Abinci ya yi tsadar da ko a mafarki ba a yi zaton haka ba


Health College

Abinci ya yi tsadar da ko a mafarki ba a yi zaton haka ba

Abban Sojoji

Farashin kayan abinci ya cilla sama zuwa kashi 25.08 a cikin Satumba. Ya tashi daga kashi 24.08 a cikin Agusta, kamar yadda Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa, wato NBS.

NBS wadda hukuma ce ta Gwamnatin Tarayya, ta bayyana wannan tsadar kayan abinci, a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da kuma kukan raɗaɗin tsadar rayuwa, sanadiyyar cire tallafin fetur da Gwamnatin Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ta yi a ƙarshen Mayu.

An samu ƙarin kashi 1.72 a watan Agusta, idan aka kwatanta da watan Yuli, 2023. Kamar yadda alƙaluman ƙididdiga suka nuna.

NBS ta ce farashin kayan abinci ya cilla sama da kashi 5.27 a cikin Agusta, bisa la’akari da watan Agusta na shekarar 2022.

Tuni dai raɗadin tsadar rayuwa ya dumfari talakawa da marasa galihu ya na dandatsa.

Kayan abinci musamman shinkafa, gero, masara, doya da wake duk sun yi tsadar da ta tilasta yawancin gidaje an daina yin girki sau uku a kullum, wato safe da rana da kuma dare.

Da yawan gidaje an koma ana yin girki sau biyu, wasu ma sau ɗaya.

Mabarata a kan titi masu kwarara cikin gari da cikin kasuwanni sai ƙaruwa suke yi a kowace rana. Haka masu shiga gidajen mutane sai ƙara tururuwa su ke yi. Sai dai abin takaici, yawancin gidajen da ake shiga ana barar ‘Allah ya ba ku mu samu’, ba su samu sun ci ba, ballantana har su rage su bayar sadaka.

Da dama masu ƙananan sana’o’i sun daina cin kasuwannin ƙauyuka masu ci mako-mako, saboda tsadar kuɗin mota.

Magidanta masu nauyin iyali da yawa sun gudu sun bar iyalin a cikin jidali. Yayin da tallafin kayan abincin da ake rabawa a jihohi, yawanci a babban birni abin ke ƙarewa, inda ko a can ɗin ma, mafi yawa sai dai su ga hotuna a soshiyal midiya kawai, ko kuma su ji labarin an raba kayan tallafi, an bar su da tallaben talaucin tsadar rayuwa.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post