Nihaad page 53 by Khaleesat Haiydar complete

Nihaad page 53 by Khaleesat Haiydar complete

 

Nihaad page 53 by Khaleesat Haiydar complete

💖💖NIHAAD 💖💖


Page 53


Mami bata tsaya ta kara sauraran Aunty Hassana ba ta mike ta shige dakinta ta shirya ta fice ta bar masu gidan daga ita har yayan nata zuwa gidan Hajiya Safeenah. Tana zaune parlon Hajiya Safeenah abun duniya ya isheta, Hajiya Safeenah tace "Na fa ce ki kwantar da hankalinki Hajiya Fatima, yarinyar da har nude video dinta yayi yawo a gari ai kinsan dama can idonta a bude yake kome aka ce ta aikata to zata iya aikatawa, ke dai kawai Allah ya shirya mana zuri'a, kuma babu tantama kila gidan nasu ta koma, ke kuma kina nan duk kin bi kin daga hankali" Mami dake ta kallonta tace "You have a point, sai yanzu da kika yi maganan nan na tuna wacece yarinyar, duk yaron da idonsa yayi budewar da nata yayi koma meye zai iya aikatawa gaskiya kika fada, ni fa wallahi bani da yanda xanyi ne amma ni ba wai son zamanta nake a gidana ba, haka kawai taje ta kara aikata wani abun da ba shikenan ba, gashi baka gane gabanta balle bayanta, nukurcinta yayi yawa, sannan kwana biyun nan ina ta lura da yanda Khalil din ke shige mata, sam bana son haka...." Hajiya Safeenah ta rike haɓa tace "Au, ashe kema dai kin lura, jiya bayan mun dawo gida zancen da Nadeeyah ta kawo min kenan...." Mami tayi shiru da tunani iri iri a ranta, can ta sauke ajiyar zuciya tace "Wallahi abun ya dameni, to yace mana wajen iyayenta ya zauna a kano ya zanyi masa, ga Maryam me goyan bayansa, tukunna ma dai wasu irin iyaye ne xasu hada yar su da gandameme kamar Khalil wai su taho Abuja tare sannan ya bar ta a gidansu wai zata yi karatu? A ina aka taɓa haka kamar dai garin gaɓa gaɓa aka taso? Idan ma haka ne ai kamata yayi uwar ko uban wani ya biyota sai a damka mana ita a hannu ace gata nan don Allah zata yi karatu a sa mata ido, to wai sai aka hadata daga ita sai khalil ya kawo mana ita, ko marasu addini baxa su yi haka ba, ni wallahi na rasa yanda zanyi ne, i have a big question mark on this issue, ga Maryam tayi ɓake ɓake kan lamarin sai goyan bayansa take wai sai an riketa tunda iyayenta suka rike shi, to shi ba namiji bane ko da da kafafuwansa yaje gidan nasu shi kadai, ita kuwa ai sai cikin iyayen wani ya rakota saboda halin rayuwa, komai fa na son tsari a rayuwar nan, amma sam wannan lamarin ba tsari, a hada baligi da baliga wa enda ba muharraman juna ba" Hajiya Safeenah tace "Gaskiya abun dubawa ne wannan, kuma kika ce kwanaki yayanta yaje gidan ko?" Mami tace "Ehh yaje kam, amma ko da iyayen ma baxa su biyota ba ai sai su ba yayan nata ya kawota ba Khalil ba, it's making no sense to me now, tun farko ya kamata inyi masa wannan tuhumar amma hankalina bai je ba, sannan ban taɓa jin an kirata daga can gidan nasu ba ko kuma ita ta kirasu" Hajiya Safeenah tace "Toh dai ki kara kiran layukan Khalil din ko xaki samu, aji in gidan ta koma kin ga hankalin kowa sai ya kwanta, sai kuma a koma next issue that's on ground" Mami ta sake dialing number Khalil, luckily ya fara ring, gyara zama tayi ta sa handsfree tana jiran ya daga, sai da ya kusa katsewa sannan ya dauka, tace "Khalil me ya kai ka dakin Abbanka?" Khalil ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Ajiyata na dauka Mami" Mami ta bude baki tana kallon Hajiya Safeenah, can tace "Ajiyarka? Wato khalil duk yanda zaka daga min hankali shi kake nema a rayuwarka ko? Ba nace ka fita batun abubuwanka da ke hannun Abbanka ba? Me yasa baka jin magana ta ne fisabilillah" Khalil yayi kasa da murya yace "Mami i did nothing wrong, bayan takarduna babu wani abu da na taɓa masa a dakinsa, i seriously need them Mami, tunda ke baxa ki iya dauko min ba shine fa na dauka da kaina Mami...." Mami ta buda baki, ta ma rasa abinda xata ce masa, can tayi karfin hali tace "Duk inda kake ka dawo ina nemanka immediately, sannan kada kayi making mistake din zuwa gida ka zo nan gidan Hajiya Safeenah ka sameni" Ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Toh" Mami zata katse wayar, Hajiya Safeenah tace "To baki tambayesa batun yarinyar ba" Mami da har ta manta tace "Ohh, Sannan ita kuma yarinyar can ina fatan gidansu ta tafi?" Khalil yayi shiru kamar baxai ce mata komai ba, sai kuma yace "Eh" Mami tace "Toh madallah, sai ka gaya ma iyayen nata taki zama Abujan, it's better kawai su nema mata transfer ta koma Kanon da karatu ya fi" Khalil dai bai ce mata komai ba, tace "Baka ji na ne?" A hankali yace "Ina ji" Tace "Then do as i say, kai kuma immediately ka taho gidan Hajiya Safeenah ina jiranka" Yace "Ni bana Abuja yanzu" Buda baki Mami tayi tace "Kana ina?" Yace "Ina kano" Tace "Ohh kanon ka bi ta? Kana nufin kanon ka kama hanya ka tafi ko gaya min baka yi ba? To ka kyauta, maza maza ka nemi next flight ka taho Abuja yanzu" Yace "Ba jirgin da zai tashi yau saboda weather" rai bace Mami tace "To wannan kai ta shafa ka biyo mota kawai ka dawo na gaya maka" Daga haka ta katse wayarta, cike da fada tace "Banda ma lalacewa tunda yarinyar ta zo gidan daga uwar har uban babu wanda ya taɓa kira muka yi magana da su, don su ma ji ya yarinyar take, kawai ga ta nan dai kamar bata da iyaye, kana da ya mace har hankalinka zai kwanta idan bata gabanka, babu wanda fa ke bibiyar lamarinta nake gaya maki, duk ina lura da komai, kinga ai saboda tsabar yanda idonta ya bude ai Kano ta kama hanya tayi wucewarta daren jiya, wanda bai saba ba ai baxai yi haka ba, ko tsoron dare bata ji ba, dama can ta saɓa abunta ne, Allah ya shirya" Hajiya Safeenah ta sauke ajiyar zuciya, Mami tace "Tun farko da ya samu matsala da uban Yemen nace ya tafi ya ki, na dawo nace ko zai je Uk nan ma yaki, all that while ban san yana kano ba na dai san yana Nigeria, to gidan wasu irin mutane ne ya zauna wa enda basu da kula haka? Ka sakar ma duniya yar ka mace a wannan zamanin, sannan ga dai abinda yarinyar nan tayi ko wata uku ba ayi ba amma har ku sakankance baku bibiyar lamarinta, a'a ban taɓa ganin haka ba tun da nake" Hajiya Safeenah tace "Yanzu dai Hajiya Fatima kiyi hakuri, a bi komai a sannu ki kirasa ya bar zuwan nasa gobe tunda yace ba jirgi, biyo mota daga kano zuwa Abuja ai aiki ne babba yanzu, kawai ki masa hakuri ya bari har gobe, bari in kirasa" Daga haka Hajiya Safeenah ta kira Khalil, nan ta sanar masa kawai ya bari gobe sai ya biyo jirgin safe, bayan ta katse wayar Mami tace "Dama yana dawowa duk zan amshe takardun in mayar ma uban baxan iya fitina ba, idan jiƙawa zai yi ya shanye sai ya jika ya shanye, babu abinda zai raga Khalil da shi" Hajiya Safeenah tace "Aa kar kiyi haka, ki bar wannan issue din tsakaninsa da ubansa kawai kar kiyi involving kanki, gaskiya kar kiyi haka, kamar yanda ya fada ke baki amsar masa ba kuma ya amsa sai kice xaki mayar?" Mami tace "Wallahi mayar masa shine kadai mafi alkhairi gare mu gaba daya, sai kace baki san General ba, ni duk wani abun tashin hankali bana so wallahi, har fargaban zuwa asibiti nake yanzu yanda nake ji a jikina sai ya iya yiwuwa jini na ya hau" Hajiya Safeenah tace "Allah ma baxai sa hakan ba, kawai kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki Hajiya, komai zae zo da sauki" Mami ta taɓa baki tace "Ya batun programs na bikin, kun gama shawaran da Hajiya Hauwa?"


Bayan Azahar ganin Khalil bai shigo ba Mumy na kallon Nihad tace "Ki je kiyi masa magana ya shigo ya ci abinci" Nihad da tunda tayi sallah take zaune saman darduma a bedroom din Mumy ta mike ta dauke darduman ta linke sannan ta fita, Hijab ne har kasa jikinta don ta shiga bedroom dinta ta kwaso sauran kayanta ta kawo bangaren Mumy ta ajiye, har zuwa sannan kuma Umma bata dawo gidan ba, babu kowa main parlor din ta fito compound ta gansa zaune tare da Aminu, ɗan zaman da Khalil yayi a wajen babu abinda Aminu bai sanar masa ba da ya faru a gidan bayan tafiyarsu sai wanda ya manta, dawowar Kamila gida, matsalar da Usman ya samu wajen aikinsa, rashin walwalan Abba a ko da yaushe tun tafiyarsu, yanda Umma ke fita ta dawo dab da magrib kafin Abba ya dawo motarta duk jan laka, zuwan karshen da Inna tayi gidan ta zauna nan compound tana ta tikar kuka wai an rabata da Nihad an daura mata aure da ɗan kauye tana can ita ma ta zama er kauye, sabon dreba da aka kawo me warin baki da warin hammata ga shegen gulma, murmushi kawai khalil ke yi yana kallon Aminu da ke basa labaran nan with passion babu abinda yake tsallakewa a labarin, in details yake badawa, he is so good in it, in wanda xai yi demonstrating ne sai ya tashi yayi demonstrating sannan ya koma ya zauna, yana cikin basa labarin yanda banki suka zo suka kulle gidan dake can karshen layi saboda bashinsu da ya ci na fitar hankali sai ga Nihad ta karaso, duk abinda Aminu ke cewa Khalil baya apprehending tun fitowar Nihad, don ainahin kamshin da ya santa da shi ne ya cika wajen still dai bai daga kai ya kalleta ba, Aminu ya mike yana washe baki yace "Sannu Hajiya, sannu da karasowa...." Nihad tace "Sannu Aminu" Daga haka ta kalli khalil tace "Mumy tace ka shigo ka ci abinci" Sai a sannan ya kalleta kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Kawo mana nan" Tayi shiru tana kallonsa, can ta juya ta bar wajen ya bi ya da ido har sannan kamshin na dukan hancinsa, sai da tayi nisa Aminu ya koma ya zauna yace "Kai mutumina, amma kayi jahadi wajen dawo da yarinyar nan hanya mai bullewa, wallahi duk jikina yayi sanyi kamar ba Nihad din da na sani ba a baya, dubi fa yanda ta zama ta gari, ko da dai dama wannan matar uban nata ce ke zugata duk mun sani, wani nutsuwa na musamman fa take da shi yanzu, shi yasa jiya da naganta ta dawo ita kadai na maza na kiraka inji ina kake don na zata guduwa tayi, ashe dai ta nutsu, sannan ga...." Khalil ya dakatar da shi ta hanyar cewa "Ina jinka, sai bankin suka kulle masa gidan" Aminu ya gyara zama yace "Wallahi kuwa in gaya maka, bawan Allahn ya fito yayi ta birgima a layin nan duk muka taru kansa, ga matansa da ya'yansa a gefe abun dai zar tausayi, an fa ce caca yake yi, kuma ɗan giya ne....." Khalil ya dinga kallon Nihad da ta fito, hakan yasa Aminu yayi shiru yana ɗan murmushi ganin Khalil bai ma san me yake cewa ba, har ta iso inda suke da tray din abincin ta durkusa gabansa ta ajiye, shi dai kallonta kawai yake, ta mike tace "Me sanyi ruwan za a kawo?" Sae a sannan ya dauke idonsa yace "Duk wanda kika kawo" Juyawa tayi ta bar wajen still ya bi ta da ido, the perfume is just something else, Aminu dai sai wani murmushi yake irin na rubabbu, yau wai Nihad ce ke kawo ma Khalil abinci har ta durkusa ta ajiye masa a gabansa yarinyar da har hana a basa abinci tayi a gidan, Aminu ya rike haɓa uwa ɗan daudu yana nazari... Sai bayan la'asar Khalil ya shiga cikin gidan shi ma Sudais ne ya zo yace masa Mumy na kiransa, parlor ya samu Mumy, Mumy tace "Kana ta zama a waje Ibrahim" Ya ɗan yi murmushi yace "Muna tare da Aminu ne" Tace "Kuma ba rana" Yace "Aa babu" Tace "Toh ko bayan magrib ne sai ku tafi can gidan Inna ku gaisheta" Yace "Toh Allah ya kai mu" Bai wani jima a parlon ba tunda ba wai hira suke da Mumy ba ya fita ya koma gun Aminu, Mumy ta koma parlonta tana kallon Nihad tace "Me yasa baki je dakin er uwarki ba Nihad?" Nihad dake game da wayar Mumy tace "Naga kamar bata son magana ne, i don't want to inconvenience her" Mumy ta zauna tana kallonta tace "Amma ai ta shigo nan har sau nawa saboda ke Nihad" Nihad tace "Ko ta shigo ba magana take ba, i don't know why she is silent" Mumy bata kuma cewa komai ba, bayan few minutes tace "A ina kuke a Abujan?" Nihad tayi shiru, sai kuma ta daga kai ta kalli Mumy ganin kallonta take, ta sauke idonta a hankali tace "Maitama" Mumy ta ɗan bude ido tace "Maitama kuma? Akwai wani maitaman ne bayan wanda na sani?" Nihad ta girgiza mata kai tace shi wannan din ne, da mamaki Mumy tace "Wajen wa a Maitama?" Ita dai farooq yayi assuring dinta sosai yace ta kwantar da hankalinta Nihad is doing very fine, idan ya zo kano za su yi magana, iyakar abinda ya gaya mata kenan amma bai gaya mata anguwan ba ko inda take, Mumy tace "Kin yi shiru" Nihad ta ajiye wayar hannunta a hankali tace "Gidan iyayensa" Mumy look so confuse, tace "Wani iyayen nasa kuma?" Nihad ta sauke idonta tace "He is the son of General Jikamshi" Kallonta kawai Mumy take, can tace "Are you okay Nihad?" Nihad ta kalli Mumy, a hankali tace "He disguise himself, I don't know his reasons, I don't know.... but they are rich, he is the son of General Abubakar" Mumy da duk kanta ya daure tace "Ke ban gane ba, wani general din? Sannan ba Aliyu bane ɗan gidan General? Kanki daya kuwa Nihad, ko dai zaki je ki kwanta ne...." Nihad tayi wani murmushi kawai, can ta girgiza kai ta goge hawayen da ya taru idonta tace "Aliyu lied to me, ba shine yaron jikamshi ba, Jikamshi is just his uncle which is Khalil's father" Sai kuma ta fashe da kuka cikin sanyin murya tace "Mumy naga abubuwan iri iri in just 3 months from every angle, Khalil isn't who we thought him to be, i don't know his intent of coming to our house, I don't know his intent of coming here as a driver, they are super rich, his father is a General, his mum is from Yemen, i don't just...." Sai kuma ta hade kai da gwiwa tana kuka a hankali bayan ta tuno abubuwa da yawa, Mumy was speechless, ta ma rasa me xata ce, sai kallon Nihad din take inna State of confusion, kuma har cikin ranta taji bata yarda da abinda Nihad ta fada ba, seems bata da lafiya, Mumy ta mike ta dagata tace "You need rest, go and have some rest" Har dakinta ta kai ta ta kwantar da ita saman gado, Mumy na ta kallonta har ta rufe ido sannan ta juya ta fita daga cikin dakin. 

Bayan Magrib Nihad ta gama shiryawa ta sa Hijab dinta har kasa, tun labarin da ta ba Mumy da la'asar Mumy bata dawo dai dai ba kuma ba wai ta yarda da zancen Nihad bane, a'a kawai gani take kamar ƙwaƙwalwarta ya fara taɓuwa ne as a result of all what she passed through, gani take she isn't in her right senses, gani take kawai sambatu take ba wai don tasan abinda take fada ba, Mumy ta nuna mata inda Makullin motarta yake, Nihad ta dauka, a hankali tace "Sai mun dawo Mumy" Mumy bata iya ta ce mata komai ba ta bi ta da kallo har ta fita daga dakin, Mumy ta jingina da kujera rai ba dadi, ita dai tasan Nihad bata da lafiya don sanyin nata ma yayi yawa, Mumy bata san sanda ta fashe da kuka ba tana fatan kada ace ƙwaƙwalwarta ne ya samu matsala. Khalil na tsaye parking space bayan ya gaisa da Abba, sae dai Babu yabo babu fallasa Abban ya amsa masa har ya shiga ciki, yana ta jiran Nihad har ta karaso ta mika masa makullin motar ya amsa yana kallonta, ita dai bata bari sun hada ido ba duk da ta dai ga ya canza kayan jikinsa, ta zaga ta bude kofar gaba zata shiga yace "Aa koma normal spot din ki...." Ta ɗan yi jim sai kuma ta sauka ta koma back seat, ta madubin mota yake kallonta har ya tada motar yayi warming suka bar gidan, She doesn't look like the normal Nihad anymore, seems abubuwa da yawa suna damunta a zuciya, this is a new Nihad he is seeing for 2 months now, har suka isa gidan Baffanta bata sani ba don tayi nisa a tunanin da take, yayi parking yana kallonta, ta dago kai ta kalli anguwan da suke da sauri, sai kuma ta bude motar ta sauka shi ma ya sauka. Tana gaba yana bin ta har suka shiga gidan, Hamid na zaune parlor Nihad bata kallesa ba ta shiga bangaren da Inna take, Khalil ya karasa har inda yake ya basa hannu sannan ya juya ya nufi bangaren Inna, Inna ta tsaya rike da darduman hannunta tana ta kallon Nihad, sai kuma ta fashe da kuka kamar yar yarinya ta ajiye darduman hannunta a gefen gado, ta zauna kasa tace "Allah ya isa tsakanina da duk wanda yayi sanadin rabani da ke, ko ma waye Allah ya saka min, Allah ya walakanta shi...." Sai kuma ta kalli Khalil da ya durkusa bakin kofa, ta wani tsuke fuska tace "Kai kuma haka ake yi kawai ka dau yar mutane ka tafi da ita kauyen Nijar saboda Allah ya ci da kai an aura maka ita babu ko sisinka, yau ga karfin hali ni patu, kai ba kowan kowa ba dillalin kashi a leda zaka dau min jika ka mayar kauyenku? Ashe haka buzaye suke basu da kamun kai basu da lissafi bamu sani ba, yau ko da kudinka aka aura maka ita zaka dauketa ka kaita kauyen ku balle babu kwandalarka, ina ma kaga kudin aurenta, wato ka samu xukekiyar yarinya a bagas shine ka tafi kana ta fafa da ita a kauyenku kai ga ɗan banza" Shi dai khalil kansa na kasa sai ɗan murmushi yake, Nihad kuwa banda hararanta babu abinda take tana turo baki, Inna ta rike haɓa tace "Tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin wannan azababben karfin halin ba, banda kaddara me Nihad zata yi da kai ɗan nan, ai kai ba ajinta bane tafi karfinka ta ko ina, iyaka kayi aikinka na dreba ka kama gabanka amma ina kai ina auran yar masu gida banda ƙaddara da ta riga fata, ɗan gidan Habubakar Jikamshi ne saurayinta fa wannan dai da kayi ma walakanci kwanakin baya, wanda da ba don mutuncina da na ubanta ba da ya daureka har karshen rayuwarka ka rube a gidan yari, wallahi mun sha gaisawa da shi yafi a kirga ta waya, abinda idan bashi da number mutum ma baya samunsa ba ko wani gaja yake waya da ba, sai in shi ya yi niyyar kiran mutum" Nihad tayi karfin halin cewa "Dama gaisheki muka zo yi" Inna tace "Toh ya tashi ya tafi sai kin huta haka kuma, wato ga ki ya sameki a banxa sai dai Ibrahim ya tura masa kudi kaca kaca, shi gashi ai sai kyau yake yana kara budewa uwa kirjin zai yage, ke kuma duk kin tsamure kin kanjale ke da kudin ubanki, da kyar idan kina samun abinci ma kina ci sau uku a rana" Khalil ya daga kai yana kallon Inna, a hankali yace "Toh bari muje ta debo kayanta Inna" Inna ta masa wani shegen kallo tace "A ina??" Yace "Gidan da muka ajiye kayan" Tace "Wani gidan ne?" Yace "Nan cikin gari" Tace "Toh wai da daga ina ku ke?" Yace "Kauyenmu" Ta buda baki tana kallonsa, can tace "Toh maza maza tafi ka debo mata kayanta, kauyen uban wa, kaga tayi kalar yar kauye banda dai baka tsoron Allah duk girmanka, kaiii Ibrahim ma dai sai Allah yayi masu hisabi da Nihad, don ya cuceta ya gurbata mata rayuwa, wallahi ya cuceta" Khalil ya mike yana kallon Nihad dake ta kallonsa, yace "Za muje ki debi kayan ne, don ban san wanda zaki bukata ba" Mikewa tayi, Inna tace "Ta debi me, Bawan Allah dukka zaka tafi ka kwaso mata ka kawo nan inyi jinyar jikata ko zata marmaro, shi kuma Ibrahim yaje hakkinta ma baxae bar sa ba duk da ni nace na yaɓa da hankalinka kawai a aura mata kai, bansan kai ma mugu bane, ashe kauyen da dadi ka gudo ka dawo birni ka nemi tukin mota, maza tafi ka kwaso mata kayanta" Nihad tace "Toh ai ni xan je in xaba kayan, ba dukka nake sa wa ba fa" Inna tace "Duk da haka kuje ki kwaso su gaba daya, baki ji yace wajen ajiya kayan suke ba, idan aka kwashe maki kaya ta ina za a fara...." Nihad tace "Toh" Khalil na kallon Inna yace "Sai anjima" da sauri tace "Toh" Juyawa yayi ya fita ta bi sa da harara, Nihad ta bi bayansa, Inna tace "Maza kiyi ki dawo" Har suka iso mota babu wanda yace komai cikinsu. Bayan sun bar layin ya juya ya kalleta yace "Kala nawa zaki debo kayan?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Ko dukka za a debo?" Ta hade rai tace "Ni nace maka zan koma ne?" Yace "Ai ban sani ba" bata kuma ce masa komai ba bayan tafiyar kusan minti talatin ta gansu gaban wani hotel, ta kallesa, ya fiddo wayarsa dake ring ganin Mami ke kiransa ya jinginar da kansa jikin kujeran motar, can dai ya daga ya kai kunne a hankali yace "Ina yini?" Daga daya ɓangaren ba tare da ta amsa ba a takaice tace "Karfe nawa zaka taso goben?" Yace "Da safe" Tace "Ai dai ka ji inda nace kaje idan ka sauka ko?" Yace "Toh saboda me?" Mami tace "Ohh kace saboda me? To in baka da hankali ka shigar masa gida idan ka shigo Abuja, wai ma in tambayeka kana da wani kudurin na daban ne a ranka da yasa ka dage sai ka amshi takardunka dake wajensa bayan babu abinda ka rasa yanzu?" Ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Ba komai, just in case of necessity" Mami tace "Toh kana sauka Abuja xaka bani in mayar masa kuwa" Khalil ya bude baki yace "Ki mayar masa kuma Mami?" Tace "Haka nace" Shiru yayi, yana jin ta kashe wayar ya ajiye, bayan few seconds ya kalli Nihad yace "Mu je ki dau wasu kayan naki da kika bari a Abuja na taho maki da su" Yana fadin haka ya bude motar ya sauka, ta bi sa da kallo sai kuma ta sauka, sai da ya kulle motar sannan ya nufi cikin hotel din ta bi bayansa, makullin dakin ya amsa tana biye da shi har zuwa dakin da ya sauka dazu da safe, a hankali take tafiyar har ta shiga cikin dakin ya kulle kofar, taga ya shiga bandaki ya dauro alwala ya fito, nan dakin ya shimfida darduma zai yi sallan don an idar a masallaci, Nihad dai ta dinga bin dakin da kallo don bata ga alamar jaka balle kaya ba, can dai ta nufi bandakin ita ma tayi alwala ta fito, ta dau wani darduman ta shimfida xata yi sallan...

Bayan ta idar da sallan ta kallesa don kwanciya yayi kan gadon ya rufe idonsa kamar me bacci nan ko ba bacci yake ba, kawai neman mafita yake na chakwakiyar nan da yake ciki, he don't even know where to start from, it's doesn't look easy at all, definitely yasan ko harbesa Abba zai yi baxai mayar masa da takardunsa ba, to shi wannan ma ba damuwarsa bane, babban tashin hankalinsa daban yanzu, wanda da ya tuna sai gabansa ya fadi, throughout ranan kuma Nadeeyah bata kirasa ba, a hankali ya bude idonsa daga karshe yana kallon Nihad yaga ta kwantar da kanta saman gadon tana daga zaune kan darduma tana bacci, mikewa zaune yayi still yana kallonta, can ya sauka daga saman gadon, ya nufi switch din dakin ya kashe, sannan ya dawo gabanta yayi patting dinta, bude ido tayi da sauri amma taga ko ina duhu ta gyara zamanta da sauri tana gwalo ido, yayi kasa da murya yace "Tashi...." Gabanta na faduwa tace "Ni baxa ka kai ni gida bane?" Ji tayi ya dagata ta zaro ido kafin tace komai ya cire mata hijab din jikinta kamshinta sai da ya kusa Knocking dinsa down yaji ya kasa tsayuwa da kafafuwansa, gaba daya ta rikice zata duka ƙasa yaki barin ta, instead taji ya ja ta suka fada saman gadon, ta sauka kansa da sauri, cikin rawan murya tace "Don Allah kayi hakuri mu tafi gida kaga dare yayi" Kamar wanda ya sha wani abu yana lumshe ido yace "Saboda me?" Ta hadiye abu da kyar tace "Za a neme ni" Yace "Ke da wa ku ka fita?" Ta kasa cewa komai sai zaro ido take xuciyarta na bugawa, murya can kasa yace "I am asking you, ke da wa ku ka fita?" Still taki cewa komai tana neman sauka daga saman gadon, taji ya danneta, zaro ido tayi, kamar me rada yace "Answer me" jikinta na rawa tace "Mijina" Bata rufe baki ba ya daura lips dinsa kan nata giving her a deep snog...


*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post