Tabarmar Ƙashi page 9 by H U G U M A

Tabarmar Ƙashi page 9 by H U G U M A

 

Tabarmar Ƙashi page 9 by H U G U M A

*H U G U M A*

_*TABARMAR ƘASHI*_💔

*Arewabooks: huguma*

https://arewabooks.com/u/huguma

Page 09

           Kwana file din yayi a nan,bayan sallahr asuba ta kammala azkar dinta ta jawoshi tana zaune daga saman abun sallarta,ta buda a hankali ta fara karantawa kamar yadda yaa muhyi yace tayi din.

            Very interesting,komai na kamfanin a tsare yake cikin wani tsari mai burgewa,banda batajin son aikin cikin ruhinta zata iya cewa company din ya burgeta,kuma kamar tana da gudunmawar da zata iya bayarwa tabbas gurin saitashi. Tsayawa tayi cak da biron dake hannunta bayan ta kammala signing tana duban sunan CEO din dake rubuce cikin ruwan gold daga gefen takardar MUHAMMAD TAUFEEQ. Zame hannunta tayi a hankali daga saman takardar tana kallon sunan,a hankali tunaninta ya koma can baya,sai yanzun ta tuna yaa muhyi ya gaya mata zasuyi aiki ne tare da yaronsa


"Jaffal qalam" ta fada can qasan ranta tana maida file din ta rufe,ta riga ta saka hannu,tabbas data janye,batason a kaita sashen da zatayi aiki tare da kowa,amma ya zatayi?,yaa muhyi ya riga ya daureta da jijiyar jikinta.


          A gaggauce ta isa parking lot na gidan sanda yake shirin shiga motarsa,ya dakata ya waiwayo yana dubanta tana dan haki saboda saurin da takeyi,file din ta miqa masa


"Ya akayi?" Ya tambayeta tun kafin ya buda bayan ya karba


"Na cike yaaya" ta fada tana langabe kanta,sosai murmushi ya wadaci fuskarsa,alamun maganar tayi masa dadi sosai,ya fara buda file din ya duba sannan ya dora idonsa a kanta


"Thank you sisi,na gode da baki bani kunya ba baki kuma watsa min qasa a ido ba" yadda yayi appreciating nata saita kasa neman komai daga wajensa,ta saki qaramin murmushi ta gyada kai kawai


"Next week on Monday zaki fara shiga office dinki,komai da kike buqata kiyimin magana baki da matsalarsa in sha Allah,already shi partner din naki ya fara shiga cikin wannan satin" yana maganar yana danne danne a wayarsa. Daga kai yayi 


"Na saka miki kudi ko zaki buqaci yin siyayya"


"Oh no yaaya,ina da kudi a account dina fa,sannan last week yaa Saifullahi ya sakamin shima"


"I know,hal jaza'ul ihsani illal ihsan" kai ta jijjiga a hankali,sai taji cikin ranta tana jin dadin abinda tayi masan,tunda shima har qasan zuciya da fuskarsa abun ya faranta masa.


           Ciki ta koma ta fara shiryawa don wucewa gida,already dama tana da intention na zuwa yin shopping din,akwai kayayyakin amfaninta da sukayi low.


**********Lafiyayyun motocine qirar range rover baqaqe sidik ke wulwula gudu saman kwalta wata nabin wata har guda hudu a jere. Tun daga inda suka taho wato cikin filin sauka da tashin jiragen saman malam aminu kano wato aminu kano international airport har zuwa cikin rukunin gidajen dake unguwar nasarawa GRA,duk inda suka gifta daukan idanu da kuma hankulan al'umma sukeyi tare da saka kokwanton cikin zukatan al'umma na tunanin mamallakan motocin da babu cikakkiyar number a jiki kamar ta kowanne abun hawa,sai wasu qididdigaggun haruffa da kuma lambobi da sukazo a jere data sauran kowacce mota dake bin 'yaruwarta.


         A hankali suka nutsa cikin nasarawa,sannan kai tsaye suka fada titin guda abdullahi road,kafin su tsaya qofar bristol palace. Cikin gaggawa kuma security din dake tsaron qofar gidan suka wangale musu gate ba tare da tsananta bincike ba,dukka motocin suka shige ciki,suka kuma samu wajena gurbin da aka tanada don ajjiye motoci suka faka. Cikin qasa da minti daya dukka qofofin motar suka bude banda guda daya tak,mutanen dake ciki sanye da baqaqen suit suka firfito,kowa ya samu guri ya tsaya,biyu daga cikinsu kuma suka bi hanyar da zata sadasu da reception na hotel din cikin sassarfa.


          A qalla mintuna biyar kyawawa sai ga mutum biyu daga cikinsu ya dawo,cikin azama da zafin nama ya isa ga motar dake tsaye dukka qofofinta a kulle yayi knocking baqin glass din motar,aka dan zugeshi kadan,yayi magana ta mintina sannan yabar wajen,ya koma bayan motar ya dage,yasa hannu ya fidda wasu kyawawan luggage guda biyu,biyu daga cikin mutanen dake tsaye daga bayansa suka matso,kowa ya riqe guda daya,sannan ya sake zagayawa right side na seat din bayan motar ya bude qofar,yaja baya cikin girmamawa don bawa mamallakin motar fitowa.


           Sakanni sittin cif kafin qafarsa ta fara fitowa,Sannan ya zuro qafarsa cikin kyakkyawan takalmi qirar kamfanin hermes na qasar france,sai daukar idanu yake saboda tsananin kyau da tsafta,ya sake daukar wasu sakannin kafin ya zuro dukka jikinsa zuwa waje. Zara zara yatsun hannunsa ya sanya yana qoqarin cire wayar dake maqale a kunnensa,kyakkyawar fuskarsa mai cike da wani irin kwarjini haiba da cikar zati a dinke tsaf!,babu alamun fara'a ko kadan tattare da ita.


             Fari ne,amma ba zaka kirashi kar ba,wani irin fari da bai cika haske da yawa ba,me murjajjen jiki da babu wani waje da yake a rame ko ya nuna alamun qashi,saima qaqqarfar siffarsa da cikakken zatinsa daya nuna kansa da kansa ta jikin lallausan yadin vicuna mai asalin kyau da tsada dake jikinsa,wanda aka yiwa wani irin dinki na musamman mai jan hankali,duka duka tsahon rigar bai wuce gwiwarsa ba,dogon hannu ne da rigar daya bai qarasa tsintsiyar hannu ba,an qawata hannun rigar da wasu irin links masu zubin gold,daga qasansu kadan kuma kyakkyawan agogon hannu ne baqi qirar kamfanin Casio daya kwanta luf saman fatarsa dame lullube da gargasa baqa sidik mai santsi,wadda ta fito har zuwa saman hannunsa da kuma saman kowanne yatsa nasa,zobe ne qwaya tal daga tsakiyar hannun nasa na wani irin qarfe mai daraja,wanda shi ba gold bane,hakanan ba azurfa ba.


              Yadda sumar kansa take baqa sidik a nannade sannan kuma a kwance,hakan gashin daya qawata gefe da gefen fuskarsa,zaka iya kiransa qasumba,saidai baiyi kama da qasumba hakanan baiyi kama da saje ba,saboda wani irin gyara na musamman da akayi masa,wanda yasa yafi qasumba kyan gani,yafi kuma saje tsari da qawatuwa,tun daga kumatunsa zuwa habarsa,ya kuma hade da qasan hancinsa. Baqar sumar da baqin yadin dake jikinsa suka hadu suka haska farar fatarsa tarrrr tamkar fitowar rana a farkon wuni. Eye glasses din daya sanya kuma ko kadan bai boye kyawawan qwayar idanunsa ba dake da wani irin shape mai matuqar fusgar hankali,idanun dake cike da wani irin kwarjini mai tarin yawa,kwarjinin da a kullum yake lullube da fushi da kuma fusata.


           Ko yaya ka qara taqi kadan kusa dashi kana iya shaqar daddadan qamshin turarensa da ba lallai ka gane ainihin wanne irin turare bane,saidai yakan sanya nutsuwa ga duk wanda ya shaqeshi,ya kuma qara kwarjini ga ma'abocin qamshin.


            Dukka hannayensa ya zube a aljihun lallausan yadin jikinsa,ya kuma daga kai yana kallon tsororuwar ginin hotel din cikin kamewa da nutsuwarsa,tamkar wanda yake nazarin wani abu,yayin da dukka mutanen suka zamana a tsare cikin shirin kota kwanar karbar umarni daga gareshi. Iska ya furza ya taka zuwa gaba,abinda ya sanya mutum biyu daga ciki sukayi gaba kamar masu masa jagora,sauran kuma suna biye dashi,yayin da daya daga gefansa wanda ke riqe da wani babban folder ya matso gefansa kadan


"May I continue sir" ya fada cikin matuqar girmamawa a russune,da hannu yayi masa nuni da eh,yaci gaba da takawa shi da sauran mutanen,yana biye dashi yana karanto masa komai daki daki. Dukkansu suka fara kutsa kai zuwa cikin main entrance na hotel din.


            A gaggauce suka wuce zuwa lipter da zai sadasu da dakin da zai sauka,cikin mintunan da ba zasu wuce sakanni sittin ba ta tsaya,suna biye dashi har a sannan ta bude dukka suka fito. Kai tsaye har zuwa qofar dakin. Daga daga ciki yayi scanning card a bakin qofar,tayi qaramar qara alamun samun izinin shiga. 

           Palace suit,babban dakin dake da aqalla zai iya daukar mutum bakwai cif,two ensuite bedroom da kuma master bedroom guda daya,living room dining room kitchen da kuma corridor. Wannan shine cikakken zabinsa ga masauki,bayason takura bayason matsi,duk sanda tafiya ta kamashi zuwa wani gari da bashi da gida nashi mallakin kansa,ko kuma yake buqatar kebewa ko sauka ya huta sosai ba tare da kowa yasan ya shigo ba.

           Yadda yayi cak a tsaye yana sauraron bayanin da inyamurin ke kwararo masa haka sauran mutanen da suka shigo tare dashi suke a tsaye,dukkansu na jiran wani umarni nasa ne. Sosai ya kafe mutumin da idanu,duk da cewa bai kalleshi ba amma tsantsar kwarjinin da idanunsa ke dashi ya hudashi,tun daga fatarsa har zuwa jinin jikinsa ua harbawa kwanya da zuciyarsa,take muryarsa ta fara rawa,ya fada kwan gaba kwan baya cikin bayanansa,sai ya lumshe kyawawan idanunsa kawai, qwaqwalwarsa ta fara kaishi inda yake zato ko hasashe.


"Where is musaddiq?" Karon farko da muryarsa me taushi da wani irin amo a cikinta ta bayyana cikin sigar tambaya da alamun gajiya da jin soki burutsun bayanan da ake masa. Daya daga cikin mutanen ya matso da hanzari ya amsa masa


"Sir.....on his way"


"Ka kirashi,ka gaya masa yayi sauri,idan yazo ya karbi dukkan folders din dake hannun peter kafin ya nemeni,you can go" ya fada a taqaice yana sanya kansa ciki.


             Gaba daya gumi ya rufe mutumin da aka kira da peter din,tabbas yasan qaryarsa ta qare,tun daga watan da aka sanar da yiwuwar zuwansa kamfanin,yaketa shige da ficen ganin ya binne komai,ya kuma rufe bakin dukka wanda zaiyi ruwa da tsaki wajen kawo tarnaqi cikin walwalarsa,sai gashi a karon farko......tun ba'a je ko ina ba alamu sun fara nuna kansu. Ya san yaron sarai,bawai tun yau ba,aiki ya taba hadasu sau daya tak dashi kafin su suma ya karkata hankalinsa zuwa wata qasar,bai kwashe da dadi a hannunsa ba,yaji babu dadi qwarai,sai gashi wata mummunar qaddarar ta sake dawowa tana neman budadeshi.FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post