ZAFIN KAI page 8 complete by Mamuhgee

ZAFIN KAI page 8 complete by Mamuhgee

 

ZAFIN KAI page 8 complete by Mamuhgee

_Arewabooks@Mamuhgee_

8

Hankalinsu duka baa kwance ba suka isa gida saidai cikin saa har lokacin Ababa bai dawo gida ba Hande ce kawai taketa fadan sun samu sake sunyi dare babu wanda yayi magana acikinsu saida tagama yi musu tatas kafin suka hanzarta yin sallah suka fito suka karbarwa Annensu aikin da bata gamaba har lokacin.

Wani sabon wankin ne suka fara cikin dare basu gamaba sai guraren karfe tara na dare 

Daqyar sukai sallah sukaci dan abincin da aka basu suka kwanta kowannensu gababin jikinsa na ciwo.

Washe gari haka guraren 9 na safe suka isa makaranta.

Sumayyah kai tsaye libry ta isa sbd acan zasuyi karatu da wadda sukai jiya,

Tana isa zata shiga ta nema id card dinta ta rasa,

Gefe ta koma ta zazzage jakarta tafara dubawa hankalinta na fara tashi sbd batasan ya zatayi ta samu wani ba komai Benazir ce take yi mata bata iya zuwa da kanta.


Dubawa takeyi da gaske tana bin pages damuwarta na bayyanuwa duk da tanada tabbacin yana jakar bata fiddasa ba.

Duk abinda yake jakar tayi masa daddaya amma bata gansa ba,

Tattara kayanta tayi ta maida jakar ta nufi gurin Benazir cikin dan sauri da damuwa,tsoronta da tashin hankalinta shine ace sai ka biya kudi zaa maka wani,

Ina zata samu kudin?Ababa idan suka fada masa saiya kusan rabata da duniya kafin ya bada kudin,ya Allah yasa ta gansa kokuma baa biyan kudi ake bada wani.


A yau dinma tashin hankalinta bai bari tana tantance inda take saka kafafunta ba kanta a qasa har ta isa department dinsu Benazir din.


Kiris ya rage tayi karo da wanda yake tahowa yana amsa waya cikin nutsuwa da sanyin hali 

Da sauri ya dago hannuwansa yayi saurin tareta sbd kada jikinsu ya hadu.


A firgice ta dago tana ja da baya cikin qarfin gaske sai gata a qasa 

Bata damuba ta miqe da sauri kanta na yin qasa a sanyaye ta basa hakuri tana sake sauke kai kaman wadda take gaban Ababa.


Cikin dan mamaki ya kalleta  yana tabbatarda itace mai student id card din hannunsa,

Juyawa tayi zata wuce batareda ta dago ta kallesa ba zuwa lokacin jikinta rawa yakeyi sosai dan gabaki daya Azabar Ababa kawai take jin har tafara sauka jikinta.


"Hey Miss" yafada da muryarsa mai kamala yana taba Aljihun tsadaddun qananun kayan givenchy dake jikinsa baiji card din ba ya dan rintse ido a hankali yana tino yana cikin motar daya shigo makarantar jiya da ita.

Ba damuwan komai a ransa ya ambaci sunanta kai tsaye daya tina shine a jikin katin ganin tana sake sauri kaman mai tsoron mutane a bayyane sai kawai ya qyaleta ya wuce yana duba time din agogonsa sbd ba lokaci zai bata ba a school din zaiyi magana ne kawai da prof ya wuce gurin aikinsa.


Yana wucewa Sumayyah data labe daga gefen wasu students ta futo tana kallon inda yabi da ido tsoronta na qaruwa sbd ta tina fuskarsa shine ta gani jiyan ya tsaidata.

Meyake so a gurinta?

Baiyi kama da student ba sbd shekarunsa da jikinsa tareda maturity dinsa sun bayyanarda hakan,

Kyawunsa da kwarjininsa tsoro ya bata matuqa tareda firgitata,babban tashin hankalinta kada ya sake tsayar da ita wani yagani tsautsayi yasa Ababa ya sani Alkiyamarta ta tsaya.


Benazir data qaraso gurinta tana dafata daga baya saida sumayyar takusa shaqewa sbd tsoro da tashin firgita,tana waiwayowa taga Benazir ce wasu hawayen mutuwat jiki suka ciko idanuwanta ta sauke tana kokarin hanasu saukowa.


Benazir data ga hakan hankalinta ya tashi cikin mamaki qasa qasa sbd kar ajisu tace"


Me yafaru?

Ababa yazo nan ne?

Wani abu yafaru ne?


Kasa magana sumayyah tayi ta silale ta zube zaune kan  gurin zama tana kokarin daidaita numfashinta dayake futa da sauri na tashin hankali biyu datake ciki na batan student id card dinta dakuma mutumin daya tsayar da ita wadda sunfi kaunar hadarin mashin da wani namiji ya tsaidasu.

Shafa bayanta Benazir ta ringa yi ahankali ta cikin hijab dinta tana cewa


"Ki kwantar da hankalinki kada ki bari yanayinki ya sauya asan halinda muke ciki kaman yanda Ababa yafada mana."


A hankali ta ringa sauke numfashi tana kokarin daidaito nutsuwarta har tsowon mintina kafin ta dan dawo daidai ta dago idanuwanta da har sunyi jajir ta kalli Benazir dake jiran bayaninta cikin fargaban idan ba wani abin ne ya sameta ba.


Bude baki tayi ahankali ta yiwa Benazir din bayanin batan student id card dinta tareda kasa fada mata mutumin da yayi mata magana sbd tinowa da hakan kawai girgiza kayan cikinta da zuciyarta yake bare iya bude baki ta fadawa ko Benazir cewan wani namiji ya tsaidata.


Shiru Benazir tayi sbd itama batasan ta ina zara fara ba tunda ba muaamala sikeyi ba da mutane bare su tambaya qarin bayani.


Shiru sukayi sun jima a hakan batareda sanin abin yi ba,ganin hakan Sumayyah taji gabaki daya hankalinta ya qara tashi suka fito daga department din suka nufi gurin da babu mutane sosai suka zauna take Sumayyah ta fashe da kuka mara sauti tana jin yanda zasu sanar da Ababa hakan.


Shiru benazir tayi itama jikinta na mutuwa sbd tasan bawai tsallakewa zatayiba itama hadasu zaiyi ya musu hukunci daya.

Kasa cewa Antyn tata sumayyah ta dena kuka tayi sbd batasan wane qwarin gwiwar zata bata ba dan haka sukai tsit sai kukan sumyayah da ita kadai ce take jin sautinsa.


Basu san zaune suke gefen wata lafiyayyar black beymack ba saida mai motar ya doso gurin kai tsaye idanuwansa akan Sumayyah wadda idanuwanta sukai jajir jikinta yai sanyi gaba daya.


Kallo daya Benazir tayi masa tayi qasa da kanta bugun zuciyarta na tsananta tareda wata irin fargaba mai tsanani wadda ta sanya numfashinta fita da sauri saidai tinda tayi qasa da kanta bata dago ba.


Shi kuwa sumayyah data qarasa rikicewa da ganinsa yake kalla mamakinta na sake kamasa sbd kai tsaye ya gane tsoron maza takeyi kokuma irin tarbiyar da aka bata ne daga gidansu.


Tsoro ya hana sumayyah dauke idanuwanta daga kansa hannuwanta dake qanqame da jakarta suna rawa.


Kasa shiga motarsa yayi sbd zuciyar kulawa da tausayi tareda sanyi da Allah yayi masa fiyeda kowa a familynsa ya juyo ahankali cikin nutsuwa ya dawo gabansu ya tsaya murya a kamale yacewa sumayyah


"Student id card din ki na gurina nayi kokarin baki a jiyan amma baki tsaya ba,

Yau kuma ban fito da motan dana barsa ba a jiyan amma insha Allah gobe zan sake shigowa wani abin zan taho dashi ki jira ni anan around 4 haka lokacin na shigo sai na baki"


Daga sumayyah din har Benazir a tare suka dago suka kallesa suna masa wats irin godiyar data bayyanar da fadawar tashin hankalinsu.


Da mamaki ya zubawa Sumayyah idanuwansa masu haske yana cewa

"Kina kuka ne sbd Batan card din ne?"

"Are you for real?

Share hawayenta ta hau yi tana sauke kanta qasa daga idanuwansa dasuka fara firgitata.


Kamanninta da Benazir yasashi fahimtar 'yar uwarta ce kuma kusan halinsu daya na rashin iya kallon mutune da alama itama tsoron mazan takeyi.

Wani gajeran murmushi ya saki tareda bude motarsa ya fada ya tada tabar gurin yana kallansu ta mirror harya bace basu dago sun kalla inda yabi ba.


Ajiyar zuciya Sumayyah ta ringa saukewa a jere tana jin sanyi na mamaye zuciyarta data kusa bugawa da tsoro.

Tashi sukai suka koma kowannensu ya nufi gurin da zaiyi lectures basu koma gida ba sai 6 saura.

Suna isa sallar magrib kawai sikai sika fito aikin wanki saida suka gama aka basu abincinsu suka zauna sukaci tareda Annensu dake dan fama da zazzabi kwana biyun sbd yammacin dasuke kaiwa aikin na mata yawan dayafi karfinta.


Basa karatu gida ko sun dawo sbd basuda abin haskawa haka suke hakura duk yanda sukazo karatu musamman sumayyah datakeson Benazir din ta ringa dan wayar mata da kai akan wasu kalmomin.


Washe gari tinda suka wayi gari sike cikin faduwar gaba da fargaban yanda zasu tafi gurin wani namiji karban student id card din na Sumayyah,

Sumayyah tafi Benazir din shiga tsoro da fargaba sbd itace tayi sakacin yar da card din hakama saninsu ne Ababa wasu lokutan yana sakawa ana bibiyarsu dan haka sike cikin fargaban.


Har sika isa makaranta babu mai walwala ko nutsuwar zuciya,

Haka sika wuni ba sukunin rai har 4 din tayi sika isa inda yace din suka tsaya suna waige waige ciki fargaba.

Sam hankalinsu bai kwanta ba da haduwar dan haka a matse suke kusan mintina ashirin kafin motarsa ta danno kai a gurin dan shi tini ya manta dasu din saida ya qaraso gurin ya gansu tsaye ya tina Allah yasa da motar yazo.


Yana parking tin bai fito ba ya ciro card din ya miqa musu ta window

Hannu biyu sumayyah tasaka ta karba batareda ta dago ba cikin girmamawa mai tsanani sukai masa godiya kaman wanda yayi musu wata babbar kyauta.


Mamaki suka sake basa tareda birgesa musamman sumayyah wadda Sanyinta da rauninta dayake bayyane yafi basa tausayinta da burgewa.


Juyawa sukayi suka bace bat daga gurin qafafunsu na sarkewa.


Saida suka bacewa ganinsa kafin kowannensu ya saki boyayar ajiyar zuciya basu cewa juna kala ba suka tinkari hanyar ficewa daga makarantar zuwa gida.


Saida suka isa gida suka shiga dakinsu suka zauna kusa da Annensu hankalinsu ya kwanta daidai suka sake ajiyar zuciya a tare batareda sunyi yunqurin zantawa akan komaiba game da lamarin batan id card din gaba daya.******kaddara zaace ko tsautsayi kokuma rabo?

Haduwar sumayyah da Bilal kaante daga wannan lokacin sai ta zama kaman wainda ake turowa dan kuwa kusan babu ranar da zai shigo makarantar Allah bai qaddara haduwarsa da sumayyah ba wadda tsoro da firgicin datake shiga a duk lokacinda zata gansa yake sake qarfafa masa tinanin hulda da ita dan kuwa nutsuwarta da kamala tareda tarbiyarta a bayyane take,

Rauninta kaman wani abin birgewa ya zama garesa dan kuwa hawayenta a kusa suke

A kwai ranar daya tsayar da ita ga mamakinsa hawaye yaga suna gangaro mata sai hakan ya sake sakasa tinani da kwadayin son saninta a ransa.

#MAMUH#

#DD KAANTE#BENAZIR#

#LOVE

#MARRIAGE

#ROMANCE#

#BILAL KAANTE#SUMAYYAH#

ZAFAFA BIYAR🔥

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR 'KASHI

Safiyya Huguma

-FURAR DANKO

Billyn Abdul

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400

Pay at

09033181070

09032345899

Zafafa🫶🔥🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post