Kukan Zuci page 5 - Novels Elite

Kukan Zuci page 5 - Novels Elite

Kukan Zuci page 5 - Novels Elite

 *💔💔 Kukan Zuci 💔💔*

_Written by Novels Elite._


Wannan labarin ƙirƙirarre ne idan kaji yayi da rayuwarka/ki ayi haƙuri domin banyi hakan da wata manufa ba sai don nishaɗi. 


Page 5.


A firgice Kabir ya farka tare da yi salati, sannan ya ja wani dogon numfashi ya ɗauki ruwan dake gefen gadon sa ya sha, tsorace ya tashi ya shiga sashin mahaifin nashi inda ya tabbatar da lallai mafarki yake yi, ko da ya dawo ɗaki ya kasa natsuwa bare kuma yayi bacci, ganin haka ne yayi alwala ya yi nafilfi tare da yin addu'o'in neman tsari, anan dai ya kai har asuba ba tare da yayi bacci, ko da ya dawo masallaci ma azkhar kawai ya cigaba da yi har gari yayi haske alamun rana ta fito. Kabir ya tafi sashin mahaifinsa domin min gaida shi, yayi Sa'a kuwa yana nan, ya gama gaida shi ya fita ya koma ɗakinsa don ko ya je sashin Hajiya Rabi yasan basu tashi ba.


Kamal kuwa harkoki sun buɗe sosai sakamakon zama babban dilan miyagun kwayoyi wanda ƙananan diloli a wajen sa suke karɓar ƙwayoyi, ba kowani jami'in tsaro ne ke kama kayanshi ba saboda ya siyesu dukka don haka yake cin kare sa ba ba baka, Kamal yayi nisa yadda baka tunani sauran yan'uwansa ma ya jawo su cikin harkar tare da sahalewar mahaifiyarsu Hajiya Rabi.

Duniyar tayi musu daɗi basa ta mahaifinsu bare kuma Kabir, Safiya tana tausaya mishi sosai tasan tabbas ana zaluntar sa a mayar da shi kamar ba ɗan gida ba.


Tun da ta koma gidan, ta kasa zaune ta kasa tsaye, kalaman Hajiya Rabi ne kawai suke mata yawo a ƙwaƙwalwa, saidai tayi doguwar ajiyar zuciya sannan tayi ƙwafa don abin na cin ta a rai. Tana ta fama ƙulle ƙullen yadda zata ɓullo ma ƙawarta don tana so ta haɗa auren ɗiyarta da ɗan ƙawar na ta ko ta halin ƙaƙa, to amma abinda bata sani ba shine itama fa ƙawar nata a shirye take kar ta san kar.


Ƙarfe takwas na dare ranar Alh. Mahi na Zaune a ƙofar gida, tare da 'yan maƙwabtarsa suna hira bayan sun fito daga sallar isha'i, kwatsam Alh. Mahi yaga abinda baiyi tunanin gani ba, Kamal ne rungume da 'yan mata guda biyu gidan su ya nufa tare da su, cikin tsananin ɓacin rai Alh. Mahi ya dakawa Kamal tsare tare da ce masa "kai Kamal duk iskancin naka a waje bai ishe ka bane sai ka dawo gida, Allah wadaran irin wannan halin naka" Kamal na buɗe baki ya ce ma mahaifinsa "kai meyasa bakayi ba a lokacin ka? Wannan lokaci a ne saboda haka kada a kara min." Nan take ya yanke jiki ya faɗa sakamakon ɓakin cikin maganar Kamal. Salatin da mutanen wajen ne sukayi ya sa Kabir ya fito da sauri, ganin mahaifinsa kwance a ƙasa yasa jikinsa ya fara ɓari da sauri ya ɗaga shi da taimakon makwabtar nasu aka kai shi asibiti. Saidai tunda aka kaishi asibiti babu wanda yaje asibitin a cikin sauran yaran, saidai Hajiya Rabi itama bata daɗe ba a asibitin.


Likitoci sun duba shi saidai sakamakon faɗuwar da yayi ya sami mutuwar ɓarin jiki wato "paralyzed" Kamal ya shiga tsananin damuwa don ganin halin da mahaifin nasa yake ciki, shike ta ɗawainiya dashi domin Hajiya Rabi da yaranta basu damu da Alhaji Mahi ba, domin ko zuwa duba shi basa yi, Kabiru kuka kawai yake yi mara sauti idan ya kalli irin halin da mahaifinsa yake ciki. 


Sannu a hankali ya fara iya bude ido amma fa komai saidai ayi masa Magana ma ba a iya gane abinda yake fada saisdai yayi nuni da hannu. Bakin cikin Kamal dai shi kadai ke masa yawo a cikin zuciyarsa. In banda zafafan wayaye ba abinda zaka gani a idanunsa saidai Kabir yayi ta rarrashinsa.


Hajara kuwa idan kaganta baza kace ta taba shan wuya ba, tayi kyau sosai wanda dama tana da jiki mekyau wahala ne kawai, amma kasancewar ta a Gidan Prof. Umar yasa duk kyawun jikinta ya dawo ta yadda idan Hajiya Rabi zata ganta sai ta ji kamar ta sa wuka ta yankata nan take, dama Hajaran tafi Hajiya Rabi Kyau ita dama bata iya gyara dakin ta ma bare kuma jikinta.

Professor ya dauke ta tamkar ‘yar uwarsa wanda suka fito ciki daya, ganin haka ne yasa ita ma Hajara take mutuntasu ta yadda suma ‘din suka dauketa. 

A’isha, in ji Saratu


“na’am Umma”


kin ji duk yadda muka yi da Hajiya Rabi akan aurenki ko?


Naji Umma, meyasa tunda bata so zaza ki rabu da ita bamu hakura idan to shima din baya sona fa?

Hakan ya nuna min cewa lallai baki da tunani, duba da yadda suke da tarin dukiya masu yawa, ko da baki auri yaron Hajiya Rabi ba to tabbas sai anyi biyu babu domin zan bi ko wacce irin hanya ce don ganin na salwantar da dukiyar su ta haka ne kawai hankali na zai kwanta ban damu da irin halin da su shiga ba, tun da taki ki amincewa da muradina na hada ‘ya’yan mu aure a tsakaninsu.


Haba umma da dai kin rabu dasu su kawai Allah shine wanda yake azurta bayin sa ta yadda ya so a lokacin da yake so, ni a ganina ki kyalesu Allah ya bamu namu arzikin.


Saratu ta tabe baki tare da jan dogon tsaki sannan tayi sassanyar aziyar zuciya, cikin takaici ta kalli A’isha, “duk abin nan da kika ga ina yi saboda ke nakeyi domin ci sami miji mai arziki wanda zaki huta, bana son ki auri wanda zaki sha wahala a Gidan sa, haba kamar……… Aisha ta katse ta da cewa, “shikenan tunda haka kikeso kiyi duk yadda kika gay a dace, am matsayinki na wacce ta haifeni.



Ko ke fa, yanzu na san lallai wannan Aisha ta ce, tabbas zan fara shirye-shirye don ganin na durkusar da Hajiya Rabi.


 Domin faɗin ra'ayoyin ku, kuyi magana a comment. Ko Whatsapp.

Novels Elite

08062334828

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post