Kurkukun Ƙaddara chapter 9

Kurkukun Ƙaddara chapter 9

 

Kurkukun Ƙaddara

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*


*_daga alƙalamin Boss Bature ✍️*_


 dedicated to Aunty kubra❤


قصة حزينة جدا عن السجناء🥺💔


*E9*

 


     

Suna Cikin tattaunawar nan, Suka jiyo hon ɗin motar su, Da gudu Angel ta zabura Zata sauko daga saman gadon, Aneelerh ta ruƙo hannunta"ki bari su ƙaraso Ciki mana"


Komawa tayi ta zauna jikinta har wani rawa yake yi duk ta ƙagara taga daddynta,

Baba maigadi na buɗe masu ƙopar, A tsiyace suka shigo da motar bayan sunyi parking ɗinta Taj ya kashe motar,


Uzair ya kalli shi ganin yadda zufa keta tsatstsafo mashi ya haɗa uban gumi"banaso su gane wani abu ya faru pls, Ka daidaita natsuwar ka"


Kallon shi taj ya yi "natsuwa fa ka ce?tayaya  kenan? akan idona fa mutane suka rikiɗa suka canza halittarsu, kuma akan idona suka handame mutun da ya'yan shi, wlh ko a film naga hakan saina girgiza ballantana kuma a zahiri, ni wlh ka cuce ni, danasani tunfarko ban biye maka ba, da duk banga wannan tashin hankalin ba" ranshi duk ajagule ya yi maganar,


"Amma ae koba komai, mun ƙaru ko?tun da kaga yanzu mun samu a bunda zamu taimaki al'umma,"uzair ne yayi maganar,

  Wani kallo Taj ya jefa mashi"mu taimaki al'umma, ka yi hauka ne"?


Bai ba shi amsa ba, sai ma ya fito daga motar, ya nufi cikin gidan, Jiki a sanyaye taj ya fito daga motar yabi bayan Uzair suka nufi cikin palourn,


Kusan atare suka haɗa baki wurin yin sallama, jin muryoyin su yasa Angel da aneeleeh suka fito daga ɗakin, da gudu angel taje ta faɗa ma daddynta,

  "Nayi fushi sai yanzu zaka dawo,duk ka tayar mun da hankali, ko bacci na kasa yi"

  Zuƙunnawa yayi saman gwiwowin sa, yadda tsawon shi zaizo dai dai da nata,

   Sosai yayi hugginta ɗinta"Am sorry angel, Nasan nayi laifi, ayi mun afwa,"aɗan shagwa6e tace"shikenan amma kada ka ƙara," amsa mata ya yi da toh batare daya rabata da jikin shi ba, sam baiso ta gane halin da yake ciki, hawaye ne cike tab da idanuwan shi, tamkar ya rushe da kuka haka yake ji bakomai yafi tsaya ma shi a raiba fa ce yacce waɗannan Mutannan marasa imani suka fatattaki malamin nan da kuma ƴa'ƴan shi, Yanzu shikenan sun kashe su, Babu su a doran duniya, tabbas waɗannan mutanan sun san me suka taka,


Aneelerh da uzair tuni sun shige ɗaki,

 "Sannu da dawowa" batare da ya kalle ta ba, ya nufi toilet zai shiga,

  "Wai meke faruwa ne? Nayi maka magana baka amsa min ba,"

  Juyo wa ya ɗanyi Yana kallonta a lokacin ya ruƙe handle ɗin ƙopar toilet zai shiga, "To matar ɗan jarida, ba za ki bari  na samu natsuwa ba" cikin zolaya ya yi mata maganar,


Murmu shi taɗan saki, shima ya mayar mata da martanin murmushin kafin ya shige cikin toilet ɗin.


Tunawa da taj yasa Aneelerh miƙe wa Ta fito falon, Bata same su a nan ba hakan na nufin ya ɗauki angel sun tafi gida.


Ta so ace tayi ma shi sannu dawowa, ga shi kuma Ya tafi, Ta wani 6angaren kuma ji take kamar wani abu Ya faru ba daidai ba, Tun daga kan yanayin Uzair, da kuma shi taj ɗin.


Hakanan taji hankalin ta bai kwanta dasu ba, sam babu natsuwa a tattare da su, Juyawa ta yi zuwa cikin ɗakin a lokacin uzair Ya fito daga toilet ɗin, da alama Ruwa yaɗan watsa ma jikin shi, short ne kawai ya bari ajikin shi,


"Sannu da fitowa" ta faɗi tana kallon shi,

  "Yawwa madam,"

"Bari na kawo maka dinner ɗin ka, nasan ka kwaso yunwa,"

Da sauri ya dakatar da ita "No bana jin yunwa, bacci nake ji" yakai ƙarshen maganar tare da nufar Cikin ɗakin wurin Closet ɗin shi, Ya buɗe cikin jerin jallabiyoyinshi ya ɗauko ɗaya Ya zurata ajikin shi,


Juyawa yai Still aneelerh tana a tsaye tana kallon shi, Ta gefenta yabi ya wuce ya kwanta,


"Nayi tunanin zaka yi missing ɗina," tayi maganar tare da takawa Ta koma gefen gadon,

    "Kodai wani abu ya faru ne? naga duk ka sauyamun, Shima taj ko sallama banyi ma shi ba, Ya ɗauki angel sun tafi gida"

  Ganin zata takura mashi da surutu ne yasa shi yin saurin janyota jikin shi, wata irin runguma yayi mata, sai ga shi tayi tsit bata ƙara cewa uffan ba,


Taj kuwa bayan Sun koma gidan, Upstairs Ya wuce da angel, Yakaita bedroom ɗinta, Yasan aneelerh bazata barta da yunwa ba,


Dawowa down Yayi a hanzar ce ya shiga bedroom ɗin shi Ya faɗa toilet, shaf shaf yayi wanka ya fito, wuri ya samu saman kujerar gaban mirror ya xauna, wasu zafafan hawaye ne su ka soma yin zarya akan fuskar shi, Uban tagumi ya zabga tamkar marayan da ba shi da ma fadi aduniya,


"Daddy"muryar angel ce ta katse shi, ta cikin madubin yake hangenta, tana a tsaye bakin ƙopar,

  Da sauri ya share hawayen dake a kan fuskashi cikin sanyin murya yace"Ba ki yi bacci ba?

  Ƙarasa shiga cikin ɗakin tayi"daddyna ba ka da lafiya ne?


  "Lafiyata ƙalou me kika gani ne"?yayi tambayar tare da ɗan juyawa yana kallon ta, a lokacin ta ƙaraso in da yake zaune,

  "Ni dai inaji araina, baka da lafiya,"

daƙyar ya ƙaƙaro murmushi yace "Waya faɗa maki bani da lafiya?

  "Naji a jikina" ta yi maganar tana ƙare mashi kallo,

  "Bana hana ki yawo da daddare ba kallabi ba"? da biyu ya yi mata maganar don ya mantar da ita wancen zancen,

  "Mantawa nayi,"

Nuna mata hanyar fita yayi da hannun shi"Oya go back to ur room ki ɗaure kanki da kallabi, before ki kwanta"

 Maƙe mashi kafaɗa tayi"Ni dai zan kwana anan, muyi bacci a tare"

  Ɗaure mata fuska ya yi"Za ki wuce  ko sai nayi ball dake" a faɗa ce ya yi mata maganar,nan da nan yanayin fuskarta ya canza, ƙwalla ta ciko tab a cikin idanuwanta, cikin shessheƙar kuka tace

"Dan Allah daddy ka bari in kwana anan yau kawai" ta ƙarasa maganar tana matsar ƙwalla,

  Gyaɗa kai yayi"Shikenan Ki fita waje Ki jirani zan kira ki" juyawa tayi da sauri ta koma daga waje, ta jingina bayanta jikin wall,


Miƙewa ya yi jiki ba ƙwari ya nufi wardrobe ya ɗauko kayan baccin shi, ya soma sanya su a jikin shi,


"Daddy in shigo" jin muryarta ya sa shi yin murmushi tare da cewa"ban kammala ba"


Sai daya ƙarasa zura kayan a jikin shi, tukunna Ya kira Sunanta Angel, Shigo wa tayi cikin ɗakin A kwance ta same shi saman gado, Ƙarasawa tayi ta haye saman gadon, Can kusa da shi ta kwanta,

   Addu'a ya shiga jerowa yana tofa masu, Kafin Ya janyo ta jikin shi, a daren ranar da ƙyar ya samu bacci Ya ɗauke shi,


****Boss Bature****


A washe garin Ranar, Angel ta farka bata same shi a saman gadon su ba, Tunda ya tafi sallar a suba bai dawowa ba.


Ita kaɗai acikin gidan, Ga yunwa tana ji, fito wa ta yi daga bedroom ta sauko down kaitsaye ta nufi cikin falo, Fridge ta buɗe ta ɗauko Fura a cikin roba, Ta koma saman sofa Tana sha, duk in taji kamar motsin mutun saita kalli ƙopar taga idan shi ne Ya shigo,


Wuraren ƙarfe tara na safe Ya shigo Cikin falon, A kwance ya sameta, Tana ta bacci, ga robar furar data sha a jiye saman table,


 Ƙarasawa yayi a gabanta ya zuƙunna tare dakai hannu yana shafa gefen fuskarta, Yasan tayi neman shi har ta gaji, Shi kan shi baisan ya akai bacci ya ɗauke shi a masallaci ba, Kodan jiya bai samu isasshen bacci ba ne,

  Kasa janye eye ɗinshi ya yi daga kan fuskarta, hakanan ya dinga jin bugun zuciyarshi na ƙaruwa, sallamar uzair ce ta katse mashi kallon nata da ya ke yi, Miƙewa taj ya yi tare da juyawa Yana kallon shi,

  Gaisawa suka fara yi, kafin suka rungume juna kamar yadda suka saba,

  "Inason magana dakai" acewar uzair,"

  Nuna mashi wuri yayi saman sofa"bismillah"

Zama Yayi saman 2 seater, taj kuma ya zauna a saman 1 seater, kallon kallo su kayi ma junansu na tsawon mintuna biyar batare da wani daga cikin su yace ƙala ba, Sai da taj ya gaji da zaman tukunna yace

 

"Ina sauraronka"?

A tsanake uzair ya soma magana"game da waɗannan mutanan da muka gani jiya"

 "Suwa kenan"? yadda yayi tambayar tamkar baisan komai ba,

"Ina nufin waɗannan Miyagun da suka Kashe malamin nan da ƴa'ƴan shi,

Wani irin kallo Taj ya yi ma shi"Wai dama ba mafarki bane"?

 

Harara uzair ya ɗan jefa ma shi"take it serious pls, Banason wasa so nake muyi magana a kansu,'

Girgiza kai taj yayi"badani ba wlh, Na riga da nabar komai a matsayin mafarki, Bana so kasa ke tunamun a bunda ya faru jiya,"


"Kana nufin xamu ƙyalesu ne suna aikata 6arna acikin ƙasarmu"?acewar uzair ,A harzuƙe taj yace"ƙwarai kuwa, tunda bamu da yadda zamu yi da su, sunfi ƙarfin mu, mubar su da Allah shi kaɗai ne zai yi mana maganin su,


Uzair yace"Ba haka na sanka ba taj, Nayi tunanin zamu haɗa hannu a matsayin mu na ƴan jarida wurin ganin mun fallasa su, don a ɗauki mataki a kansu,"


Taj yace"Allah ya taimaka, Amma ni dai babu hannuna a ciki, kaima kuma ina gargaɗin ka akan ka manta da su, tamkar baka ta6a sanin su ba, In ba haka ba zaka jefa kanka cikin matsala ne , domin kuwa waɗannan mutanan da kake gani Shaiɗanu ne, sunfi ƙarfin hukuma ita kanta ballantana kuma mu da muke ƴan jarida"


Abu kamar wasa, suka soma gaya ma juna magana, Shi uzair yasa kafiya  a kan saiya bi ƙwaƙƙwafinsu don ya tona masu asiri, Shi kuma taj yana ƙoƙarin fahimtar da shi irin haɗarin da zasu jefa kan su, a ƙarshe dai Uzair Ya miƙe rai a6ace yace"idan har ban tona masu asiri ba,tabbas zan ajiye aikina na ɗan jarida ne, domin ban cancance shi ba" yana kai ƙarshen maganar shi ya fuce, Taj dai yana a tsaye ya yi kasaƙe yana kallon bayan shi, har ya 6ace ma ganin shi,


Duk wannan surutun da su ke yi akan kunnan angel tun ɗazu ta farka daga bacci, duk da bata fahimci me suka tattaunawa ba,


"Daddy faɗa kuke da Daddy uzair?" a ɗan ruɗe Ya kalleta, da sauri yace"a'a, muna tattaunawa ne, game da zuwan Uncle abdallah, na faɗa mashi cewa Ya bari mu fara zuwa buzaye shi kuma yace dole mu jira su dawo Sai mu tafi atare"


 Murmushi tasa ki"Nima nafi so mu tafi tare da su mommy adama"


"Me zaki Ci in kawo maki"?


"Komai zaka ci nima zanci" miƙewa ya yi tare da juyawa Ya nufi kitchen, don yau ba aikin safe gare shi, Sai wurin mare ce zai fita.


Zama tayi tana Jiran dawowar shi, almost 15 mins Ya fito hannun shi ɗauke da plate, indomie ce daga sama Kuma  wainar ƙwaice, Asaman table ya ajiye masu,Kafin Ya koma kitchen ɗin Ya haɗo masu tea a cup biyu,Yazo ya ajiye gefen plate din


tare suka zauna Suna ci, still zuciyarshi a cunkushe take, Yana so ya taimaka ma uzair wurin fallasa asirin waɗannan mutanan ta wani 6angaren kuma Yana jin tsoran su jefa kan su Cikin masifa, tunda mutanannan sunfi karfinsu nesa ba kusa ba, Allah ne kaɗai zai Iya dasu, ga kuma angle din shi bayaso wani abu ya faru da ita ta sanadiyar shi gaskia yana cikin tsaka mai wuya


Ya yi zurfi cikin tunani, muryar Angel ce ta katse shi, "Daddy!" 


Firgigit ya yi tare da kallon ta, "Na'am!" 


Fuskarta da alamun damuwa ta ce, "Tun ɗazu ina ta kiran ka amma ba ka amsa mini ba. Daddy kamar kana cikin damuwa."


Girgiza mata kai ya yi, "Am ok, ba wani abu. Kawai ina tunanin rayuwar duniya ne mai ban al'ajabi, rashin tsoron Allah ya yi ƙaranci a zukatan wasu mutanen. ban sani ba neman duniya ne koko mene ne yake jan hankalin su har su manta cewa wata rana za su mutu? Kuma za su koma ga Allah, sannan duk wani abu da suka mallaka ba za a ta6a binne su da shi ba, a gidan duniya za su bar shi."


Tun da ya fara magana Angel ta ƙura masa ido tana kallon shi, sam ba ta fahimtar kan me yake magana. Shi kansa ya manta da wa yake magana? Abin ne ya dame shi yasa yake ta sambatu ko ya samu ya rage raɗaɗin dake cikin zuciyarsa. 


Haɗa ido sukayi da ita, lokaci ɗaya yaja bakin shi ya yi shiru, da mamaki akan fuskarta take kallonshi, can dai tace"Daddy, Meya faru"?


Ƙaƙaro murmu shi ya yi"halan kinji inata zuba ko? wani programme ne da zamu gabatar a gidan radion mu shine nake tsara yadda zanyi shi"


Murmushi tasa ki"Allah ya taimaka daddy, I wish u all the best' ya amsa mata da ameen,


*ANEELER*


A zaune su ke ita da uzair saman dining chairs suna fuskantar Juna, gaba ɗaya hankalinta na akan fuskar Uxair tunda ya ruƙe spoon yake ta jujjuyashi Cikin abincin da ta zuba ma shi a plate sam ya kasa cin shi sai kacaccala shi yake yi kamar ƙaramin yaro, ta lura da canzawar da yayi daga  daren jiya zuwa yau kamar wani abu na damun shi bama kama bace tabbas akwai abinda ke damun shi. 


Gyaran murya ta ɗanyi ma shi, Ya ɗago suka haɗa ido tace"My man, kaƙi faɗamun abunda ke damunka, tun ɗazu nake kallon ka, sam ka kasa Cin abinci why pls"?


Daƙyar ya iya bude baki yace"don't worry ur self am ok, just bana jin daɗin zuciyata ne,"


"daka daure ka faɗamun may be in sama mana solution"


Murmu shi ya ɗansaki cikin  zolaya yace"Matsalar bata asibiti bace balle kice za ki yi mun allura inji sauƙi"


Ta6e baki ta ɗanyi tare da mayar mashi da martanin murmushin "kana nufin matsalar data shafi asibiti kaɗai zan iya magani"?


Girgiza kai yayi"karfa ki dauka da zafi, It was a joke"

Kallon shi kawai tayi kafin ta mayar da eyes ɗinta akan abincin dake gabanta,


Wuraren ƙarfe shida na marece,  taj, Yana daga kishingiɗe saman Sofa, jikin shi na sanye Cikin jeans da white shirt, a lokacin angel tana can cikin ɗakinta, 


Ƙwanƙwasa ƙopar falon shi a kayi daga waje, A hakanlali ya ɗan buɗe i danuwans hi tare da tambayar wanene, Ba abashi amsa ba aka turo kopar ɗakin, uzair ya gani a tsaye Sanye da jallabiya, fuskar shi babu walwala, miƙewa zaune taj yayi yana kallonshi yace"Shigo ciki mana"


Ƙarasa shigowa Cikin falon yae tare da samun wuri saman Sofa ya zauna, batare da ya furta mashi komai ba,


"Meke damun ka ne aminina? naga sauyi sosai akan fuskarka"


harara ya dan jefa mashi tare da cewa"Kaine damuwata Taj, saboda kaƙi bani haɗin kai akan abunda nakeson Cimmawa"


Murmushin takaici taj yayi"cos You wanna get yourself into trouble shiyasa naƙi goya maka baya, Idan suka kama mu munayi masu leƙen asiri what do you think will happen next? They will kill us as soon as they find out that we are investigating them,"


Jinjina kai Uzair yayi"Yanzu haka zamu zuba ido ana aikata 6arna batare da Mun hana ba"?


"Ƙwarai kuwa, Saboda bamu da yadda zamuyi,illa iyaka Muyi addu'ar Allah ya kawo mana ƙarshen su, that's the only solution"


Jiki a sanyaye Uzair ya miƙe ya soma tafiya har yakai bakin fita daga Falon ya ɗan dakata

  "Ka manta alƙawarin da mu ka yi ma juna tun kafin mu fara aiki'? shiru taj ya yi yana kallon bayansa,


Cigaba da magana uzair yayi" duk runtsi duk wuya zamu ƙarfafa ma juna gwiwa wurin ganin mun taimaki ƙasar mu, amma sai gashi kaine na farko daka fara sare mun gwiwata, Narasa goyon baya daga gareka, ji nake tamkar narasa wani sashe na jikina,"


Miƙewa tsaye taj yayi tare da nufar inda Uzair yake atsaye Ya soma magana"Ina jiye mana tsoron abunda zai biyo baya ne, akan idon mu suka kashe mutun da ƴa'ƴansa, a haka kuma ka ke so Mu yi bincike akansu?wannan fa ba aikin mu bane, shin wai kai baka tsoron asirin mu ya tonu su gane cewa muna bibiyar su?ko ba don saboda mu ba, ka tuna kana da mata ni kuma inada ƴa, So ka ke Mu jefa su cikin masifa ne? Yana kai ƙarshen maganar shi uzair yace"In sha Allah hakan bazata ta6a faruwa ba, Nidai inaso ka bani haɗin kai kawai"


Duk yadda Taj yaso ya fahimtar dashi amma Yaƙi ya gane, ba don yaso ba, Ya amince mashi akan suyi Bincike akansu, don su samu hujjojin da zasu fallasa su, har hukuma ta ɗauki mataki a kansu, Tun daga wannan Lokacin Suka soma tunanin ta ina zasu fara neman su, A ƙarshe Uzair ne ya ba shi shawarar su koma inda suka fara ganinsu acikin dajin nan, Cikin sa'a ranar da suka je again suka sake ganin miyagun mutanan nan sun kamo wani mutumin, kamar yadda suka kamo malamin nan, da alama Leƙen asiri shima Yayi masu, Akan idonsu suka koneshi, ranar Taj hankalin shi ya tashi matuƙa har yace ma Uzair shidai zai Cire hannun shi, kusan faɗa sukayi da uzair akan hakan, daƙyar suka sasanta kansu, kuma suka Cigaba da bibiyan Alhazawan nan, Sai dai duk wannan tsawon lokacin da suka ɗauka suna Bibiyarsu Allah bai basu damar sanin kosu wanene su ba, daidai da fuskokin su ba su sani ba, Abu ɗaya kawai suka sani inda suke yankewa mutum hukunci wato Cikin dajin nan a bakin ƙorama, Abunda su taj basu sani ba, duk wani motsinsu akan idanuwansu suke yin shi, Sunsan komai game da bibiyar su da su ke yi zuba masu ido kawai su kayi, yayin da su basu san da hakan ba, Lalube kawai su ke yi acikin duhu............


Ganin babu Riba a bindiddingin su da sukeyi ne yasa Taj ya cire hannun shi, uzair kuma yasa naci Akan binciken shi, duk yadda taj ya gargaɗeshi  amma Ya sanya kafiya, ashe ajaline ke kiran shi.


*************************

A daren Ranar Alhamis ne Wannan mummunan ƙaddarar ta riskesu wadda tayi silar rasa rayukan su,


Wuraren ƙarfe 9 na dare, Taj na zaune tsakiyar gadon shi, ya tasa laptop ɗinshi agaba yana ta ƴan danne danne acikin, har ma ya yi shirin kwanciya singlet ce ajikin shi tare da short, wani aiki ne ya tsayar da shi, Allah Allah ya ke yi ya gama aikin ya je ya kwanta, sai hamma yake yi, ba zato ba tsammani yajiyo bugun ƙopar falo,


Agogo ya kalle, Cike da mamaki Ya sauko daga saman Gadon ya fito ɗakin ya nufi cikin falon, a baƙin ƙopar ɗakin ya tsaya tare da tambayar wanene? Daga waje yajiyo muryar aneeleerh,ka bude mun kopa nice" muryarta Cikin shessheƙar yaji sautinta, jiki na rawa ya buɗe mata ƙopar har saida gaban shi ya faɗi ganin Yadda fuskar ta tayi jawur saboda kukan da ta sha, kayan Bacci ne ajikinta riga da wando sai mayafin data yafa akanta, gefen goshinta kwantaccen gashin kanta,


Aruɗe yace"Aneelerh? Lafiya? me meya faru ne? Ya akai naganki acikin daren nan'?


Daƙyar take iya kallonshi, da runannun idanuwanta wadanda suka yi jawur da su,

  "Uzair ya fita bansan inda yaje ba Cikin daren nan, na farka bangan shi ba, hankalina bai kwanta ba, na je wurin baba mai gadi don in tambaye shi ko sun yi magana da uzair kafin fitar shi,  yace mun eh  sunyi magana da shi kafin ya fita amma bai faɗa ma shi inda zaije ba,......" tunda ta soma magana hankalin taj ya ɗungunzuma, jikin shi ya soma kakarwa, fargabar shi kada ace uzair ya tafi Wurin mutanan nan, dama yace mashi bazai fasa bindiddiginsu ba, idan kuwa hakane to kuwa tabbas yaje yi masu leƙen asiri ne,


Jin yayi shiru bai ce mata komai ba  yasa tace"ko kasan inda ya tafi ne"? girgiza mata kai yayi alamar a'a, saboda bai son ya tayar mata da hankalinta,

"Kin kira layin shi"? ya yi tambayar yana kallonta,

  "Na kira shi har bansan adadi ba, Amma bai ɗaga ba, kuma kiran yana shiga"jinjina kai yayi" Bari na jaraba kiranshi, ki shigo Ciki ki zauna" yakai ƙarshen maganar yana nuna mata sofa,


Cikin sanyin murya tace"bazan Iya zama ba," tausayinta duk ya kamashi, bedroom dinshi ya koma a hanzarce Ya kai hannu ya ɗauki wayar shi dake a jiye gefen laptop ɗin shi, Ya shiga call logs, ya  danna ma uzair kira, tana fara ringing, uzair yayi picking call ɗin,

  Rufe shi da faɗa yayi ta inda ya ke shiga bata nan yake fita ba,

  "Duk inda kake ka dawo gida yanzu yanzu, kasa baiwar Allah sai kuka take yi, Saboda rashin hankali, Ka kama hanya ƙarfe tara na dare ka tafi ka barta batare da ka sanar da ita inda kaje ba, Anya kuwa kasan me ka ke yi? wai shin ina kaje ne ma.......? duk wannan suratan da taj ke yi uzair baice mashi uffan ba, A ƙarshe ma saiya yan ke kiran gaba ɗaya, jikin taj ba ƙaramin sanyi ba, tunani ya shiga yi wai shin dawa ma yake waya? idan uzair ne meyasa bai yi ma shi magana ba? kuma ya  ɗaga kiran Anya kuwa ba'a samu matsala ba, sake kiran Layin ya yi a switched off ya samu wayar, Nan fa jikin shi ya mutu, hankalinshi Ya tashi


Saman bedside drawer Ya ɗaura wayar, ya fito daga ɗakin ya koma falon, Cike da zullumin amsar da zai ba aneelerh,

Lokacin da ya shigo falon ya ƙaraso inda take tsaye, sai ya shiga Yin ƴan kame kame,

  "Bai ɗaga kiran ba ko" ta yi tambayar a ƙagare,

  Muryarshi na inda inda yace"Am..um..kingane..eh..muyi waya dashi, ki kwantar da hankalin ki, Yana kan hanyar dawowa gida, yanzu ki koma ki kwanta,  kada ki takura kan ki,"

  Wani irin kallo yaga tana yi ma shi kallon ban yadda dakai ba, da sauri yace"kiyi hakuri ki koma gida, nan badajimawa ba zai dawo"

Jiki asanyaye Ta juya ta fuce daga falon, Ko bayan tafiyarta saida ya kuma kiranta awaya, Ya ƙara kwantar mata da hankalinta,


Kasa zama ya yi, zarya ya shiga yi tsakanin ɗakin shi zuwa palour, ya rasa meke yi ma shi daɗi duniyar nan, duk bayan ƴan mintuna sai ya jaraba kiran Layin Uzair don yaji in ya bude wayar amma a kashe yake samun ta,


Bawan Allah ya rasa ta zama, duk ya shiga damuwar rashin amininsa, juyawa ya yi da sauri Ya haye upstairs ɗakin angel, ya tura ƙopar ɗakin a hankali, ko'ina duhu, ya lalauba jikin bangon ya kunna switch, tare dakai idanuwanshi kanta, Sai bacci take yi, ta ƙudundune Cikin bargo, murmushi ya ɗan saki kafin ya ɗauke i danuwan shi daga kanta, ya mayar dasu kan wall ɗin dakinta, Zanunnukan da tayi ne tare da kalaman da ta rubuta ma shi, a kullum ya kallesu sai yaji farin Ciki acikin zuciyar shi, duk mun baƙin Cikin da yake ciki,


A hankali Yake tafiya cikin ɗakin nata, ta 6angaren hagu ya zagaya saitin inda take kwance saman gadon, Kneel down Yayi tare dakai hannu Ya yaye blanket ɗin data rufa da shi, rigar bacci ce ajikinta,


Kyakkyawar fuskarta Ya ƙurawa ido yana kallonta, Hakanan ya dinga jin bugun zuciyar shi na ƙaruwa, wani irin matsanancin faduwar gaba, a cikin zuciyarshi ya shiga ambaton Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" ya ambaci hakan ba iyaka,


"Daddy" muryar ta ce ta katse shi, kallonta yayi ganin ta buɗe manyan idanuwanta a kan fuskar shi,


"Dama bakiyi bacci ba"? murmushi ta sakar mashi tare cewa"Nayi mana, yanzu na farka" hands ɗinshi ya sanya ya tallabo fuskarta"ƴar kyakkyawata,  Allah yabar mun ke,"

 "Ameen daddy, gobe uncle da aunty zasu dawo ko sai mu tafi buzaye ? tayi tambayar tana ƙoƙarin mikewa zaune,

  Girgiza mata kai yayi"Till next week nake tsammani"

 

Ta6e baki ta ɗanyi"daddy ka kwana ɗakina yau"yatsina fuska yayi"Gadonki yayi mun ƙanƙanta" cikin zolaya ya yi mata maganar,

Turo mashi baki tayi"To muje ɗakin ka mu kwana" maƙe mata kafaɗa yayi"A'a, kowa ya kwana a ɗakinsa," shagwa6a ta soma yi mashi, sosai ta ba shi dariya, suna Cikin Yin fira, Ya tuna da uzair, Rass yaji gaban shi Ya faɗi, Da sauri ya kali agogo, Ƙarge goma da rabi mayar da idanuwanshi kan angel yayi" ki koma ki kwanta, Sai da safe"  yana ƙoƙarin mikewa tayi saurin ruƙo hannunshi da sauri kallonta ya yi idanuwanshi sun taunta sosai, ƙaƙaro murmushi ya yi don ya gane me take nufi, Kiss ya mannata mata a saman forehead ɗinta, Yasa hannu ya kwantar da ita tare da lullu6e mata jikinta da bargo, addu'a ya yi mata, kafin ya kashe hasken ɗakin,


Lokacin daya fuce daga ɗakin yana jiyo sautin muryata tana faɗin"I love u so much daddy, Allah yabar mun kai, ina matuƙar ƙaunar ka habibi" murmushi yasaki A hanzarce Ya sauko down stairs, ya faɗa ɗakin shi, daga gefen gadon shi Ya zauna tare da ɗaukar wayar shi, ya ci gaba da jaraba layin Uzair, still a kashe yake samun ta, Zuciyar shi tajima da karaya, A sukwane ya ɗaura wayar saman bedside drawer, a  wannan yanayin ne Bacci ya yi awon gaba da shi, sama sama yake yin baccin na shi, 🥺🥺🥺 


Sannu a hankali agogon bangon ke harbawa, yana ba da sauti tik-tik-tik. Sakamakon dare da ya tsala don time din karfe ɗaya da rabi na dare, wayar da ke ajiye saman bed side drawer ƙirar Samsung Galaxy ta soma ruri da ƙarfi gaske. A lokacin ya yi nisa a cikin barcin nasa, kusan sau uku kiran na shigowa yana katsewa. A kira na huɗu ne, sautin ya daki dodon kunnansa, a firgice ya farka yana faman ambaton sunan Allah, 


Kafin ya zame hannunsa daga kan fuskarsa wani kiran ya sake shigowa wayarsa a hanzarce ya mika hannu saman drawer ɗin ya ɗauki wayar, 


Lokacin daya kalli screen ɗin wayar Sunan Aminina ne Ya bayyana, ajiyar zuciya ya ɗan sauke dama jiran kiran shi ya ke yi, A tunanin shi ya dawo gida ne, Shiyasa ya kira shi dan ya sanar ma shi game da dawowar shi, picking call ɗin yayi  tare da manna wayar a kunnansa tun kafin ya yi sallama, kunnuwansa suka jiyo masa sautin harbin bindugu. A gigice ya furta, "Aminina!" Kafin Ya ƙarasa rufe bakinsa, muryar Aminin nasa ta katse masa hanzari, a ruɗe yake faɗin,"Na ba ni na lalace, shikenan tawa ta ƙare."

 

A firgice ya dakatar da shi, "Ka nutsu ka yi mini bayanin me yake faruwa ne?"


"Sun kama ni ina yi musu leƙen asiri, yanzu haka sun biyo motata, na san kashe ni za su yi, kai ma kuma ba za su ƙyale ka ba. ba zan so ka yi irin mutuwar wulakancin da zan yi ba, don Allah na roke ka, ka gudu kai da Angel, ba na fatan laifina ya shafe ka Abokina. Bayanan sirrin da na ɗauka a wurinsu, yana a cikin memory ɗina, ita kaɗai ce hujjar da asirinsu zai tonu..." Bai kai ƙarshen maganar ba, ɗif ya ji kiran ya katse.


A gigice yake kwaɗa masa kira na fitar hayyaci sam ya manta da cewar wayar ta katse, sake kiran layin nasa ya yi cikin sa'a aka ɗaga kiran, abin da bai ta6a tsammani ba, sautin kururuwa ya ji a cikin kunnansa mai matuƙar razanarwa, wata kausasshiyar murya ya jiyo tana magana ta cikin wayar, "Idan kana son sanin meke faruwa, ka kalli screen din wayarka." Jiki na rawa ya ɗago da wayar yana kallon screen ɗin yayin da suka canza kiran zuwa Video Call.


Saboda tsabar firgita, a ruɗe ya diro daga saman gadon, Idanuwansa sun firfiro waje tamkar ƙwayar idon za ta faɗo kasa. Ba komai ne yasa shi firgita ba, face motar Amininsa dake ci da wuta, akan idonsa suka zazzaga wa motar fetur, yana hango yatsun hannun amininsa ta tagar motar, wuta sai cin naman jikinsa take yi. Wata irin zufa ce ta wanke masa fuskarsa, a kiɗime ya shiga furta, "No, no!" Duk ya firgice, rejecting call din suka yi.


(Saboda wadanda sukace bai budewa yasa na sake turowa ,Yayi yawa ne , zaku ga na dawo farkon labarin don kusan inda zamu tashi,


   

*💋Boss Bature✍️💋*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post