Jikar Iya Complete Chapter 5&6


Health College

Jikar Iya Complete Chapter 5&6

 

Jikar Iya 5&6

🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️

    JIƘAR IYA

🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️

https://chat.whatsapp.com/CkC6Od7XwwuGUibnLd5D1D

   Mallakin 

      Teemerh Cool

         08161316781

Page5️⃣🆒6️⃣

_____Mai gari ne suka dawo rai a ɓace akan anfasa auren Ƴarsa, sun daɗe suna jiran ango da waliyansa amma shuru, sun ƙira waya shima basa ɗaukawa hakan yasa shida kansa ya tafi har zuwa gidansu angon tare da tawagansa, amma duk da zuwan mai gari baisa sun kasa baiyana abun da yake ransu na faɗa musu cewa sun fasa auren ƴar tasa, nan fa hankalin mai gari ya tashi ya rasa inda zai saka ransa, ƴarsa mace ƙwaya ɗaya tillo da ya ɗauki son duniya ya ɗaura mata ita ce ta rasa mijin aure, dan kaf ƙauyen nan an auran da sa'aninta, hakan ba karamin ciwo yake masa ba inya tuna, wannan dalilin yasa yanzu da aka samu wanda ya ce yana sonta suka yi murna, sannan kuma suka ɗauki buri duniya suka ɗaura akan wannan auren yanzu kuma ace an fasa.

Dan lami uban gulma ya zo ya tadda labarin yadda akayi da Iyata Indo a kofar mai gari, yaso ace a gabansa akayi, bai san za'ayi haka ba da ya hakura da zuwa jin wancan segumin da yabi tawagan mai gari dan jin abun da yasa yan ɗaurin auren basu zo ba.

Duk jama'a gari babu wanda zai iya faɗawa Mai gari abun da ya faru anan kofar gidan, da kuma yadda Indo ta ce" auren nan baza ayi shi ba," kuma gashi anyi haka.

Iya Ladi tunda ta samu ta shiga gidan mai gari sai kai kamo zuwa bayi take, dan zuwa yanzu tayi  sugune yakai sau tara, ba karamin surewa ta yi ba, da jiran fargaban abun da za'azo ace mata ya faru akan wannan biki.

Nan gidan biki kowa na tsaye akan ƙafarsa ya kasa zama, musamma uwar amaryan, dan abun ba ƙaramin taɓa mata zuciya abun ya yi, hakalinta a tashe yake dan kawai jiran dawowar mai gari ta ke, nan dai kowa da abun da yake ransa, wasu kuma wanda kaikayi bai bar jikinsu ba sai susa suke yi, basu da ta cewa, wanda kuma abun ya bar jikinsu sun rike baki sun suƙe, dan ji suke in suka buɗe za su mai da yadda akayi ma Indo za ta ji su, ko zata gane sunyi maganarta hakanne yasa su kayi shuru, wasu kuma na famar haɗa kayansu dan yau ba karamin abu suka ji ajikinsu ba, dan haka suke shirin tafiya suna cewa, "Allah bamu alkhairi maso inta haihu, amma biki kam Alhamdulillah yau munsha shi" haka dai al'amarin ya kasance a gidan mai gari.

Yana isowa ya yi cikin fadarsa dan su tattauna da mutanen fadar, nan yake kara tabbatar musu da al'amarin da ya faru a ɓangaren su ango akan an fasa auren, jimami sukai tayi kowa da abun da yake faɗa, wasu suce a rasa wanda za'a rainawa hankali sai mai gari, ai dan bamuje bane da mun bajaj dasu, wasu na cewa kawai a koresu a garin kar suga dan suna da ƙuɗi ne, ina ruwan mai gari da arzikin nasu, dan Allah ya horewa mai gari kam, shikam Ɗan Lami kamar sikararsa ake yi ya rasa nutsuwarsa, kawai abun da yake so shine ya fito da wannan zance ya fara faɗawa mai gari kuma bayason zancen ya fito daga bakin kowa sai nashi, dan zai fi jin daɗin haka.

"Ranka ya daɗe wannan batun tun kafin mu ƙarasa gidansu Ango nan aka baiyyana auren nan bazai yuba," nan fa kowa ya fara dawo da kallonsa ga Ɗan Lami, dan ba wanda baisan halinsa na gulma ba a garin.

Nan aka fara jefo masa tambayoyi da kuma ya'akayi ya sani bayan shi nan suke tare dashi suka tafi, nan ya ƙwashe labarin yadda akayi tas ya basu, nan aka aika aje a taho da Iya da Jiƙarta, ba jimawa aka kawo su nan fa kowa ya yi shuru a faɗa, dan kowa jira yake yaji ta baƙin mai gari, nan ita kuwa Ido sai kallon faɗar take a zuciyarta ta ce" au ashe an ƙara gyara rabona da nashigo daga ciki ai tun ranar da muka kawo wa mai mai gari ziyara daran-dare," abun da ta faɗa kenan a zuciyarta a fili kuwa tayi sheme sheme, ganin shurun ya yi yawa babu mai cewa komai sa ta samu shinƙiɗa, nan aka ƙara zuba mata ido ana kallonta tare da mamakin rashin kunya na wannan yarinyar.


"Iya ni zan tafi in lokacin da zaiyi magana ya yi ƙya ƙirani a gidansu Musa," ta yi maganar tana koƙarin tashi.


Hannu Iya tasaka ta durkusar da ita tana faɗin "ke Indo zauna a gaban mai gari muke, ƙyalesa ya jan ajin nasa inma ya kama ya ja da makaranta ma mu zamu jira shi, tunda ance mana mubi shugabanmu" ta yi maganar tana watsawa mutanen da suke zaune harara.


Gyara murya ya yi tare da faɗin  "Iya muna son jikarki ta maimaita abun da ta faɗa dazu" zare ido Indo ta yi tare da faɗin, "ikon Allah ni kuma mai na faɗa, kuma waye ya ce nace wani abu" ta yi maganar tana fashewa da kuka, nan fa kowa ya mai da kallonsa akan Ɗan Lami wanda ya bawa Sarki labarin haka.


"Ɗan Lami maimaita abun da ka faɗa dazu," cewar Mai Gari ya kara kallon Indo alamar taji laifinta.


Nan fa ya fara rawan baki yana nace ta ce, ya kasa faɗar kalma ɗaya wacce za'a gane abun da yake faɗa, nan ya fara kame kame dai, dan ba ƙaramin sorata ya yi ba da jin yarinyar ta ƙaryata zancen, gashi kuma shi ba ganon bane jiyaune.


Nan fa Ƴan fada suka daƙa masa tsawa tare da faɗin " kai Ɗan Lami nan fa faɗa ce dan haka ka nutsu, kuma karka yadda kayiwa mai martaba ƙarya domin kuma yin haka kuskure ne, dan za'a yanke maka babban hukunci" a faɗa wani dogare dake tsaye a gefe, kamar wani bushiya baya motsi a wajen.


"Wlh Ranka ya daɗe nima faɗamun akayi kuma Hadi ne ya faɗa mun" ya yi maganar yana sakin fitsari a jikinsa, dan baisan tun farko za'asa shi a cikin maganar ba, kuma gashi Indo tasan shi ya faɗa, ko iya hukuncinta ma aka barshi da shi yasan ta isa, ballantana abun yafi karfin na mutun ɗaya.


Ita kuwa Indo sai shure-shure ta ke yi da ƙafa tana kuka, kamar irin yaron da aka ƙwacewa alawa a hannu, nan Iya take bata hakuri da kiyi shiru Allah ne shedanki, marainyar Allah ke za'ayiwa sharri.


Kowa na zaune sai ga Hadi da Bafada sun shugo tare, nan jama'a suka mai da kallonsu garesa, ita kuwa Indo ko ɗaga kai batayi ba, dan bata ma son a ga ta kallesa, nan ya samu waje ya durkusa kamar yadda kowa ya yi.



"Hadi so nake ka faɗa mana abun da ka faɗawa Ɗan Lami,?" abun da mai martaba ya faɗa kenan.


"Naratse maka da Allah yau ni bamma haɗu da Ɗan Lami ba, hana rantsuwa na ce maka jiya na gansa, amma yau kam inna gansa Allah yasa naga ranar mutuwata kenan" ya kai rantsuwar yana nuni da yatsa kamar wanda aka sakawa duka.


Kowa mamaki yake yi a cikin fadar, waye mai gaskiya a cikin su, kowa da mamakin wannan al'amarin yake, duk da ansan Ɗan Ladi babban Magulmaci ne, amma kuma duk gulmar da ya kawo to ya gani ne, kuma baya samun sukuni sai ya faɗa, sannan baya faɗan abun da ba'a faɗa masa ba, hakanne ya ƙara basu mamaki.


" Kunga irinta ba, ƴar marainyar Allah tana zaune tana cin abinci tana shirin yin wanka taje makarantar allo amma gashi kun katse mata karatun yau, wannan ma kaɗai ai hakki ne" a faɗar Iya tana taunar goronta.


" Yanzu duk ba wannan ba, Ranka ya daɗe ba Ɗan Lami ya ce da mai Babba ɗaki aka fara faɗar ba, a gafarceni ina nufin ko zaka tambayeta ne, kaga ita kam inma boyewa suke yi ita baza tayi ƙarya ba," a faɗar wani Bafada kenan.


Nan Mai gari yasa aka kirawo masa duk yan gidan bikin su fito nan akwai magana, nan aka cika sosai mutane kamar wanda ake sallan idi, kowa ya yi shuru dan jin dalilin ƙiran da aka musu.


Nan Bafada ya shiga gaishe da Mai Babban ɗaki wato Iya Ladi, tare da yiwa Indo nuni da hannu akan ta mike tsaye, nan ta tsaya kowa ya mai da kallonsa gareta, kan kace me wasu sun fara hawaye, wasu kuma fitsari ne ya fara ɗiso musu.


" Mai Babban ɗaki ko ɗazu zaki iya faɗa mana abun da wannan yarinyar ta faɗa, sannan kuma kunyi wai hatsaniya da Iya?", ya cefa mata tambayar.



Da gudu taje ta gurin Iya ta rungumeta ta ce "Aminiyata sai yanzu ki ka zo ke da nake sa ran ganinki tun jiya, haka jiya muka sha taushe baƙyanan".......




Wannan littafin na kuɗi ne, ki biya kuɗinki ki karanta shine mutuncinki, ban yadda a fitar mun da littafi ba dan kin siya, duk wata mace mai aji bazata karanta littafin sata ba, ki mallaki naki akan naira 300 kacal post kwana biyar a sati, special 500 post kullum , 9048703453 Fatima Muhammad Aliyu opay bank, sai ki turo shedar biyan kuɗinki ta wannan number 08161316781, in kuma kati ne MTN,  AIRTEL,9MOBILE, duk ina using dashi, sai a turo hoton Katin, na gode sosai.


TEEMERH COOL🖊️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post