JANHANKALI: A KULA SOSAI DA MATAKAN DA NA LISSAFA DON YIN NOMA MAI RIBA. A GUJI ZUBA MANYA KUDADE KAFIN A KWARE WAJEN IYA NOMAN. KA FARA KWAREWA KAFIN KA SHIGA DA DUKIYARKA.
Noman doya a buhu Abu ne wanda zai yiwu, wanda kuma baya bukatar waje mai yawa. Ga kuma matakan da ya kamata kabi Don ka koya kuma ka kware akai. Don yin noman doya cikin sauki da kuma samun riba mai tarin yawa.
1-matakin farko( ka zabi iri maikyau wanda ake noman lambu dashi ). Ka tatbata ka zabi irin doya mai kyau wanda kasan yana fitowa a buhu ko kuma a bokiti. Ko kuma wanda ake noman lambu dashi. Ka zabi doyar da take da zare ajinta Don zatafi bayar da abinda ake so.
2- mataki na biyu
Ka tatbata irin da ka samu yanada kyau baya dauke da wata cuta wadda ka iya hanashi fitowa ko kuma girma kamar yadda ya dace. Sannan kuma ka nemi iri mai kyau wanda zai iya jure addabar kwari wato (pest resistance. Ka nemi wajen da yake an sansu da samar da irin doya mai kyau Don siyan irin doyar da zaka shuka.
3-Mataki na uku
Ka shirya buhun ka ko kuma container da zakayi shukar dashi. Ka kuma tattbata zai iya daukar ruwa daga lita ashirin da biyar zuwa talati (25 to 30). Don jijiyoyi doyar su samu damar girma yadda ya kamata. Sannan kuma ka samar da hanyoyin da ruwa zai iya bi daga kasa wato abinda a turance ake cewa( water drainage).
4-mataki na hudu
Ka samar da kasa mai kyau tare da sinadaren da doyar ke bukata . Samun irin wannan kasar abu ne mai yi wuwa domin da zarar ka samu takin gida kuma a cakudasa da kasar shuka. Irin wannan kasar ce zaka iya yin shukar da ita.
5- kayayyaka doyar sannan kuma ka hadata da cement ko kuma toka Don gudun rube wa bayan ka shuka. Ko kuma idan bazaka hadata da cement ba to ka tattabata ka bar ta ta bushe tsawon wadansu kwanaki kamar biyu haka.
6- shuka doyar da ka yanka
Kayayyaka doyar ta zama kanana . Amman a ringa barin bawonta ajikinta yadda yin hakan zai bata damar fitowa. Irin yanka taswirar pyramid zai taimaka sosai.Bayan ka yanka ta sanna kuma ka samar da kasar noman ka mai hade da takin gida wato abinda a turance ake cewa organic fertiliser sai ka sanya doyar aciki. Wato tsininta yana kallon sama. Aduk cikin buhu ko kuma bokita daya za ka iya saka doya daya, biyu ko kuma uku.
7 bayar da ruwa da kuma kulawa da ita
Katatbata ka zuba ruwa bayan ka shuka. Yadda kasar zata jiku kuma ta kama doyar. Ka lura da ruwan da kake bata har zuwa lokaci da zata girma.
8-kasa ka Ice koda kuwa karami ne da zarar ta fara girma domin bata support din da ya dace domin jijiyoyinta su samu damar girma yadda yakamata. Kuma ta tsaya a tsaye yadda ya kamata.
9- hasken rana da kuma yanayi
Tabbas doya tana bukatar hasken ranar da a kullum zai kai tsawon awa shida zuwa takwas (6 to 8 hours). Sannan kuma tana bukatar yanayi da bai huce degree 24 to 29 har zuwa lokacin da doyar ka zata gama girma.
10-mataki na goma
Bayar da taki da kuma kula da cututtuka da ka iya da mun doyar
Yanada kyau ka ringa bayar da incorporate fertiliser a duk bayan sati hudu zuwa shida Don samar mata da sinadarai masu kyau. Yana kuma da kyau ka kula da irin cutar da ka iya damun doyar ko kuma kwari da ka iya adabbar ta. Wanda galibun su nematode da aphids ne.
11-Girbi ko kuma harvesting bayan ta girma. Domin a duk lokacin da takai wata shida zuwa takwas za,a iya fara harvesting dinta. Ko kuma da zarar ganyenta ya fara zama yellow bayan ta kwashe wata shida zaka iya fara cirota daga cikin buhunta ko kuma bokiti ko dai abunda da kayi shukar aciki. Sai kabar kanannan doyoyin Don yin shuka ta taba. Kayi amfani da manyan.
Allah yasa mudace
Positive minds