Kurkukun Ƙadara page 7

Kurkukun Ƙadara page 7

Kurkukun Ƙaddara

💋KURKUKUN ƘADDARA💋


Daga alƙalamin Boss Bature


E7


"Amma kinsan kina irin wannan bad dream ɗin shi ne baki  ta6a sanar mun ba"?


"Banaso na tayar maka da hankaline, Aunty aneelerh tace in dinga faranta maka rai, kada na 6ata maka rai, Zaka Iya mutuwa ni kuma banso na rasa ka, sometimes ma in nayi yinqurin fada maka sai wani abu ya daukemin hankali na manta" fashewa tayi da matsanancin kuka,


Da sauri Ya janyota jikinshi sosai ya rungumeta, baisan lokacin da hawaye suka soma sauka akan fuskar shi ba, yana jin kukanta har cikin zuciyarsa


"In sha Allah zanyi iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin na ceci rayuwarki, Bi'iznillahi duk wani mai nufinki da sharri zai koma masa ne, Tabbas akwai wani maison shiga tsakanina dake, akwai wanda yake Yi mun maƙarƙashiya, Bansan wanene ba!!Amma Allah ya sani, Kuma zai bayyanar mun dashi ne, duk mun daren daɗewa"!


Yayi maganar ne don yasan Yana da maƙiya a wurin aikin shi, masu yi mashi hassada saboda ɗaukakar daya samu, kuma har akan idon shi suna nuna mashi ƙiyayya, shiyasa ya yi zargin kodai wanine keson ya 6ullo mashi ta bayan fage, shine a kayi amfani da ita wurin cutar dashi,


Sun jima a wannan yanayin manne da juna shi da ita, sai da aka fara kire kirayen sallar la'asar, tukunna Ya ɗago da ita daga Jikin shi, Ganin ta fara bacci Ya dan jijjigata,  firgit ta farka"time din sallah yayi daga yanzu bana so kina wasa da sallah, kinji ko'?


Ɗaga mashi kai tayi alamar eh,ya kuma cewa"Addu'ar shiga toilet kin iya"?ɗaga mashi kai tayi"Eh"yace to karantamun, nan ta shiga karanto mashi, ya kuma tambayarta addu'ar kafin a kwanta bacci da kuma in an ta shi daga bacci duk ta karanto mashi Yace"masha Allah, haka nake son ji My daughter, Sannan kuma zan koya maki azhkar da zaki dinga yi na safe dana marece, pls ki bani haɗin kai, ki dage kin ji indai bakyaso a rabani dake"da sauri tace" zanyi daddy,"yace that's good, yanzu tashi ki shiga toilet kiyi alwala ina jiranki"


Amsa mashi tayi"toh" da sauri ta sauko daga saman gadon ta nufi toilet ɗin, harta kusa shiga ya dakatar da ita"wait" ta tsaya tare da waiwayowa tana kallon shi, saukowa daga saman gadon ya yi ya nufi can cikin ɗakin wurin closet ɗinsu, buɗewa yayi tare da kai hannu ya ɗauko hijabi da mayafi, asaman gadon ya ajiye mata hijabin shi kuma mayafin ya taka zuwa inda take ya ɗaura mata shi a kanta, sosai ya lullu6e mata gashinta"yawwa daga yanzu haka nake so gashin kanki ya kasance a lullu6e, sannan kuma idan kin kammala sallah, ki dinga karanta surorin da nake koya maki" amsa mashi tayi"toh"kafin ta bude toilet ɗin ta shige ciki,"


Tsayawa ya yi har saida ta fito tukunna ya sanya mata hijabin,kafin ya wuce cikin toilet, lokacin daya fito salla ya same ta tana yi, baisan lokacin daya saki murmushi ba,yaji daɗi har acikin ran shi,


Da sauri ya fuce zuwa masallaci, a bakin gate suka ci karo da Uzair yana ƙoƙorin shigowa ciki, dama biyo ma shi yayi don su tafi masallaci atare,


Bayan tafiyarshi, Angel ta kammala sallah ta zauna tana karanta surorin daya koya mata irin su falaki da nasi, su ta yi ta biyawa, duk don saboda yace tadinga yi indai bataso  a rabasu, Tana cikin yin ƙira'ar, Wayar shi daya manta saman gadon su ta soma ringing,


Zumbur ta miƙe takai hannu ta ɗauke ta, Sunan Uncle ne Ya bayyana, Kafin ta ɗaga kiran ya katse, ganin wayar babu finger print din daya ke sanya mata, dama tun lokacin da suka shirya da ita ya cire security din wayar shi, Zama saman gadon ta yi ta dinga buga game na spider man,


Sai da ta yi mai i sarta tukunna ta shiga contact dinshi, Numbobi ta haɗa daga cikin kanta ta buga kira, wani bayerabe ya ɗaga yanata gwaranci ta dinga tikar dariya, Har ya katse kiran, ta kuma haɗa wasu numbobin ba'a ɗaga ba, kusan number waya biyar ta kira ma shi wasu ba'a ɗaga ba, Sai na ƙarshene a ka ɗaga kiran,


Shiru tayi taƙi magana,tana jiran jin wanene zaiyi mata magana, shiru taji ba'ace mata uffan ba, kusan mintuna kafin wata sanyayyiyar murya so sexy ta karaɗe kunnuwanta"who is on the line"?


Ƙunshe dariya tayi yayin da take karkaɗe kafarta tace"Angel ce,"


Mutumin dake akan layin ya kuma tambayarta"kinsan dawa kike magana"?


Girgiza kai ta yi tamkar tana agaban mutumin da take waya dashi tace"a'a,"


"Ur age"? ya tambayi shekarunta,da alama ya gane yarinya ce ƙarama,


"7yrs" voice ɗin shi da alamun mamaki ya maimaita"7yrs? ina mai wayar yake'?


"Daddyna ne, ya tafi masallaci ni kaɗai ce agidan, shine na hada numbobi na kira don in gaisa da mutanan duniya"


"Can i call u video"?


Da sauri tace eh,


Nan take ya mayar da kiran Video call, ɗago da wayar angel tayi tana kallon screen din wayar bayan ta yi picking, Bata ga komai ba a screen ɗin sai duhu sosai, Amma shi wanda  take wayar dashi da alama yana kallonta,


"I can't see u" ta yi maganar tana faman gwale ido,


Shiru ta ji baya magana, saukowa ta yi daga saman gadon, a tunaninta rashin network ne, yasa bata ganin shi a video din, Tana Cikin zagaye palour Tajiyo Sallamar daddyn ta,


A gigice ta katse kiran,ta shiga goge numbers ɗin data kira, tana gamawa ta cillar da wayar saman gadon,ta haye itama ta kwanta tamkar maiyin bacci,


Atare da uzair suka shigo falon, saman sofa suka zauna suna fuskantar juna,


"Ban fada maka bane kawai, Amma nida aneelerh mun jima muna hasashen tana da  aljanu, zai fa iyayiyuwa acikin toilet ta same su tunda a nan Benazir ta haifeta, kuma kaga shi toilet madaddalar su ce,"acewar uzair, 


Jinjina kai Taj ya yi"Yanzu menene mafita"?

Uzair yace"Mu tayata da addu'a, Sannan Muyi ƙoƙarin ganin mun bi duk wasu sharuɗɗa na bata kariya da malam mai salati ya faɗa maka, in Allah ya yarda za'a dace ne,"


Taj yace"Allah Ya yarda, duk na damu wlh,"


Uzair yace"ka kwantar da hankalin ka, da yardar Allah zamu San abun yi,


Sun ɗauki tsawon lokaci suna tattaunawa tare da uzair kafin ya yi mashi sallama ya tafi gida,


Tundaga wannan Lokacin, bai ƙara yin sakaci wurin kula da ita ba har tahfeez ya sanya ta, ya ci wahala kafin ya samu tafara zama Makarantar islamiyyar, da yake a kusa dasu makarantar take, idan ya kai ta yana barin makarantar take kamo hanya ta dawo gida, Kowa ya yi mamakin yadda a kai ta ke guduwa daga makaranta, dakyar ya samu tafara zama, tun tana yi ma shi kukan ba ta so harta haƙura ta zauna, bai ta6a bari ta zauna tana shiririta ba, Kullum sai ya tasa ta gaba tana maimaita karatun haddar da aka bata, babu abunda bai siya mata ba, Wanda ya danganci karatun addini, Cikin ikon Allah sai ga shi tafara sanya naci tana yin karatun tunkafin ma yace mata ta yi take yi, wani lokacin ko bacci take yi ta dinga sambatu kenan tana Bitar karatun da a ka koya mata, Hakan ba ƙaramin daɗi ya ke yi mashi ba, Uzair da aneelerh ba ƙaramar rawa suka taka ba, wurin taimaka ma taj akan angel, dama sun ɗauketa tamkar ƴar su, Allah ya bata kaifin basira,wani irin ƙoƙari gare ne ita duka boko da islamiyya ko'ina yabon ta su ke yi, Kowa sonta yake yi, duk wani Competition da za'ayi Tsakanin makarantu, ita ke ciyo ma school ɗinsu, shiyasa su kansu malaman Ji su ke da ita, duk in tayi fashi bata zo school ba, Sai sun kira taj a waya sunji dalili, sometimes har gidan suke zuwa ganinta,


A kwana a tashi ba wuya wurin Allah  Angel ta shiga Cikin shekarata Goma, a wannan Lokacin suka Shirya Mata Party na taya murnar zagayowar ranar haihuwar ta, tun ana saura kwana biyu, Aneelerh ta kai ta wurin Saloon, gyaran gashi akayi mata mai kyan gaske, tare da ƙunshi na jan lalle, da ya rage saura kwana ɗaya birthday ɗin nata, gaba ɗaya suka shirya don zuwa yi mata siyayya A shopping Mall,


Kaya sosai suka siya mata a kasuwar, sai da suka gama kashe mata kuɗi, Tasa masu rigima akan Tana son a siya mata Piano da kuma drawing materials, A lokacin sunyi ƙarƙaf, sun gama kashe ƴan canjin da suka rage masu, Lallashinta su ka soma yi akan tayi haƙuri next time idan suka ta shi dawowa zasu siya mata, Ƙin yadda ta yi a ƙarshe ma ta  rushe masu da kuka tana fadin ita dai su siya mata su take so, ko kuma amaida sauran kayan da aka siya mata don kuɗin su isa a siya mata Piano, sosai Angel ta sanya masu rigima, tun mutane basu lura ba, har hankalin kowa ya dawo kansu, Ganin Yadda yarinyar take ta ruskar kuka, Aneelerh taso ta siya mata, Taj ne ya hanata saboda yasan ba isassun kuɗi gareta ba.


A haka suka koma gida, Sosai ya yi mata faɗa akan ta daina yi ma shi rigima Cikin mutane, tunda yace mata ba shi da kuɗi meyasa zata takura shi, so take ta kunya ta shi a idon jama'a, daga ƙarshe yace mata ta yi hakuri idan ya samu kuɗi zai siya mata komai take so, shi kan shi baiji dadin yadda ya gaza siya mata Abubuwan da takeso ba, Don ta ƙwallafa rai a kan su sosai,


A washe garin ranar ya kasance Juma'a, ranar birthday ɗin ta, Gagarumin party suka haɗa mata, tun bayan sallar asuba aka soma shagali don a wannan lokacin ne Angel tazo duniya, Ƴan uwa da a bokan arziƙi duk sun hallara don tayata murnar birthday ɗinta, Kaya kala Uku ta sanya aranar, aneelerh ce ta shiryata ta yi mata kwalliya, Musamman aka ɗauko photographers, Su ka yi masu hotuna, taro yayi albarka Anyi kulu washrabu hani'an, Kowa ya shaida ya nishanɗantu


Angel ta samu Kyaututtuka masu yawan gaske daga wurin a bokanan aikin shi, Wasu gifts ɗinma baisan su wanene suka aiko mata dasu ba, baba mai gadi ake aikowa daga waje,ya kawo mata su cikin gidan, bakomai ya fi Ba shi mamaki ba, face wata kyuatar bazata da a kayi ma angel, Abun ya ɗaure mashi kai, Abunda angel ta kwallafa rai akan shi ne Aka samu wani ya siya mata su, piano da kuma kayan zane da ta sa masu rigima a shopping mall, Ya yi mamaki sosai har baba mai gadi ya tambaya waye ya aiko mata da gift ɗin don shi ya miƙo su Cikin gidan, Baba maigadi yace ma shi bazai Iya shaida fuskar wanda ya kawo ba, Matashin saurayi ne dai kuma ya sanya facemask a fuskar shi, Sannan kuma Acikin mota ya zo, har tambayar baba maigadi ya yi kobya lura da kofato a ƙafar mutumin daya kawo su? Baba gadi ya yi dariya Tare da cewa Bazai iya tantance  ƙafafune ko kofato ba,tunda ya sanya takalma,


jikin taj dai yayi sanyi sosai, ko angel bai bari taga kayan ba, Ya 6oye su a ɗaya daga Cikin ɗakunnan gidan, Kafin a kammala shagalin sun ke6e da Uxair ya sanar da shi game da kayan da aka siya ma angel, shima ya yi mamakin jin hakan, Amma sai yace mashi  Ya kwantar da hankalin shi, Shi yafi tunanin Cikin mutanan dake kallonsu A mall ɗinne lokacin da angel tasa rigima akan su siya mata kayan, Shine aka samu wani na Allah ya siya mata su, don haka ya cire damuwa aranshi Ya bata kayanta, kada ya hanata yin amfani da su, Iya ka ci dai kafin tafara amfani da su, Ya tofe su da addu'a, kuma kada Ya dinga barinta tana yawan yin kiɗa, ko ƴan zane zane sai ya dinga lura, Sosai Uzair ya ba shi shawara, Har saida yaga hankalin shi Ya kwanta,


Bayan kwana ɗaya da yin Birthday ɗin nata, Sai ga ɗan saƙo an aiko daga wurin Alhaji ubaid, Gift ne Ya aikoma jikarshi, danƙareriyar waya ƙirar i phone tare da Laptop, Bayan ya kar6esu daga hannun ɗan saƙon,Yakaisu ɗakinshi ba zato ba tsammani Sai ga alert na 1.5m ya shigo wayarshi, again daga alhaji ubaid, Ba ƙaramin farin Ciki ya yi ba, Yana ƙara Jin ƙaunar mutumin kodan saboda kyautatawar da yake yi ma ƴar shi, shi kaɗai ya damu da ita duk cikin family ɗin benazir babu wanda ya ta6a tuntu6ar shi koda a waya ne ya tambayi ya angel ta kwana, duk da yasan halin su ko lokacin auran shi da benazir dayawansu basu so ya aure ta ba, saboda arziƙin shi bai kai ya mallake ta ba, shiyasa sam babu ruwansu da abun da ya shafi tajudden, Alhaji ubaid ɗin kaɗai ne ya damu da su, kusan kullum sai ya kira don yaji ya lafiyar jikar shi,


har uzair ya tuntu6a Don su yi shawara da shi game da Kuɗin da alhaji ubaid Ya turo mashi,Yace mashi Yayi amfani da su,Wurin Gyara mata bedroom ɗinta, Inda zata koma da kwana, ya sanya mata kayan wasanni da zasu dinga ɗebe mata kewa, Sauran kuɗin Kuma Akwai hidindimu masu Zuwa, ya ajiye mata su, Duk yadda taj yaso ya ɗauki wani a bu daga Cikin kuɗin yaƙi kar6a, Sai da ƙyar ya samu ya kar6i dubu ɗari,


a tare da aneelerh suka tsara mata komai na bedroom dinta, Wani haɗaɗɗen gado suka sanya mata, Headboard ɗinshi Sak Jikin butterfly ne, Komai na bedroom ɗinta Pink Colour ne, Ba abunda ba'a sanya mata ba, Yaci wahala kafin ya samu angel ta koma kwana dakinta,Saboda sabon da su ka yi da juna, sai ya bari bacci ya ɗauketa tukunna yake kaita ɗakin ta, idan tafarka ko ƙarfe nawa ne na dare saita sauko daga Upstairs ta dawo ɗakinshi da yake ya dawo downstairs bayan sun raba daki, Sai dai kawai yaji ta Kwance ajikin shi, 


sai da yabi komai asannu tukunna ya samu Tafara sabawa da kwana a ɗakinta, yanzu da kanta take yin wanka ta sanya kaya har ma tayi kwalliya, har lokacin angel batasan an bata gift din piano da Kayan zane ba, Saboda ya 6oyesu Laptop kaɗai ya bata, wayar kuma da aka bata shi yaci gaba da amfani da ita, don bazai bari ta ruƙe waya ba, Saboda wayon dake gareta, kuma zata iya  ɗauke mata hankalinta daga yin karatu,


Acikin waɗannan kwanakin taj yaso yaje buzaye wurin Dangin shi, Amma Uzair ya dakatar da shi, Akan ya bari Su uncle su dawo Nigeria, in ya so sai su ɗunguma su tafi a tare, ba don yaso ba Ya amince ma shi,


Tuni angel ta kammala primary school ɗinta a yanzu haka tana a Jss 3 Sunyi Exam na first term, tunda suka samu hutu ba  inda take zuwa Kullum tana gida bata zuwa ko'ina, taj Ya damƙa mata Piano ɗinta, Idan ta zauna ta soma yi masu kiɗa ko gajiya ba ta yi, Sai in Lokacin Karatunta ya yi ko sallah take tashi, sam ya hanata Yin kallo In ba cartoon ba, Shima cartoon ɗin Sai ya tabbatar Baida wani abu da zai 6ata mashi yarinya tukunna yake barinta ta kalla, Ya sanya mata ido sosai, duk wani motsinta a tafin hannun shi, idan zai tafi wurin aiki, Gidan su Aneelerh yake turata, koda basa nan mai aikin gidansu Ana tana nan, A wurinta take zama kafin su dawo  


Wannan kenan,


a gajiye ya ke driving a daidai bakin gate, ya soma dannawa mai gadi hon, Da hanzari baba mai gadi Ya fito daga ɗakinsa, ya buɗe ma shi gate ya shigo da motar Jikin gidan, Fitowa daga Cikin motar ya yi, Jikin shi na sanye da Shadda green Colour ba ƙaramin kyau tayi ma shi ba, Sai daya fara tsayawa suka gaisa da baba maigadi tukunna Ya nufi Cikin gidan,


Tunda yayi sallama a palour Yaji shiru ba'a amsa mashi ba, ran shi ya ba shi cewar Ko bata dawo gida bane, yanke shawarar zuwa bedroom ɗinta Yayi, walking slowly Ya nufi stairs ɗin ya haye, a tsanake ya ke tattaka steps ɗin benan harya samu Ya haye sama, Kaitsaye Ya nufi inda ɗakinta yake, Da sallama a bakin shi ya tura ƙopar ɗakin, Yana shiga idanuwanshi suka sauka akan gadon, wayam baiganta ba, Hakan na nufin bata dawo ba, tana agidansu aneelerh, Ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da juyawa zai bar ɗakin, Karaf idanuwan shi suka sauka akan Zanen fuskar shi da angel ta yi a jikin bangon ɗakinta, Cike da mamaki Yaci burki tare da nufar Bangon yana kallon Zanunnukan da ta yi, da kuma rubuce rubucen da ta yi duk a jikin bangon, 


Motsa lips ɗinsa ya soma yi yana karanta abunda ta rubuta a jikin bangon


_To my biggest hero_


_There's no better role model than you,_

_There's no one I'd rather look up to than you._

_I'm so proud to be your daughter_

_You're my one and only dad,  and you'll always have a special place in my heart._

_Dad, you've made all my favorite memories._

_Dad, you've always been my hero._

_I'm so lucky to have your love and guidance in my life_

 

ya ma rasa mi zai ce lokacin daya kammala karanta Rubuce rubucen da ta yi ma shi, Wani irin tsantsar farin Cikine Ya bayyana akan Fuskar shi, Tuni hawaye su ka wanke ma shi fuskar shi, slowly ya zube saman gwiwowinsa, a yayin da hawayen ke cigaba da bin kuncin shi, kalamanta ba ƙaramin faranta ma shi rai su ka yi ba, maimakon Ya ji haushin 6ata bangon ɗakin da tayi sai ma yaji ya ƙara sonta a cikin zuciyar shi,


Haƙiƙa angel ta ba shi mamaki, ta san ya shi farin Cikin da bazai ta6a mantawa ba,


Da sauri Ya juya ya kalli ƙopar ɗakin Jin motsin mutun, Bakowa bace face angel

Jikinta na sanye da jallabiya, daidai tsayinta, Tayi rolling mayafi akanta,


"Daddy sannu da dawowa Nayi missing ɗinka sosai" ta ambaci hakan fuskarta ɗauke da murmu shi, buɗe mata hannayen shi ya yi alamar tazo gare shi, da gudu ta ƙarasa ta faɗa saman faffaɗan kirjin shi, Ya sanya dukkan hannayenshi Ya rungumeta sosai, Yana faɗin"kin sani farin Cikin da bazan ta6a mantawa ba angel, I luv u so much, bansan da wasu kalmomi zanyi amfani wurin bayyana maki irin ƙaunar da nake yi maki, Allah yabarnmin ke angel, Allah ya kare mun ke daga sharrin maƙiya da mahassada, Allah ya yi maki albarka"

   Amsa ma shi tadinga yi da ameen daddy, kusan mintuna goma suna manne da juna, batare daya raba jikin shi daga nata ba, wani irin yanayi yake ji attare da shi, sam baya son yana tuna mutuwa, Saboda yasan ita kaɗaice zata Iya raba shi da angel, ko yana so ko bai so, dolene bayan ita kuma sai wata ƙaddarar rayuwar wadda baya fata,


Ɗagowa tayi daga Jikin shi ta sanya hannu tana goge mashi tears ɗin dake sauka akan fuskar shi"daddy kadaina pls, banason ganin hawayen ka na zuba"


Kallonta ya yi da runannun idanuwan shi waɗanda su ka yi jawur da su, sam ya kasa furta mata komai,


Huggin ɗinshi ta ƙarayi tana shafa sumar kanshi, bacci ya soma Ji hakan yasa shi miƙewa Ya lalla6a ya haye saman gadonta, ya kwanta duk da ya yi mashi ƙanƙanta,


  Gefen gadon ta zauna tana kallon shi, jikinta duk ya yi sanyi tace"daddy baka lafiya"?


Eyes ɗinshi arufe yace"kinci abinci"?


"Naci a wurin aunty aneelerh, Ko inje in kar6o maka naka" girgiza mata kai yayi"a'a,Bana jin yunwa, kizo mu kwanta muyi bacci"


Ƙarasa hawa saman gadon ta yi a gefen shi ta kwanta, Ya sanya hannu ya janyo ta jikin shi, Cikin ƙankanin lokaci bacci yayi awon gaba da su,


Wuraren ƙarfe 4 ya farka daga Baccin, Lokacin a nata kiraye kirayen sallar la'asar, saukowa daga saman gadon yai tare da nufar toilet ɗin ɗakin ta Ya shiga ciki,


After some minutes ya fito yana share ruwan alwalar dake a fuskarshi, Kafin ya nufi inda angel take a kwance tana bacci,


Cikin sanyin murya ya soma kiran sunanta"My angel!"shiru bata motsa ba, hannu yasa tare da ɗan bubbuga ƙafarta, nan take ta farka tana mutsu mutsun bude idanuwanta,


"Lokacin Sallah yayi, Ki ta shi kije ki yi alwala, ni zan tafi masallaci"


Muryarta a disashe tace mashi"a dawo lpy daddy,"


Bayan tafiyar shi, ta sauko daga saman gadon ta shiga toilet,


Jim kaɗan tafito ɗaure da alwala, ta ɗauko carpet ta shimfiɗa, Ta zura hijab ajikinta a tsanake ta soma Yin sallah,


Lokacin data idar da sallar zama tayi saman dardumar tana karatun alqur'ani mai girma daga cikin kanta,


Tana cikin yin qira'ar, Ya dawo daga masallaci, murmushi yasaki Yayin da ya ke shigowa  Cikin ɗakin, Ba ƙaramin daɗi yake ji ba aduk lokacin daya sameta, Saman darduma tana Yin sallah ko tana yin karatun al'qur'ani mai girma,


Sai da takai ƙarshen ayar da ta janyo tukunna ta juyo ta kalleshi"daddy sannu da dawowo"


"Yawwa daughter, Kin daiyi mana addu'a ko"? jinjina mashi kai tayi"eh,Ae kullum sai nayi"

"Haka nakeson ji, My daughter"


Shiru ya ɗanyi kafin Yace"Zamu fita tare da daddy uzair ɗinki, Zaki zauna a gida ko In kai ki wurin aneelerh"?


"Daddy bazaka tafi dani ba" aɗan shagwa6e tayi maganar,

"Am sorry, Ba cikin gari bane bazan iya yin tafiya mai nisa dake ba,"


Tuni idonta sun Ciko tab da kwalla sam bataso yana tafiya yana barinta a gida, musamman yanzu da babu school, islamiyace kaɗai yau kuma Alhamis ne basa zuwa da juma'a,


"Dan Allah daddy......."tunkafin ta ƙarasa yayi saurin katse mata hanzarinta"yi mun shiru nace maki ba cikin gari bane,"


Shiru tayi Ƴar kwallar da take 6oyewa ta soma gangarowa akan fuskarta,


Ƙarasawa Yayi tare da sanya hannayen shi gaba ɗaya ya ɗauketa, yana ɗan bubbuga bayanta"Idan kikayi mun kuka Allah zan fasa zuwa buzaye dake ne"

 Cikin shessheƙar tace"bazanyi ba"

 "Haka nakeson ji my angel"

Sauke ta ƙasa ya yi tare da ruƙo hanunta, suka fito daga ɗakin ya ja ƙofar ta rufe, Kaitsaye suka nufi gidansu aneelerh, lokacin da suka shiga falon gidan a tsaye suka gansu shida Aneelerh, Ya kammala shirin shi cikin boyel, aneelerh kuma na sanye cikin Turkish dress, Riga da wando blue, ta ɗaure kanta da mayafin kayan.


Gaisawa suka fara yi da aneelerh kafin Ya damƙa mata angel,


Batare da 6ata lokaci ba, su ka yi mata sallama atare a cikin motar Uzair suka tafi,


Saman Sofa suka zauna ita da aneeleerh,

  "Kina jin yunwa"? ɗaga mata kai tayi alamar eh,

 "Hawayen menene akan fuskarki"?tayi tambayar tana kallon fuskarta,

   "Daddy inata roƙon shi ya tafi dani amma ya ƙiya"

Murmushi aneelerh tayi"Shine kike kuka? idan ki ka yi haƙuri ae ba kwana zasuyi ba," ta ambaci hakan tare da miƙewa ta nufi kitchen,


Kishingiɗawa angel tayi tana jiran dawowarta, fitowa aneelerh tayi daga Cikin kitchen ɗin hannunta ɗauke da plate, mai ɗauke da farfesun naman Kaza, da alama ba'ajima da kammalashi ba, don sai huci ke tashi ga ƙamshi,


A saman table ta ɗaura plate ɗin,tare da samun wuri gefen angel ta zauna,


  Jin ƙamshi Yasa angel mikewa ta gyara zamanta,

   "Aunty aneelerh,duk ke kikayi wannan"?

  "A'a bani nayi ba, Ana ce ta yi shi"

 Yatsina fuska angel tayi"wannan matar kamar munafuka,Ni ban yadda da ita ba Allah, Kullum tana aɗaki kunshe, Ita bata fitowa sai zata yi girki ko gyaran gida,

  Dariya sosai Aneelerh tayi"Zaki fara tsegumin naki ko"?

  Ta6e baki ta ɗanyi, tare da zura hannu cikin plate din tana ɗan tsakurar naman, Har wani jinjina kai take yi saboda daɗin da ya kai mata karo, zuba mata ido aneelerh tayi tana kallonta,

  "Aunty aneelerh,"

 "Menene"?

 "Mutane dayawa suna cewa Ni matar Manyace, irin matan masu kuɗinnan, Allah idan na girma mai kuɗi zan aura, inda zanje in huta, Bani aikin komai sai dai Ƴan aiki  suyi mun ina daga kwance,"

  Tunda ta soma zuba, Aneelerh ta ƙura mata ido tana kallonta,Wato Zuzuta kyanta da mutane suke yi suna cewa ita matar manya ce, Shine ta haddace maganarsu acikin kanta, har tafara sawa ranta aure inda zata huta,

  "Bakya son talaka"baneelerh ce ta jefa mata tambayar,

  Yatsina fuskata tayi"ae annabima yace mu nemi tsari da talauci,"


Murmushi Aneelerh tasaki, tasan halin angel da gaddama, shiyasa bata ja zancen da tsayi ba,


(Mu haɗu a next page in Allah yakai mu da rai da lafiya masu neman ƙarin bayani su yi mun magana ta whatsapp 08103884440,)

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post