Nihaad page 55 by Khaleesat Haiydar complete

Nihaad page 55 by Khaleesat Haiydar complete

 

Nihaad page 55 by Khaleesat Haiydar complete

💖💖 NIHAAD 💖💖


Page 55


Khalil na isa gidan Hajiya Safeenah, ya ga motar Mami a compound din alamar tana ciki, ya karasa har kofar shiga parlon gidan yayi Knocking, ba a dau lokaci ba aka bude kofar suka yi ido hudu da Nadeeyah, juyawa tayi zata bar wajen ya bi parlon da ido ganin babu kowa ciki ya jawota da sauri yace "C'mon Babe, did i offend you in anyway?" Nadeeyah dai bata ce masa komai ba, ya karaso cikin parlon ya kulle kofar still yana rike da ita yayi kasa da murya yace "Haba Nadeey, nayi maki wani laifin ne? In ma nayi kiyi hakuri don't punish me plss" Taki kallonsa, a takaice tace "Pls aiki muke yi a kitchen, let go of me" Ya sake bin parlon da kallo sannan ya rungumeta a hankali yace "I am sorry dear, I'm deeply sorry...." Kamar jira take ta fashe masa da kuka tace "Saboda ga budurwarka ta gudu shi yasa zaka daga hankalinka haka har ka dinga shareni ko?" Da sauri yace "Noo Nadeey, budurwata kuma? Haba... Kawai ya zama dole in daga hankalina saboda parents dinta trusted me har suka bari na taho da ita Abuja ta zauna a gidanmu, Kinga idan wani abu ya sameta i don't know how to explain to her parents, bansan da wani idon zan kallesu ba, wannan shine dalilin da yasa kika ga hankalina ya tashi Nadeeyah, but Alhmdlh she is home now, ba shikenan ba" Hawaye na bin kuncinta tace "Ko farin cikin sa mana rana da aka yi baka yi ba, u are not even saying anything about the wedding, balle mu yi wani shirye shirye, You've been ignoring me for at least 2 weeks now...." Ya wara ido yace "Ko ba wata daya aka sa ba? ina fa lissafi Nadeey, i know yau saura 15 days in sha Allah, and kinsan ni bana son duk occasions din nan da ake yi ko events a biki, i told u that years back, so ba wani abu da xa ayi, just wedding fatiha sai walima a gida, but if su Mami za su yi wani program fine za su iya, kema in za kiyi da frnds dinki it's okay the expenses will be on me, but count me out of any event....." Nadeeyah dai bata ce komai ba, ya share mata hawayen idonta a hankali yace "You know i love you always dear, kuma baxan so ranki ya baci saboda ni ba.... Don Allah kiyi hakuri kin ji wife" Jin bude kofar kitchen yasa ya saketa da sauri ya koma baya, ya wara ido yace "Ina su Mami?" Bata kai ga basa amsa ba ya jiyo muryarsu, Ya kashe mata ido yace "Bari in karasa ciki Baby" Daga haka ya nufi kofar parlon Hajiya Safeenah, Nadeeyah ta bi sa da kallo, yana shiga parlon da sallama Mami ta dinga kallonsa, ya zauna ya gaida Hajiya Safeenah da ladabi ta amsa da fara'a tana tambayarsa ya hanya, yace "Alhamdulillah" Ya ɗan kalli Mami da ke kallonsa har sannan yace "Ina yini Mami" Mikewa Hajiya Safeenah tayi ta fita daga parlon ta basu waje, Mami na masa wani kallo tace "Ban ga komai a hannunka ba bawan Allah" a hankali yace "Kamar me fa Mami?" Ta jefa masa wani kallo tace "Kar ka raina min hankali mana, ina takardun da makullan da ka kwashe?" Khalil yayi shiru bai ce mata komai ba, Mami tace "Na lura baka son kwanciyar hankali na Khalil, duk wani abu da zai daga min hankali baka gudunsa a rayuwarka, banda haka what are you lacking in this life? Rasa motar hawa kayi ko rasa gidan zama kayi? Nawa ne salary din naka dukka? Sannan nawa kake samu currently a wata? Ka gaya min ko banbancin da wani tazara, ko kuma rashin godiyar Allah ne ke damunka?" Kallonta kawai Khalil yake ya kasa ce mata komai, A fusace Mami tace "Instead of you to sit and plan ur wedding cikin tsari sai ka ɓuge da dauko mana magana, Is this the rightful time da zaka amshi abubuwanka khalil in ba dai kana da wani kuduri na daban a zuciya wanda mu bamu sani ba, are u even okay? A kan bikinka that's by the corner zaka yi concentrating yanxu ko takardunka?" Yayi kasa da murya yace "Kiyi hakuri Mami, ni ban yi hakan don ranki ya ɓaci ba, i am very sorry Mami...." Mami tace "Aa kayi ne don raina ya ɓaci don sarai kasan kaina komai zai dawo, you are lacking nothing, akan me zaka damu da takardu ko makullin gida? Yanzu maganar da ka jawo min dai dai ne?" Shi dai yayi shiru bai ce komai ba, tace "Toh duk inda ka kai su ma kaje ka kawo min su ina jira, duk da ba shiri ku ke da shi ba but he is planning on sending 6million da za a hada maka lefe shine kaje ka aikata wannan shirmen, sannan da ka kwantar da hankalinka nasan dole xai baka makullin gidanka idan anyi auren tunda nan din dai amarya zata tare.... Amma ban san meye manufarka nayi abinda kayi ba" Khalil ya daga kai ya kalleta, Mami ta girgiza kai tace "I am very disappointed Khalil" A hankali yace "Kiyi hakuri Mami, i am so sorry" Mami tayi shiru, can tace "Sannan ita Maryam akan wani dalili take kiranka for many days now baka daga kiranta?" Ya ɗan buda ido yace "No ban ga kiranta ba, or may be ban lura ba, but zan kirata" Mami tace "Ita kuma yarinyar can wato gidansu ta koma ko" Khalil ya sauke idonsa yace "Ehh" Mami tace "Ikon Allah, toh Allah ya kyauta, dama can ba wai ta saki jiki bane a wajen nawa, gwara ta koma gaban iyayen nata su kara sa mata ido don har ga Allah hankalina bai kwanta ta zauna wajen mu ba, kada taje ta ci gaba da abubuwan da take a makaranta mu muna nan gida bamu sani ba, so i am happy da ta koma gida" Shi dai Khalil bai ce mata komai ba, Mami tace "Don yarinyar na bukatar sa ido sosai, a shekarunta in zata iya aikata abinda ta aikata a social media to komai ma zata iya yi, dubi dai yanda babu tsoro ta bi dare ta kama hanyar kano, abun nan yayi mugun daure min kai wallahi" Still Khalil dai bai ce komai ba, Mami tace "Toh ya ku ka yi da iyayen nata da kaje can din?" Ya girgiza kai yace "Ba komai, the most important part is that gida ta koma ko da dai bamu iya mun rike masu ita ba" Mami tace "Aa baka masu bayanin yanda mu ka nemeta muka rasa bane? Ae ba wanda ya ki riketa, kin zama tayi instead" Yace "It's not necessary Mami, kinga sanda take gidan Aunty Maryam ai bata taɓa attempting barin gidan ba, she was sad and cried all throughout bayan tafiyar Aunty Maryam" Mami dake ta kallonsa tace "Toh me kake nufi yanxu?" Yace "Aa ba komai" Nadeeyah ta shigo parlon da sallama ta ajiye masa tray me dauke da ruwa da lemo a kai, tana kallon Mami tace "Sannu Mami" Mami tace "Sannu Nadeeyah, kun gama girkin" ta girgiza kai tace "Aa da saura" Daga haka ta mike ta nufi kofa, khalil ya dau ruwan gora ya bude ya sha, Mami tace "Tashi zaka yi ka tafi ka dauko min takardun yanxun nan" Yace "Toh, amma ki bari sai gobe Mami, it's almost magrib yanzu" Mami tace "Why not today?" Yace "Baya nan kusa sai naje na dauko" Mami tace "Toh Allah ya kai mu, da baka aikata wannan abun ba ko ni zan same Abban naku ince ya bada makullin gida za aje kai kaya ina da tabbacin baxai hana ba wllh, amma ka zo ka ɓata sha'anin" Khalil dai yayi shiru yana kallonta, don yanzu gaba daya hankalinsa yayi can gida bai son gari ya fara duhu bai koma ba, Mami tace "Ka ɗan samo min fruits masu kyau idan na koma gida xa a min fruit salad" Yace "Babu a gida ne?" Tace "No, i need fresh fruits" Yace "Ohk" Daga haka ya mike yace "But ba fa mota a gurina Mami" Tace "Ka amshi makulli wajen driver na yana waje, i will call him ya baka" Mikewa Khalil yayi ya nufi kofa ya fita, Nadeeyah na zaune parlor ya karasa kusa da ita yace "Zan je grocery in dawo yanzu Babe" Ta daga kai ta kallesa tace "Can we go together?" Yace "Sure" Ta mike tace "Bari in gaya ma Mumy" Daga haka ta tafi dakin Mumy, shi kuma ya fita ya samu sojan dake tsaye compound kusa da Motar Mami, yana isa ya mika masa hannu babu yabo babu fallasa yace "Bani makulli" Sojan ya mika masa don Mami ta riga ta kirasa kafin Khalil ya fito banda haka da baxai basa ba, in akwai wanda Khalil ya tsana a rayuwarsa bai wuce soja ba, ji yake kamar ya makuresu, he detest the sight of them, ga shi sun fi goma a gidansu, fuska daure ya bude motar ya shiga, yana ta zaune driver seat har Nadeeyah ta fito looking so cute, kallo daya yayi mata ya dauke kai, ta karaso ta bude gaban motar ta shiga sannan mai gadi ya bude masu gate suka bar gidan, Khalil na Driving din yace "So where did u suggest i should rent an apartment for us??" Tace "Amma wannan gudun na meye kake yi haka?" Yace "Abokina na jirana before magrib kinga ai it's almost magrib now shi yasa nake sauri" tace "Toh amma ka rage speed din pls...." Yace "Ohk" Tace "Duk inda kaga ya dace nan za mu zauna ai ko?" Yayi Murmushi ya gyada mata kai kawai, bayan ya siya ma Mami fruits Nadeeyah tace "Pls ina son zan ɗan yi shopping amma ba me yawa ba" Yace "Ki bari gobe Nadeeyah kinga sauri nake yanzu" Ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Toh Allah ya kai mu" Bai fasa gudun da tace ya daina ba har suka iso gida, bayan yayi parking ta bude motar ta sauka, ya ɗan zaro ido, don shaff ya mance bai mata tayin ice cream ko pizza ba tunda tana so sosai, kuma basu taɓa fita tare suka dawo bai siya mata komai ba sae yau, Yayi kasa da murya yace "Nadeeyah" Juyawa tayi ta kallesa, a hankali yace "I am sorry na mance i didnt get you anything, but let me order...." da sauri tace "Noo it's fine, ai sauri kake shi yasa, gobe idan mun fita sai mu siya in sha Allah" Yayi mata murmushi yace "Thank you" a mota ya bar fruits din Mami ya sauka ya ba drivern makullin sannan ya bi bayanta suka shiga gidan, Yana tsaye parlon Mum din Nadeeyah ya sanar ma Mami fruits din suna mota, Mami tace "Baxa ka tsaya ka ci abinci ba? Saurin meye haka kake yi" Da sauri yace "Aa Mami, ni a koshe nake" Tace "Toh wai saurin me kake haka?" Ya ɗan buda ido yace "Aa ni ba sauri nake ba kawai bana son a kira magrib ina nan ne" Mami tace "Toh gidan naka ka bude ka shiga??" Sai da yaji gabansa ya fadi, lokaci daya ya girgiza mata kai da sauri yace "Not at all, ina gidan abokina ne fa" Mami tace "Gobe karfe nawa zaka kawo takardun?" Yace "Da safe" Tace "Toh Allah ya kai mu" Daga haka yayi mata sallama tace "Ka jira mu fita tare mana sai mu ajiyeka inda zaka, nima yanzu zan tafi gida" Yayi karfin halin cewa "Noo i am fine Mami, Bolt na jira na a waje tun dazu" a hankali Mami tace "Toh Allah ya tsare" Yace "Ameen" Daga haka ya fita daga parlon ta bi sa da kallo, Ko sallama bai yi ma Nadeeyah ba balle Mum dinta ya bar gidan. Ana idar da magrib Khalil ya isa gidansa don sai da ya tsaya eatry ya siyo abinci with drinks da bottle water, 3 houses away from his house yaga sojoji hudu a tsaye kofar gidan, nan ya fara imagining gidan waye wannan kuma har da sojoji masu gadinsa, ya tsani yaga an cika ma gida sojoji a bakin gate, ya ciro Makullin gidansa a aljihu ya bude ya shiga ciki, yana bude kofar main parlon Nihad ta mike tsaye da sauri, ya kulle kofar ya karasa ciki yana kallonta don kana ganinta zaka san ta ci kuka ba kadan ba, taki yarda su hada ido ta koma ta zauna saman Carpet ta dauke kai ta wani hade rai, ajiye ledan hannunsa yayi ya wuce sama ta bi sa da harara, har bayan minti goma bata ga ya sauko ba, ta jawo ledan da ya ajiye a hankali tana duba ciki, taga jollof rice ne da fried rice a takeaway daban daban sae kaza, jollof rice din ta dauka ta fara ci, har kuma ta gama cin abincin bai sauko ba, ta mayar da empty takeaway din sannan ta matsar da ledan daga kusa da ita, sae gashi ya sauko sanye da jallabiya bata taɓa ganinsa da jallabiya ba sai yau, ya karaso cikin parlon ya bude ledan ganin empty takeaway ya daga kai ya kalleta for like 20 seconds, sai kuma yace "Ke fa hana mutane abincin kike a gidanku, nan ba a hanaki ba an siyo baki jira a baki ba kin dauka, who does that?" Sai a sannan ta kallesa kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Toh me mutum yayi kafin aka hanasa abincin a gidan namu?" As if that was what he was waiting for ya zauna yace "Ba abinda yayi kawai baƙin hali yasa aka hanasa" Ta masa wani kallo tace "Aa ya dai tuna abinda yayi" Kallonta ya dinga yi, ta turo baki ta mike ta dau goran ruwan da ta rage, ta koma can jikin wani kujera ta zauna, sai kuma yayi murmushi, ya bude fried rice din da ta bar masa ya fara ci, lokaci lokaci yake daga kai sai su hada ido don kallonsa take, da sauri kuma take dauke idonta, sun yi hakan kusan sau uku, a na hudun ne ta mike da sauri, yace "Ina za ki?" Bata bari sun hada ido ba ya ga ta wuce sama ya bi ta da kallo, nan parlon yayi isha ya kai sauran abincin kitchen ya ajiye, babu abinda babu a katon kitchen din kamar da mace a gidan, komai kuma sabo ne, ko gas din gidan ba a taɓa kunnawa ba, ya kashe wutan kitchen din ya fito, ya haura sama, master Bedroom ya shiga ya yi wanka sannan ya saka pajamas dinsa yana zaune gefen gado ya dau wayarsa ganin kiran Nadeeyah ya kirata, tana dagawa yace "Hello dear" Tace "Shine ka tafi ba ko sallama Dr?" Yace "Ai nace maki sauri nake ana jirana" a hankali tace "Ohk, ya hanya?" Yace "Alhamdulillah, Mami ta tafi gida ai ko?" Tace "Yea tun daxu" Yace "Ohk, ya ake ciki?" Tace "Dama ina son zan maka maganar kayan da za muyi fitar biki ne...." Yace "Ohk, kawai kiyi shawara da frnds dinki sai ki gaya min" Tace "Alright?" Yace "Shikenan maganar?" Da mamaki tace "Are u eager to cut the call?" Da sauri yace "Noo, kawai dai i am tired ina son zan kwanta ne da wuri" tayi shiru, yace "Hello?" A hankali tace "Ohk, good night" Yace "Hope u ain't taking it personal?" Har hawaye ya cika idonta tace "Yaushe rabon da mu yi magana a waya, kai idan ban kiraka ba baka kirana, kuma na kiraka yanzu kana ce min bacci zaka yi, shikenan kayi baccinka kawai ba damuwa" Ya sauke wani ajiyar zuciya yace "I am sorry Nadeeyah, to yanzu meye labari?" Tace "Noo, kawai kayi kwanciyarka sai da safe" Yace "I will sacrifice that because of you my love" Taki ce masa komai, sarai yasan kuka take.... A hankali yace "Nadeeyah" taki amsawa, yayi kasa da murya yace "Ke komai kuka, duk randa na maki kishiya shikenan haka zaki dinga mata kuka ita ma har ta raina min ke?" Diff yaji ta katse wayar, ya wara ido, nan ya dinga kiranta taki dagawa, ya kirata ya kusa sau hudu bata daga ba, ya ajiye wayar sai ga kiran Aunty Maryam, sai da gabansa ya fadi, for almost 3 days now yake ignoring kiranta don yasan dalilin kiran nata, yana ta kallon wayar har ya kusa katsewa can dai ya daga a hankali ya kai kunne, yayi gathering courage yace "Hello Aunty" Daga daya bangaren tace "Shaye shaye ka fara yi ne kana ganin kirana baka dagawa Khalil? Kiran na wa kake ignoring??" Da sauri yace "No ba haka bane Aunty, kawai i am not my self this days ne shi yasa, amma kiyi hakuri don Allah" Aunty Maryam tace "Yanzu dai ina Nihad? Mami tace min ta koma gidansu, garin yaya hakan ta faru Kjay? And did the parent accept her??" Yace "Gidansu Nadeeyah Mami tace ta koma saboda su Aunty Hassana, ita kuma a ranan ta bar garin which means bata son zaman gidan...." Aunty Maryam ta bude baki cike da mamaki tace "Ikon Allah, kaga kuma Mami bata gaya min haka ba wallahi, ce min kawai tayi an nemeta an rasa, daga baya aka gano ashe gidansu ta koma" Khalil dai yayi shiru, Aunty Maryam tace "Amma Mami bata kyauta ba, yanzu saboda su Aunty Hassana ta ki rike baiwar Allahn nan? Me yasa Mami tayi haka kai me baya? Gaskiya ban ji dadin jin haka ba, ka tabbatar kuma gidan nasu ta koma Khalil? Kar fa wani wajen daban ta tafi" Khalil yace "Can ta koma Aunty, naje har gidan nasu, i came back today" Aunty Maryam tace "Allah sarki, to me ya samu wayar da na bata ba a samunta, Ayman ma har ya gaji da kiranta" Khalil yace "I think charging point din ne ya lalace" Aunty Maryam tace "Toh ai kana da number Mamarta ka turo min yanzu" Khalil yace "Oh ohk, amma ba a wannan wayar nake da number ba, idan na kunna wancan wayar zan tura maki" Aunty Maryam tace "Toh yau nake son ka turo min Malam, don't keep me waiting" A hankali yace "Ohk" tace "And lastly Mami tace min ka kwashe takardunka da Cv a dakin Abbanku, ta kuma ce zata amsa ta mayar masa, to shawaran da zan baka kada ka kuskura ka bata ko me zai faru kuwa, ban san me ke damun Mami ba kwata kwata wallahi, don't make that mistake of giving her na gaya maka, idan ma ya kama ka bar masu garin ne ka bari gaba daya, ta yaya ita bata kwatar maka hakkin ka ba ka kwata da kanka kuma take neman amsa ta mayar masa, wannan wace irin rayuwa ce?" A hankali Khalil yace "Ban san yanda zan yi ba Aunty, and she is taking the issue so personal" Aunty Maryam tace "Kaga idan ya kama kawai ka taho inda nake kayi zamanka cikin kwanciyar hankali, with ur qualifications zaka samu aiki me kyau a nan, kada ka wani tsaya biyewa Mami...." Khalil yayi murmushi yace "Nagode Aunty" Tace "Toh ni dai na gaya maka, kuma ina jiran number Maman Nihad" Khalil yace "Toh Aunty" Daga haka ta katse wayar, ya sauka ajiyar zuciya ya ajiye wayar yana nazari, bayan few minutes ya mike ya fita daga dakin, dakin da Nihad ke ciki ya nufa ya bude a hankali, zaune ya ganta gefen gado ta daura sabon towel da ta gani cikin press din dakin tana shafa turarurrukan ta alamar wanka tayi, tana ganinsa ta jawo hijab dinta ta rufe duk jikinta, ya tsaya jikin mirror ya rungume hannunsa yana kallonta ga kamshinta da ya cika masa hanci, bayan few seconds ta daga kai ta kallesa tace "I need space" Ya ki ce mata komai kuma yaki barin dakin, ganin hakan ta mike ta dau doguwar rigar baccinta zata shiga banɗaki yayi saurin riketa, zaro ido tayi tace "Ni wallahi ka sakeni in je in sa kayana, meye haka mana" Ya janye hijab din ya jefar saman gado dama tana ganin haka ta rike towel dinta gam tana zazzare ido, hankalinta a tashe kamar zata yi kuka tace "Meye haka kake yi don Allah? It's not proper plss" Ya kai bakinsa kunnenta ya rada mata magana a hankali, sannan ya kalli fuskarta to see her reaction, ta marairaice zuciyarta na bugawa amma ta kasa hada ido da shi, maganar nasa yayi mata nauyi sosai, mamakin yanda baya jin kunya ko kadan take, murya can kasa taji yace "Agreed?" Still taki kallonsa balle ya sa ran amsa, zai dago kanta taki barin yayi hakan gaba daya a tsorace take, ya kai hannu towel din ta rike hannunsa da sauri muryarta na rawa tace "Why are you doing this plss? Ni fa ba er iska bace" Ya kai bakinsa kunnenta a hankali yace "Toh ni ne ɗan iska?" Ta kasa ce masa komai banda bugawa babu abinda zuciyarta yake, amma kuma a ranta taji gwara ta amince da abinda yace mata tunda iya hakan ne kawai, bata hanasa ci gaba da kwance towel din ba amma kafin ya cire ta rufe fuskarta jikinsa da sauri jikinta na rawa tace "Ni akwai haskeee" yanda tayi maganan just turned him on the more, ga kamshinta da ya gama rikitasa, Yana rike da ita ya nufi wajen switch din duk da yanda kafafuwansa suka masa nauyi, ya kashe wutan dakin, tun tana nonnoke masa har bata san sanda ta sakar masa jiki gaba daya ba kamar ba ita ba, he made sure she savour every bit of that moment, he let her forget the global she was in, lokaci daya hankalinta ya dawo jikinta bayan kusan minti sha biyar, tana zaro ido ta fara turasa tace "Kace min banda shi, wayyo na shiga uku, You excluded that..." cikin shaky voice yace "Plsss" ta fashe masa da kuka tace "Nooo, baxan iya ba wallahi" Bashi da option haka ya kyaleta cike da karfin hali ya koma gefe yayi kwanciyarsa upside down, har sannan jikinta rawa yake ta jawo hijab dinta da sauri ta saka, tashi taga yayi wanda hakan sai da ya tsoratata ta koma edge din gadon da sauri jikinta na rawa, sai taga ya sauka daga kan gadon, ta bi sa da kallo cikin duhun har ya shiga bandaki, sai da ya kusa minti ashirin kafin ya fito taga ya kwanta a kasan dakin, ita dai tana ta kallonsa cikin duhun, har dai ta gaji ta kwanta a hankali ta rufe idonta amma ta kasa bacci, tana ta kwance har kusan sha biyu, tana jin yanda yake juye juye a kasa da yake kwance, ta mike zaune tana kallonsa, can kuma dai ta sauka daga kan gadon ta koma inda yake ta durkusa dan nesa da shi duk da ba sosai take ganinsa ba saboda duhu tace "Are you okay?" A hankali taji yace "I am not" Bata san sanda ta isa dab da shi ba ta durkusa tace "Baka da lafiya ne?" You could tell from her voice that she is worried, taji ya jawota jikinsa with trembling voice yace "I promise i won't hurt you, i promise, i promise" Sae da taji wani mugun faduwar gaba, ta fara kokarin tashi daga jikinsa ya ki saketa yana maida numfashi yace "Plsss, i promise it won't hurt, trust me Nihad" Bai bata damar cewa komai ba ya cire hijab din jikinta ya jefar.


Mami ta kasa bacci tun da taji fitar motocin operation biyu na sojoji dake gidan wajen karfe biyun dare, kuma General na gidan, gaba daya ta kasa samun nutsuwa, ta kira Khalil yafi sau goma bai daga ba, kuma tasan bashi da nauyin bacci, ko karfe nawa ka kirasa na dare zai daga, sai ta fara tunanin to ko yana zaton maganar takardun zata masa yasa ya ki dagawa, ita kuma so take taji inda yake, daga karshe ta kira Aunty Maryam, Aunty Maryam na dagawa Mami tace "Maryam yanzu naji fitar motocin operation a gidan nan, to gaba daya hankalina yaki kwanciya, you know how cunning general can be, to na kira Khalil baya daga kirana, ki kirasa ki ji yana ina, though ni dai yace min ba gidan nasa yake ba, amma ki kirasa pls" Aunty Maryam tace "Toh bari in kirasa" Ba a dau lokaci ba Aunty Maryam ta kira Mami tace "Mami wallahi baya dagawa" Mami taji hankalinta ya kara tashi, a hankali tace "Toh shikenan Maryam" Aunty Maryam tace "In sha Allah babu abinda zai faru Mami ki kwantar da hankalin ki, balle ai General din ba sanin inda yake yayi ba" Mami tace "Toh shikenan, sai mun yi magana" Daga haka ta katse wayar ta ajiye tana ma ɗan nata addu'ar neman tsari daga Abbansa.


*TWINS NEEE......

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post