Nihaad page 59 by Khaleesat Haiydar complete

Nihaad page 59 by Khaleesat Haiydar complete

 

Nihaad page 59 by Khaleesat Haiydar complete

💖💖 NIHAAD 💖💖


Page 59


Tun da Nihad ta hango Aliyu tsaye bakin kofar Main parlor bayan sun fito bangaren Janar ta rikice ga shi ba abun tace zata juya ba ko zata canza direction, in ma tayi hakan ina zata? Ga khalil sai tafiyarsa yake duk da ya gansa, lokaci daya ta fara bobboye fuskarta da hijab dinta tana sisinne kai kamar munafuka, gaba daya ta daburce ta rikice, shi ko khalil tunda yayi ma Aliyu kallo daya ya dauke kansa walking Majestically, Aliyu ya dinga kallon Nihad don reaction dinta ne ma ya fara jan hankalinsa gareta, at first he didn't even care to notice who she was, amma yanda yaga take yi ya sa ya dinga kallonta, Khalil ya kai hannu ya bude kofar parlon, Aliyu ya cire wayar kunnensa a hankali ya mayar aljihunsa yana kallon Nihad keenly kamar wanda ya gano abu, her eyes, her scent, the way she walks, Nihad dai taki yarda ta kallesa kuma bata fasa rufe fuskarta da hijab ba ga wani faduwa da gabanta ke ta yi, sai harde kafa take tsabar rudewa, tana isa dai dai kofar bata san sanda ta daga idanuwanta suka hada ido da shi ba, ta sauke idonta da sauri tana kokarin fita yayi hanzarin fizgota ya janye Hijab din da ta rufe fuskarta da shi, ya wani zaro ido yana komawa baya yace "Nihad????" Ko rufe baki bai yi ba yaji an wani tura sa yayi baya kamar zai fadi, Khalil na masa wani kallo cikin husky voice yace "Do not ever try that again...." banda zare ido babu abinda Aliyu yake with confusion yana bin Nihad da kallo, ita dai Nihad tuni ta fita compound a rikice har tana neman faduwa, Aliyu ya cakumo Khalil yana masa wani kallo yace "How dare you?? A ina ka santa kake warning dina?" Wani wawan naushi Khalil ya kai masa, Aliyu yayi saurin kaucewa yana zare ido, Aunty Hassana da ta fito daga bangaren Janar rai a dagule ta zaro ido tana kallonsu ganin abinda ke faruwa tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Meye haka???" da gudu ta nufesu ta shiga tsakaninsu ganin ana kokarin kai naushi, Khalil na ganin haka ya fice daga parlon kamar zai tashi sama, Aunty Hassana na kallon Aliyu idanuwanta kamar za su fito tace "Ina ruwanka da ɗan wiwin nan zaka tsaya kana ɓata lokaci a kansa har ku ke neman ba hammata iska? Ina kai ina shi? Responsible somebody like you, kai da zaka fita Germany ma gobe meye na biye mara aikin yi wanda ake tsoron daurasa kan harkokin arziki?" Aliyu na zare ido cikin wani yanayi yace "Mum, mum budurwata ce na gani a gidan nan, ita ce wallahi, Nihad ce, what is she doing here?" Aunty Hassana tayi galala tana kallonsa tace "Budurwarka kuma? A ina budurwar taka?" Aliyu na nuna mata waje yace "He just left with her now, wa ya kawota gidan nan? Wajen wa ta zo?? Mum Nihad ce fa" Aunty Hassana dai ta saki baki tana kallonsa, can tace "Wai yarinyar nan da ya fita tare da yanzun nan kake magana?" Da sauri Aliyu yace "Ita Mum, ita nake nufi, wajen wa ta zo a gidan nan??" Aunty Hassana tace "A'a, anya kanka daya kuwa Aliyu, yanzu fa yarinyar ke cewa ya zauna a gidansu a kano...." Aliyu da kansa ya gama daurewa ya dinga kallon Aunty Hassana babu ko kiftawa, a hankali yace "Gidansu kuma? Me yaje yi gidansu?" Aunty Hassana tace "Wai driving, yanzun nan da bakinta take gaya ma Janar wallahi....." Still Aliyu yayi yana kallon mum din tasa baki bude, Aunty Hassana tace "Kaga ka fitar da ni a duhu Aliyu, kai a ina kasan yarinyar?" Yayi karfin halin cewa "A kano na santa, budurwata ce kuma ita nake son zan aura, wallahi budurwata ce" Aunty Hassana ta rike haɓa a hankali tace "Budurwarka? Wai fa matarsa ce an daura masu aure, da bakinta yanzu take gaya ma Janar wai ubanta ya daura mata aure da shi" Aliyu ya dinga kallonta babu ko kiftawa, a hankali yace "Shi ya aureta dama??" Aunty Hassana tace "Wallahi haka nan ta ce" A hankali Aliyu ya juya mata baya with different thought running his mind all at the same time, Driver? Khalil ne sabon drivern gidan nasu da take gaya masa dama? girgiza kai yayi da sauri not wanting to believe that, sai kuma ya tuna encounter dinsa da so called sabon drivern a ranan da yaje ya sameta a Mall, Aliyu ya dinga jin zuciyarsa na bugawa, wait!! is this really happening??? Aunty Hassana dake ta kallon ɗan nata tace "Naji kayi shiru, ko dai kawai kaga kama ne Aliyu, amma me zai kawo budurwarka gidan nan ana zaune lafiya, kamar dai a wasan kwaikwayo...." Lokaci daya Aliyu ya juyo yana kallonta da karfi yace "Budurwata ce Mum, duk duniya kuma babu macen da nake so sama da ita, ita fa nake ce maki zan aura kwanaki, ita ce fa, dalilin da na zo nace maki na fasa auren a lokacin Video dinta with just Underwear aka yi leaking a internet...." Aunty Hassana ta buda baki hangangan, murya kasa kasa tace "Ita ce dama da gaske a videon??" Aliyu bai ce mata komai ba, Aunty Hassana ta gyada kai a hankali tace "Ai ko Janar bai sani ba sun boye masa... Na gaya maka yarinyar fa cewa tayi Khalil din ya zauna gidansu a matsayin dreba na shekara daya, ashe duk tsawon lokacin da baya gidan yana can gidansu, sannan ta dawo tace ubanta ya aura mata shi, da yake asirinsu ya fara ci Janar ko kallon banza bai yi ma Khalil din a parlon ba, ita kuwa uwar sai kukan munafurci take, yanzu kana nufin ka taɓa soyayya da yarinyar???" Aliyu na kallon Mum dinsa yayi wani murmushi, calmly yace "Idan kuwa da gaske shi aka aura ma Nihad, to ina me tabbatar maki in dai ina numfashi wallahi baxai yi rayuwa da ita a matsayin matarsa ba, yanda naki jininsa baxan taba bari yayi rayuwa tare da warce nayi soyayya da ba, ko da kuwa ba aurenta xan yi ba, he is Mad...." Yana kai wa nan yayi hanyar dakinsa kamar zai tashi sama, Aunty Hassana dai ta bi sa da kallo, can ta gyada kai a hankali kamar me nazari, sai kuma ta bi bayansa da sauri. Tun barinsu gidan Khalil ke driving yana kallon Nihad da ta kauda kanta taki kallon inda yake gaba daya, wani mugun haushinsa take ji har ranta, a tsorace tayi wani kara bayan ya kauce ma wani motar da ya kusa colliding ma a gabansa, duk da haka kuma sai da ya gurji motar, ta juya da sauri tana kallonsa tana zaro ido, bude motar yayi ya sauka ya nufi motar don me motar ma yayi parking ya sauko, hakuri ya dinga ba mutumin, Allah kuma ya so me saukin kai ne, ya koma motarsa kawai, Khalil ya koma nasa motar ya shiga, ya jinginar da kansa jikin kujeran motar ya sauke ajiyar zuciya, Nihad dai sai kallonsa take, irin kamar wanda baya ganin gabansa din nan don ma Allah ya takaita, ya juya a hankali ya kalleta, sai ta wani hade rai ta dauke kai, murya can kasa yace "Will u mind driving the car pls?" Sai kuma ta juyo ta kallesa, ya girgiza mata kai a hankali yace "Baxan iya ba" Shiru tayi bata ce komai ba, Sai taga ya bude motar ya sauka, a hankali ta bude side dinta ta sauko ita ma, suka yi exchanging seat, ya sa mata driving direction din a Google map a wayarsa ya ajiye mata, sai daga baya Nihad ta fahimci dalilin kasa tukin nasa, don kuwa har suka iso gida kallonta yake, even for a second bai daina kallonta ba as if his life depends on that, Ita dai tayi concentrating kan driving da take kawai, ganin bai sauka ya bude gate din ba duk da sun iso gida ta juya ta kallesa, wani murmushi me narka zuciya ya sakar mata, ta kasa daina kallonsa, ya kamo hannunta a hankali, sai kuma ya saketa ya sauka daga motar ya bude gate din gidan ta shiga ciki da motar tayi parking a parking lot, Bata jirasa ba ta nufi kofar shiga gidan da sauri, sai dai dole ta tsaya ya zo ya bude kofar, yana budewa kuwa ta shige ciki ya bi bayanta da sauri ya rikota, bata san sanda ta fashe masa da kuka ba, ya rungumeta jikinsa sosai, yana jin kukan nata har cikin zuciyarsa, murya can kasa yace "I am so sorry Nihad, i am very sorry, i am sorry i hurt you much...." Kuka take tana tuna irin azaban da yayi mata, bata ankara ba taji ya dauketa ya wuce sama da ita, ta kankamesa saboda tsoro, bai direta ko ina ba sai saman makeken gadonsa dake master Bedroom ya hau aikin lallashin da bai samu yayi mata all through that day ba, da ya ga ta hakura da kukan ya shiga bandaki ya hada mata ruwa a bathtub dinsa, ya dawo ya dauketa zuwa bandakin, he did everything for her, ita dai ta kasa hada ido da shi..... Daren ranan Khalil bai wani rintsa ba all his thought was with Mami, kukan da yaga tana yi ya tsaya masa a rai, tun kafin su kwanta ya so kiranta amma bai ma san me zai ce mata ba, infact ba ma shi da courage din kiran nata, kawai ya hakura da kiran, all through the night Nihad na jikinsa bai saketa ba, and she slept soundly. Karfe takwas na safe Khalil ya kira Ya farooq bayan kiran da Janar yayi masa na cewa su shirya shi da Nihad before 9:30 za a zo a daukesu, wayar na fara ringing Farooq ya daga, bayan sun gaisa farooq ya tambayesa ya Nihad, Khalil yace "She is fine Alhmdlh, ya Kaduna?" Farooq yace "Ina kano ai" Khalil ya fara tunanin ta ina ma zai fara sanar masa, can dai yace "Erm... dama Dad dina ne za su je kano wajen Abba yau su gaisa, so i don't know how it's going to be...." Farooq yace "Ohk, ba damuwa zan sanar masa in sha Allah, Allah ya kawo su lafiya" A hankali Khalil yace "Ameen" Don har ya fara jin kunyan Abban Nihad da Mum dinta, Farooq yace "Kamar karfe nawa kenan?" Khalil yace "Zuwa sha daya in sha Allah" Farooq yace "Allah ya kai mu" Daga haka suka yi sallama Khalil ya ajiye wayarsa ya jinginar da kansa da kujera, yau kam bai ma san da idon da zai kalli Abban Nihad ba, he wish Abbansa zai yarda yaje gidan without convoy, but that will never be possible, can kuma ya ji dama Abban ya bar sa shi kadai yaje gidan ba sai anje da shi da Nihad din ba, ya sauke wani ajiyar xuciya ya mike daga karshe ya nufi sama ya shiga dakinsa, har sannan Nihad bacci take, kana kallonta kasan it's a peaceful one, ya zauna gefen gadon a hankali yana kallonta ko kiftawa babu, abubuwa da yawa ne suka hau dawo masa tun farkon da ya fara zuwa gidansu, and he couldn't help it but smile and he wish she will go back to her former Nihad me tsiwa, wauta, fada, masifa, amma banda walakanta d'an Adam da bin kawayen banza. Aunty Maryam na zaune gefen gado a dakin Mami ta jingina jikin gadon tayi shiru bata cewa komai, can ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace "Aa Mami kar ki ce baza ki ba tunda har Janar din da kansa yace ki shirya...." Mami ta dakatar da ita a fusace tace "Akwai wanda zai tilasta ni in je ne idan nace baxan je ba? To nace baxan je ba, kuma baxan je din ba" Aunty Maryam ta girgiza kai tace "Ni health dinki nake jiye maki Mami, don Allah ki kwantar da hankalinki abi komai a sannu, tun jiya nake gaya maki haka amma kin ki fahimtata" Mami ta kalleta tace "Wallahi ban ga amfanin zuwanki ba Maryam, na zata da kika zo za ki tayani a san ta inda za a billo ma lamarin nan, amma sai dai ki zauna ki kura ma mutane idanu baki cewa komai...." Aunty Maryam ta sauke wani ajiyar zuciyar tace "Ni so nake abi komai ne a sannu Mami, ni kaina i am shock, i am really shock don yarinyar bata taɓa ce min ae da aure tsakaninsu ba kuma ta bude min cikinta sosai during her stay a gidana, amma dae na fi tunanin shi ne ya hanata fadi ita kuma babu yanda zata yi, ni sai nake ganin tunda auren yayi ba shashanci ba ae da sauki da dai ace neman mata yake Mami..." Mami ta dinga kallonta ta ma rasa abinda zata ce mata don takaici, Aunty Maryam tace "That is just it Mami, wannan ne ma yasa na sa ma kaina nutsuwa ban daga hankali ba, duk da lamarin akwai shock, but one have to try and reason, though i am not in support of what khalil did da har zai yi aure babu knowledge dinku, amma ai sai abi komai a sannu" Mami bata tanka ta ba ta dalilin wayarta dake ring, ta dau wayar nata, ganin Hajiya Safeenah ce ta dinga kallon screen din wayar, can dai ta daga ta sa handsfree kawai, nan suka gaisa faram faram, Mami tace "Kina ta kirana jiya da daddare ban samu dagawa ba Hajiya, wallahi maganin bacci na sha, bana ɗan jin dadi" Hajiya Safeenah tace "Subhanallah, ya jikin yanzu?" Mami tace "Aa Alhamdulillah naji dama dama" Hajiya Safeenah tace "Toh zuwa karfe sha daya zan shigo in sha Allah" Mami ta ɗan yi shiru sai kuma da sauri tace "Koh??? kuma gashi za mu je kano tare da Janar amma yau din za mu dawo" Hajiya Safeenah tace "Ahh to shikenan, sae dai kun dawo kenan, ita Nadeeyan sae ta tafi ita kadai kawai, dama tace min zata gun Noor anjima maganar anko" Mami tace "Allah sarki, to in sha Allahu muna dawowa zan kira ki" Nan dai suka yi sallama Mami ta ajiye wayar a hankali, lokaci daya jikinta yayi sanyi, Aunty Maryam dake ta kallon Mami tace "Kin ga gwara da kika ce mata haka kar ta zo ta ganki a wannan yanayin da kike ciki" Mami dae bata ce komai ba, Aunty Maryam tace "Ga kuma Nadeeyah tace zata zo wajen Noor, kar kuma ta zo ta ga kina nan, ba gwara kawai ki shirya a tafi kanon ba, na tabbatar idan kika je kanon zaki fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali, sai kuma a san next step da za a dauka" Aunty Maryam na fadin haka ta mike ta shiga bandaki.... Farooq yayi sallama kofar parlon Abba ya shiga ciki, ya zauna kasa ba tare da yayi interrupting din Inna dake ma Abba magana ba, Umma ma na zaune parlon ta rafka uban tagumi sai kallon innar take, Inna na kallon Abba a ɗan fusace tace "Ya kake kallona haka Ibrahim, ni fa ba kai nace ka dauko masa yan sandan ba, to wa ma zai sa ka ka lalata mana al'amarin, ni da kaina zanje gidan yan sandan in gana da ogansu daga nan ya sa a cika min mota daya da kurtaye mu je har gidan nasa su nakada masa shegen duka shi ma, kafin mu tafi da shi.... Ai ni da kaina zanje ko ɗan rakiya bana so, don ma dai kaf zuri'a bamu da soja ai da shi zan aika ya ci min ubansa kafin a kai sa gidan yan sanda" Farooq dai sai kallon Inna yake, Inna tace "Sai kace er banza ya samu ya doka da za a yi shiru a kyalesa, to ni ba gantalaliya bace, wallahi sai an bi ma jikata hakkinta" Farooq yace "Duk wannan abun fa bangarenta kawai aka ji ba aji nasa bangaren ba Inna, ku daina saurin zartar da hukunci daga jin bangaren mutum daya" Inna ta wani jefa masa shegen kallo tace "Allah ya tsine masa shi da bangaren nasa, ya nakada mata shegen duka ya hadata da saki daya kace mu jira mu ji bangarensa?? Anya farooq? to wai ko dai kai ka sa shi yayi mata wannan abun ne bamu da labari farooq??" Shi dai Abba bai ce komai ba a parlon, Umma ma ta kasa cewa komai abun duniya ya isheta, Inna tace "Toh kuwa bai doki Kamila a banza ba sai inda karfina ya kare a wannan kes din wallahi, ga duka ga saki??" Farooq ya dauke kai yana kallon Abba yace "Abba dama Khalil ne ya kirani yanzu wai mahaifinsa zai zo gaisheka yau, zuwa karfe sha daya" Inna tace "Waye kuma Khalil?" Umma ta daga kai daga tagumin da tayi tana kallon Farooq, Farooq na kallon Inna yace "Mijin Nihad" Sake baki Inna tayi kamar warce ta ji mugun abu, can tace "Lallai duniya ta tara marasu lissafi, yanzu su yan kauyen zai zauna jira baxai fita aikinsa ba? Yau ga dai fitina kiri kiri" Abba na kallon Farooq yace "Allah ya kawo su lafiya" Mikewa Farooq yayi ya fita daga parlon, Inna ta kalli Abba tace "Kai kuma zaunawa zaka yi ka jira kauyawan?" Shi dai Abba bai ce mata komai ba, Umma ta sauke ajiyar zuciya tace "Yanxu inna ya kika ce za ayi?" Inna tace "Kamilar ta zura Hijabi muje har gidan yan sandan su ga abinda matsiyacin yayi mata, daga nan su bani mota daya muje su ci ubansa, sannan mu tafi kotu..." Umma tace "Toh ai bata iya ko tashi Inna" Inna tace "Sai a min hotonta in kai masu su gani" 


Wani soja ne ya bude ma Nihad kofar motar dake parke kofar gida, ta juya ta kalli Khalil dake kulle gidan, yayi mata alamar da ta shiga, a hankali ta shiga cikin lafiyayyen motar, Khalil ya karaso ya shiga motar shi ma, suka bar anguwan, direct airport motar ya nufa da su, kusan kuma a tare suka isa airport din da Convoy din Janar, Nihad dai sai kallon ikon Allah take, Lounge na manyan kasar aka yi Conveying dinsu kafin tashin jirgi.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post