*H U G U M A*
*_TABARMAR ƘASHI_*💔
Page 06
*Arewabooks:huguma*
https://arewabooks.com/u/huguma
Sai data fara busar da kanta da ya jiqe,sannan ta shirya cikin wasu cotton kayan bacci masu tsananin taushi,riga da wandon da bai sauka har qasa ba,kadan ya rage yakai idon sahu,ta mulke kanta da turaren gashi kamar yadda ta saba ya zame mata al'ada,hakanan ta shafe jikinta da nau'ikan turarukan da sai zatayi bacci take using nasu.
Cikin sofa bed ta kalmashe qafafunta bayan ta rage haske dakin,ta ja wayarta ta kunna data,tanason shiga media ta karanta news ko zata rage tsahon daren sai taji ana knocking,ta daga manyan idanunta da suka rusuna zuwa lokacin ta kallo qofar sannan ta bada izinin shigowar. Baraka ce,cikin girmamawa ta isar mata da saqon farheen na ta fito taci abinci,kai ta girgiza
"Am okay,kice mata saida safe ma hadu" kai ta jinjina sannan ta juya zata fice
"Ammm,amma idan zan samu black tea ko coffee ina so"
"Babu amma yanzu yanzu saina hada miki"
"Na gode" ta fada a tausashe,baraka ta juya ta fita tana ja mata qofar.
Tana shirin buda wayar saiga kira ya shigo mata,tsaiwa tayi cak tana kallon numbers din dake faman harbawa saman screen din wayar,baquwar number ce don babu ita cikin kaf 'yan tsirarun contact da ta adana cikin wayarta. Ba kowacce number take saving ba,sai number dake da matuqar muhimmanci da amfani a tattare da ita. Wannan yasa taqi daga kiran,har ta gama ruri ta katse,saita sake kunna data din ta shiga abinda tayi niyyar yi tun farko.
Ba'a dauki dogon lokaci ba kiran ya sake shigo mata,taja qaramin tsaki tana jin kamar tayi rejecting,amma saita fasa,taci gaba da kallon yadda wayar ke neman a kawo mata agaji,harta gaji da ɓurari ta sake yankewa,katsewarta da minti daya kacal saqo ya shigo
_"please......do me a favor,ki daga kirana koda na second biyar ne,zan gode da hakan,mahmud abba gana"_
Wani dogon tsaki ta saki kamar zata cire halshenta,wani abu mai tauri yazo ya tsaya mata a wuya,ta lumshe ido tare da danne makashin wayarta yana kasheta gaba daya qirjinta na wani irin dokawa,kenan afifa ta raba number wayarta?,me yasa afifa zatayi mata haka,ta rufe ido kamar batasan komai ba......kamar komai bai faru ba?". Ita daya cikin dakin amma bacin rai ya cikata,haka ta dinga hararar wayar dake ajjiye a gefe kamar itace mahmud din,cikin ranta tana qiyasta gamuwarta da afifa,a haka farheen dake cikin shigar wasu lafiyayyun kayan bacci masu matuqar kyau da daukan hankali ta turo qofar ta shigo dakin, hannunta dauke da coffe din sãahar.
Da kallo sãahar din tadan bi farheen,zamanta da ita ta koyi abubuwa masu tarin yawa,ta kuma gane ashe a baya ita din amsa sunan mace kawai takeyi ba tare da tasan ma'anar hakan ba,sai data zauna da farheen din na tsahon shekaru biyu da Wani abun,taci gaba da kallonta cikin rai da zuciyarta tana jin inama itace farheen din,bata da wata damuwa kaf rayuwarta,Allah ya bata miji irin yaa muhyi dinta,ya kuma azurtata da zuri'a yara lafiyayyu har guda biyu,gidanta tamkar ita ta zabawa kanta shi,duk ko me takeso tana samu,inda itace ita me zata nema kuwa a duniya?.
"Gayamin ta yaya zakiyi kumari,kin kama black tea da coffee kin riqesu tsam" farheen ta fada tana dire cup din saman bedside,idanunta akan fuskar sãahar tana qoqarin karantar yanayinta da take shinshinar kamar ya sauya.
Karamin murmushin da yafi kama da yaqe ta dan saki
"Bana jin yunwa,bazan iya cin abinci kuma banajin yunwa ba" kallonta farheen tayi tayi murmushi
"Koda bakiji yunwa ba ki kamanta ci koda babu yawa" lumshe ido kawai tayi ta gyada mata kai
"Ba wani abu da kike buqata ko?" Kai ta sake gyadawa tana qoqarin zama sosai saman sofa bed din
"To sai da safe"
"Khalipha fa?" Waiwaya kadan farheen tayi
"Kina buqatar dan tayin kwana ne?" Kai ta gyada
"Kin manta ne tare muke kwana dama duk sanda nazo?"
"Haka ne,zan sa baraka ta kawo miki shi,saida safe"
"Allah ya kaimu" ta amsa tana miqa hannu ta jawo mug din tana kaiwa bakinta.
Ba jimawa baraka ta shigo da khalipha wanda keta faman barci,an shirya shi cikin kayan bacci da alama ya jima dayin baccin,ta kwantar mata dashi saman gadon taja mata qofar. Ko rabin coffe din bata sha ba taji ya isheta,ta maidashi saman qaramin plate din tangaran din da farheen ta hado mata dashi,ta miqe a nutse ta shiga toilet tayi brush sannan ta dawo ta rage hasken fitilun dakin,ta hanye gado tana lullubesu da bargo ita da khalipha bayan taja yaron cikin jikinta tana jin tamkar ita ta haifeshi.
Ajiyar zuciya ta saki mai nauyi sanda ta lissafa shekarun yaron,yazo dai dai da shekarun faruwar wani abu daya sameta a baya,ta gyarawa yaron kwanciyar cikin jikinta,tana iya jinsa sanda yake sauke ajiyar zuciya,sai wasu hawaye masu dumi suka ratso ta idanunta,ta sanya tafin hannunta da sauri tana gogesu,qasa qasa bakinta na furta
"Aamantu billah, Alhamdulillah ala kulli haal" ta qarashe maganar ne tare da rintse idanuwanta hadi da tilastawa zuciyarta kauda dukka wani abu da zai kawowa mata hutu da nutsuwa cikin sassanyan daren da wata iska me dadi wadda ke dauke da hadari take kadawa. Sai Allah ya taimaketa bata jima a duniyar tunani tana bulayi ba bacci yayi nasarar daukarta yayi awon gaba da ita.
Washegari tun bayan sallar asuba bata koma ba,wannan din kusan dabi'arta ce,tana zama ne saman abun sallah har sai alfijir ya keto gari ya danyi haske. Ko yau dinma tana zaune,tana dab da kammala addu'o'in ta khalipha dake barci farka,ya miqe ya zauna sosai saman gadon yana murza idanunsa,a nutse ta waiwaya tana kallonsa,suka dan zubawa juna ido na wasu sakanni,sai ya sauko daga saman gadon da sauri,ta bude masa hannayenta ya fado ciki ta maida ta rungumeshi tsam tana sakin murmushi
"Kaji dadin ganina?" Ta tambayeshi har cikin ranta zuciyarta na mata sanyi,sanyin daya hadu dana hasken azkar din data gama yi,ya kuma gauraya da iskar safiya me dadi dake kai kawo tana kutsowa harta windows din dakin bayan ta samu nasarar daga labulen dake maqale a jiki kadan kadan. Kai ya jinjina yana dariya
"Na cewa daddy dama ya kaini,yace sai weekends,i missed you small mom" kyakkyawan murmushi ya qwace mata,tasa hannu taja kumatunsa
"I missed you too my little dad". Tun daga lokacin bai barta ta huta ba,akwai sabo sosai tsakaninta da khalipha din,wanna yasa yake sakewa sosai da ita fiye da momynsa farheen,yayita mata hira da tabara ita kuma tana biye masa. Allah ya halicci zuciyarta da matuqar soyayyar yara da kuma qaunarsu,duk inda taga yaro hankalinta yana kai,haka tayita hidima dashi,tayi masa wanka itama tayi,ta kintsa dakin da kanta ba tare data jira su baraka ba,taja hannunsa suka wuce kitchen abinda ta jima batayi ba,tana tambayarsa me yakeson ci,ya gaya mata ta soma fiddo kayan da zata hada breakfast din dashi.
Mamaki ya kama lubabatu sanda ta samesu a kitchen
"Da kinyi magana saina taso na hada miki abinda kike da buqata,yau din hutun qarshen mako ne,nasan masu gidan basa tashi da wuri,shi yasa banyi safkon fitowa ba"
"Karki damu" ta amsata a taqaice,saita miqa mata abinda zata tayata dashi taci gaba da hidimar hada break din tana sauraren khalifa. Ita kanta a jikinta yau dadi takeji,ko ba komai tadan motsa jikinta,don ta jima batayi girki ba,duk da yana daya daga cikin hobbies dinta,amma wani dalili mai nauyi ya kasheshi murus daga ruhinta.
Awa biyu ta gama komai ta zubawa khalipha komai a plate daya,yanata murna yau an hada mishi delicious,yaqi yarda ko lubabatu ta dauka masa plate din takai masa Parlor. Sãhaar na murmushin wauta da dadin quruciya irin na yaro ta sakashi a gaba suka fito.
Suna fitowar sukayi kacibus da farheen,a shirye tsaf tana zuba qamshi,hannunta dauke da aleena da tayi mata kwalliya da wata designer overall kusan shigarta ta ko yaushe kenan
"To bismillahi,shi yasa yau banji ifce ifcensa a parlor ba,ashe an tafi inda akafi kauri" farheen ta fada tana kallon khalipha,wanda tuni shi ya samu guri yayi zaman dirshan abinsa. Sãahar dake kallon khalipha tana sha'awar rayuwarsa,bashi da wata matsala ko damuwa,abinci kam zaici duk wanda aka bashi a sanda kuma yaso,baisan ma mommyn nasa nayi ba,ta maida idonta ga aleena daketa bangala mata dariya tana kuma dago mata hannu alamun tanason ta dauketa ne
"Beauty na baxan daukeki na bata wannan kwalliyar ba,banyi wanka ba"
"A hakan?" Farheen ta fada
"muna tashi kitchen muka shiga,bari na watsa ruwa nazo muyi hira" sãahar din ta fada tana juyawa da dan hanzari
"Dubiya ma zaki rakani,kada ki jima,so nake muje mu dawo daddyn khalipha yacemin da azahar zayaje daurin aure".
Batason zuwa yau ko ina saboda jiya ta fita,to amma dubiya ce tasan daga asibitin ba wani gurin zasu wuce ba. Minti kusan talatin ta kwashe a toilet din sannan ta fito,ta tsane jikinta ta fara mulke fatarta da lotion.
Cikin qasa da minti talatin ta shirya cikin vintage bubu gown ta chiffon material,ta yane kanta da dan siririn veil din da yazo hade da rigar tayi rolling dashi, kyakkyawar fuskarta ta fita ta tsakiyar mayafin,siririn agogon casio ta daurawa tsintsiyar hannunta wanda yazo ne tare da qaramar barimar data sawa kunnuwanta,don ba kasafai takeson kaya masu damu ko nauyi ba,saidai idan ya zamana ba yadda zatayi. Bata dauki komai ba banda wayarta data riqe a hannunta bayan ta feshe jikinta da turarukanta na dindindin guda biyu masu tsananin sanyin qamshi da jimawa a waje basu bar gurin ba,ta zura takalmanta masu matsakaicin tudu Golden goose brand ta fita a dakin.
A tsaye ta samu farheen tana serving yaa muhyi dake sanye da jallabiyya,da alama tashinsa a barci kenan yunwa ta fiddo shi,don ba kasafai yake cin abincin a sassan ba.
Tana juya masa tea ta dago ta kalli sãahar
"Tabarakar rahman" farheen ta fada tana murmushi,saboda har ga Allah ta gaza jurewa kyan da sãahar din tayi,cikin ranta da zuciyarta ta cika da fatan ubangiji ya shiga lamarinta. Daga kai yaa muhyi yayi ya kalli farheen din
"Me ya faru?"
"Bakaga auta ba?" Idanunsa ya maida ga sãahar sannan ya dawo dasu kan farheen bayan ya karbi tea din daga hannunta,shi kansa kowacce rana sallolinsa biyar tana cikin addu'o'in sa,ajjiye mace kamar sãahar din a gida abune da bazaiyiwu ba,duk kuwa girman jarrabawar data fuskanta,gidan aure shine solution.
Cikin girmamawa ta qaraso ta gaida yaa muhyi din,cikin ranta tana addu'ar Allah ya kauda hankalinsa,kada ya sake tayar mata da dukka wata magana data shafi aikin company din nan,saidai addu'artata bata ci ba,suna gama gaisawa ya jeho maganar
"Kiran wayar professor ne ya tasheni......yanamin tuni game da batunki" shuru ne ya ratsa saboda ta rasa amsar bashi,shi kuma kamar bai kula ba ya dora
"Kiyi qoqarin hada amsarki nan kusa,don kusan nashi shirin ya kammala,cikin satin nan ko sati na gaba zaku kama aikinku"
"To,in sha Allah" ta amsa masa a sanyaye,gabanta yana dan faduwa,zasu kama aiki ko ita dawa dawa?,ta tabbatar harka ce data shafi mu'amala da maza,magana ake ta company wanda bazaiyiwu ace mata bane zallah.
Wannan maganar ita ta sake sanyata ta zama so silent sanda suke hanyar asibiti ita da farheen,duk da cewa ita ke driving,amma yadda ta bawa kwalta dukka hankalinta ya isa ka fahimci tana wani nazari ne da daban.
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*
+22799643131
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥