayanmu ina kwana?" Yace "Cool, are you having lectures today?" Tace "Yeah, yau muka yi resuming ai" Yace "Good, Nile ne makarantar naki ko Baze?" Tayi er dariya tace "Yanzu yaya har ka mance makarantar da nake, to su Noor ke zuwa Baze, but i and Farhana NUN ne" Yace "Ohk i now remember, did you have idea on when Jamb is commencing this year?" Mimi tace "Registration is still on progress, an kusa zana jamb din ma ai" Yace "Good, that girl... Ta samu admission a makarantar ku but she have to present her jamb result, don haka you take her with u zuwa center din da ku ka yi jamb registration tayi register" Mimi tace "Ohk, but that will be after my today's lectures right? May be around 2" Yace "Ohk, ku tafi makarantar da ita kawai" Mimi tace "Ohk then" yace "But do not tell Mami about the jamb registration, xan baki admission letter dinta kiyi mata presenting kice zaku tafi makaranta da ita kawai shikenan" Mimi tace "Ohk" Juyawa yayi ya fita daga dakin, Bayan Mimi ta gama shiryawa ta tafi can dakin da Nihad take, ta tarar ita ma tayi wankan har ta shirya tana zaune gefen gado tayi shiru, yau din ma she is moody, gaba daya taji bata son zaman gidan nan, she isn't comfortable, Mimi na kallonta tace "Good morning Neehad, yayanmu yace za mu je kiyi registering jamb yau, so xa mu fara zuwa school cause ina da lectures, after my lectures sai mu je wajen" Nihad na kallonta tace "Ohk"Juyawa Mimi tayi ta fita. A parlon Mami suka yi breakfast, daga nan Mimi ta sanar ma Mami tare za su tafi makaranta da Nihad, Mami tace "Wani makarantar ne nata?" Mimi tace "Makarantar mu daya" Mami tace "Really?" Mimi tace "Yeah, this is her admission letter" Mami tace "Toh Allah ya sanya alkhairi" Mimi ta fito tare da Nihad daga parlon Mami suka kusa cin karo da khaleel, daga sama har kasa yake kallon Nihad that's putting on veil, though ba karami bane, don yawanci duk medium veils Aunty Maryam ta siya mata ba irin wanda ta saba sa wa a gida ba, Mimi tace "Za mu tafi yayanmu" Yace "Ohk" Nihad ta wucesa, Mimi na biye da ita ya bi su da kallo har sai da suka yi nisa yayi saurin cewa "Hey Mimi" Mimi ta juyo tana kallonsa, Nihad dai tsayawa kawai tayi bata juyo ba, shima abinda yasa ta tsaya bata son tafiya zuwa main parlor din ita kadai ne, ya nufesu har ya isa inda suke yana kallon Mimi yace "Erm sorry wayana zaki dauko min a dakina" Mimi tace "Ohk" Ta mika ma Nihad laptop dinta dake hannunta tace "Rike min pls" Nihad ta amsa, Mimi ta juya ta bar wajen, yana ta tsaye har ya daina hango Mimi, Nihad dai ta hade rai tayi backing dinsa taki juyowa, ya zaga ya tsaya a gabanta fuska daure yace "Baki da hankali ne zaki fita da gyale?" Bata san sanda tace "Saboda me baxan fita da gyale ba???" Yana kallonta da kyau yace "Saboda dama ke kina da baƙin taɓon da duk inda kika shiga dole xa a ganeki sai dai wanda bai san labarinki ba" Shiru Nihad tayi tana kallonsa babu ko kiftawa, lkci daya zaka iya ganin yanda jikinta yayi sanyi, ya buda hannu yace "So however u wish to dress is ur business not mine, kuma naga ai har nikab da hijabs Aunty Maryam ta sa maki a kayanki, but saboda ke kin saba tallan jikinki baxa ki iya sa su ba, to nan ba inda zaki yi abinda kika ga dama babu me sa maki ido bane" Ta sauke Idonta daga kallonsa tace "My dressing, my choice!!!" Tana fadin haka ta kara juya masa baya, Kallonta yake ko kiftawa babu, a haka Mimi ta dawo ya nufeta da sauri ya amshi wayarsa yace "Thank you" daga haka ya juya ya tafi parlon Mami, Mimi xata amshi laptop dinta Nihad ta ɗan kirkiro mata murmushi tace "I will hold it for u" Mimi tace "Oh thank you" a haka suka ci gaba da tafiya, luckily babu kowa parlon har suka fita compound, tuni wanda zai kai Mimi makaranta ya taso, ta fara shiga bayan motar sannan Nihad ma ta shiga, ya tada motar ganin Nihad bata kulle motar ba Mimi tace "The door Nihad" Nihad ta kalleta sai kuma a hankali tace "Plss baxan bata maki lokaci ba idan na koma ciki for just some minutes?" Mimi tace "Mantuwa kika yi?" Nihad ta sauke idonta daga kallonta tace "I am not comfortable with my dressing" Da mamaki Mimi ta dinga kallonta daga sama har kasa tace "What's wrong with it? But you look smart dear, there is nothing wrong with you dressing, or is the veil too big?" Nihad ta ɗan yi murmushi tace "I will prefer i change" Mimi tace "Ohk then, xa mu jira ki" Sauka tayi daga motar ta koma cikin gidan. Da sauri ta wuce main parlor ta haura Upstairs har zuwa bangaren Mami sannan ta shiga dakin da take, she is just changing because kamar yanda ya fada xa a iya ganinta a ganeta amma ba don wai ya mata magana ba, hijab dinta ta dauka har kasa ta saka sannan ta dau nikab ta daura, baka ganin komai sai fararen hannunta da manyan idanuwanta with long lashes ta cikin nikab din, dama kuma Aunty Maryam tace mata ta dinga yawan saka Nikab in xata fita, tana fitowa ta sauko main parlor da sauri, Aunty Hassana da ke kokarin haurawa sama ta dayan stairs din ta bi ta da kallo, tadai san duk gidan babu me saka Nikab, sai kuma tace "Keee" Da sauri Nihad ta juya amma bata tsaya ba, Aunty Hassana ta sauko daga matakala biyun da ta hau ta nufota, hakan yasa Nihad ta tsaya gabanta na faduwa tana kallonta, Aunty Hassana ta isa har gabanta ta fizge Nikab din tace "Ke wa ya kawo ki gidan nan?" Nihad ta sunkuyar da kanta, a fusace Aunty Hassana tace "Baki jin ina maki magana ne" cike da karfin hali Nihad tace "Karatu nake yi" da mamaki Aunty Hassana tace "Karatu a ina? Wa ya kawoki kiyi karatu? Ke yar uwarsu Maman Mimi ce?" Nihad ta daga kai da kyar alamar eh, Aunty Hassana ta dinga kallonta daga sama har kasa, Mimi ce ta shigo parlon jin shiru shiru Nihad bata fito ba, Mimi na kallon Aunty Hassana tace "Good morning Aunt" Aunty Hassana tace "Wace makarantar take?" Mimi tace "Makarantar mu daya?" Aunty Hassana tayi shiru tana nazarin anya ba yayanta bane aka daura ma biyan kudin makarantar? Anya ba kawota gidan aka yi don yayanta ya dinga biya mata kudin makaranta ba, Aunty Hassana tayi mitsi mitsi da ido tace "Daga wani garin take?" Mimi ta buda hannu tace "Nima ban sani ba Aunty, Mami ce ta sani" Aunty Hassana tace "Ke baki ta6a saninta a er uwarku ba?" Mimi tace "Yan uwanmu suna da yawa wa enda ban sani ba, so she might be among them" Aunty Hassana ta gama nazare nazarenta  sannan ta kara kallon Nihad ta juya ta bar wajen, Mimi ta kama hannun Nihad suka fice daga parlon. The day was so hectic for Nihad don ta mance rabon da ta fita, NUN ya wuce yanda take tunaninsa, and it has always been one of her dream school don shi ta gaya ma Abba tana so amma yace Abuja yayi nisa sai yayi suggesting mata Maryam Abatcha and yayi assuring dinta she will like the school, though babu wanda ya san sunyi hakan, amma sai da taje ta gaya ma Umma which she is regretting right now, sai gashi yau she is going to be a student of her dream university amma kuma bata farin ciki da hakan, Ayman really whiled away her time a makarantar kafin Mimi ta gama lectures, sun dade suna magana da shi a waya tun bata son amsawa har dai ta fara amsa masa, shi ma saboda teasing dinta da yake ne sai tace sai ta rama, and she really enjoyed conversing with him caused he is so friendly and jovial, still tana makarantar Aunty Maryam ma ta kirata, sun kusa minti sha biyar suna waya, Aunty Maryam ta kara jaddada mata kada dai tace xata ma Ayman walakanci ta basa chance baxa kuma tayi da na sanin hakan ba, Nihad tace "Toh nagode Aunty" Daga haka Aunty Maryam tayi mata sallama, Nihad tace "A gaida min Mus'ab" Aunty Maryam tace "In sha Allah" Daga haka ta katse wayar. Sai bayan la'asar suka koma gida, tun da drivern motar yayi parking a parking space Khalil dake zaune karkashin wasu bishiyu da suka kawata makeken compound din yake kallon motar, Mimi ta sauka daga motar ta nufesa tana murmushi tace "Yayanmu good evening" Yace "How are you" tace "Alhmdlh, we are done with the registration, nan da sati biyu ne exam din ma ashe" Khalil yace "Ohk..." Juyawa tayi tace "Let me go in and take a shower" Daga haka ta juya taga har Nihad ta isa entrance din shiga cikin gidan, ta bi bayanta da sauri. Sai da suka fara shiga parlon Mami su gaisheta, kallo daya Nihad tayi ma Nadeeyah dake zaune parlon da Noor, ta dauke kai ta juya ta fita daga parlon, Nadeeyah ta kalli Noor da mamaki tace "Who is she?" Noor was speechless and astonished, ke baki yi sallama ba, kin shigo kin tadda mutane a parlor ba gaisuwa ba komai kin masu kallon tara saura quarter kin juya kin fita, Mimi ta sauke ajiyar xuciya tace "She is tired, yanzu muka dawo, it's an hectic...." Noor ta daka mata wani tsawa ta dakatar da ita tace "Pls get lost, ke da kika shigo baki yi mana sallama ba? Ko baki gaishemu ba? How dare she? Who did she think she is?" Mimi dai bata sake cewa komai ba, Noor ta ci gaba da jaraba kamar xata ari baki, Nadeeyah ta sauke ajiyar xuciya tace "Calm down Noor, kilan kamar yanda Mimi ta fada ta gaji ne, so kiyi mata uzuri...." A fusace Noor tace "Baxan yi ba, kuma wallahi na sake ganin ta shigo inda nake tayi repeating nonsense din nan da tayi i won't take it likely with her" Mimi dai ta karasa ta leka bedroom din Mami, ganin bata cikii ta juya ta bar masu parlon, Noor was still fuming with rage, Nadeeyah tace "Easy pls Noor, ya riga ya wuce ko? Stop the nagging pls" Noor tace "Nahhh bai wuce ba, i could slap her if she should repeat such kuma ba abinda xai faru" Nadeeyah tace "But who is she? Ranan na ganta gidan Aunty Maryam" Noor tace "How will i even know who she is, ni ban ma damu insan wacece ba tunda ba gabana take ba, i hate nonsense, na dai ji Aunty Maryam na ce ma Mami ai gidan iyayenta Yaya Khalil ya zauna when he was in kano, they were kind to him, they did that, they did this, bla bla bla, ita kuma tana so ta fara karatu ba a son ta zauna hostel, shine wai zata zauna nan gidanmu, cause at first Mami bata amince da zamanta a nan ba, but Aunty Maryam insisted, ta dinga kawo silly backups har sai da tayi forcing Mami yarinyar ta zauna gidan nan" Kallonta kawai Nadeeyah take babu ko kiftawa, can tayi karfin halin cewa "But who brought her here?" Noor ta karyar da kai tace "We saw her a day after yayanmu came back, which means tare kenan suka zo gidan, yes tare ma suka zo" Nadeeyah ta hadiye abu da kyar tace "Tare??" Noor tace "Yeah, and you know what?" Nadeeyah ta girgiza kai, Noor tace "You remember the video of a lady with undies that went viral last month?" Nadeeyah tayi shiru, Noor tace "Wani video that's all over social media na wata yarinya babu kaya jikinta?" Nadeeyah tace "Yeah, i heard about the video amma i didn't bother watching, so ban ta6a gani ba" Noor tace "Toh yarinyar ce" Nadeeyah ta zaro ido with surprise tace "Wace yarinya?" Noor tace "Yar rainin wayon da ta fita yanzu, ita ce a video din sure" Buda baki Nadeeyah tayi tace "Wai da gaske?" Noor tace "I mean it, bani da video din da na nuna maki, su Sajidah da Hanan ne ke da shi a waya" Nadeeyah was over shock, tayi karfin halin cewa "Kuma gidansu Kjay ya zauna a kano?" Noor tace "Yes, she was once a student of Maryam Abatcha" Nadeeyah ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh Allah ya kiyaye" Noor tace "Waow its been long i hala this way, har kaina ya fara ciwo wallahi, shi sa bana son magana da yawa amma wannan yar kauyen ta sa ni magana, As i was saying...." Nan ta ci gaba da ba Nadeeyah labarin da take bata cikin nutsuwa irin na big babes, but gaba daya Nadeeyah was absentminded, Nihad ta tsaya mata a rai sosai, abinda ta mata ranan da suka hadu gidan Aunty Maryam ya fado mata, ita kuma a ranan bata dauka as komai ba, sai yanzu brain dinta ya tunatar da ita cewa warce suka hadu a mall a can kano ce fa da Kjay, mamaki da fargaba ya cikata, but why did he have to bring her all the way from kano to his parent house, sannan even for once bai ta6a ce mata tare suka dawo ba gashi yau satinsu uku, Noor dake ta magana ta lura gaba daya hankalin Nadeeyah baya wajen ta kai hannunta fuskarta tana waving, da sauri Nadeeyah tayi blinking idonta, Noor tace "What are you thinking of?" Nadeeyah bata ce komai ba amma kana ganinta kasan there is something bothering her, she looks so disturbed, Noor ta kamo hannunta tace "Tell me plss, me ya faru" Lkci daya Nadeeyah taji hawaye ya kawo idonta ɗon saurin kuka ke gareta, tana kokarin ganin bata fashe da kuka ba tace "He neva told me he came all the way from kano with her, even for once bai gaya min ba" Noor ta zaro ido tace "Ohh that? Meye abun damuwa a nan bayan dai kinsan aurenki zai yi? In 3 days time fa xa a kai kudin aurenku da shi, and baxa a sa ya wuce sati biyar ba, so why bother ur self about one filthy lady that's all over social media half naked? ke sai kace baki san halin KJay ba? Ba abinda ya hada sa da yarinyar banda gidansu da ya zauna don ni tunda ta dawo gidan nan ma ko magana bana ganin yana hadasa da ita, you know he have class" Nadeeyah ta sauke ajiyar zuciya bata dai ce komai ba tana share idonta, Noor tace "C'mon chill plss, wannan bata kai ta sa ki shiga damuwa ba har ki zubda hawayenki a banza, me xai yi da ita? Da akwai wani abu tsakaninsu ma ai baxai fara kawota gidan nan ba, kuma saboda mugun abinda tayi shi yasa ma ba a son ta zauna hostel may be parent dinta suka yi requesting ta zauna a nan, shi sa ma kika ganta a nan" Nadeeyah ta gyada mata kai kawai, Noor ta ci gaba yi mata hiran da take mata a nutse..... Har karfe biyar khalil na zaune inda yake a cikin compound din yana danna waya, so yake ya maida Nadeeyah gida kafin ya je inda yake son zuwa, wayarsa dake hannunsa ya fara ring, ya dinga kallon number wanda ke kiransa, ya dai yi picking daga karshe yakai kunne, bayan sun gaisa Farooq yace "Dama wani aiki ne ya shigo da ni Abuja yau, so gobe da safe in sha Allah xan koma kd, shine nake son inji wani wajen ku ke a Abujan?" Khalil ya sauke idonsa yace "Ohk, maa sha Allah, goben za ka zo kenan?" Farooq yace "No, na gama abinda nake yi yanzu, goben da sassafe nake son tafiya" at first khalil ya rasa abinda xai ce masa, Farooq yace "Hello" Khalil yace "Eh ina jin ka, xan tura maka address din yanzu" Farooq yace "Toh ina jira" Daga haka ya katse wayar, Daga nisa ya dinga kallon Nadeeyah har ta iso inda yake, ta dauke kai tace "Xan tafi gida" Ganin mood din ta yace "What happened Nady? Are you okay?" Ta ki ce masa komai, ya mike yana kallonta, lokaci daya hawaye ya cika idonta, da damuwa yace "Talk to me plss, me ya faru?" Cikin rawan murya tace "But you neva told me ba kai kadai ka dawo Abuja ba" Yace "Shit... Toh menene tsakanina da warce na dawo da? There is nothing Nady kawai karatu ta zo yi a garin nan, and she have no where to stay shine take zaune gidan nan, bayan nan babu wani abu kuma trust me" Ta goge Idonta tace "Naji, I want to go home" yace "Noo, not in this manner pls, but ta maki wani abu ne?" Nadeeyah tace "Kawai shigowa tayi ta hararemu ta fita babu sallama balle gaisuwa" Khalil yayi wani sigh yace "But you guys shouldn't have taken it personal, she is a sociopath...." Nadeeyah ta tabe baki dai bata ce komai ba, khalil ya kalli wayarsa dake ring da sauri, ganin Farooq ne ya daga yace "Ina tura maka ne" Farooq yace "Ohk" Daga haka ya katse wayar, Khalil yace "Look Ki koma ciki yanzu, i will be having a visitor immediately, idan ya tafi sai muje ki sha ice cream sannan in maida ki gida" Murmushi kawai tayi ta juya ta fara tafiya, yea dama murmushin kawai yake son yaga ta yi which means komai ya wuce kenan, ya sauke ajiyar zuciya ya zauna ya shiga sending ma Farooq address.....

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post