Jikar Iya chapter 3&4 complete by Teemerh Cool

Jikar Iya chapter 3&4 complete by Teemerh Cool

 

Jikar Iya

🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️

*JIƘAR IYA*

🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️


   Mallakin 

      Teemerh Cool🖊️  

         08161316781


*🦅MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*🦅


Bismillahi rahamanir rahim 

Da sunan Allah mai rahama mai girma, Amincin Allah ya tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad S.A.W da ahlinsa da sahabbansa baki ɗaya.


Page3️⃣🆒4️⃣


______Zama suka yi tana buɗe musu ledan, washe baki ta ƙara yi wanda ya baiyana haƙoranta da suka yi yellow tsabar datti, ba tare da ta wanke hannu ba ta soma biyar cikin ledan taliyar yaran, tare da kai loma bakinta, ita ma Iya ba'ayi babu ita ba, haka ta zage ta saka hannun taci ta ƙoshi, suna ci suna haɗawa da bireɗin.


Sai da suka kai karshen taliyar tas tukunna suka cire hannun su daga ledan tare da siɗe yatsunsu.


" Allah sarki Marainiyar Allah kice dai mafarkin ne ya tabbata" a faɗar Iya tana washe baki, kamar wacce aka bata kyautar kujerar makka.


" Eh Iya kamar yadda na gani a mafarki aka cemun naje na ɗauka a inda na gani a mafarkin, acan naje na gani a ajiye babu kowa a wajen" tayi maganar ta na kai wata katuwar bread bakinta.


" In ba maraya ba ai babu mai wannan baiwar, marayan ma sai wanda Allah ya zaɓa" ta yi maganar ta na miƙewa ɗauko goronta.


Sai da ta tashi tukunna Indo ta washe baki ta na dariya, da sauri Iya ta juyo tana tambayar ba'asin hakan, amma sai ta ce da yan uwanta marayu take dariya, sai da Iya ta ɗauko goron nan ta samu waje kusa da Indo ta zauna.


A jikin abun goga goron ta shiga gogawa, sai da ta samu damƙa ɗaya takai baki tukunna ta ce" Indo kenan marainiyar Allah yanzu kuma mai suka ce miki?" ta yi maganar tana daidaita nutsuwarta tare da zubawa Indo ido, kamar wata mai ɗauƙar darasi.


" Cewa akayi yau za'a fasa auren Jummai Ƴar Mai Gari" shine abun ya bani dariya.


Zare ido Iya tayi tare da riƙe baki ta na faɗin "Indo dan Allah ki rufa mana asiri kar wannan zance ya fito daga bakinki, dan wallahi mai gari bazai raga mana ba" ta yi maganar kamar za ta yi kuka.


"Haba Iya mai ya isa ya mun ne, karfa ki manta ni Indo ta Iya babu wanda ya isa yaja dani sai Allah, naci dubu sai ceto ta yi maganar tana wani mika tare da rabe hannaye biyu gefe da gefe, kamar wacce take neman hanyar fita.


Iya kam tsuru-tsuru tayi da idanunta, dan wallahi duk rigamar da Indo za ta nemo mata bai dameta ba, za ta iya yin komai amma banda na gidan mai gari, musamman wannan ƴar da kamar wacce akayiwa asiri bata taɓa samun mashin shini ba sai yanzu Allah ya kawo kuma za'ace baza'ayi auren ba.


Tunanin da Iya ta lula kenan, inda ta dawo daga tunanin ta samu Indo tuni ta fita da gudu.


Cikin ɗaki tayi da gudu ta zari mayafinta a hannu, sai da takai ga karasawa wajema ta saka mayafin akanta, inda take waige waige bata san ta inda zata fara neman Indo ba, " gabas zanyi ne ko yamma?" ta yiwa kanta tambayar, takalminta da yafi karfinta ta shiga jan ƙafarta tana zuba sauri kamar wacce za ta tashi sama, tsohuwa ce jigib wanda zata iya kaiwa shekara tamanin, dan kusan duk ƙauyen ita ce babba, shiyasa duk abun da Indo take yi ake rage mata albarkacin tsohuwar nan ne, wasu in sunga yadda take tafiyar cikin sauri dariya take basu, wasu kuma tana gilmawa suke faɗin to za'aje ayi masifa, dan wannan sauri sai dai wani ya taɓa Indo ne?, kowa da abun da yake rayawa a zuciyarsa, da fili kuma jijjina bala'in da wanda ya taɓo Jiƙar Iya, dan yau za'ayita a garin Dan Batta.


Gidansu Musa ta wuce Iya faɗawa tayi ba tare da sallama ba, "Iyar Indo lafiya ki ka shigo babu sallama?," a faɗar Innar Musa.


" Ke tsuwar bazawara ina Indo bata zo gidan nan ba, sannan kuma ina wannan hatsabibin yaron naki" Iya ta jefa mata wannan bakaƙen maganganun, dan inda sabo Innar Musa ta saba, "ɗazu da safe dai ta zo sun fita, amma kuma ya dawo shi kaɗai tare da biroɗi, kuma ya ce ita ta bashi.


"Eh Tsohuwar Bazawara, kuma yau kun ɗanɗana arziki da ya ke tare da marainiya" ta yi maganar tana yatsine fuska, dan amsar tambayarta taji Indo bata nan, kuma inba Indo da take zuwa gidan ba, babu wani dalilin da zaisa tazo gidan tsohuwar bazawara.


Gidan Mai gari ta wuce nan ta tarar da mutane suna ta kai kawo, can gefe kuma ana kiɗar shantu, nan ta washe baki ta manta abun da ya kawota, nan ta samu ta kusa cikin jama'a, kan kace ƙabo Iya mai neman Indo tayi cikin fili.


Kowa matsawa ya yi ganin Iya ta shigo dan ansan yanzu za ta fara rawan nan nata na zufin mahaukata.


Gyara ɗaurin zaninta tayi a filin, dan kowa kallon yadda ta ɗaura zanin ya ke, dan wani ƙaton wandon ne ya bayyana wanda ake kira da fatari, juyawa tayi taga masu buga gangan sun tsaya ta ce" saƙar mun sauti ɗannan, dan Allah ina waliyin mai gari?, a shirya mun kari" ta yi maganar tana baje baki, wanda babu hoƙora a ciki sa, juya wa ta shiga yi tana zama tana tashi, tare da cilcilla hannaye kamar wacce zata fire sama, nan mutane suka shiga yi mata liki suna tayata, ganin sun fara cika mata filin da take rawa ne yasa ta magantu da faɗin" dan Allah ku gushe ku bani guri, in kuma ba haka ba yanzu zan kira muku Indo" ta yi maganar tana mamul mamul da baki, wanda babu haƙora acikin su, nan mutane suka fara ja baya danjin an anbaci Indo, dan wlh su ko hanya basa fatan ya haɗa su da Indo, dan kana ganinta ba alkhairi ba ne, sai Iya Ladi ce taƙi ta fita a filin, nan ta mai da kallonta gareta, "au kece hatsabibiyar tsohuwa yar tasha ko, gaki tantiriya baza ki fita ki bani guri ba kenan," Iya tayi magana ta na rike kugu kamar wacce take shirin yin dambe.


" Bazan matsa ba ɗin, tantiriya kuma kece bani ba, sannan kuma nida ke naga wanda zai matsa daga filin nan, dan wlh sai dai ke ki fita" ta yi maganar ita ma tana masowa kusa da Iya.


" Mu zuba nida ke Iadi" Iya tayi maganar tana cire zaninta tayi jifa dashi.


Nan mutane suka saƙi dariya dan ganin yadda Iya ta yi cikin fatari, wanda kamar za'a saka kalan Iya biyar ciki baza su cika ba.


"Dawa ku ke kewa dariya, dani kuke to wlh duk sai kun gane kunyi mun, dan Allah bazai barku ba kun wulaƙanta mai rikon maraya" Iya ta yi maganar tana sakin kukan munafurci dan ta hango Indo ta na zuwa.


Nan Indo ta bayyana a cikin filin, kowa ido yake zubawa da kokarin yadda za su yi subar filin nan, dan zuwan wannan yarinyar dole sai abu ya faru da su, dan ƙwata ƙwata babu wani alkhairi dangane da kallonta, wasu kuma na tsaye sai sunga abun da ya turewa buzu naɗi.


"Yauwa ga Indo ta zo sai naga wanda zai kara mun dariya" tayi maganar tana ɗaga ƙafarta sama ta buga, sai yanzu ma wandon ya karayin abun dariya, amma kowa yasawa bakinsa linzami, babu wani mai ƙwaƙwaran motsi a wajen.


Kowa ta shiga bi da kallon inda duk suka sun kuyar da kansu kasa, hakanne ya bawa su Musa, Auta da kuma Lami daman zagasu suna binsu ɗaya bayan ɗaya suna zuba musu ƙarara ajinkinsu, ba tare da sun sani ba dan furawa suke yi da bakinsu, ita kuma sai kara musu alama take yi da ido, nan ta fara duban Iya Ladi, wanda tuni ta zube akan gwiwarta tana haɗa majina da hawaye, dan yau tasan kashinta ya bushe, nan ta fara rarrafe tana ƙarasowa wajen da Indo ta ke tana dafa ƙafarta, "ke tsohuwar mara kunya daina taɓani da wannan hannun naki duk diasease, bake baki da mutunci ba, dan kina ganin auren Jikarki ake yi hakanne zai baki daman cin mutuncin Iyata, kuma kakata sannan fa ita ce garkuwar jikina," sai ta danyi kamar abun tausayi sai ta ce, "bisa abun da kika aikata anyanke miki hukuncin auren jikar nan taki baza'ayi ba, dan sai anfasa shi tunda kin ɓatawa marainiya rai" ta yi maganar tana juyowa kan mutanen da ke tsaye suna kallonsu ta ce " ku kuma masu mata dariya duk sai kun fara kuka yanzu, kafin kace me ai duk sun fara susa, wasu na karasowa wajenta suna rarrabe suna cewa dan Allah ki mana afuwa, mu samu albarkacin marainiyar garinmu.


Kowa da abun da yake faɗa, nan Iya Ladi ta karaso tana cewa, "Allah wuci zuciyarki Indo ta Iya yar albarka, ki yafemun ayi auren wannan jikar tawa mana, taci albarkacin Ubanta mai gari mana" ta ƙarashe maganar tana kuka tare da rike bakin mayafinta tana share hawaye.


Iya kam tuni ta samu waje tana ta kallon ikon Allah tana faɗin" Allah shi ƙara baku ba ku da mutunci ba, ƙadan ma kuka gani" ta saƙi wata dariya cikin muryan tsofofi tare da kallon Iya Ladi ta ce "au ashe ke yar barikin ƙarya ce, ni ca nake zaki nunamin anan ai, da kuwa na nuna miki nawa yafi ƙarfin naki, banda ƙaddara ma da maraici mai zai kawo Indo wannan ƙauyen, ai ko kallonta sai ya muku wuyan gani" tayi maganar tana zun gurin ƙeyar Iya Ladi.


Nan wajen dai ya ƙarade da koke koken mutane, dan kowa sai faman susa yake yi amma banda Iya Ladi da aka faɗa mata abun da ta kommace ace itama susan take yi, akan wannan batu ma fasa auren jikarta.


Nan ta basu umarni kowa ya ɓace mata daga gani, nan wasu na gudu wasu kuma na rarrabe, Idi mai kanti kam harda sakin fitsari, dan bayason yaci karo da Indo kar ta ce"za'a fasa aurensa" nan ya samu ya rarrafa tare da fitsarin da ya gama mamaye dukkan jikinsa.


Ita ma Iya Ladi daƙyar ta iya yin rarrafen, dan abun da yasa ta tafi kar taƙi kuma ace mata Malam zai saƙeta ko ya mata kishiya, hakan yasa ta tafi da rarrafe sai da ta ɗanyi nisa ta samu ta zura da gudu......


Wannan littafin na kuɗi ne, ki biya kuɗinki ki karanta shine mutuncinki, ban yadda a fitar mun da littafi ba dan kin siya, duk wata mace mai aji bazata karanta littafin sata ba, ki mallaki naki akan naira 300 kacal post kwana biyar a sati, special 500 post kullum , 9048703453 Fatima Muhammad Aliyu opay bank, sai ki turo shedar biyan kuɗinki ta wannan number 08161316781, in kuma kati ne MTN,  AIRTEL,9MOBILE, duk ina using dashi, sai a turo hoton Katin, na gode sosai.


TEEMERH COOL🖊️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post