Nihaad page 71

Nihaad page 71

Nihaad page 70

 💖💖 NIHAAD 💖💖


71


Sai bayan Magrib Mumy ta tada Nihad dake ta bacci tun dazu, Nihad ta bude ido a hankali, Mumy tace "Ki daure ki tashi kiyi sallah, anyi magrib" Mikewa zaune tayi, cikin sanyin murya tace "Mumy ya jikin Abbana?" Mumy tace "Da sauki, je kiyi alwala" sai da Mumy ta ga shigarta bandakin sannan ta fita daga dakin, Nihad na ta zaune kan darduma bayan ta idar da sallahn tana son tashi ta tafi bangaren Abbanta ta dubasa amma kasala ya sa ta kasa tashi, Mumy ta dawo dakin tana kallonta tace "Ki tashi kije ki samesa a parlor" Mumy na fadin haka ta bar dakin, Nihad ta mike da kyar ta fito parlon Mumy ta ga Khalil a zaune, Tun da ta fito yake kallonta don gaba daya a sanyaye take, kana ganinta ka ga damuwa karara a tare da ita, ta zauna saman kujera tana kallonsa amma bata ce komai ba, tashi yayi ya koma kusa da ita ya zauna ya kamo hannunta cikin kwantar da murya yace "Abba will get better soon in sha Allah, ki kwantar da hankalinki kin ji" Kamar jira take ta fashe masa da kuka sosai, cike da damuwa yace "Noo pls, i am assuring you he will be fine in sha Allah, trust me" Girgiza masa kai kawai tayi amma ta kasa cewa komai, ya rungumeta yana lallashinta, har dai ya samu ta daina kukan, wayarsa ne ya fara ring ya ciro ganin farooq ne ke kiransa yace "I am coming back now" Daga haka ya mike ya fita daga parlon, Nihad ta bi sa da ido hawaye na sauka fuskarta, Khalil na fitowa main parlor ya tafi bangaren Abba, yana cikin duba sabbin magungunan Abba da Farooq ya siyo Inna ta bude kofar dakin ta shigo rike da katon cooler, Duk suka daga kai suna kallonta ta ajiye coolern hannunta, sai kuma ta rushe da kuka tace "Allah ya tashi kafadunka Ibrahim, Allah ya baka lafiya, saura kiris ina tahowa yanzu mota ta bigeni saboda rashin nutsuwa, da yake babu wanda ma yasan na fito daga gida, da kafa na zo gidan nan wllh" Farooq yace "Ba dazu kika tafi ba Inna ai da baki sake dawowa ba sai gobe, kinga ai jikin nasa da sauki Alhamdulillah" Cikin kuka inna tace "Ina zan ga nutsuwar jira har gobe in dawo Farooq? Ai gwara in dawo nan din gaba daya kawai, Abincin da aka kawo min ko budewa ban yi ba na dauko kawai na saɓa gyale na biyo hanya in kawo masa ko zai iya ci" Khalil ya ajiye maganin hannunsa a hankali yace "Ina yini Inna?" Cikin rawan murya tace "Lafiya lau" Daga haka ta tafi wajen Abba dake ta bin ta da ido ta zauna gefensa tace "Yanda baka kashe ubanka ba ko uwarka to babu ɗan ɗa zai kasheka Ibrahim, in Allah ya yarda ba baƙin ciki bane ajalinka, Allah zai baka lafiya kayi rayuwa me tsayi ka ci gaba da bauta masa, sannan ka ci gaba da taimakon bayin Allah kamar yanda ka saba" Khalil ya mike kawai ya fita daga dakin, Main parlor ya koma ya zauna, har sannan ya ji ya kasa yarda da abinda Farooq ya sanar masa akan Nihal, he is still finding it hard to believe this, Mumy ta fito daga kitchen rike da cup din kunu, ganinsa a parlon tace "Ibrahim abincinku kai da farooq na can dakinsa" Khalil yace "Toh mun gode" Zata wuce yayi karfin halin cewa "Mumy ina son ganin Nihal" Mumy ta juya tana kallonsa, ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "To ina zuwa" Bangarenta ta tafi dama kuma dakin Nihal din zata shiga ta dau makulli a bedroom dinta tana kallon Nihad da ta kwanta gefen gado sai juye juye take tace "Za ki sha kunu ko?" Nihad ta kalli Kunun hannun Mumy sai kuma ta gyada mata kai a hankali, Mumy tace "Ina zuwa" Daga haka ta fita daga dakin ta tafi dakin Nihal, bayan ta bude ta shiga dakin, kwance ta sameta kan gado idonta biyu, pillownta yayi jagab da hawaye, Mumy ta ajiye Cup din hannunta ta zauna gefen gadon tace "Ibrahim wants to speak with you Nihal" Nihal ta dinga kallonta alamar bata san wani Ibrahim din ba, Mumy tace "Mijin er uwarki" Nihal bata iya tace komai ba, lokaci daya wasu hawayen suka cika idonta, Mumy ta juya ta fita, bayan ta koma main parlor tana kallon khalil tace "Ka karaso Ibrahim" Mikewa yayi ya bi bayan Mumy har zuwa bakin kofar dakin Nihal, sannan Mumy ta juya ta bar wajen, a hankali ya murda kofar dakin hade da sallama ya shiga, Nihal dai na zaune gefen gado, ya karasa har gaban mirror din ya rungume hannunsa yana kallonta, ita dai ta kasa barin su hada ido, haka nan kawai yaji tausayinta ya dirar masa a zuciya, a hankali yace "Nihal" Ta daga idanuwanta da suka kumbura tana kallonsa, lokaci daya ta fashe masa da kuka, ya girgiza kai yace "Ba kuka na shigo ki min ba, now tell me who is responsible??" Kuka kawai take bitterly ta kasa ce masa komai, yace "Who is responsible Nihal?" Ta hade kanta da gado still crying loudly, sauke idonsa yayi daga kallonta, yana jin tausayinta har cikin ransa, ya barta tayi kukan me isarta sannan yace "Now tell me who is responsible" Ta dago kanta a hankali tace "Abdallah" Yace "Who he is? And a ina kika san sa?" Cikin rawar murya tace "Babansa Minister ne" Khalil ya ɗan yi shiru, can yace "Minister of what" ta girgiza masa kai tace "Nima ban sani ba" Yace "Toh a ina ku ka hadu da shi?" Tace "ABU yaje wajen wani abokinsa da yake masters a can" Yace "Sai me ya faru?" Bitterly tace "Yana ta bi na a makaranta for like two days requesting for my phone number, he said he only wants us to be friends, shine na basa amma ni bana son waya da shi, har na dawo gida hutu sai yayi ta kirana bana dauka, Umma tayi noticing shine ta sa na fara picking calls dinsa ba da son raina ba, har cewa take in bata su gaisa da shi, sanda ya zo kano yace zai gaisheta sai ta tafi gidan friend dinta Mama Turai ya sameta a can suka gaisa, tun daga sannan Umma take forcing dina sai na dinga kulasa sosai" Kuka take sosai kamar ranta zai fita, khalil yace "Ina jin ki" Tace "Dalilin da yasa na fara kulasa kenan, duk weekend yana shigowa Zaria wajena" Yace "Daga ina yake zuwa" tace "Abuja" Khalil yace "Sai me ya faru?" Tace "He is always requesting to take me out for shopping, dama Umma tace kada ince zan bi sa wani waje kuma kar ince zan shiga motarsa, shine ranan ya kirata yace za mu je yayi min shopping amma nace masa ta hana ni fita daga makaranta yana neman excuse to go out with me for shopping, shine Umma ta amince ya fita da ni ranan" Shiru tayi tana goge hawayen idonta, Khalil yace "Go on" tace "Muna shiga mota muka tafi yayi min shopping, bayan mun fito daga shopping mall din ya dau drink a motarsa ya bani nace masa am okay, sai ya nuna min bai ji dadi ba... Shine na amsa kawai, sai da muka koma makaranta na sha drink din da shawarma dat he bought me" Khalil yace "A ina kika sha?" Ta daga kai ta kallesa tace "A motarsa" Yace "Why did u eat in his car?" A hankali tace "He insisted, shi ma a ciki ya ci nasa, shi yasa nima na ci" Khalil ya gyada kai, a hankali yace "And then?" Wasu hawaye na sauka idonta tace "I don't really know what happened after that, I don't understand" A hankali Khalil yace "Did u pass out?" Tace "Noo, but i wasn't my self, i remember him telling me bari mu siyo wani abu mu dawo, shine ya kai ni wani waje, i still can tell ko gida ne ko ba gida bane...." Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka, Khalil ya kasa cewa komai yana kallonta, ta goge hawayen idonta tace "Bayan wannan incident din sai yayi ta threatening dina that he have my video if i should say no to him zai yi leaking dinsa, i was confuse on what to do and who to tell.... I was so confused" Khalil yace "Me yasa baki gaya min ba?" Ta kasa ce masa komai hawaye na ta sauka idonta, tace "Shikenan, and i neva said no to him ko me yace min, saboda ina tsoron threat dinsa" Khalil yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, and he kept on using u?" Ta gyada masa kai, yace "Did u tell him about the pregnancy?" Ta gyada kai tace "He blocked me bayan na gaya masa" Khalil yace "Kina da hotonsa?" Ta girgiza masa kai tace "Na goge dukka har da numbersa, but i have his IG handle yana so hotunansa a can" Ya ciro wayarsa yace "Gaya min handle din nasa" a hankali ta gaya masa, yayi searching sunan a Instagram, yana fito masa ya fara shiga hotonsa, Still Khalil yayi yana ta kallon hoton da mugun mamaki yace "This is Abdullahi" Nihal dai tayi shiru tana kallonsa hawaye na sauka idonta, Khalil ya kasa rufe baki ya kalleta da sauri yace "I know him, he is Aliyu's friend, is he the one u are saying about now??" Nihal ta fashe da kuka ta hade kanta da gado tana shessheka, Khalil ya girgiza kai sadly yace "He lied to you, ba ɗan minista bane shi kamar yanda ya gaya maki, gaba daya Clique dinsu ba su da aiki sai na karyan identity da yaudaran yaran mutane, makaryata ne na karshe... Aliyu is his very close frnd" Khalil yayi wani murmushin takaici yace "In his next life bazai sake lalata kowa ba...." daga haka ya juya ya fice daga dakin, Nihal dai ta bi sa da kallo hawaye na sauka idonta. Khalil ya koma dakin Farooq ya zauna yana tunanin ta yanda zai billo ma lamarin nan, banda tafarfasa babu abinda zuciyarsa yake, he is going to make sure Abdullahi bazai sake moruwa a rayuwa ba, yanda ya lalata ma Nihal rayuwa shi ma sai inda karfinsa ya kare na ganin ya lalata masa rayuwa kafin hukuma su shigo ciki, And he felt so bad he didn't listen to her ranan da ta kirasa yana tare da Nadeeyah, he wish yayi taking excuse daga gun Nadeeyah ya tafi gefe ya saurareta may be da abubuwan sun zo da sauki, yana ta tunane tunanen nan Farooq ya shigo dakin, Farooq ya ajiye wayarsa gaban mirror yana kallon Khalil yace "Ka zuba abincin ka ci" Khalil ya kallesa yace "Ka ba ma Nihal listening ear?" Farooq ya girgiza masa kai kawai ya shiga banɗaki alamar bai ma son zancen, Mikewa yayi ya fice daga dakin ya tafi waje gun Aminu a bakin gate, tun shigowarsa gidan dazu da rana Aminu ya sanar masa abinda ke faruwa a gidan, wanda sai da ya samu benchi ya zauna saboda shock, yana shiga cikin gidan kuma Farooq ma bai boye masa komai ba ya sanar masa abinda ke faruwa, Aminu na hango Khalil ya mike tsaye, har Khalil ya karaso, Aminu yayi kasa da murya cike da damuwa yace "Jikin me gidan da sauki yanzu? Ni dai dazu da na shiga dubasa bakin ya sake rufewa" Khalil yace "Da sauki Alhamdulillah" Aminu yace "Allah Ubangiji ya tashi kafadunsa, Allah ya basa lafiya, mutumin kirki wallahi" Khalil yace "Bari in shiga Masallaci Aminu" Daga haka ya fita daga gate din zuwa masallaci. Karfe tara saura Khalil yayi sallama kofar parlon Mumy, bayan ta amsa masa ya shiga, Nihad na kwance saman kujera ga kunun da Mumy ta kawo mata ta kasa sha, tayi amai kuwa ya fi a kirga, Mumy tace "Kun ci abinci dai ko?" Yace "Ehh, Mamina ce zata maku magana" Mumy tace "Toh" wayarsa ya kai ma Mumy, Mumy ta amsa ta kai kunne hade da yin sallama, Mami ta amsa daga daya bangaren bayan sun gaisa ta tambayeta jikin Abba, Mumy tace "Jiki Alhamdulillah mun gode Allah, ya yaran?" Mami tace "Alhamdulillah, Allah Ubangiji ya tashi kafadunsa, ya basa lafiya" Mumy tace "Ameen Hajiya nagode" Mami tace "Zan sa ya tura min numberki inyi saving in sha Allah" Mumy tace "Toh ba damuwa" Mami tace "Nihad na kusa?" Mumy tace "Eh ga ta" Daga haka ta mika ma Nihad wayar, Nihad ta mike zaune bayan ta amshi wayar ta kai kunne, suka gaisa da Mami, Mami ta tambayeta jikin Abba sannan tace "Hope kina ɗan cin abinci?" Nihad ta gyada kai a hankali tace "Ehh ina ci" Mami tace "Toh maa sha Allah, mu kwana lafiya" Nihad ta mata sai da safe sannan ta katse wayar Khalil ya karasa ya amsa, bai jima a parlon ba ya fita. Wajen karfe sha daya saura Khalil na wajen Abba tare da Farooq da Usman da ko awa biyu bai yi da shigowa gidan ba, sai yayan Abba Alhaji Abubakar dake shirin tafiya gida, Inna ma na makale dakin taki tafiya wai gidan zata kwana, Abba na ta kallon Alhaji Abubakar da ya mike yana lallaba inna ta tashi su koma gida da kansa zai dawo da ita gobe da safe, a hankali Abba ya buda baki yace "Akwai maganan da zan yi Alhaji" Alhaji Abubakar ya kallesa sannan ya koma ya zauna, tun bayan da ya sha magungunan da Khalil yayi prescribing din masa dazu da yamma yake ɗan iya bude baki yayi magana har ya fito, Alhaji Abubakar yace "Ina jin ka Ibrahim" Mikewa Khalil yayi yana son barin dakin Abba yayi masa alama da ya koma ya zauna, inna warce ke ta farin ciki ɗan nata ya fara bude baki har aji abinda yake cewa ta kalli Khalil da sauri tace "Koma ka zauna Halilu ai ka zama ɗan gida yanzu... Duk daya muke da kai" Khalil ya koma ya zauna, Abba ya kalli Farooq yace "A kira min duk yan gidan, har Nihad da su Kamila" Farooq ya mike ya nufi kofa walking slowly ya fita, Bangaren Mumy ya fara zuwa ya sanar ma Mumy sannan ya juya ya fita, tun dazu Mumy ke son taje dakin mai gidan nata ta duba jikinsa amma ta kasa saboda Inna da tayi bake bake a dakin sannan kuma Alhaji Abubakar tun isha yake gidan, Nihad ma ita ta hanata zuwa saboda yanayin jikinta duk da yanda ta damu tana son zuwa amma tsayuwan kirki bata iya yi for long balle tafiya zuwa bangaren Abba, Farooq na fita side din Mumy ya tafi bangaren Umma, tana zaune kan darduma can karshen bangon dakinta sanye da dogon hijab hannunta rike da carbi, tun da tayi sallan asuba take wajen nan, sai dai taje ta sake alwala ta dawo ta zauna, Farooq ya sanar mata kiran Abba sannan ya juya ya fita, shi ma duk kamar ba shi ba, gaba daya a sanyaye yake, sosai gaban Umma ya fadi, amma haka ta dake ta mike tana jin jiri idanuwanta sunyi bulu bulu, circle din idon yayi bakikirin tsabar kuka da tashin hankali, duk ta fice hayyacinta ta dawo gata nan gata nan ne, sai da ta shiga bandakinta ta sake dauro alwala sannan ta fito tana jan kafa ta tafi bangaren Abba, har bedroom dinsa ta shiga da sallama, nan taga har Mumy da Nihad a dakin, ga Inna da Alhaji Abubakar, Khalil da Usman, Kamila da Amina, Nihal ce kadai bata dakin, Umma ta nemi gefe ta rakube amma bata bari ta hada ido da kowa ba na parlon, Farooq ya karasa ya zauna inda yake, Abba dai bai ce komai ba sai kallon ceiling yake, lokaci lokaci Inna ke sauke ajiyar zuciya take girgiza kafa, Alhaji Abubakar yace "Ga su nan gaba daya Ibrahim, muna kuma sauraronka...." Abba ya dinga bin su da kallo a parlon kafin a hankali yace "A da na so barin abinda zan fada a yanzu ya zamo wani sirri tsakanina da Sumayya sai kuma Maryam, amma yanzu hakan bazai yiwu ba saboda there is need for me to speak out, don haka nake sanar da cewa for almost a month now babu aure tsakanina da Sumayya, zaman 'ya yanta kawai take a gidana, na kuma bata dama ta ci gaba da duk harkanta kamar yanda ta saba a gidan nan" Kowa na dakin sai da ya girgiza barin Farooq da ya kasa daina kallon mahaifin nasa, Umma dai kanta na kasa taki dagowa, Inna ta saki salati ta mike tana tafe hannu tace "Ka saki sumayya??" Alhaji Abubakar yace "Ki koma ki zauna Inna" Ta koma ta zauna tana kallon Umma baki sake, Abba yace "Bayan ni da ita babu wanda yasan dalilin sakin nata, don hatta Maryam ban sanar ma ba, ta dai san babu aure tsakaninmu amma yanzu zan sanar ma kowa na dakin nan dalilin da ya sa na saki Sumayya kafin in shigo da ainahin maganar da yasa na tara ku a dakin nan...." Banda hawaye babu abinda Umma take, Nan Abba ya basu labarin wayan da ya tadda Umma ke yi a bandaki da kuma abubuwan da kunnuwansa suka jiye masa a ranan, Inna ta fashe da kuka ta mike jiki na rawa tana kallonsa tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, anya kunnuwanka sun jiye maka da kyau kuwa Ibrahim? Wannan sumayyar ko wata daban dai kake nufi?" A hankali Abba yace "Ga ta nan ki tambayeta ko ba ayi haka ba Baaba, ki tambayeta...." Umma ta fashe da kuka da karfi tace "Ko ma me nayi kai ne silla Ibrahim, kai ne ka kai ni ga duk halakan da na shiga a rayuwa, babu uwar da zata so taga ana nuna ma 'ya yanta halin ko in kula a kan 'ya yan kishiyarta, babu warce zata iya daukan wannan masifar, ka fifita Nihad akan nawa 'ya yan da na haifa maka kafin a haifeta, ka nuna Nihad ita ce er ka sauran kuwa ba naka 'ya yan bane hatta Nihal da take sa'arta baka damu da lamarinta ba sai na Nihad, ka banzatar min da nawa 'ya yan duk a kan Nihad, ka nuna ita ce er so, kaf gidan nan babu ɗan da ka cire kudi ka biya ma tsadadden makaranta tun daga Primary har secondary sai Nihad, a kan Nihad Kamila bata samu cikakken kayan daki ba ka gwammaci ka kai ta Private University bayan ni tawa er ka kai ta federal ka ajiyeta, kafin ka biya ma 'ya yana bukatansu daya ka biya ma Nihad bukatunta goma, shine nima na nuna nafi kowa sonta don ta haka ne kadai zan iya cimma burina na rama duk abinda kayi ma 'ya yana a kanta, you caused everything Ibrahim, duk abinda nayi ma Nihad kai ka jawo, barin ta zuwa hotels, clubs, party, bin kawayen banza.... kai ka kaini ka baro Ibrahim" Inna da ta hangame baki kamar yanda Mumy tayi ta dinga kallon Umma a tsorace, Kuka sosai Umma ke yi tana girgiza kai tace "Gashi yanzu ta dalilin son kanka duk wani mugun abu da na so ma Nihad a duniya sai da ya dawo kan nawa 'ya yan, ka cuce ni da yarana Ibrahim, ka cucemu...." Ta Kasa ci gaba tana kuka sosai kamar ranta zai fita, a mugun fusace Inna ta nufeta tana kunduma mata zagi tace "Allah ya tsine maki Sumayya, Allah ya isa tsakaninmu dake, dama can zuciyar kafurai gareki kada ki laka ma ɗa na, dama can ke kafura ce mara tsoron Allah, idan bai so Nihad ba wa zai so dama?? abinda uwarta sai da tayi shekara kusan talatin bata haihu ba a gidan nan babu irin walakanci da cin kashin da Maryam bata hadiya ba a wajenki, babu irin gorin haihuwan da baki mata ba sai wanda kika manta amma matar nan ta mika lamuranta ga Allah kuma bata fasa zama zuciya daya dake ba tana bin ki, kin xata duk mun manta wannan? sannan don ubanki da kike cewa an banzantar da 'ya yanki, ke kika rainar min farooq da Usman?? Ba duk wajena suka gama har sakandari ba kafin su tafi jami'a?? Wani abu ne na gata Ibrahim bai masu ba wanda har ita Nihad din ban ga ta samu irinsa ba? Wani kula ne Ibrahim bai ba yaran nan ba da suke wajena Sumayya?? Wani kudi ne bai kashe masu ba? Kamila da kika ce kudin kayan dakinta bai cika ba karya fa kike son yi ya nuna maki bazai iya ba, yar gwal ce ita da za a siya mata kayan daki kusan miliyan goma a zamanin nan??? Sannan Nihal da kike cewa bai damu da al'amarinta ba ta ina ya shaku da ita yarinya duk kiwuya kowa ta maida shi dodo?? Ina ce har ni bata yadda da ni a sanda take karama? Kuma har yanzu da girmanta kin ga tana zuwa wajena? A ina kika taba ganin yaro me kiwiya an shaku da shi? Ai sai dai uwarsa, don haka duk sharrin da kika laka ma ɗa na Allah ya saka masa, Allah ya isa tsakaninsa dake, Wato har bedio da aka ce yana ta yawo na Nihad har da sa hannunki kenan??" Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka ta koma ta zauna, Nihad dai sai kallon Umma take hawaye na sauka idonta, shi kam Abba was speechless, Khalil ne ya fara tashi ya bar dakin, Inna tace "Aa dole ka tashi ashe duk ga warce ta gurbata rayuwar matarka tun yana er yarinya bamu sani ba" Sai kuma ta rushe da kuka tace "Allah na tuba ka yafeni da hadin bakina fa aka dauke Nihad daga wajen uwarta aka ba Umma ashe matar da sharri take nufinta bamu sani ba" Alhaji Abubakar sai share zufan da ke keto masa yake yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" A hankali Abba ya lumshe ido with tears in his eyes yace "I have failed as a father"

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post