Nihaad page 80 Last Page

Nihaad page 80 Last Page

Nihaad page 80 Last Page

💖💖 NIHAAD 💖💖


80


LAST PAGE


4 months later


Nihad ta fito bandaki Aunty Maryam na biye da ita a baya, Aunty Jamila ce tsaye jikin press din kayanta tana duba mata kayan da zata sa, Aunty Maryam ta fita daga dakin don dauko abu ta dawo, Aunty Jamila na juyawa taga Nihad durkushe gaban Babynta dake kwance cikin cot dinsa sai kallonsa take babu ko kiftawa, Aunty Jamila ta rike haɓa don bata da aiki sai kallon jaririn ko a gaban waye kuma, in ko bata gansa ba irin anje masa wanka to sai ta bi sa, Aunty Jamila tace "Toh wai ko mayar da yaron nan ciki za kiyi ne?" Da sauri Nihad ta bar wajen tana murmushi, Aunty Jamila tace "Ikon Allah, Ke ko kunyar surkanki da sababbin ido bakya yi, toh kar in sake ganin kina makale masa kina masa wannan kallon kamar zaki cinyesa, idan duk aka watse daga yau zuwa gobe sai ki zauna daga safe har dare kina kallonsa babu me hanaki, amma yanzu ki rufa mana asiri don Allah" Ita dai Nihad bata ce komai ba ta sunkuyar da kanta, Aunty Jamila ta ajiye mata kayanta tace "Ta shi ki shirya, ina Aunty Maryam take ajiye maki socks din naki?" Nihad ta nuna mata sannan ta mike ta shirya cikin kayan da Aunty Jamila ta dauko mata, Aunty Maryam ta dawo dakin rike da glass din ruwa da drugs dinta, tana bata ta sha ta fita da glass din, Yau kwana sha biyar da haihuwan Nihad, a jiya kuma aka yi suna wanda za a iya cewa bikin da ba ayi a baya bane aka samu privilege din yi yanxu, don kuwa sunan nan ya samu halartar manya manyan kasar daga garurruka daban daban kai kace biki kawai ake, yan yemen ma duk sun zo kwansu da kwarkwatansu don taya Mami murnan samun first grandchild, Hajiya Safeenah dai abu nasu maganin a kwabesu, tayi kokari tayi bajinta sosai don kaya na gani na fada ta hada ma jaririn bayan sun dawo US, Janar ya kashe kudi me sunan kudi a sunan nan don a gidansa aka yi sunan, Nihad kuma ta samu kudi iya kudi don kamar ba a son kudin aka dinga bata, kawayen Mami ne, Abokan Janar, yan uwa da abokan arziki, kudi dai kam ta samu, shagali sosai aka yi a sunan nan abinci iri iri da nama kuwa ba a cewa komai sai wanda ya gani, komai irin na yan gayu aka yi a sunan, har Umma sai da ta zo sunan da autarta Amina ta kuma ga abinda bata taɓa zato ba don ma dai Aunty Jamila na ta jan ta jiki duk don ta sake ayi komai da ita kamar yanda dai matan Alhaji Abubakar suka saki jiki ana ta hidima da su, Nihal tayi aurenta da Ayman wata daya da sati daya da suka wuce baya, wanda Mumy na daga cikin wa enda suka kai ta har UK where Ayman is based, family dinsa dake Uk din suka amshi Nihal hannu bibbiyu don duk abinda ɗan uwansu ke so su ma suna so, Nihad taji takaicin rashin zuwanta bikin er uwartata saboda nauyin da tayi a lokacin amma Su Mami da Noor da Khalil har Hajiya Safeenah da Nadeeyah duk sun tafi, gashi har Nihal ta tafi bata san gidan Nihad na Abuja ba, don kwantar mata da hankali Khalil yace idan ta haihu da wata uku zai kai ta har Uk din gun Nihal. Kamila ma dai ba a bar ta a baya ba wajen zuwa suna duk da ita ma dai tana ta shirye shiryen komawa gidan tsohon mijinta zai mayar da ita, Farooq zuwansa hudu gidan Janar tun da Nihad ta haihu don ya dawo Abuja da aiki, Usman kuma sai ranan sunan ya zo daga kaduna yaga Baby, ko wannensu was so happy for their lil sis, dubu dari Usman ya bata ta siya duk abinda take so, Farooq kuma ya siya mata tsadaddun atamfa har biyar da kayan baby iri iri, duk wanda ya ga Inna ranan sunan nan kuwa sai yayi tunanin ita ta haifi Janar din gaba daya, Babu kayan fitan sunan da Khalil yayi ma Nihad don Janar yayi mata yayi kala talatin a gidan kuma duk kayan da ta saka babu na banza a ciki kaya ne masu sunan kaya, Mami ta siya mata jaka da takalmi dai dai da kayan fitan sunanta, Aunty Maryam kuma ta siya mata jewelries masu shegen kyau da tsada, Jaririn ma daga waje aka yi masa order din duk kayayyakinsa banda wanda Khalil ya siya masa tun ba a haifesa ba, hakan yasa Khalil ya siya ma Nihad dankareren dankunnen zinari da sarkansa don tana da zobuna da Mami ke bata sun yi biyar ynxu, yaro ya ci sunan Abban Nihad za kuma a kirasa da Aaryan, Inna kuka ta dinga yi wiwi jin sunan da aka sa ma yaron.. Tun kafin EDD din Nihad ya cika dama suka fita US da Mami don sun bi duk process a can suke son ta haihu, daga baya kuma Khalil ya bi su don kawai azarbabin Mami ya sa ta tafi da ita kafin lokacin haihuwan, sai da ya dai dai ci saura few days EDD dinta sannan ya dau leave a wajen aiki ya bi su, sun kusa kwana goma a US kafin Nihad ta haifo santalelen ɗan nata, after 3 days bayan ta huta kuma suka juyo suka dawo Nigeria. Duk da 2 days ago aka yi suna amma har yanzu da sauran baƙi a gidan da suka zo daga nesa. Nihad na ganin Aunty Jamila ta fita, ta mike da sauri ta koma gun Babynta tana kallonsa, yaron kamar ubansa yayi kaki, komai na Khalil ya dauko har hancin da bakin, the baby is so cute and fair, with pink lips, ta durkusa kusa da shi tana kallonsa with smile all over her face wani farin ciki na musamman take ji idan tana kallon yaron nata, murya can kasa tace "Abbana" Yaron ya bude ido a hankali yana kallonta kamar ya ji abinda tace, wani dadi taji har ranta har da kyalkyalewa da dariya, ta lumshe ido ta manna masa kiss a soft cheeks dinsa tace "I love you so much" dai dai shigowar Aunty Jamila, tsaye tayi bakin kofa tana kallonta baki bude, Nihad ta mike ta bar wajen da sauri tana kame kame tace "Aunty na ji yana kuka ne shine na dubasa" Aunty Jamila dai bata ce mata komai ba ta karasa cikin dakin, Nihad ta zaro ido ganin warce ke bayan Aunty Jamila, da sauri ta tafi ta rungumeta cike da farin cikin ganinta, Mami dake tsaye gefen Mumy tayi murmushi tana kallonsu, Mumy tace "Menene haka Nihad? Ke baxa kiyi hankali ba har yanzu" Nihad was more than happy seeing her mother don har ta cire ran zuwanta da ta ga har an yi suna bata zo ba, Mumy ta dau jaririn bayan ta zauna tayi masa addu'a ta saka masa albarka sannan ta maida shi cikin cot dinsa, Nihad dake ta kallonta tace "Wallahi nayi missing dinki Mumy" Ita dai Mumy murmushi kawai tayi bata ce mata komai ba, Mumy bata wani dade a gidan ba ta bi Hajiya Safeenah zuwa gidanta wai can zata kwana zuwa gobe kuma ta koma kano, babu yanda Mami bata yi da ita a kan ta zauna gidan ba amma taki, kana ganin reaction din Mumy kasan eh lallai jinin fulani ce... Daren ranan Mami na guess room tare da Aunty Jamila da Aunty Maryam wanda ita ta kirasu zuwa dakin saboda baƙin dake bangarenta kuma tana son masu magana ne, Mami tace "Jamila kin tuna lokacin rasuwan mahaifin Nihad Janar yaje tare da wani amininsa a lokacin? Duk da dai abokan nasa da suka je suna da yawa amma wannan idan dai ba mantawa kika yi ba suna tare always..." Aunty Jamila tayi shiru sai kuma tace "Kamar na so in ganesa, he is a bit fair nd tall ko?" Mami tace "Yauwa kin ganesa kuwa, to tun dai sanda Hajiya Maryam ta fita takaba ya nuna interest dinsa na aurenta, shi ma dai matarsa ta rasu yau shekara bakwai kenan, yaransa uku a duniya biyu maza sai mace daya, Babban ɗan sa is 30 yanzu, me bi masa kuma is 28, kuma duk basa kasar yanzu haka a waje suke aikinsu dukkansu, autarsa ce dai me suna Maryam she is just 17 years now kuma tana wajen matar kanin baban nata, to tun dai da ya nuna interest dinsa bayan fitar ta takaba Janar ya sa na kira Hajiya Maryam a lokacin nayi mata magana amma sai ta nuna ita kam ba wani auren zata yi ba tana son ta kula da yaranta maza biyu babu aure a gabanta, sannan step children dinta ma duk a gabanta suke ita ke rike da su, This man is also a Lieutenant General sunansa Ahmad, kuma na tabbatar da yana da wani flaws that can't be tolerated Janar will neva take him serious balle har ya sa nayi ma Maryam magana, to ban san ko ta maki maganar ba this happened almost 3 months ago, kuma har yau Janar Ahmad bai hakura ba, ni kuma gaskiya naki basa numberta don idan na basa ban san yanda zata dau hakan ba, to zuwan da tayi gaida janar dazu ai suna tare da Janar Ahmad din a parlonsa, shine Janar ya kirani ya sa in sake mata magana, na kuma yi mata kafin ta tafi gidan Safeenah, but still abinda ta gaya min a baya shi ta sake maimaita min yanxu ma, sai ban ji dadi ba da naga tana hawaye, i know it's not easy but dole life have to go on, she have to move on, balle ma naga ita er uwar Nihad din ma ai tayi aure bata ma kasar yanzu, ina ce ita kadai ce step daughter dinta da take rike da" Aunty Jamila ta sauke ajiyar zuciya tace "In sha Allahu zan mata magana Aunty, ina ga can gidan Hajiya Safeenar ma zan je in kwana duk za mu hadu mu yi mata magana" Mami tace "Toh don Allah kiyi iya kokarinki, Janar Ahmad zai rike mata yaranta maza, he said this tun farkon maganarsa da Janar, kuma kin ga shi ma a nan Abuja yake" Aunty Jamila tace "In sha Allahu we will talk to her Aunty" Kamar yanda Aunty Jamila tace gidan Hajiya Safeenah ta tafi ta kwana don yi ma yayar tata magana don tasan idan Hajiya Safeenah ma tasa baki kilan su rinjaye ra'ayinta. Har kusan karfe biyun dare Hajiya Safeenah bata hakura ba sai da ta cusa ma Mumy ra'ayinsu na son ta amince da auren Janar Ahmad. Washegari duk aka gama watsewa a gidan Janar kowa ya koma various destination dinsa, Duk yanda Mumy ta so tafiya ranan Hajiya Safeenah bata barta ta tafi ba har sai da Janar Ahmad ya zo ya sameta a gidan. Rayuwa kenan, babu yanda Mumy ta iya haka ta hakura da auren bayan shi kansa Janar Jikamshi ya zaunar da ita yayi mata magana ta nutsuwa da fahimta, Inna ma ta saka baki, babu yanda Mumy ta iya haka tayi accepting auren, a cikin sati biyu kacal aka daura mata aure da Janar Ahmad, amma bata yarda ta tare ba sai da ta ga Kamila ta koma gidan mijinta, Alhaji Abubakar duk shi yayi mata wasu sabbin kayan dakin don daga ita har Umma suka siyar da tsofaffin kayanta, bayan kwana biyar da komawar Kamila gidan mijinta, Mumy ta hada komai nata a kano ta bayar don Janar Ahmad yace mata babu abinda babu a gidansa, a Private jet aka tafi da su Abuja ta tare da yaranta maza biyu a Mansion din Janar Ahmad, daughter dinsa Maryam me sunan Mumy ta dawo wajen Mumyn da zama, dalilin rufe gidan Abba kenan aka sallami su Aminu, Isiya, Saminu da dreba, duk aka rabu ana kuka, Aminu had nothing to loose don da taimakon Khalil ya gina dankareren gidansa a kauyensu ke kya ce ba me gadi bane don gidan duk ya fi na yan kauyen, sannan Khalil ya basa jarin miliyan daya ya fara kasuwancinsa a cikin garin kano. During period din nan kuma aka sa ma Noor rana da babban ɗan Janar Ahmad dake Turkey don dama shi ne saurayinta, as at that time Nadeeyah dake masters dinta tana tare da wani Young Brigadier general wanda sun fi shekara biyu da sanin juna but bata basa lokacinta ba sai yanzu and he and his family are fully prepared su je gaida dangin Mahaifinta a Yemen, idan ba message din Khalil ta gani a WhatsApp ba ita har mancewa take da shi a Abuja, gashi dai zumunci suke yi sosai da Nihad don a lokacin da ta haihu kullum sai taje gidan har aka yi suna amma Khalil kam mantawa take da shi wllh.... Sai da Nihad tayi 50 days a gidan Mami, bayan Mami ta tabbatar tayi mata duk gyaran da ya kamata tayi mata Hajiya Safeenah da frnd din Mami suka maida ta dakinta tare da Mimi that will be of help to her zuwa wani ɗan lokaci saboda jego, da yammacin ranan suka bar gidan, Mimi made sure ta gyara ko ina na gidan ta sa turaren wuta. Karfe biyar da rabi Khalil ya dawo aiki, he was so happy to see his wife and son don bai san ranan za su dawo ba, Mami dai ta amshi spare key din gidan nasa kusan kwana shidda da suka wuce a baya, kullum sai ya dawo aiki yake zuwa can gidansu ganin family din nasa, kuma sai kusan karfe goma yake komawa gidansa yau kam yana dawowa ya gansu a gidan and he was very happy, sai dai kuma Farooq da ya gani a gidan nasa made him believe what he was thinking before, kusan duk dare idan yaje can gidansu sai ya ga Farooq a gidan sai yanzu ya sake tabbatar da cewa wajen Mimi yake zuwa ba Nihad ba amma sai ya fake da kamar gun er uwarsa yake zuwa, ita kuwa Nihad tuni ta gano zuwan me Farooq yake kullum, sai bayan magrib Farooq ya bar gidan, Mimi ta kai ma Yayan nata shayi a parlonsa kamar yanda ya bukata, da sallama ta shiga parlon, Nihad dake zaune kusa da Khalil dake rike da Aryaan ta amsa mata sallaman, bayan ta ajiye shayin Khalil na kallonta yace "Wajenki farooq ke zuwa ko?" Ta wani zaro ido ta dafe kirji tace "Ni??" Dariya kawai Nihad tayi tana kallon Mimi da ta daburce, Khalil ya jefa mata wani kallo yace "Tafi ki bani waje with ur hypocrisy" Ta sunkuyar da kai kamar munafuka ta juya tana murmushi ta nufi kofa. Daren ranan Khalil ya nuna ma Nihad yanda yayi kewanta sosai, ita ma kuma tayi kewan mijin nata, she truly missed him soo much. Washegari da ya kasance asabar Khalil baya fita aiki, wajen karfe goma na safe ya fita shopping da Nihad leaving Mimi and little Aryaan at home, Nihad ta dau duk wani abu da tasan za su bukata a gida, bayan ya biya kudi aka kai masu mota, tana kokarin shiga mota taji ana kiranta, waigawa tayi taga wata mata ta nufota da sauri fuskarta rufe da Face mask, matar na karasowa kusa da ita ta sauke Facemask din, ko kusa Nihad bata gane ta ba, Matar tace "Nihad ni ce fa" Sai a sannan Nihad ta dau muryarta ta zaro ido da mugun mamaki tace "Zully???" Shi dai khalil har ya bude driver seat ya shiga yana kallonsu, Zully ta cire face mask din gaba daya tace "Ni ce Nihad" Da mamaki Nihad tace "Me ya sameki haka? Where u sick??" Zully ta fara kikkifta ido sai kuma ta fashe da kuka a hankali tace "Ehh wallahi na kwana biyu bani da lafiya amma na fara samun sauki yanzu tunda gashi har ina fitowa" Nihad na kallonta daga sama har kasa tace "Me kike yi a nan?" Zully ta sunkuyar da kanta tayi shiru, daga sama har kasa Nihad ke ta kallonta don she look so tattered and unkept, sae bugawa ma take, ga wani ramewa da tayi ta koma bakakirin maimakon fara da Nihad ta santa a baya, dama can ita iyayenta talakawa ne sosai don uwarta ma a kauye take ubanta kuma ya rasu, Naf ce dai er masu kudi a cikin su ukun, lokaci daya jikin Nihad yayi sanyi, a hankali tace "Husnah fah?" Zully ta kara fashewa da sabon kuka tana girgiza kai tace "Ai Allah ya mata rasuwa ko sati biyu ba ayi ba, tayi fama da cancer ga kuma HIV daga karshe kuma rai yayi halinsa" Nihad ta dafe kirji tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Husnah ta rasu??" Zully ta gyada kai cikin sanyin murya tace "A gidansu ta rasu a garin kaduna don babu kudin zuwa asibiti, kafin ta rasu ta damu tana son ganinki, kuma an je har gidan ku nemanki amma aka tarar babu kowa a gidan an ma kulle da kwado" Hawaye na sauka idon Nihad tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Zully ta kara fashewa da kuka sosai tace "Don Allah ki yafe mana Nihad duk abinda ya sameki mu ne muka ja maki wallahi daga karshe kuma sai gashi ya zame maki alkhairi, wannan video din naki Husnah ce tayi sa amma ba da nufin ta yada shi a social media ba, lokacin da Aliyu zai turo iyayensa gidanku Umma ta kira Husnah duk ta zuzzugata wai haka za mu sa ido ɗan Janar guda ya zo ya aureki muna gani alhalin mu har yanzu ba mu yi aure ba duk kuma mun girme ki, sai Husnah take ce mata ai ko me za mu ce maki baza ki ji ba don son Aliyu ya rufe maki ido akansa har rashin mutunci kike mana a kansa, Umma tace to mu bi maki ta karkashin kasa mana, da so tayi ma mu bi ta zuwa gidan Malamai amma ko wacce xata kawo ɗan abinda za a ba ma malam don tace bata da kudi ita a lokacin, shine Husnah ta tuna wannan video dinki dake wayanta wanda tayi maki sanda kika koma hostel da zama, ranan mun je zaria mun sauka wani hotel za ayi Birthday din wata kawar Naf, gaba dayanmu sai muka sa maki kwaya a drink dinki kin fita kiyi waya da Abbanki, mu ma duk mun saka a namu tunda mun saba sha, wllh wllh ba don video dinki ya tafi viral aka yi ba Nihad, mun yi sa kawai saboda nishadi, we did it da wayar Husnah just for fun saboda yanda kika dinga reacting very drunk after taking the juice, Da Umma ta kawo mana batun zaki yi aure ki bar mu and we are doing nothing about it kuma ta nemi mu kawo kudi ta kai mu gidan malami sai Husnah ta tuno da video din da tayi maki, wallahi Umma ce cause din sakin wannan video din a social media, da mun bi ta Naf ma baza a saki Video din ba don she was against that amma saboda son zuciya ni da Husnah sai da muka bi bloggers muka tura masu video din duk don Aliyu yace ya fasa aurenki, don girman Allah ki yafe min Nihad, ita dai Husnah ta rasu, ni ma dai kinga ga yanda rayuwa ta mayar da ni a yau, bani da sauran gata a duniya mahaifiyata ma cewa tayi in koma inda na fito kar in kashe mata aure da naje wajenta a kauyen da take, duk samarin sun gama amfani da mu sun gujemu ga cuta mun kwaso ma kan mu, duk inda muka yi gudunmu ake yanzu, karatun ma Naf kadai ce ta gama a cikin mu ita din ma dai da pass, tana gamawa kuma babanta ya aura ma abokinsa me mata biyu ita..." Kuka Zully take sosai kamar ranta zai fita kana ganinta kasan tayi nadama ainun, Khalil ya dinga kallonta fuskarsa daure yana jin zuciyarsa na tafarfasa, Nihad ta kasa cewa komai banda hawaye babu abinda ke sauka idonta abubuwa masu yawa na dawo mata, no wonder ta kasa gane inda aka yi video din don in da a hotel dake garin kano ne dole zata sani, har kasa Zully ta durkusa tace "Kiyi ma girman Allah ki yafe min Nihad, ya kai ya kawo sai ina bin eatry da manyan malls ina baran abinda zan kai baki, duniya ta juya min baya ga ciwo ina fama da shi kuma bazan boye maki ba wallahi nima HIV din gareni Nihad, yanzu haka karfin hali kawai nake, da kinga inda nake kwana ma zaki san ta kare min a rayuwa Nihad" Khalil ya kalli Nihad yace "Shigo mu tafi Baby" ta kallesa hawaye na sauka idonta tace "Pls let help...." Wani tsawa ya daka mata wanda bai taɓa mata irinsa ba, ba shiri tayi shiru, ya wani hade rai yace "Shigo mota nace" Zagawa tayi ta bude motar a hankali ta shiga, Zully ta biyota da gudu tana kuka tace "Don Allah ki ɗan taimaka min ko da kudin magani ne Nihad...." Khalil ya kulle motar ya sauke glass yana kallonta da kyau yace "This should serve as a lesson to people with the kind of ur heart" Yana fadin haka ya ja motarsa ya bar wajen Zully na kuka sosai tana bin motar da kallo, Nihad dai sai share hawayen da yaki tsaya mata take, bayan sun isa gida Nihad ta shiga dakinta duk jikinta a sanyaye maganganun Zully na dawo mata, dama su suka yi mata video din nan har suka ba Bloggers suka baza shi a duniya they cause all her pain in life, tunanin hakan yasa ta fashe da kuka sosai, a haka Khalil ya shigo dakin ya sameta, ya rungume hannunsa yana kallonta a hankali yace "Duk abinda ya faru ya faru ne in ur favor Nihad, and kin yarda cewa every disappointment is a blessing in disguise?? Ur disappoinment was nothing but a blessing to you Baby, da basu maki hakan ba u will end up marrying Aliyu, who is a bloody liar and a gangster, his wicked mum will become ur mother inlaw, abinda baki sani ba Aliyu ko 5 daily sallah baya yi, ba shi da aiki sai shaye shaye da neman mata daga wannan kasar zuwa wancan kasar duk da kudin Abbana, we grew up together na fi kowa sanin waye shi nasan mugayen halayyansa, babu kalan giyar da baya sha, ya saukar maki da kai ne saboda ya gama cin duniyarsa yana neman mace warce yasan ba a lalata ba ya aura yayi settle down, da ace kin auri Aliyu sai kin fi regretting akan abun da ya sameki a baya, mahaifiyarsa bata san Allah ba, bata kuma kadaita Allah ba, she is a devil in human form, amma kin ga da yake zuciyar Mum dinki is clean and pure shi yasa Allah ya sauya maki jarabawan auren Aliyu zuwa wani daban...." Nihad na goge hawayen da suka ki tsaya mata tace "Haka ne" Ya karaso ya zauna kusa da ita ya jawota jikinsa, murya can kasa yace "Da duk abinda suka faru basu faru ba, da ba mu yi aure har mun samu Aaryaan ba" Ta lumshe ido tana shaƙar daddadan kamshin jikinsa cikin sanyin murya tace "Ina alfahari da kasancewar ka mijina, Allah Ubangiji ya bani ikon yi maka biyayya in bi ka sau da kafa har karshen rayuwata, Allah ya tsare min kai da tsarewarsa ya kara maka arzikin da zae amfani al'umma mijina...." Ya rungumeta sosai yace "Ameen my wife, Allah ya sa ki haifo min yan biyu sau biyu" Ta lumshe ido tana murmushi a hankali tace "Ameen my world" ya dago kanta yace "Aryaan na cika 3 months zaki yi resuming school, and in sha Allah har masters sae kinyi Baby...." Nihad ta kasa ce masa komai tana jin sabon sonsa na shigarta, cikin sanyin murya tace "Promise me duk sanda mu ka kara ganin Zully zaka taimaka mata da duk abinda Allah ya hore maka kaga tace magani zata siya" Yayi shiru sai kuma yace "I promise u my love" Tayi kissing dinsa tace "Thank you Abuu Aryaan" kissing her also yace "U are welcome Ummu Aryaan, some other time xan baki labarin encounter dina da Husnah when she came to spend the night at our place back in kano" Daga kai tayi ta kallesa da sauri, taga yana murmushi.... lumshe ido yayi ya fara kissing dinta passionately.


Mumy ta samu kwanciyar hankali fiye da yanda tayi zato a gidan Janar Ahmad, so na hakikanin gaskiya bawan Allahn ke mata, taga yana da wasu dabi'u in common da marigayi Abba, he is such a caring husband, and bai rageta da su Fadil da komai ba a gidan, Ga er sa Maryam warce hankali har yayi mata yawa, Mumy ta dauketa kamar ita ta durkusa ta haifeta, Mumy bata yanke alaqarta da Umma ba don suna yawan gaisawa ta waya duk bayan wani lokaci, har ma Amina kan zo gun Mumy ta mata kwana biyu a Abuja sannan ta koma, ba a cikakken sati biyu sai Nihad ta je gidan mahaifiyarta, don wannan satin in taje gun Mami, to wani satin gun Mumy zata je, lokaci lokaci kuma tana zuwa gidan Hajiya Safeenah, at times kuma saboda Nadeeyah take zuwa gidan wanda suka zama very best of frnds yanzu.....


And every one of them lived happily ever after!!!😊


*Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! a nan na sauke littafina me suna NIHAAD* darussukan dake ciki Allah ya sa mu amfana da su, kurakuren dake ciki kuma Allah Ubangiji nake rokon ya yafe min.... *Na kuma sadaukar da littafin nan zuwa ga Mijina Barrister Ibrahim Khalil, ina alfahari da kai ina kuma godiya da ara min some of ur time to do what makes me happy... Allah ya saka maka da gidan Aljanna ya daura ka kan makiyanka, Allah ya kara maka arziki da zai amfani al'umma, thanks for the encouragement and support from the beginning of the book Nihad till the end, u were always by my side all through the long journey, i appreciate you so much dear, Allah ya kara mana zaman lafiya da kwanciyar hankali.....*

 My *Mother* Hajiya Hajarah and my sweet *Dad* Alhaji Bello Ahmad.. Allah ya kara maku lafiya da kwanciyar hankali, Allah ya saka maku da gidan aljanna, Allah ya kara maku arziki da wadata ta inda baku zato, ina alfahari da kasantuwarku iyayena. My siblings Allah ya raya min ku gaba daya, Maryam Bello ga gaisuwarki a kyauta!!! My cousins ina kewanku gaba daya, Allah ya raya min ku....


.


07087865788


Taku har ko da yaushe Hauwa Bello Jiddah AKA _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post