Kurkukun Ƙaddara page 6


Health College

Kurkukun Ƙaddara page 6

Kurkukun Ƙaddara page

 *💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

*daga alƙalamin Boss Bature ✍️*

 dedicated to Aunty kubra❤

قصة حزينة جدا عن السجناء🥺💔

*E6*

A hankali ya tura ƙopar falon ya shigo Ciki,  dawowar shi ke nan daga masallaci, ya ɗan tsaya sauraron wa'azi,  jikin shi na a sanye da jallabiya ash colour, da sauri ya nufi bedroom ɗinsa, Da sallama a bakin shi ya shiga, tunkafin ya ƙarasa shiga ya same ta a kwance tsakiyar gado tana ta sharar baccin ta hada minshari, Agogo ya kalla shida ta kusa, ƙarasa shiga Cikin bedroom ɗin ya yi a gefen gadon ya zauna, tare da ɗan juyo wa yana kallonta, tayi ɗai ɗai a saman gadon, Kayan baccin da ya sanya mata jiya sune a jikinta riga da wando blue sky, curly hair ɗinta duk ya cukurkuɗe ya nannaɗe,


a Hankali ya sanya hannu tare da jan hancin ta, yatsina fuska tayi tare da juyar da kanta gefe batare data farka ba,

  "Wake up My lovely daughter" Cikin kunne yayi mata raɗa,

  Buɗe gray eyes ɗinta ta ɗanyi slowly tana kallon fuskar shi biji biji,

  "Nauyin bacci ko? Oya wake up, kada muyi late, ki tashi inyi maki wanka, in girka maki abinci mu ci mu ƙoshi, kafin na sauke ki a school ni kuma na wuce wurin aikina


Jin tayi shiru ba ta ce komai ba, yasa shi fara Yi mata cakulkulo, lokaci guda ta 6a66ake da dariya, white teeth ɗinta kamar gonar auduga, saboda tsabar kyau, kai kace wani abinci bai ta6a giftawa ta cikinsu ba saboda hasken su,


Sosai ya sanya ta nishaɗi, a ƙarshe Ya ɗauke ta saman kafadar shi Ya nufi toilet da ita, almost 15 mins Ya fito da ita Goye saman bayan shi, Ya ɗaura mata towel ajikinta,


A saman  mirror chair  ya zaunar da ita, Hair dryer Ya ɗauko acikin drawern dake ɗauke da madubin, Ya jonata ajikin Socket,Nan take Iska ta soma busowa buuuuu, runtse ido tayi tana dariya mirmishi ya saki ganin yadda ta ɗan zabura, zura hannun shi ɗaya yayi acikin sumar kanta yana cakuɗata sosai ya busar mata da gashin, Bayan Ya kammala ya kashe dryer din, ya mayar da ita inda ya ɗaukota, ya kuma ɗauko Comb,Ya shiga sharce mata gashin, Sai faman sakin murmushi take yi, A duk lokacin da taga daddynta yana yi mata hidima kamar sarauniya ba ƙaramin daɗi ta ke ji ba, har tunani take yi anya kuwa akwai yaron daya fita samun gatanci?


ta cikin mirror taj ke kallonta, ganin ta ƙurawa madubin ido da alama wani abu ta ke tunani, Man gashin ta Ya ɗauko Ya shiga shafa mata, Bayan ya kammala Ya ɗauki ribbom ɗinta da ke a jiye gaban mirror din, Hannu yasa yana ƙokarin tattara gashin kanta, Abun mamaki daga ya haɗa zai ɗaure saiya watse, Yawan gashi ne da ita ga tsayi, don a yanzu gashin ta ya kai mid back ɗinta, sai da taj yayi da gaske tukunna Ya samu ya ɗaure mata shi,


   "Daddy ni da kai wa ya fi kyau" ta yi tambayar tana sakar ma mirmishi

  Dungurin kanta yayi"Kinfi kowa sani ae" ya yi maganar tare da juyawa ya nufi closet ɗinsu, Hannu yasa ya buɗe murfin, Jerin kayan sawan shi ne da kayanta, Uniform ɗinta Ya ɗauko mata riga fara sai mini skirt red colour, Abaya fara ƴar short, a yanzu angel tana a class 5 saboda ƙoƙarinta, ga wayau da Allah ya yi mata uwa dila agari,


bayan ya kammala sanya mata uniform ɗin Ya feshe mata Jikinta da turare, Ya zaunar da ita gefen gado"Am coming now" ya ambaci hakan tare da juyawa Ya fuce daga ɗakin, jim kaɗan Ya dawo hannunshi ɗauke da Food basket ɗinta, madara ce me sanyi Acikin roba, tare da slide bread ya sanya mata aciki,Sai ƙaramar kula mai ɗauke da chips,

    Ajiye mata yayi a gefen gadon, Shaf shaf ya shige toilet Yayi wanka, Ya fito sanye da short, zuba mashi ido ta yi tana kallon shi,.  

  Harara ya ɗan jefa mata"Zansa kaya"

 ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tayi, tamkar bata ji me yace ba,

  Gyaran murya yayi mata"Can't u hear me? Ki koma Falo inaso zan shirya".

 Maƙe mashi kafaɗa tayi cikin shagwa6a tace"Amma ae ni har wanka ka ke yi mun, kuma kana ganina ba kaya, Amma ni kullum sai ka kore ni in zaka sanya kaya'


Tashin Sense, zaro ido waje ya yi yana kallon ta Cike da mamaki, Ya ma rasa gane wai me take nufi, sai lokacin ya gane kuskuran sa na rashin ɗaukar mai aikin da zata dinga kular ma shi da ita da wankan da yake mata har wannan lokacin,


"Angel don't waste my time, Oya hold ur basket, ki jira ni a falo,"

Ganin ya ɗaure fuska ba wasa Yasa ta sauko daga saman gadon tana tur6une fuska takai hannu ta sungumi basket ɗinta ta fuce falo, Saman sofa ta zauna tana Cika tana batsewa, Bayan ya kammala shiryawa cikin suit,  Ya fito daga ɗakin Ya nufe ta, Hannunta ya kama suka fito daga falon,


Baba maigadi ya samu, A harabar ajiye motocinshi, Yana goge ma shi motar da zai fita da ita,


Tunkafin su ƙarasa baba maigadi ke ta faman washe ma angel baki, ita kuwa ta tsuke fuska, Dama aduk lokacin data ɗauki wanka ta san ta yi kyau, Daƙyar ta ke ma mutane magana,


Suna ƙarasowa bakin motar, Baba maigadi Ya miƙa mashi hannu suka soma gaisawa, kafin Ya kalli angel"Ƴan mata makaranta za'a tafi"?

Ɗaga mashi kai tayi alamar eh"

  "Allah ya bada sa'a Angelata"maƙe mashi kafaɗa ta yi"Ni ta daddy ce"dariya su ka yi gaba ɗayansu,


Taj yace"Bari mu wuce kada mu makara" baba maigadi yace "Allah ya tsare adawo lpy" ya amsa ma shi da ameen kafin ya buɗe mata motar ta shiga ciki, ya zagaya ta left hand, ya buɗe ya zauna a driver seat,


A tsanake Yayi ma motar key, tare da karya kwana Ya nufi gate ɗin, da sauri baba mai gadi Ya riga shi ƙarasawa Ya buɗe mashi gate ɗin, Ya fuce daga gidan,


A hankali yake driving, Ta wutsiyar idonshi ya kalleta, Ta natsu ta kame kanta,

  "Karfa kiyi mun bacci mun kusa ƙarasawa"

  "Ba bacci nake ba,Ina tunani ne"

"Daddy wlh ni banaso mu rabu, dama ka dinga tafiya dani wurin aikin ku"

  Murmushi ya ɗan saki"Karatun naki fa"?y ayi mgnr yayin da yake ƙokarin juya sitiyarin moyar don ya kwarya kwana,

   Shiru bata amsa mashi ba,

"Ni inaso ki yi karatu angel, sai da ilmi ita kanta rayuwa ta ke yin kyau, ko bakyason nan gaba ki zama wani abu da mutane za su yi alfahari dake"?


"Inaso" ta amshi amsa a takaice,

"To faɗamun me kikeso ki zama"?

Da buɗar bakin ta sai cewa tayi"house wife" ae baisan lokacin daya tuntsire da dariya ba, zuba ma shi ido ta yi tana kallonshi, fuskarta babu alamun wasa don ita dagaske ta yi maganar,

  "Daddy why are u laughing? did i say something wrong"?

 Girgiza kai yayi"a'a,May be u did'nt understand my question, Ina nufin wani aiki ki ke son Yi idan kika girma, a aikin gomnati? ya yi tambayar adai dai lokacin daya ƙaraso bakin gate ɗin makarantar, Ya danna hon Mai gadi Ya buɗe mashi gate Ya shiga da motar Cikin school ɗin, A parking space ɗinsu Ya tsayar da motar,


  Fitowa yayi tare da zagayawa Ya buɗe mata murfin motar "baki amsa mun tambayata ba"?

   Ɗagowa tayi suka haɗa ido da shi 

 "Daddy my answer is the same, I wanna be a house wife" Sakin baki yayi galala yana kallonta, Ya rasa taya ya akai tafara tunanin zama house wife, dududu fa primary school ta ke,

  Gudun kada ya makarar da ita,Yasa shi yin shiru bai ƙara tanka mata ba, Ɗauko mata food basket ɗinta ya yi  kafin ya ruƙe hannunta suka nufi Cikin makarantar, kamar kullum har Cikin class ɗin su Ya kai ta, English teacher ɗinsu ya taras a jin Mrs favour,Cikin harshen turanci suka gaisa da shi, ya damƙa mata angel kafin Ya fito daga class ɗinsu Ya nufi motar shi, Zuciyar shi a cunkushe duk ya rasa sukuni, tunani ya shiga yi taya za'ae ya canza mata ra'ayinta na zama matar aure? don wannan ba ƙaramar matsala bace agare shi, ƴar ƙaramar yarinya tana tunanin zama matar aure,


Karasa shige wa Cikin motar yayi a tsanake Yayi mata key, Ya nufi gate ɗin makarantar mai gadi ya buɗe mashi ya fuce,


Harya haura saman titi, Hankalin shi na akan Kalaman angel, shi da yake da burin ta zama babbar ma'aikaciyar gomnati, ashe ita sam Ba wannan bane agaban ta, A ƙarshe dai ya yanke shawarar idan ya ta shi daga aiki ya ɗaukota suka koma gida, Zai zaunar da ita ya yi mata karatun ta natsu, Ko ya samu ya canza mata ra'ayinta,


Wuraren ƙarfe biyu na rana, Ya tashi daga aiki,Sai daya fara zuwa masallaci Yayi sallah cikin jam'i, tukunna Ya nufi school ɗinsu, Lokacin daya karasa makarantar, tunkafin ya fito daga cikin motar, maigadi ya sanar dashi cewa Dr tazo ta dauketa,


Ba ƙaramin daɗi yaji ba, kaitsaye 6atare da 6ata lokaci ba, yaci gaba da da driving, har ya ƙarasa Gida Tun a bakin gate ya tambayi baba maigadi ko aneelerh ta kawo angel, Yace mashi a'a, hakan na nufin tana a gidan su,


Bayan ya ajiye motar Ya nufi Cikin gidan, Bedroom ɗinsa ya shiga, Shaf shaf Ya rage kayan Jikin shi Ya fada toilet don ya yi wanka, ko yaji daɗin jikin shi,


Adai dai wannan Lokacin Aneelerh ta shigo Cikin gidan, ɗauke da angel da alama ta yi bacci, lokacin da ta shigo falo tana ta kwala sallama ba'a amsa mata ba, kawai sai ranta ya bata cewar ko bai kaiga dawowa gidan bane, don bata lura da motar shi da ke ajiye ba, hakan yasa ta nufi bedroom ɗin shi kai tsaye, ta tura ƙopar kafin tasa kai Cikin ɗakin, Asaman gadon shi ta kwantar da angel, short gown ce ajikinta daga gani hada wanka aneelerh tayi mata ta kuma canza mata kayanta,ranƙwafawa ta ɗanyi daga tsaye tana shafa sumar kanta,


Jin motsin ƙopa yasa Aneelerh tayi saurin ɗagowa tare da juyawa bayanta don taga wanene, ba zato ba tsammani idanuwanta suka sauka akan Taj dake fitowa daga Cikin toilet,daga shi sai short a jikin shi,


Burki yaci lokacin da yayi arba da ita, duk tabi ta ruɗe a gigice ta watsa da gudu zata fuce daga ɗakin, Unfortunately ta take rigarta dake jan ƙasa, gaba ɗaya ta tafi zata kife kasa da hanzari Taj Yayi ƙwaƙƙwaran Taku Ya ruƙota, ta dawo jikinshi tana faman sauke ajiyar zuciya, taji tsoran faɗuwa ƙasa don ba ƙaramin buguwa za ta yi ba.


Sam ta manta Jikin wa take, ta ƙaƙameshi sosai, har sai da ya ɗanyi gyaran murya tukunna ta dawo hayyacinta, ta yi saurin raba jikinta daga na shi, duk kunya ta rufe kowannan su,


Daƙyar ya iya buɗe baki yayi mata magana

  "Sai ka ce kin ga dodo, kawai daga gani na kin zabura zaki gudu, yanzu da kinji ciwo fa? so kike uzair Yasa a ɗaure ni ko"?

  Murmushi ta ɗan saki ba tare da ta ce uffan ba, idanuwanta na akan yatsun hannunta,

  "Thank u so much aneelerh, kina ɗawainiya da angel ɗina, tamkar mahaifiyarta, naso ace benazir tana da kyakkyawan hali irin naki sai dai kash ni ban yi sa'ar mata ba,"

  Juyawa ta ɗanyi jiki a sanyaye ta soma tafiya tana tunkarar ƙopar ɗakin sai da takusa fita tukunna ta ɗan dakata da yin tafiyar, A tsanake ta soma magana,

  "Zan ta ya ka addu'a Allah ya baka mace ta gari wadda ta fini" tana kai ƙarshen maganarta, da sauri ta fuce daga ɗakin,


Murmushi taj ya ɗan saki, tare dakai hannu ya shafa sumar kanshi, juyawa ya yi tare da koma wa gaban mirror,  lokaci guda kasala ta baibaye shi, ƙamshin turaren aneelerh ne, Ya cika mashi hancin shi, ita koda yaushe Cikin ƙamshi take, Zama ya yi a saman chair din gaban mirror, Ya kura ido yana kallon fuskar shi ta cikin mirror,


A 6angaren aneelerh kuwa, Da sauri ta fuce daga Cikin gidan, Tana shiga falon gidanta, A saman sofa ta zauna tana faman mayar da nunfashi kamar wadda tasha gudu, tarasa dalilin dayasa a ƴan kwanakin nan take jin faduwar gaba aduk lokacin da ta ci karo da taj,


A tsanake Ya kammala Shirya kanshi Cikin farar t shirt,tare da jeans ya feshe jikinsa da turare mai kamshi,


Yasan aneelerh bazata bar angel da yunwa ba, Shiyasa ma baiyi tunanin shiga kitchen ba,


Wayarshi ce ta soma ringing, da sauri yakai hannu ya dauke ta daga saman drawer,


  Kallon screen ɗin wayar yayi sunan Aminina ne ya bayyana akai, murmu shi ya ɗan saki tare da yin picking call ɗin ya manna wayar a kunnanshi"Assalamu alaikum, ɗan uwana rabin raina"

  On the other hand Uzair yace"Ka koma gida lafiya"?

 "Lafiya lou, Yanzu na fito daga wanka ma"

 "Ka ci abinci"?

 Dariya taj yayi sosai, jin irin tambayoyin da yake yi mashi sai kace wani ƙaramin yaro,

  "Meyasa ka ke mun dariya? yau nafara tambayarka hakan"?

 Tamkar yana agaban shi Ya girgiza kanshi"Nop, just naji abun wani irine, kana tunamun rayuwar mu agidan Uncle"

    Muryar shi ya jiyo da sautin murmushi "Unforgettable momeries, Allah Yabar ƙauna aminina, Zan shiga stadio Sai mun haɗe anjima"


  Taj yace"Okey, take care of ur self for me pls"

  Uzair yace"U too"  fuskarshi ɗauke da murmushi ya yi rejecting call ɗin,


Yana ajiya wayar saman drawer, Yajiyo muryar baba maigadi daga Can cikin falo, Yana kwala sallama,


A hanzarce Ya nufi hanyar fita daga bedroom ɗin, Yayin da yake amsa mashi sallamar"Wa'alaikum Salam"


Cikin falon Ya nufa, A bakin entry ɗin ya same shi a tsaye, ƙarasawa Ya yi yana kallon shi,

  "Barka yalla6ai"ya amsa mashi da "yawwa barka"

 "Dama baƙo ne ka yi"

Da ɗan mamaki akan fuskar taj yace"baƙo kuma"? yayi tambayar ne don shi a iya sanin shi, ba su yi da kowa  zai zo gidansa ba,


 "yalla6ai, Wannan malamin ne daya ta6a zuwa yi ma angel ruƙiya?' cike da son fahimtar da shi baba maigadi ya yi maganar,

  "Kana nufin maisalati"?

Da sauri baba mai gadi yace"kwarai kuwa shi ne"

  "Okey, Ka ce ma shi ya shigo"

 "To yalla6ai," Yakai ƙarshen maganar tare da juyawa yabar falon,


Tajo na atsaye Yana jiran ƙarasowar malamin Ya ji sallamar shi, Fuskar nan dauke da murmushi, Jikin shi na sanye da jallabiya wadda tsayinta bai kai idon ƙafar shi ba, Hannunshi na ruke da cazbaha Kanshi yasha uban rawani, Wani irin ƙamshine ke fita ajikinshi,


Sakar ma shi fuska taj ya yi tare da miƙa mashi hannu cikin girmamawa suka soma gaisawa

  "Allah ya gafarta malam, barka da rana Ya iyali ya jama'a ya ƙoƙari, Allah yataimaka, Allah Ya kara ɗaukaka"

 "Ameen ameen tajo, Fatan na sameka lafiya ya aiki, ya kuma ɗiyar mu"


Taj yace"Alhamdulillah, Duk muna lafiya Mu shiga daga Ciki," ya ruƙo hannunshi, suka nufi sofa ɗin falon, maisalati ya zauna asaman 2 seater, Sae faman sakin murmushi yake yi, Dama shi haka yake kullum fuskar nan a washe, Da wuya kaga bakin shi a ƙulle.


"Bari na kawo maka ruwa" da sauri Malam maisalati ya dakatar dashi"samu wuri  ka zauna tajo, Magana ce mai mahimmanci ce ta kawo ni,"


Tunda Taj yaji hakan, Sai ya zauna saman 1 seater ya tattara kwandon hankalin shi a kan maisalati yana sauraron shi'


"Game da ƴarka injila" da sauri taj yace"Angel sunan ya ke"

  "Oh toh, eh ita ɗin dai" shiru ya ɗanyi yana tunanin ta yadda zai fara yi ma shi jawabi.

  Taj kuwa ya tsare shi da ido, Jikin shi har tsuma yake yi, don a ƙagare ya ke ya ji me angel ɗin ta yi,


Gyaran murya malam maisalati Ya yi kafin ya soma magana a tsanake,

  "ranar da aka kirani Inyi mata ruƙiya, nayi wani laifi laifin kuwa shine bansanar dakai wani abu da nake hasashe akan yarinyar ka ba, bama hasashe bane inanda tabbaci kan shi,"

  Tunda taj yaji hakan,nGabannshi ya faɗi rass aruɗe yace"malam wani abu kenan"?

  Numfashi ya ɗanja kafin yaci gaba da kora mashi jawabi tiryan tiryan

  "Akwai abunda na gani a tattare da yar wurin ka, A lokacin da nake yi mata ruƙiya, Sai dai tsoro da firgici ya hana in faɗa maka, gaskia yana da matuƙar daure kai saboda ba ƙaramar sarqaqiya bace a cikin lamarin kuma ni kaina na kasa tantance sihiri ne a jikinta ko kuwa saboda gaskiya abunda nagani a jikinta babbar al'amari,

  Tuni jikin taj ya soma kakarwa, muryar shi na kerma yace"Malam dan Allah ka yi mun bayani, hankalina a tashe Yake wlh"


Cigaba da magana malamin ya yi"Kaitsaye bazan Iya ce maka ga abunda nagani atattare da ita ba, Amma ina da tabbacin akwai wani abu dake faruwa da ita a jikinta .......",


  Muryarshi na ɗan rawa yace"am..amma malam ni inaga kamar lafiyarta ƙalau, yanzu haka da nake maka magana mun samu sasanci a tsakanina da ita, Tana sona ina sonta ba kamar lokacin baya ba"


Murmushi maisalati ya yi dama yasan zaiyi wuya taj ya fahimce shi, jinjina kai yayi tare da cewa"Shin ka ta6a tunanin ka zauna da ita ka tambaye ta game da abubuwan da take yi maka a baya gamon kanta ne ko kuwa? kuma bata ƴan gane gane haka"?


Shiru taj ya ɗanyi, Shi kaɗai yasan halin da zuciyar shi ta ke aciki, duk da yana kokwanto akan kalaman malamin amma kuma yana tsoron Zancen shi ya zama gaskiya," girgiza kai yayi alamar aah, gyara zama ya yi to gaskia abinda ya kamata kayi kenan dan musan Mike faru da ita ta hakane xamu samo bakin zaren"

  "Shikenan malam in sha Allah zan tambayeta,"

 

Maisalati yace"Yawwa ko kaifa, Sannan kuma shawarar da nake so na baka, Ka tabbatar kana Yi mata addu'o'i akai akai, idan bata iya ba ka koya mata, hada azhkar na safe dana marece, ka kuma koya mata addu'ar shiga toilet, idan zata kwanta da dare ka yi mata addu'oi'in neman tsari, kuma a koda yaushe ta kasance kanta akwai ɗankwali, ka lullu6e mata gashin kanta, Hatta kaya idan zaka sanya mata ka yi mata addu'o'a, Daso samu ne ma duk in zaka kwanta bacci ka kunna maku karatun al'qur'ani mai girma ku kwana da shi," sosai malam maisalati ya ba shi shawarwari a ƙarshe yace"Idan Allah yasa ƙarshen wahalar ta kenan sai kaga Allah ya yaye mata, Amma dai ina ƙara gargaɗinka kada kayi sakaci wurin Yi mata addu'a akoda yaushe, na manta ma ban tambayeka ba, Tana zuwa islamiyya"?


Dakyar ya iya buɗe baki yace"Eh amma ta jima ba ta je ba,


Girgiza kai maisalati yayi"Banso haka ba tajo, kanaso ka yi mana buƙulin samun Hafizar al'qur'ani, wadda zata yiwa addini hidima nan gaba, kamar yadda nake fata, Allah ya baka yarinya mai wayo tubarkalla, ga hali kamar na manyan mutane, bai kamata kayi wasa da wannan damar ba, Gaskiya ina mai baka shawara ka hanzarta mayar da ita makaranta, idan da hali harma tahfeez ka sanyata,"


Ajiyar zuciya taj ya dan sauke"in sha Allah zanyi hakan, Nagode sosai malam, Bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin gode maka, Allah ne kaɗai zai iya biyanka, Allah dai yasa ka maku da alkhairi," sosai taj ya yi ma shi godiya, Koda ya miƙe zai tafi saibda taj ya ƙara tambayar shi ya kawo mashi ruwan sha,

  Yace a'a, Shi dai burin shi ya yi ƙokari wurin ceto rayuwar ƴar shi, Shi ma kuma zai taimaka mata da addu'o'i shida ɗalibansa,daga haka su ka yi sallama dashi Yabar gidan,


Tofa, Bayan tafiyar malam maisalati, kasa zama taj ya yi saboda ruɗanin da zuciyar shi ta shiga, Zarya ya shiga yi a falon, Zuciyarnshi a cunku she take, wani irin faduwar gaba yake ji, tabbas yanyi kuskure sosai akan angle wurin rashin maida hankali ya yi bincike sosai lokacin da take cikin wannan halin"


A hanzarce Ya juya ya nufi bedroom ɗinnshi, tunkafin Ya ƙarasa shiga Ya hango angel zaune saman gadon Ta jingina bayanta jikin headboard(kan gadon)

  

Ƙura mata ido ya yi yana kallonta, ganin ta lumshe i danuwanta, tamkar mai tunanin wani abu,


Shiga cikin ɗakin yayi tare da samun wuri daga gefen gadon ya zauna yana fuskantar ta,


 "My daugher" da buɗar bakin ta sai cewa tayi"Daddy, Malam mai dogon gemu yazo ya cika ka da surutu kamar radiyo mai jini ko" idanuwan ta a rufe ta yi maganar,


Da mamaki akan fuskarshi yace"Taya akai kikasan yazo ke da kinke acikin ɗaki"?


Bude idanuwanta ta yi a hankali,


"Tun dazu nafarka daddy, har leƙa ku nayi,"


"Kinji me muka tattauna dashi" girgiza kai tayi"ae ka hanani yi maka la6e, shiyasa ban tsaya ba, nadawo na zauna"


Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, Kafin ya kuma cewa wani abu ta riga shi cewa"aunty aneelerh ce ta kawoni gida"? ɗaga mata kai ya yi alamar eh,

 "ta kawomin uniform ɗina da kuma bag dina"?ta kuma jefa mashi tambaya,

  "A'a,zanje na kar6o maki su anjima"


Jinjina mashi kai kawai tayi,


Shiru sukayi na dan wani lokaci,kafin ya ruƙo hannunta cikin na shi,

"My daughter"!

Ware ma shi manyan idanuwanta tayi"na'am daddy"


Murmushi ya ɗanbsaki, ya rasa ta ina zai taro zancen, kamar maijin tsoron ta,


Can dai ya daure Ya soma yi mata magana antsanake"Nasan kina sona sosai,bkuma kina kyautatamun, koba haka ba?


Da sauri tace"Hakane daddy"


Jinjina kai yayi"um..Yanzu kina sona,nba kamar lokacin baya ba da kika ɗauramun karan tsana tamkar ni ba daddyn ki ba ne, Pls inaso na tambaye ki, a wannan lokacin ke ki ke ƙuntata mun da kan ki ko kuwa akwai wani ɗan mutun mutumi dake sanya ki kina yi mun"?


Cikin rashin fahimta tace"daddy i don't understand me ka ke nufi"?


"Ina nufin, A time ɗin da kike 6ata mun rai, Wake sanya ki kina yi mun,i know there must be a reason, babu yadda za'ae ki tsani mahaifinki lokaci ɗaya,"


Wurga eye balls ɗinta sama ta yi tana kallon ceilling, ganin ta ɗauki tsawon lokaci tana kallon ceilling ɗin yasa shima ya ɗaga kai yana kallon shi, wai ko zaiga abunda take gani,


Ganin bata da niyar daina kallon ceilling ɗin yasa shi dakatar da ita ta hanyar yi mata magana"Pls explain to me kin ji babyna"


Mayar da idanuwanta kan shi ta yi taɗan turo baki irin na shagwa6a66u,


"Nidai bansani ba, Amma bani nake yi ba, kamar ana ce mun inyi kaza ni kuma sai inyi" takai ƙarshen maganar tana ƙyafƙyafta mashi ido,


"Magana a ke yi maki acikin kan ki ko kuwa"? ya kuma tambayarta,

"Daddy nifa bana ganewa"

"Angel kina mafarki"? ya kuma tambayarta, bubbuga hannuwanta ta yi saman Mattress ɗin"Wlh daddy ni ka yi disturbing ɗina, kana rikita ni"

Lallashinta ya shiga yi"Am sorry, wannan ce tambaya ta karshe, idan ki ka bani amsa, Zan ba ki wayata, kiyi game," yasanta mayyar wayace, aikuwa da sauri ta soma kora ma shi jawabi

  "Daddy, ko yanzu dana kwanta,na yi mafarki kuma kullum ina yin mafarki,"

  "Faɗamun meke faruwa acikin mafarkin"?a ƙagare ya yi maganar,

Angel tace"Ina ganina a cikin wani ƙurmin daji mai duhun gaske mai ban tsoro, kuma idan nayi mafarkin ina ganina Acikin wasu mutane masu sanye da baƙaken kaya, Bana iya ganin fuskar su, hannunsu zako zako da akaifa, Ni kuma Ina sanye Cikin jajayen kaya, riga da wando,kuma bani kadai bace hada wasu ƴan yara, Kuma suma red uniform ne a jikinsu,Daddy akwai tsorofa mafarkin Kuma babu alkairi a cikinsa"

Tunda ta soma magana zuciyar taj tashiga harbawa da ƙarfi da karfi, tamkar zata faso daga kirjinshi,

Mu haɗu a next page, masu neman ƙarin bayani 08103884440 whatsapp only,

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post