Tabarmar Ƙashi page 18 by H U G U M A

Tabarmar Ƙashi page 18 by H U G U M A

Tabarmar Ƙashi page 18 by H U G U M A

 *H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

*Arewabooks:Huguma*

https://arewabooks.com/u/huguma

Page 18

      "Eheenn" sãahar ta furta a taqaice da alamun dake nuni da neman qarin bayani takeyi,sake zare hannunsa yayi daga kan system din,ya sanya idanunsa cikin nata a hankali kamar masu narkewa,wani abu me kama da fushi yadan ratsa ta tsakanin zagayayyun qwayar idanunsa

"Waye ya sallameki?" Ya fada kansa tsaye yana qanqance idanunsa cikin nata. Sai data kalli agogon hannunta sannan ta amsashi,tana jin kamar ta bude idanu taganta ba cikin office din ba,inda yasan yadda ta tsani hada hulda da maza da bai bari ta zauna tsahon mintunan da tayi a tare dashi ba,tana qoqarin hadiye fushinta ta amsa masa,saidai hakan bai boye tata izzar ba

"Lokacin daya kamata naci gaba da zama ya cika,inajin babu wani sauran abinda ya kamata na sani,inda akwai da ka sanar dani din"  yadda take maganar with confidence ya bashi mamaki,karon farko da wata diya mace ta taba tsaiwa a gabansa cikin nutsuwa irin wannan ta bashi amsa takai tsaye,ta kuma amsa masa da abinda ya fito kai tsaye daga zuciyarta. Hannu yasa ya jawo wani file dake gefansa

"Inason nayi alerting naki abu daya,ki tsaya iya matsayinki,kada maganganun Dr ya rudeki,kina da naki limit din,so do not exceed that limit,right?"

"Don't bother" ta amsa masa a taqaice,duk da tanason ta gaya masa sama da hakan,to amma a yanzun bata da buqatar doguwar magana,sannan bai kamata ta take maganganun dattijon da bai dade da gama gaya mata su ba,bata sake bata koda second biyu ba ta juya ta fice abinta ba tare data tsaya jiran abinda yakeson gaya matan ba.

           Sanda ta koma office sai abubuwan suka yita dawo mata,tanason taci gaba da aikin,amma kuma abinda ya faru cikin office din yana ta dawo mata a rai,a hankali sai zuciyarta ta fara zafi,ta dinga jan tsaki a jejjere,daga qarshe ta tabbatarwa kanta ba zata iya ci gaba da aikin ba,sai ta ture komai ta fara hada tarkacenta,ta dan debi wasu files da take tsammanin may be zata iya dubasu a gida,tabar office din bayan ta yiwa miss sameera umarnin ta rufe,ta dan bita da kallo tana mamakin yadda ta tashi abinda duk da lokacin tashi baiyi ba,bayan qaqqarfan jan kunne da CEO ya ajewa kowanne ma'aikaci akan makara da kuma tashi kafin cikar lokaci,a taqaice ma dai a kwanakin kusan kowanne ma'aikaci yana d'ara lokacin tashinsa,saboda yadda kowa ya maida hankalin wajen kawo daidaito da gyaruwar lamuran kamfanin.

           Tana driving a hanya zuciyarta tana dada yin zafi,ta yaya zata iya aiki da wannan mutumin?,ta yaya zata jure aiki dashi?,kwata kwata nashi da manners,baisan darajar mutum ba,koda wayeshi,kowanne irin matsayi yake dashi,itakam ba zata taba jure ya takata ba,ba zata dauki kowanne banzan hali daga wajen kowanne d'a namiji ba yanzun.

          Da wannan fushin da zafin zuciyar ta isa gida,tayi parking ta fito tana tattaro files din data taho dasu,fuskar nan a dinke na walwala taji takun afifa. 

        Ta cikin motar ta daga kai ta dubeta sanda take tahowa tana amsa waya,sanye da wata free gown,da alama tun dazun ta taso daga nata aikin,saita maida kanta taci gaba da abinda takeyi.

        Tana isowa gurin ta gimtse wayar tana dariya qasa qasa

"Oyoyo mr president,bari na kwashi tabarraki" ta fada tana murmushi tare da qoqarin karbar folders din hannun nata,batayi jayayya ba ta sakar mata,ta fara kulle motar,afifa na gyara zaman folders din a hannunta tace

"How was your day today?" Yi tayi kaman ta cilla mata harara amma sai ta fasa,ganin cewa ba ita takar zomon ba,don haka ta amsa mata cikin miskilancin nan nata

"Bad" ta fada a taqaice tana soma takawa zuwa ciki,afifa tabi bayanta da hanzari

"Kaman yaya?,your first day at work fa" kai ta jinjina mata kawai tana lumshe ido ba tare da tace mata komai ba,sai afifan itama bata qara tambayarta ba,sukaci gaba da takawa zuwa ciki.

        Maama ce zaune cikin falon,saman cinyarta wani dan bowl ne dake dauke da strawberry tana gyarawa,cikin kulawa ta amsa sallamar tasu idanunta akan fuskar diyar tata

"Barka da gida maama" sãahar ta fada tana isowa gabanta gami da duqawa,ta kuma dora saman cinyarta kadan. Murmushi ta sauke tana dubanta,gaba daya jiki da zuciyarta sun nuna gazawa xda gajiyawarta,saita zare hannunta daga cikin strawberry din ta dora saman kanta

"Barka kadai president dinmu,ya aikin?" Tabe baki tayi kamar wadda zata saki kuka,itako sunan batason a tuna mata,don da alama yaa muhyi ya bata aiki me wahala qwarai

"Ba dadi maama,ya muhyi yayi punishing dina ne kawai da wannan aikin" dariya afifa ta saki yayin da maama tayi murmushi

"Ba haka bane,da sannu dai zaki saba,qila ma ki dinga jin dadin aikin nan gaba kadan fiye da yadda muke tunani" miqewa tayi tana dan tura baki

"Anya maama zanso wannan aikin?"

"Ba wanda yasan gobe sai Allah" kai tadan jinjina

"Abba bai iso ba?"

"Ya kusa,inajin sai an idar da sallar magrib".

            Zasu wuce baaba rabi ta iso zata karba strawberry din da zata markada,cikin fara'a da girmamawa ta amsa barka da gidan da sãahar tayi mata

"Barka dai farar d'iya,tun dazun nake dakon isowarki,abincinki ya kammala" 

"A shiryamin dan kadan,bamai yawa ba,ina fitowa yanzu"

"A fito lafiya ummin abba" ta fada cikin nuna kulawa,maama dake zaue ta kalleta

"Rabi kece kike sake sakalta sãahar naga alama"

"Idan bamu tattalawa alhaji diya ba hajiya ai bamuyi halacci ba" sai kawai maaman ta bita da murmushi,kasancewar itadinma ba maison yawan magana bace.

            Tare suka shiga dakin ita da afifa,ta zube mata takardunta a kyakkyawar kusurwaf da aka shiryama wani kyakkyawan table da kujerarsa,dan qaramin study room a maqale da bedroom din nasu,gurin an masa shiri na musaman da zaiyi dadin karatu,ta koma parlor ta barta a dakin.

           A nutse ta cire kayanta ta watsa cikin laundry basket,ta daura wani lallausan farin towel,gab da zata shiga toilet din wayarta ta soma tsuwwa,dakatawa tayi tana duba number dake yawo saman screen dinta,zubawa numbers din dake jere reras idanu tayi,sai taja da baya ta wuce bandaki abinta,saboda number tayi mata kama da number mahmud,wadda a qalla kusan kullum tana ganin gilmawarta cikin wayarta da tarin saqonninsa da ko sau daya bata taba tsaiwa dubawa ba bare ta bashi amsa.

          Mintina kusan ashirin da biyar sannan ta fito,ta tsaya gaban madubi ta tsane jikinta,ta shafe lallausar fatarta me sulbi da mayuka sannan ta mutstsike jikinta da turarukanta masu taushin qamshin da kwantar da zuciya.

         Wani budadden cotton trouser ta saka,da wata free over size shirt me taushi,ta kama gashinta ta daure da band,idanunta suka sauka ga fuskarta da tayi wani irin fresh,babu alamun tabo ko qwarzane ko daya a kanta

_"ki tsaya iya matsayinki,kada maganganun dr ya rudeki,kina da naki limit din_" ido ta lumshe tana jin maganar na mata zafi kamar yanzun ya furta mata su,waye ya gaya masa buqatar kanta ce wai ta kawota companynsu?,baisan aikin tamkar wata tursasawa bane da karan tsaye ne da aka yiwa rayuwarta ba?,batason shafe maganar dattijon,hakanan batason zubda yaa muhyi a idanunsu,dole wani abun ta kauda masa kai,amma bafa komai ba,kuma muddin zasuci gaba da hada hanya da guy din ta tabbatar babu jimawa zasuyi batacciya,don ba zata iya shanyewa irin wadan nan halayen nasa ba,yadda yakema mata ita ba zata iya dauka ba,don ba abinda take nema daga wajensu.

            Dogon tsaki taja,sannan ta juya tana fita a dakin bayan ta dauki wayarta,ta kuma goge duk wani miscall na mahmud da saqonsa da ya shigo bayan taqi daga wayar.

          Still maama da afifa na zaune suna hira a parlor din,saita wuce saman dining tana duba abincin da baaba rabi ta ajjiye mata. Cikin wanda ta zuba din ta sake tsakurar wani,duk da bashi da yawa amma ba zai iya shiga cikinta duk ba,hakanan yanayinta yake,sanda tana qarama maaman tasha kaita asibiti,ayita bata multivitamin ko cikinta zai bude a samu cin abincinta ya qaru,saidai babu wani ci gaba,dole aka rabu da ita hakanan bayan sun fahimci halittarta ce a hakan.

            Sanda ta kammala itama qasan ta sauko ta saka baki a hirar tasu,duk da kusan rabin hankalinta yana kan wayarta,ta shiga Instagram account dinta tana dubawa.

          Har ta gota wani post saita dawo da baya a hankali. Hoto ne da aka yiwa cikakken daukan daya bala'in fita tarrrr,kana ganin hoton zakasan cewa da babbar waya akayi,irin wayoyin da sukasan haqqin fidda hoto da kyau.

_i'd never met anyone so quiet and beautiful simultaneously like him,his personality match his beautiful face MT JARMA_ Rubutun dake qasan photon kenan,sai tarin comments rututu,wanda kusan rabinsa na mata ne.

         Wani bacin rai ne yazowa sãahar iya wuya,ta fita gaba daya daga Instagram din,wasu abubuwan ba shakka laifin mata ne,irin comment data dinga gani a qasan photon kwata kwata babu tsari babu kuma aji bare kamun kai irin na 'ya'ya mata,kamar a duniya shi daya Allah ya bawa baiwar kyau?,ba dole ya dinga buga wannan iskancin ba, muddin a zahirance irin wannan rawan kan da digimin matan suke masa,ranta ya baci sosai,har afifa ta kula ta tambayeta,amma sai tace ba komai,ta jawo saman wayar ta kashe data dinta gaba daya,dai dai sanda yaa zaid yayi sallama cikin falon,yana riqe da jakar abba,abban yana biye dashi a baya.

          Cikin girmamawa kowa ke qoqarin masa sannu da zuwa,mutum me cikar kamala da kuma nuna qauna da sakewa da iyalinsa,yana da faran faran sakin fuska da kuma barkwanci,amma muddin zakayi ba dai dai ba da gangan da ganganci to fa baya lamunta,a nan ne zaka ga aihin Color dinsa.

           Sassansa ya wuce daga nan ta qofar data hada sassan biyu,maama tabi bayansa ta barsu da zaid din yana tambayar sãahar ya aikin

"Lafiya" ta amsa masa a taqaice shima,afifa dake zaune daga gefanta dariyar da taketa dannewa ta taso mata

"Adai dinga jin tsoron Allah ana fadin gaskiya,atoh" waiwayawa tayi ta kalli afifan,kaman zatayi magana saita fasa ta maida idanunta ga wayarta

"Tell me,me ya faru?,da alama akwai magana tunda permanent assistant dinki ke dariya" shuru ta danyi kamar ba zatayi magana ba,sai kuma ta buda baki sound na bacin rai yana dan fita kadan a muryarta

"Bashi da kirki yaa zaid,he was trying to insult me as kamar ina neman wani abu da kamfaninsu" dan zuba mata ido zaid yayi sannan ya saki murmushi

"Try to relieve your anger dear,ki nutsu ki fuskanceshi,ki kuma fuskanci aikinki,ba don shi kadai kike zaune a kamfanin ba right?" Kai ta gyada

"So no need ki damu kanki,do all the right things,amma don't be rude to him,ya girmeki,show some respect zaki samawa yaa muhyi din mutunci,ki zama me kawaici yadda na sanki,kada ki bari qananun abubuwa su dinga bata ranki,kin fahimta?" Nutsuwa taji tana saukar mata,Allah ya sani yadda yayyenta suke nuna qauna da kulawa a gareta ya sanya itama take qaunarsu,take kuma qoqarin bin dukka umarninsu,yanzun maganar da sukayi da yaa zaid din ya samar mata da relief sosai,sai ta dan sake sukaci gaba da hira,har zuwa sanda akayi kiran magrib,ya fita masallaci shida abba,su kuma suka wuce ciki ita da afifa.

          Ba kasafai take tashi daga saman abun salla da wuri ba duk bayan sallar magarib har sai tayi isha'i,kamar yadda takeyi bayan asuba har alfijir ya keto,saboda gurabene na amsar addu'a sosai.

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400

Pay at👇

1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070

VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post