Zain Abeed page 1

Zain Abeed page 1

 

Zain Abeed page 1

ZAIN ABEED 


_By Nimcyluv Sarauta_


 page 1


Hazon da ake yi, a 茩asar Moscow bai hana jirgin Aeroflot-Plus sauka a Sheremetyevo Airport dake nan 茩asar Moscow ba. The weather is too high pilot 蓷in da 茩yar yake  iya ganin, mai  bashi direction 蓷in sauka 茩asa. Banda Snow babu abinda yake zuba. Mai asthma kam sanyin babbar illa zai iya yi masa, zai iya sashi cikin critical condition. A hankali jirgin keyin parking har ya samu wajan tsayawa. Daga can cikin jirgin kowa passengers ne suke 茩o茩arin zame belet 蓷in jikinsu domin sauka daga ciki. A hankali yaja numfashi mai 蓷an 茩arfi yana matse hannayensa suna bada wani, sauti na gajiya. Wrist 蓷in hannunsa ya duba yaga 1:15Am na dare. Gently ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa cikin aljihun suit 蓷insa, walking slowly  ya 茩arasa Vip side. He's just thinking why har yanzu biyuninsa bai fito ba? Is he alright or what? If sanyin nan ya yi effecting health nasa? A fili yace "Ya rabb, ga bawanka" bu蓷e 茩ofar vip 蓷in yay a hankali yana mai tura kansa ciki. Cak ya tsaya saboda ganinsa da yay a kwance saman duguwar kujera. Infact bai da alamar tashi, saboda ya lumshe idanunsa tare da har蓷e hannayensa a 茩irji Numfashinsa na sauka a hankali. He's sleeping peacefully yay kyau sosai a baccin, domin gaba 蓷aya sumar dake goshinsa ya 蓷an zuba fuskarsa kamar wata mace. 茦uri ZAIN yaywa ABEED da idanunsa wanda suke cike da Zallar so da 茩aunar abokin haihuwar tasa (Twins).  茦arasa shiga yayi har zuwa inda Abeed ke kwance, yana zuwa ya saka hannunsa ya ware masa hannayensa da suke 茩irji. Shiru Zain yay ganin 茩irjin Abeed na 蓷agawa, kafin a hankali ya 蓷ura kansa a 茩irjin na Abeed domin gano what wrong with him yake jan numfashi haka? Something is fishy Abeed baya bacci cikin airplane.  Kansa ya janye kafin a hankali yace "I don't know what wrong with my Biyuni, bai san me yake 蓳oyewa ba,is he hiding something for me? No! Abeed bai zai 蓳oyan komai ba, shine rayuwata nine rayuwarsa, he can't do that.... seriously" ya fa蓷a yana 蓷aukan iphone 蓷in Abeed, sosai Zain yay mmkin ganin 20miss call na RIYA tun suna 9ja take kira Abeed, ba kira 蓷ayan da ya yi, respond. Cike da damuwa Zain yace "sorry Riya, In sha Allah zan shige maki gaba" wayar Abeed 蓷in ya saka cikin Aljihu, yana fa蓷in "I love You Biyunina" motsi Zain ya ji, ya juya da sauri ha蓷a ido sukai da Abeed, yaga duk yadda 茩wayar idanunsa take blue amma yanzu tayi wani mugun jaa. Shiru yay yana noticing 蓷in sa, amma bai gane komai ba. Cikin sakin fuska yace "Yaushe ka tashi?" Kamar Abeed ba zai magana ba sai kuma ya 蓷an bu蓷e baki da 茩yar yana yatsuna fuska, cikin slow voice yace "from i love You Said" ya fa蓷i hakan yana mi茩ewa tsaye, tare da unlock na suit nasa. Murmushi kawai Zain yay yana girmama, nauyin bakin Abeed hatta shi da aka haifesu rana 蓷aya, lokaci guda,wata guda, shekara guda wani time 蓷in banza yake masa. Da mutum uku Abeed yake rayuwa yaji da蓷i na farko, abokin haihuwar sa Zain, na biyu Mai martaba sai kuma Naila. Zain nada tsayi, fari ne shi idanunsa ma fara re ne, fuskarsa a sake bashi da wata damuwa, damuwarsa 蓷aya akan Biyuninsa. Baya 蓳oye komai yana da sau茩in kai. Abeed kuma yana da zuciya baya 茩aunar kallo ko ka蓷an idan ba wajan show yaje yana gabatar da wa茩arsa ba, baya 茩arya sam bai san yadda ake ba, Idan yace Yes of course yana nufin Yes 蓷in. Ko waye kai baka isa yay maka 茩arya ba, fari ne tass, yana da manyan idanu wanda 茩wayar idanun ta kasance blue, ga suma mai kyau har gaban goshi take sakkowa, sumar goshin kuma ita ta banbanta tsakaninsa da Zain, da ita ake iya gane waye Abeed waye Zain. Amma har gobe akwai abinda Abeed yake 蓳oyewa Zain, Meye shi?. Toilet 蓷in dake cikin jirgin Abeed ya shiga yana tafiya a hankali hannunsa zube cikin Aljihu, yana shiga cikin toilet 蓷in ya maida 茩ofar ya rufe, kana ya jingina da jikin 茩ofar yana jan numfashi da 茩yar, bai damu dan ya rasa ransa ba, amma idan ya rasa ransa wanne hali Zain zai shiga? Wannan tunanin shine yake 茩ara damun Abeed yake ya hanashi barci, domin abincike ya nuna cewa saura wata biyar ciff wa'adin rayuwarsa a duniya zai 茩are. Zain jin Abeed shiru ya sanya  蓷an yi knocking 茩ofar, tare da fa蓷in "Hey my frnd is everything okay?" Shiru Abeed yay saboda Aman da yazo masa, cikin sauri ya 茩arasa wajan sink ya fara amai wanda rabin aman duk jini ne..... Bakinsa ya wanke tas tare da wanke fuskarsa kana ya bu蓷e 茩ofa ya fito, yana fitowa cikin sauri yay gaba abinsa ba tare daya tsaya Zain ba, yay hakan ne kuma saboda baya son ya fahimci wani abu. Da idanu kawai Zain yabi Abeed dashi. Har zai fita sai yaga inhaler 蓷in Abeed girgiza kai kawai yay tare da 蓷auka yabi bayansa. A strains 蓷in jirgi yaga Abeed  tsaye kansa a sunkuye fuskar nan a ha蓷e tayi jajir, juyawa yawa yay nesa dashi yaga ashe wata baturiya ce ta kafe Abeed 蓷in da kallo, murmushi yay yace "Can i call her?" Still Abeed shiru yay, Zain yace "shall we..?" Sai a lokacin Abeed ya 蓷aga fararen idanunsa da suka fara dawo wa daidai, ya tsorawa Zain idanu, alamar akwai Abinda yake bu茩ata wajansa. Dafe kai Zain yay yana fa蓷in "Ya rabb, i almost frgt wlh" hannu ya sanya a cikin Aljihu ya 蓷auko wani mars mai kyau, kana ya matsa kusa dashi suna farcing juna yana sanya ma Abeed mars 蓷in tare da fa蓷in. "How was your body? Sanyin bai dame ka ba ko?" Abeed idanunsa ya lumshe, kana ya bu蓷e har ya bu蓷e baki zai Mgna, yaga Wannan baturiyar tana 茩ara kallonsa. Hannuna ya 蓷ura a shoulder 蓷in Zain kana ya juyo dashi gabansa hakan yasa ya rufe fuskarsa da jikin Biyunin nasa, fararen idanunsa ya wara kana ya ciro wani ring na Daimond a hannunsu ya kama hannun Zain ya zura masa, yana sakin wani cute smile murya can 茩asa kamar mai tsoro yace "Zakai replacing nawa" ya fa蓷a yana kama hannun Zain 蓷in zuwa wajan wata hadaddiyar mota da tayi parking gabansu, gaba 蓷aya a baya suka zauna, driver ya kwashi kayansu, shima ya shiga motar kana ya jasu suka bar airport.


About Azimut Hotel Tulskaya Moscow Motar tasu ta tsaya, Zain ne ya fara fitowa sai Abeed, har lokacin mars ne a fuskarsa, sai wani glass daya saka a idanunsa,  kasancewar zuwan sirri sukai yasa, Zain shima ya saka mars cikin nutsuwa ya kama hannun Abeed suka fara shiga cikin reception na hotel alrdy an gama musu komai, key kawai Zain ya amsar musu suka haura sama, room 120 suka tsaya, Zain ya bu蓷e musu suka shiga, Kallon Abeed Zain yay yace "So what about your show? A wanne hall ne?" Abeed yana cire rigar jikinsa yace "Ba zani ba" da mmki Zain yace "pardon?" Abeed ruwa mai sanyi ya 蓷auka tare da 蓳alle murfin gorar zai kai bakinsa,Zain yay saurin kwacewa babu alamar wasa yace "Are You at of your sense? Kalli yadda bakinka ke haya茩i saboda tsananin sanyi, shine zaka sha that stupid water?" Ka fa蓷a Abeed ya 蓷aga irin he doesn't care 蓷in nan, kana ya 茩ara 蓷aukan wani ruwan zai sha, again Zain ya 茩ara kwacewa cikin 蓳acin rai tare da 蓷aga murya yace "Wai baka tuna cewa lafiya bata isheka ba? Ka manta issues 蓷inka na Asthma?" Baya Abeed yay tare da zama kan kujera yana jan numfashi ya jima a haka kafin ya 蓷ago kansa ya kalli Biyunin nasa, gently ya mi茩e tsaye har zuwa inda Zain yake murya a sanyaye yace. "Mutuwa kake tsoro? To...." Cikin fa蓷a Zain yace "Kada ka sake yi min mgnar mutuwa a nan, kuma mutuwar ta rasa wa zata 蓷auka sai kai? Wlh duk sanda aka wayi gari babu kai Tabbas a rana nima zan rasa raina.." ta蓳e baki Abeed ya yi kawai, yana ju yawa ba tare da yace komai ba, ganin yadda jikin Abeed 蓷in ya yi sanyi ne ya sanya Zain saurin shan gabansa, Cak Abeed ya tsaya da tafiyar da yake, kafin ya 蓷aga idanunsa suka ha蓷a idanu da Zain, ganin yadda idanun Zain ya cika da 茩walla yasa Abeed 蓷an zare ido yace "what again?" Kasa mgn Zain yay sai kawai ya rungome Abeed tare da fa蓷in. "Stay with me Biyuni na, stay with me ABEDDEEN" Murmushi mai ciwo Abeed yay yasan cewa, 蓷an uwansa bai san meke damunsa ba, ciwon Asthmar da yake damunsa shi kawai ya sani, a ransa yace "Dole na tafi na barka, I think my mother is calling me" a fili kuma yace "Love u" A sanyaye shima Zain yace "To the rest of my life" da ga nan duk freshen up sukai na jikinsu. Kana suka kwanta bacci, Zain yay bacci cike da damuwa inda ya 蓷auki al'茩awarin zai samu tattauanawa Da Babban likita akan ciwon Abeed.


Alarm 蓷in dake jikin wayar Abeed shine ya fara 茩ara, wanda ya sanya Abeed 蓷in motsawa ka蓷an, slowly kuma ya shiga ware idanunsa saboda nauyin da sukai masa, sam bai yi bacci daran jiya ba, idan ya tuna mgnar Dr Siya yay masa, komai nasa tsayawa yake. He can't even think mene yake daidai, mene ba daidai ba. Juya ya yi bakinsa 蓷auke da addu'a ya 茩arasa bu蓷e idanunsa,  kafin a hankali ya janye duvet 蓷in daya rufe jikinsa dashi, mi茩ewa tsaye ya yi har zai shige toilet sai ya juya ya kalli Zain da har yanzu yake bacci, baya ya koma ya 蓷an ja yatsun 茩afar Zain kamar yadda ya saba, ganin ya yi motsi yasa Abeed shigewa toilet. Mi茩ewa Zain ya yi kai tsaye shima ya shiga wani toilet 蓷in. Kusan a tare suka shirya cikin wasu farar Arabian jallabiya mai taushi, Masjid 蓷in dake cikin  hotel 蓷in suka shiga, ana idar da sallar suka dawo gida. Zain ne ya zauna kan kujera cikin sauri yake danna keyboard 蓷in system, wani babba case ne dashi wanda zai ja ragamar shari'ar, criminal case domin zargi ne na fashi, har da kisan kai, the case was super bai ta蓳a samun case mai ha蓷arin wannan ba, Idanunsa ya 蓷aga yana kallon Abeed dake tsaye yana tsiyaya madara a glass cup yace. "Ina confused wani abu" shiru Abeed yay, haka nan yaji baya mood 蓷in na Magana, jin shirun yay yawa ya sa Zain yace "Arrogant..." Ta蓳e baki Abeed ya yi, kana a hankali ya dawo baya ya zauna kan kujera cikin nutsuwa yake shan Madarar, sai da ya shanye tass kana gently ya kalli Zain yana mai shafa gemunsa yace "Me kace?" 苼ata fuska Zain yay yace "Shafa kaji" Cije baki Abeed ya 蓷anyi yace "Sorry" Juyawa Abeed system 蓷in Zain yay yace "Look, already nayi searching all na abinda nake bu茩ata but..." Abeed yace "But wat?" Zain yace "firstly wanda nake zargi da akaita fashin, babban mutum ne, secondly yadda akai amfani da mace wajan gudanar da aikin, Lastly bayan fashin da mutumin yake akwai wani abu da yake da 拼an mata, wanda har yanzu shine abinda ban gane masa ba" ta蓳e baki Abeed ya yi yana Mi茩ewa tsaye yace "U hve to drop this criminal case 蓷in" tunda suka zo sai yanzu Abeed ya yi mgn mai 蓷an tsayi, da Mmki Zain yace "Kasan me kace?" Abeed na lumshe idanunsa yace "ka ta蓳a ji nai hauka ne?" Murmushi Zain yay yace "how can i knw, ina mgnar serious kana wani magana" shiru kawai Abeed ya yi, for some minutes kana ya mi茩e ya kalli Zain kamar zai Mgna sai kuma ya yi shiru, gane cewa akwai abinda Abeed 蓷in ke son fa蓷a yasa Zain yace "Speak up my friend, what's in ur mind?" Abeed ya bu蓷e baki murya can 茩asa yace "Zakai replacing nawa wajan show"... "Why? Bayan ka amshi ku蓷in jama'a, then ta yaya zan iya wa茩a nida ba aiki na ba?" Cewar Zain, gaba Abeed ya yi abinsa yana mai fa蓷in "Be ready, zaka je matsayin ni" yana 茩o茩arin shigewa cikin wani bedroom Zain yace "Oh! Hello idan aka gane cewa bani ne Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas ba fa?" Kai tsaye Abeed yace "No one knows" Ya fa蓷a yana shigewa bedroom 蓷in. Da yamma Zain na zaune watching TV, Abeed ya fito cikin dark blue 蓷in floral jacquard one button suit. Zain na ganinsa ya mi茩e tare da 茩arasa wajansa, hannun Abeed 蓷in ya kama ya 蓷aura masa wrist kana ya tsuguna ya sanya Leather shoe yana fa蓷in "Ina zaka?" Murya can 茩asa Abeed yace "I have a meeting" "meeting?" Zain ya fa蓷a da mmki, tare da sake fa蓷in "Yaushe ka tsara?" Shiru ya yi bai magana ba, ganin yadda ya 蓷aure fuska yasa Zain yace "it's okay, kaga weather garin is not good, so take good care of yourself ok?" Abeed na barin room 蓷in yace "I'll.."


*****

A wani yanki dake kudancin garin Katsina. Cikin Wata ha蓷a蓷蓷iyar prvt school ta maza da mata. Da sauri class teacher 蓷in Yake tafiya it's already late, amma har yanzu basu fito daga cikin class ba, bayan dukkan student na makarantar sun tafi, kowa ya watse what wrong with them su kullum basa ganewa, they didn't understand what is good and what's wrong. 鈥漧azy babies鈥? ya fa蓷a a Zuciyarsa, cikin class ya shiga shiru babu 茩arar komai, idanunsa ya shiga rarraba wa can ya hango su a zaune 蓷aya na drowning a mac nata, 蓷aya kuma ta 蓷ura kanta akan kujera, da mamaki Teacher 蓷in yace "SAIRAH" Wacce aka kira da Sairah 蓷in ta ajjiye color 蓷in hannunta tare da kallon Teacher 蓷in, farar yarinya ce 茩yakkyawa, kana kallon ta kasan bafulatana ce ko kuma wani yanki na Fulani, kai tsaye ba zaka fasallata kayanta ba, yanayinta kamar na Kajol馃槍tana da tawadar Allah a saman hancinta. 茦uri tayi masa da ido ganin hakan yasa Teacher yace "Haba twins yau kuma me akai maku?" Shiru tayi masa sai kawai yace "Ok tashi 拼ar uwar taki" juyawa tayi har lokacin kanta a 茩asa a hankali Sairah ta shiga tashin ta "SARA! SARA!SARA!!" ganin ta motsa yasa ta zame hannunta. Wacce aka kira da Sara ta bu蓷e idanunta Subuhanallahi, wallahi babu wanda ya isa ya iya bambance wace Sairah wace Sara komai nasu iri guda ne, tawadar Allah ce kawai ta banbanta ta Sairah a saman hanci ta Sara a 茩asa. Ikon Allah buwayi gagara Misali Cikamakin Annabawa da Manzanni, wanda yake halittar Mutane a mahaifa 蓷aya, hukumcin sa da buwayarsa ta sanya su zo duniya a tare wanda akewa la茩ani da TAGWAYEN ASALI. lumshe idanun Sara tayi kana ta 蓷an murgu蓷a baki, kasancewar ita bata barin ko ta kwana, sa蓳anin Sairah da take da mugun ha茩uri. Teacher yace "Twins 蓷in Dady mai akai maku ne yau?" Wata uwar harara Sara ta watsa masa cikin siririyar muryarta mai tsiwar gaske tace "Heyyy! Shut up... And leave" cikin sauri Teacher yace "Ok daman Dadynku yazo 蓷aukan ku" da wani sauri suka ha蓷a baki wajan fa蓷in "what? Daddy?" Sara ce ta fara yin gaba Sairah kuma ta 蓷aukar masu bags nasu. Yana tsaye a kusa da motarsa cikin shiga ta ilhama gaba 蓷aya ya na蓷a fuskarsa idanunsa ne kawai a waje, yana ganinsu ya saki Murmushi mai sauti tare da bu蓷e musu hannunsa, gaba 蓷aya suka shige jikinsa suna fa蓷in "We miss you alot Daddy" shiru kawai yay musu Sairah ta shiga gaban mota, Sara a baya kana ya jasu suka bar sclh 蓷in. Bayan sunyi nisa sosai ya 蓷auke hanyar zuwa gida ya nufi wata hanyar, Sara da bakinta baya shiru tace "Daddy ina zamu?" A ta茩aice yace "Unguwa" tun suna Shira sukai shiru bacci ya 蓷auke su har suka sake farkawa, wani baccin ya 茩ara 蓷aukan su.. cikin wani jeji ya shiga mai tsananin duhu da ban tsoro, kana ya kashe motar ya fito, da 蓷an sauri ya shiga tashin su "Sara, Sairah" kusan a tare suka farka da mmki suka ce "Daddy area nan is not good, mu koma gida" shiru yayi kawai sai ya jasu jikinsa ya rungume, sun jima a haka kafin yace "Waye ni a wajan ku?" Sara dake tafi surutu tace "Kai ka haife mu Daddy,kai ne babban mu farin cikin mu" da sauri yace "I'm not your father, ban ta蓳a haihuwa ba, bare na samu albarkar tagwaye kamar ku, Sara ki kula da 拼ar uwarki twins 蓷inki, Biyuninki, ki kula da ita a nan zan barku" da 茩arfi Sairah tace "Daddy a nan fa? Idan abu ya cinye mu fa?" Yace "Ba abinda zai same ku, rayuwarku cikin jejin nan tafi fiye da wacce za kuyi a waje na, ni ba mahaifinku bane, Zan barku a nan Ubangiji ya 茩addara saduwar mu" yana fa蓷in hakan ya shafa kawunansu, ya shige mota, tuni Sairah ta fashe da kuka tana 茩an茩ame 拼ar uwarta, Sara dake tana dakakkiyar zuciya ajjiyar zuciya kawai take saukewa, idanunta sunyi wani masifar jaa. Daddy da gudu yaja motar yana tafe a motar wani abu mai zafi ya shiga bin fuskarsa, parking ya yi kawai sai ya fashe da wani Irin kuka tare da fa蓷in "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un i lose my own children....

Yaya kuka ji? Idan yay muku kawai kuyi share馃槍 Sarautar marubuta na shirya tsaf wannan salon da ban yake da sauran....

ZAIN_ABEED

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post