Ana fargaba Shugaban Wagner Prigozhin ya mutu a wani hatsarin jirgin sama

Ana fargaba Shugaban Wagner Prigozhin ya mutu a wani hatsarin jirgin sama

Ana fargaba Shugaban Wagner Prigozhin ya mutu a wani hatsarin jirgin sama
BBC/SHUTTERSTOCK 

Shugaban sojojin hayar Wagner, Yevgeny Prigozhin ya mutu a wani hatsarin jirgin sama, tare da ƙarin mutum tara a cikin jiragen sama a Rasha.

An yi imani yana cikin jirgin saman da ya faɗi.

Tun da farko, wani zauren dandalin Telegram mai suna Grey Zone ya ba da rahoton cewa an harbo jirgin ne da wasu makaman kakkaɓo jiragen sama a yankin Tver, na arewacin birnin Moscow.

Jirgin saman, wanda ya tashi daga Moscow zuwa birnin St Petersburgh, ɗauke da fasinjoji guda bakwai da ma'aikatan jirgi uku.

Prigozhin ya jagoranci wani boren sojoji da bai yi nasara a kan rundunar sojin Rasha a watan Yuni.

Shafin Telegram na Grey Zone ya ruwaito mazauna yankin na cewa sun ji ƙarar fashewar wani abu har guda biyu kafin faɗuwar jirgin, kuma sun ga tururi guda biyu a lokacin.

Kamfanin dillancin labarai na Tass ya ce jirgin saman ya kama da wuta a lokacin da ya dira a ƙasa, inda ya ƙara da cewa tuni aka gano gawawwakin mutum huɗu.

Ya ce jirgin ya yi tafiyar ƙasa da rabin sa'a bayan tashinsa.

Kamfanin dillancin labarai na Rasha Interfax ya ruwaito ma'aikatar ba da agajin gaggawa na cewa ana kyautata zaton dukkan mutanen da ke cikin jirgin saman sun mutu, lokacin da ya faɗo ƙasa.


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post