YANZU - YANZU: Rundunar Tsaro Ta ECOWAS Ta Bayyana Ranar Da Zata Fara Fatattakar Sojojin Nijar.

YANZU - YANZU: Rundunar Tsaro Ta ECOWAS Ta Bayyana Ranar Da Zata Fara Fatattakar Sojojin Nijar.

YANZU - YANZU: Rundunar Tsaro Ta  ECOWAS Ta Bayyana Ranar Da Zata Fara Fatattakar Sojojin Nijar.
BBC/ECOWAS

Jami'an Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas) sun ce hafsoshin tsaron ƙungiyar sun yanke shawara a kan ranar da za su tura dakarun ko-ta-kwana zuwa Nijar, bayan wani taron kwana biyu da suka yi a Accra, babban birnin Ghana.

"Mun shirya shiga a duk lokacin da aka ba mu umarni".

A cewar jami'an, Ecowas ta cimma wannan matsayi ne bayan abin da suka bayyana da kafiya ko taurin kan shugabannin mulkin soja da kuma tarnaƙin da suke ta kawowa a hanyar cimma sulhu game da wannan rikici.

Da yake jawabi ga kafofin yaɗa labarai bayan taron manyan hafsoshin, kwamishinan Ecowas kan harkokin siyasa, Ambasada Abdel-Fatau Musah ya ce ba za su bayyana ranar da suka sanya ba, saboda dalilai na dabarun aikin soja.

Sai dai ya ce duk mambobin ƙungiyar tara da suka halarci taron za su ba da gudunmawar dakaru da kayan aikin don shiga Nijar.

Ya jaddada cewa ‘matakin zai kasance irin na gamo da kasawa; kuma zai kasance taƙaitacce don ganin an dawo da tsarin mulki' a Nijar.

Haka zalika sun yi la'akari da illolin tsaro da na jin ƙan ɗan'adan waɗanda mai yiwuwa matakin amfani da ƙarfin sojan zai janyo.

Sai dai, Ecowas ta ce har yanzu ƙofar tattaunawa a buɗe take don warware rikicin ta hanyar lumana kuma za ta aika wani ayarin shiga tsakani zuwa Nijar nan da 'yan kwanaki.

Wasu hafsoshin soji ne suka hamɓarar da Shugaba Bazoum Mohamed na Nijar ranar 26 ga watan Yuli, kuma suka yi biris da kiraye-kirayen Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyar Ecowas da sauran Ƙasashen Yamma na su mayar da shi kan mulki.

Lamarin dai ya harzuƙa ƙungiyar Ecowas, wadda ta ba da umarnin cewa rundunarta ta ko-ta-kwana ta ɗaura ɗamarar yaƙi.

Manyan hafsoshin tsaron dai sun kuma ƙi yin bayani kan yadda za su tura dakarun da kuma sauran muhimman bayanai game da tsare-tsaren matakin sojin.

Ƙungiyar Ecowas dai na neman lallai a gaggauta sakin hamɓararren shugaban ƙasar da iyalinsa da kuma jami'an gwamnatinsa.

Janar Abdourahamane Tchiani ya ƙwace iko ne cikin watan jiya a wani juyin mulkin da ba a zubar da jini ba.

Nijar, ƙasa mai arziƙin yuraniyam, na ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya kuma tana fama da wani mummunan rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post