Tabarmar Ƙashi page 22 by H U G U M A

Tabarmar Ƙashi page 22 by H U G U M A

 

Tabarmar Ƙashi page 22 by H U G U M A

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

https://arewabooks.com/u/huguma

22

       Baaba ramatu bata hanata janye qafafunta da take yankewa farce da take qoqarin yi ba,ta sakar mata amma ta miqe tana cewa

"Yi a hankali,gidan fa zai shigo gaba daya fadeela" baaba ramatu ta fada cikin tausayawa,ganin yadda taketa zirgillo,ta kasa tsaiwa guri daya,har sai data isa ta kama hannunta suka nufi gurin da yake ajjiye motarsa duk sanda ya dawo daga office.


            Ita dince mutum ta farko daya fara gani kuwa,don motar na tsaiwa,bai tsaya jiran guards sun bude masa ya buda da kansa ya zuro qafafunsa waje,dai dai sanda itama taketa kutsawa ta tsakanin ma'aikatan mahaifin nata,har sai data iskeshi,ya buda hannayensa dukka biyun ta fada ciki cikin matuqar farinciki,zakayi zaton ba dazu dazu bane yabar gidan,tamkar matafiyin da yayi watanni bai cikin ahalinsa.


             Ba wanda ya katse musu walwalarsu,domin idan da sabo dukka wanda ya kwana ya tashi cikin gidan ya saba da ganin hakan,saida ya fidda mata dukka wani nau'in kayan ciye ciye data lissafa masa tana so kafin fitarsa,ya damqa mata sannan ya samu ta barshi ya fito daga cikin motar,suna saqale da hannun juna suka doso hanyar ainihin cikin gidan.


           Dab da zai isa kusa da baaba ramatu ya dakata,cikin girmamawar da har yau har kwanan gobe bata gajiya da bashi ita tayi masa barka da zuwa


"barka,ya gida,ya fama da me rigima?" Kusan wannan tambayar ta zame masa tilas,kullum sai ya yiwa baba rabin ita tare da yi mata sannu,abinda ke qara mata ganin kimarsa kenan.


         Murmushi ta saki,itakam a duniya rigimar fadeela bata taba damunta ba,idan ba'a tausaya mata ba bai kamata aga laifinta ba,duk da hakan yarinyar tana da wani irin hankali sanyin rai da kuma nutsuwa,kawai dai bata iya nutsuwa muddin taga mahaifinta


"Alhamdulillah,mun yini cikin qoshin lafiya" wannan kusan itace amsar da tafi masa kowacce amsa dadi a rayuwarsa,hakan yana nufin fadeela bata hadu da hatsarin da kowacce rana,tun daga bullowar rana zuwa faduwarta zata iya fuskanta ba,lalurar dake sanyawa duk wanda suke tare dashi fargaba,suke kwana su kuma tashi cikinta.


"Hajiya qarama ma ta dawo" baaba ramatu ta fada a ladabce,abinda yasa ya dakata daga tafiyar da yakeyi,sai ya sauya akalarsa zuwa sassan da 'yan aiki suketa kai kawo,da alama suna aikin gyaran sassan ne.


            Fadeelan na biye dashi tana ci gaba da bashi labarai,wanda ayanzun ta sauya akalar labaran nata ne kan MOMMY QARAMA,kayan wasan data kawo mata da sauran tarkacen wasan yara.


            Daya daga cikin tafka tafkan sashe ne cikin sassan dake gidan,wanda kusan a manne yake da sashen da fadeela da baaba ramatu suke rayuwa a cikin sa.


           Kamar kowanne sashe na gidan,shima masu aiki ne mata ke kai kawo tsakanin makeken falon da yayi girman wasu gidajen kitchen,dining area zuwa balcony din da bedrooms din sassan suke a tsare,har ya zuwa upstairs din sassan da  nasa falon.


           Tun daga qofar falon suke zubewa suna gaidashi,ba tare da damuwa da cewa ko sau daya bai samu amsawa kowa ba a cikinsu. Sun riga da sun saba da wannan yanayin nashi,zasu iya cewa tsahon shekarun da suka dauka a tare dasu,basu taba katarin ganin koda murmushi akan fuskarsa ba bare akai ga dariya.


"Hajiya qarama fa?" Ya tambayi matar data fito a kitchen ta kuma zube a gabansa cikin ban girma


"Tana sama" bai amsa mata ba,ya fiddo wayarsa ya fara kiran wani layi. Bugun farko aka daga cikin qasa da second daya ya amsa da


"Okay" ya maida wayar aljihu,ya zauna saman daya daga cikin kujerun yaja fadeela jikinsa ya dorata saman cinyarsa yana ci gaba da bare mata chocolate din.


            Minti daya tal motsi ya fara tashi daga upstair din,kafin daga bisani sautin takalmi dake bada d'as d'as ya biyo baya.


              Farar macace doguwa sambal,ma'abociyar tsaho da kuma qibar da batayi yawa ba,koda batayi kama da toufeeq ba,amma tun kallon farko zakasan cewa akwai alaqa ta jini me qarfi a tsakaninsu,dukkansu kuma babu qarya......a duban farko kadai zaka gane ainihin yare da qabilar da suka fito wato SHUWA.


"Marhaban Muhammad" tayi maganar murmushi kwance akan fuskarta,muryarta ta sanya fadeela zamewa daga jikinsa ta doshi stairs din tana murmushin itama


"Basai kin hauro ba,saukowa zanyi UKTIE" dai dai sanda ta qarasa saukowar,saita miqe hannunta duka ta riqe fadeelan da kyau,cikin wani irin duba me cike da zallar so qauna da kuma kulawa.


         Kujerar gefansa ta samu ta zauna tana bashi duka hankalinta


"Yanzun kake shigowa?,sanda na dawo ai baaba ramatu tacemin baka jima da fita ba" kai ya jinjina,cikin nutsuwarsa yace


"Barka da dawowa,i hope komai lafiya" murmushi ta kuma sakewa,tamkar kumatunta basa gajiya da fidda murmushin


"Barka kadai jarma,lafiya alhamdulillah,inacan inata kewarku,hankalina gaba daya yana kan uktie,ina fatan tun tafiyata ba'a sake samun wata matsala ba?"  Kai ya jinjina yana lumshe idanunsa hadi da budesu,da alama hakan kusan wata dabi'a ce tasa a duk sanda yake magana


"Komai an samu sauqinsa, alhamdulillah" ya furta cike da fatan hakan taci gaba da kasancewa. Zai iya cewa komai na jin dadin duniya ubangiji ya mallaka masa shi,saidai ita rayuwa bata taba tafiyarwa bawa a yadda ya sota dari bisa dari,hakanan bata taba kubuta daga tarin qaddara da jarrabawa,lalurar fadeela na dukka abinda ya sameshi a can baya ya aminta na daya daga cikin qaddarorinsu,kuma sila na samun tawaya daga cikar jin dadin duniyarsa.


"Na dawo na tarar julia bata nan" ta fadi fuskarta na nuna tsantsar fushi


"Na sallameta" ya amsa mata a taqaice,don shi din mutum ne da bayason doguwar magana sam sam sam


"Shine dai dai hakan da kayi,ta yaya za'a dauki a ninka miki salary dinki na asali sannan ki kasa aiwatar da abinda aka daukoki dominshi?,wannan ai tsantsar yaudara da kuma cin amana ne,naso ina nan,daa kafin tabar gidan nan ba shakka sai na hada mata da hukunci" sumarsa ya shafa da hannunsa daya sannan ya miqe


"Ya wuce"


"Allah ya tsare gaba,zan saka madam Stella ta sake lalubo wata,tsayayya da zata iya kulawa da ita" tayi maganar tana shafa sumar fadeelan cikin kulawa


"Yayi,but idan aka sake samun kuskure kusa dana baya,itama zata rasa aikinta ne kamar su"


"In sha Allah wannan shine karo na qarshe,masu aiki duka babu aminci,kowacce da irin nata sakacin" tayi maganar cikin salon fada. Dai dai sanda labulen daya lullube qofar balcony din dake falon qasa ya bude,budurwa dake ciki ta fito.


          Labiba ce sanye da kayan bacci,guntun wandon da iyakarsa cinya,sai wata fingilalliyar rigarsa wadda da kadan ta dara saman cikinta,cup hand ne da ita maqallalle iya dantsen hannunta,kanta baby dankwali,sai gashinta dake daure a ribbons,kusan kowacce sura ta jikinta a bayyane take. Ganin taoufeeq ciki falon sai ya qarasa kashe mata jiki,kowacce gaba ta jikinta ta amsa,amma kuma kallon daya watsa mata ya dakatar da ita daga tahowar da take izuwa gurin,ta tsaya cak tana tuna gamuwarsu ta qarshe,marin da fuskarta tasha da kuma irin zazzafan gargadin da yayi mata. 


          Bai sake duban inda take ba ya juya ya fice abinsa daga falon a nutse cikin qasaitaccen takunsa.


           Wata ajiyar zuciya me qarfi ta sauke,sai daya fitan sannan ta samu sukunin qarasowa,idanun hajiya qarama a kanta har ta zauna


"Lafiyarki ke kuma?" Sake sakin ajiyar zuciya tayi,tana karbar ruwan tea da fried egg da daya daga cikin masu aiki ta kawo mata


"Muhammad"


"Me yasa kullum tunaninki da dukkan furucinki ko yaushe a kansa yake?" Kai ta girgiza tana ajjiye cup din da tayi niyyar kaiwa bakinta ta fasa


"Mommy,wani irin fitinannen so nakeyi masa,ba zaki gane yadda nake jinsa a raina ba,i can't imagine my life without him" wani irin duba na tsanaki hajiya qarama take binta dashi tsahon wasu sakanni ta ajiiye numfashi,sannan ta gyara zamanta.


"Kiyi qoqarin ragewa,kinfi kowa sanin halinsa,bayasin shishshigi bayason kuma a fiya shige masa da yawa"


"Zan kwatanta" ta fada badon tana jin zata iya ba,wani sashen na kwanyarta kuma na tuna mata marin da tasha a haduwarsu ta qarshe. Taji babu dadi amma bataji haushinsa ba,daga qarshe ta tattara laifin ta azawa kanta,saboda tasan kuskure ta tafka ba qarami ba,tafi kowa sanin halinsa,ita kanta batasan zata iya aikata hakan ba,amma SO DA ZUCIYA saidai a barsu kawai.


              Sanda ya isa sashensa cook dinsa ya gama shirya table dinsa,gurin kawai zaka dauka wani gurin cin abincin shugaban qasa ko wani governor ne,ya samu sajjad har yayi wanka ya sauya kaya daga cikin bedrooms din dake sassan,a nan yabar fadeela ya haura sama shima don ya watsa ruwan.


          Minti talatin da wani abu ya kammala shima ya sauko,cikin fararen pajamas marasa nauyi masu ratsin baqi kadan,mutum ne meson amfani da fararen kayayyaki,kusan first choice dinsa a color fari ne.


         Tare da tab dinsa ya sauko,ya samu tuni sunyi ready saman dining sai yayi joining dinsu. Yau kam babu laifi a sake yake,hakan kuma sajjad yasan baya rasa nasaba da alamun dorewar lafiyar fadeela.


            Suna kammala cin abincin aikin kamfanin da bayanan da jibril ya turo masa na taron yau ya saka a gaba yana dubawa. Shima sajjad din aikin yake ragewa,kowa hankalinsa yana kan na'ura,don haka falon ya dauki shuru. 


          Sajjad ne ya fara motsawa,ya jawo wata folder ya tura gabansa,ya daga kai yana dubana alamun neman qarin bayani


"Folder din president ce" qaramin tsaki toufeeq yaja,ba tare da yabi takan folder din ba yaci gaba da aikinsa. Tsam sajjad ya dakata yana dubansa


"Wai me kake nufi?,wannan folder din ita ya kamata ka fara dubawa kafin ka duba komai fa"


"Bani da lokaci" ya sake amsa masa a taqaice,sai kawai ya qyaleshi bai sake cewa komai dashi ba.


           Ba jimawa bacci ya dauki fadeela,ya tattara komai ya ajjiye,ya dauketa da kansa yabi ta siririn balcony da shi da fadeelan kadai ke amfanin dashi,ya bulla sassansu.


          Cikin falon ya samu baaba ramatu,su uku ne,ita da mai gyaran dakin fadeela zuwa sashen wato mabruka,da kuma wadda ke musu girki wato zuwaira,suna zaune suna hira,da alama daukewa baaba ramatu kewa sukeyi.


          Shigowarsa a sabe da fadeelan sai duka suka miqe,zuwaira da mabruka kawunansu a qasa suna masa barka da dare,baba ramatu kuma ta qarasa tana karbarta daga hannunsa. Idan da sabo ta saba,muddin yana gari ba kasafai fadeela ke zama suci abincin dare tare ba,yawanci sai dare idan tayi bacci yake kawota,idan kuma dare yayi sosai kwana takeyi a wajensa. Kafin baba ramatun ma ta gama karbarta zuwaira da mabruka tuni sun fece,mugun kwarjini yake musu,girmansa kuma suke gani sosai da har basa iya tsaiwa guri daya da shi idan ba shi ya nema hakan ba.


            Da kansa ya rarrage kayan wutar dake falon kafin ya juya ya fice shima.


         Inda yabar sajjad ya dawo ya tarar dashi,sai ya duqa ya tattare kayayyakinsa ya wuce daki bayan sunyi sallama.


             Saman bedside table ya ajjiye komai dake hannunsa yana dan sauke numfashi na alamun gajiya,ya cire bedroom slippers din qafarsa ya doshi qofar toilet. Alwala ya daura,sannan ya shimfida abun sallah ya tayar da sallahn.

 

          Cikin awa guda ya kammala komai,a maimakon ya hau saman lafiyayyen gadonsa dake lullube da tattausar shimfida,sai kawai ya jawo manyan duvets din dake kai har guda biyu ya shimfidasu a qasa ya sanya pillow,saidai yana kwanciyar yaji kaman ya kwanta akan wani abu. A nutse ya miqe yana duba wajen.


        Ido ya lumshe sannan ya bude yana furzar da iska


"Sajjad......inda maye ne ya kamani bazai sakeni ba" ya fada can qasa,ya zaro folder din,har zaiyi jifa da ita ya fasa,ya jawo bedside drawer ya jefa a ciki ya rufe ya maida kansa ya kwanta.


           Baiyi cikakken awa uku ba ya farka a firgice sosai,saidai duk da haka bakinsa yana dauke da kalmar


"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" wani irin birkitaccen yanayi,hautsinannen mafarkin da baya rufa wata biyu baiyi shi ba. Ci gaba yayi da maimaita addu'ar,har ya samu dukka nutsuwarsa ta dawo,saidai jikinsa ya jiqe sharkaf da gumi har ta tsakiyar gargasar dake kwance a hannunsa qirjinsa zuwa qafafunsa,ya miqe a hankali ya doshi toilet.


           Alwala ya daura bayan ya kama ruwa,yayi tsaye a gaban madubin bandakin yana ci gaba da watsawa fuskarsa ruwa,sunayen mutum biyu suna masa yawo aka tare da mafarkin daya gama yi yanzun nan a kansu


"Maji,ameesha"



FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post