Kurkukun Ƙaddara episode 8 complete

Kurkukun Ƙaddara episode 8 complete

 

Kurkukun Ƙaddara

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*


*_daga alƙalamin Boss Bature ✍️*_


 dedicated to Aunty kubra❤


قصة حزينة جدا عن السجناء🥺💔


*E8*


Murmushi Aneelerh tasaki, tasan halin angel da gaddama, shiyasa bata ja zancen da tsayi ba,

  "kinga daddy yaƙi yin aure, Da a lama sai na fara haifa mashi ƴan jikoki" takai karshen maganar tana sakin ƴar dariya,

  Murmushi aneelerh tasa ki a ranta tana mamakin yadda take maganar aure har da haihuwa ko kunya babu halin angle sai ita kafin tace"mai zai hana kisa ma shi matar aure"

  ɗan zaro ido tayi bakinta cunkushe da naman data tura, ahaka tace"Tab, salon tazo ta mallake mun daddyna, Ƙwara yayi ta zaman shi a haka babu auran,"dariya sosai aneelerh tayi"Angel kenan mai abun ban mamaki" ta ambaci hakan tare da mikewa tace"zan shiga daga ciki inaso na kwanta, Idan kin kammala ci, Ki kai plate ɗin a kitchen, kizo ki same ni a ɗaki muyi karatun haddar da aka baki islamiyya"


Ta amsa mata da toh"sai da angel ta kammala shan farfesun tukunna ta miƙe ta nufi kitchen, Bayan ta ajiye plate din,ta fito ta nufi ɗakin aneelerh

***          ***        ***        ***      ***   **


A 6angaransu taj kuwa, gidan wani abokinsu suka fara zuwa kai mashi ziyara, sun jima a gidan bayan sun baro gidan abokin nasu, Suka Nufi gidan Gonar uncle abdallah, da niyar suje su duba yadda komai ke tafiya, Kafin su dawo gida,


Gidan Gonar acan bayan gari yake cikin daji, lokacin da motar su ta ƙarasa Cikin dajin, Adai dai bakin Gidan gonar uzair ya yi parking ɗin motar, Wani tsohone daga waje saman benci yana sauraron radio da a lama shine ke kula da gidan Gonar,


Tunkafin Suyi parking ɗin motar, Ya miƙe yana ta faman washe baki don ya gane motar uzair ce,


At same time suka fito daga Cikin motar, A hanzar ce suka ƙarasa inda yake a tsaye, Jikin shi na sanye da riga da wando na yadi, Zariyar wandon har kasa kamar wani ta6a66e, Gashin kanshi duk hurhurace, Fari ne sol kanshi da rawani irin na buzaye,


"A'a wa nake gani kamar Tajo?' cike da mamaki ya yi maganar yana kallon tajuddeen, miƙa mashi hannu taj yayi fuskar shi ɗauke da fara'a yace"Nine mana, baba buzu ashe kana a raye" ya yi maganar da zolaya,

  "Amana batace haka ba tajo,Yaushe rabon da in sanyaka a idanuwana tun kana ɗan matashi,"

   "Yau dai gani nazo, kuma bada wuri zamu tafi ba, har sai ka gaji da gani na," yakai ƙarshen maganar yana dariya, shima dariyar ya yi"wuni kuka zo mun kenan aikuwa har masara zan gasa mana muci muna fira,

     

   Kafin taj ya yi magana uzair yace

  "Fatan mun same ku cikin koshin lafiya, Ya komai ke tafiya"

  Tsohon yace"alhamdulillah, Ku ƙaraso mu zagaya cikin gonakin mana," Gaba ya yi su ka bi bayan shi, suna ɗan tattauna fira atsakaninsu"


Sunjima suna kewaye gonakin har cikin gidan gonar suka shiga, koda aka fara kiran sallar Magrib, atare da baba buzu su ka yi sallar Acikin gidan gonar, ba su tashi tafiya ba, sai bayan da akayi sallar Isha'e, tukunna su ka yi sallama da shi,


Taj ne ya kar6i driving ɗin, Uzair na gefen shi, motar su na haurawa saman titi, wasu dankara dankaran motoci masu black tinted suka shararo da gudun gaske kusan su shida, A jere suka Kurɗaɗa cikin dajin,


Duk akan idonsu tajuddeen, Da mamaki akan fuskar Uzair yace"kosu wanene a cikin motocin can? Kuma ina zasu dosa ne? Ni dai a iya sanina babu wani gida dake acikin dajin nan,"


Taj yace"May be ko wani party ne za su yi, ba abun mamaki bane"


"That's impossible, Party kuma arasa inda za'ayi shi duk faɗin garin mu sai cikin dajin nan, Gaskiya ni ban yadda ba Allah, tabbas inaso nasan me zasu yi a cikin dajin can, Ka juya motar mubi bayan su"acewar uzair,


Taj yace"Ni bazan bi su ba, kawai daga ganin motoci sun shiga daji sai kace mubi su, for what reason?


"Nidai kawai kayi a bunda nace maka, Kada ka manta mu fa ƴan jarida ne, 


rai a ɗan 6ace taj yace"Mu ƴan jarida ne, Ba jami'an sirri ba, Don haka ni bazan bisu ba, Gida zamu koma"


Yana ƙoƙarin juya sitiyarin Uzair ya damƙi hannun shi, juyowa yayi suka haɗa ido, 


  "Ka yi abunda nace maka, In ba so ka ke in sauka daga Cikin motar nan ba, in bayansu da ƙafafuna"


Sanin kafiyar Uzair ne, Yasa Taj Juya motar Ya nufi Cikin dajin, Zuciyar shi duk a jagule don ba ƙaramin takura shi uzair yayi ba,


"Ka rage gudun motar" acewar uzair, a takure taj ya rage gudun motar, yayin da yake kurɗaɗawa cikin dajin  har Allah ya kawo shi wurin da waɗannan danƙara danƙaran motocin su ka yi parking, A jere su shida a bakin wata ƙorama,


Daga nesa dasu taj yayi parking ɗin motarsu, tare da kashe hasken motar su, don kada su gansu, Amma su suna iya hangensu saboda sunbar nasu hasken motocin su a kunne,


Natsuwa su ka yi suna jiran ganin Su wanene zasu fito daga Cikin motocin,


Kusan ƴan mintuna, kafin a buɗe motocin, kamar a shirin film suka fito a tare, Kowannansu Na sanye da suits ajikin shi black colour, fuskokinsu na sanye da mask, daga ganin bodyguards ne, At same suka buɗe murfin Back seat na motocin,


Wasu Manyan mutanene suka soma saukowa daga Cikin motocin, kowannan su na sanye Cikin shigar hausawa, Daga ganinsu dattawane sun kwan biyu aduniya,


Kallon juna taj da uzair sukayi a lokaci ɗaya kafin suka mayar da hankalinsu kan abunda suke kallo,


Bayan Alhazawan sun kammala fitowa daga Cikin motar, Ɗaya daga Cikin bodyguards ɗin Ya zagaya bayan motar ƙarshe, Ya buɗe boot ɗinta, Hannu ya sanya ciki tare da danƙo rigar Wani bawan Allah dake naɗe cikin boot ɗin, Ya wurgo shi waje, Gaba ɗaya mutumin ya kife ƙasa, Rawanin dake naɗe a kan shi Ya warware, Jikin shi sai kerma yake yi, kamar wanda sanyi ya kama, daga ganin shi dai Malami ne, duba da irin shigar shi,Jallabiyace ga kuma rawanin shi, hada cazbaha a hannun shi lokacin daya ɗago, La66an shi nata kerma Yana ambaton"Innallahi wa'inna ilaihirraji'in, La'ila ha'illah anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin,'duk yabi ya susuce,


Cike da taku irin na majiya karfi, Bodyguard ɗin ya kuma takawa Zuwa mota ta biyun ƙarshe Ya buɗeta,


Wasu ƙananun Yara ne guda biyu, Gwanin ban tausa yi sun ƙankame junansu mace da namiji, Sun cunkushe acikin boot ɗin,Yadda kasan irin kifin gwangwanin nan,


Damƙo wuyan rigunan jikinsu yayi tare da ɗago dasu Ya wurgo dasu ƙasa, Gaba ɗaya suka kife saman Ciyayin dake a wurin,Sautin kukansu ya ƙarade wurin, Miƙewa Yaran su ka yi da gudun gaske suka nufi wannan malamin daga gani ubansu ne, Rungumesu ya yi a jikinshi sunata kuka, A ƙalla macen bazata wuce shekara Takwas ba, Namijin kuma goma,


Tsananin tsoro ne Bayyane akan fuskokin su, Hankalinsu amatuƙar tashe yake, Daga gani bada shiri aka ɗaukosu ba, Saboda kayan dake a jikin yaran duk na bacci ne, Ita macen ko kalli babu a kanta, ɗan kitson Shukkun da akayi matane, ƙafafuwansu ko takalma babu,


Ƙawanya waɗannan Alhazawan Sukayi masu, Suka sanya su a tsakiya, Yayin da bodyguard ɗin ke a bayansu,


Wani irin kallo suke binsu dashi, kafin daga bisani wani dattijo daga cikin alhazawan Ya soma magana"Malam wa kake da suna"?muryar na kerma Malamin yace"Jazuli"


Jinjina kai dattijon yayi"sau nawa ina jan kunnanka"?


"Sau biyu" cikin shessheƙar kuka ya yi maganar,


"Okey,Saboda kafiya da taurin kai irin naka Baka daddaraba ka sake shiga hurumina ko? Meyasa ka tsananta bincike akaina? Ka sanni ne? ko ina da wata alaƙa dakai ne?ya yi tambayar idonshi akan malamin


Shiru Malam Jazuli yayi, yana ta faman mazurai, Hannunshi bibbiyu ya tallabe ƴa'ƴan shi,


"Koda zaku cutar dani, Ina roƙan alfarma ɗaya a wurinku, dan Allah kada ku ta6a ƴa'ƴana,"


Tuntsirewa su ka yi da dariya gaba ɗayan su, mai sautin gaske,


Taj da uzair dake la6e acikin mota suna kallonsu, Tuni sunsha jinin jikinsu, buɗe murfin motar su uzair ya yi da niyar ya fita, da sauri taj ya ruƙo Hannnunshi murya ƙasa ƙasa yace"baka da hankali ne, Idan suka kama mu fa"

  Uzair yace"bana jin abunda suke cewa, dole na fita" ya zame hannunshi daga ruƙon da taj yayi mashi, yasa kai ya fuce daga Cikin motar, kasa zama Cikin motar ya yi ya ƙwammace yabi bayan uzair komai zai faru ya faru, Buɗe motar ya yi tare da fitowa Yabi bayan Uzair Cikin sanɗa suke tafiya har suka ƙaraso gab da su, a bayan wata gabjejiyar bishiya, suka la6e suna kallon su,ɗan Jarida da kasada,


 "Nifa inaga,Yakamata mu tafi uzair"acewar Taj,

  Girgiza kai uzair yayi"Kaɗan jira muga Mai zasuyi ma shi, bari ma na ɗauki video,"yana ƙokarin zaro waya, Taj ya buge hannunshi"ashe baka da hankali, So kake hasken camera ya tona mana asiri, ba don yaso ba Ya haƙura da ɗaukar video ɗin,


Suna Cikin yin Maganar nan, Su ka ji wani irin gurnani mai matuƙar tsoratarwa, A ruɗe suka ɗago suna kallon su,


Wannan dattijon ne Ya rikiɗa nan take yazama wata irin halitta mai matuƙar tsoratarwa,Ya shiga girgiza jikinshi Yana wani irin gurnani,


Su na Cikin Maganar nan, Su ka ji yo wani irin gurnani, A ruɗe su ka ɗago suna kallon su,


Wannan dattijon ne Ya rikiɗa nan take ya zama wata halitta mai matuƙar tsoratarwa, Ya shiga girgiza jikin shi Yana wani irin gurnani,


Tashin hankalin da ba'a sama shi date, Wani irin tsoro ne ya bayyana a kan fuskokin su, Tuni zufa ta wanke su sharkaf, Don tunda Allah ya halicce su basu ta6a ganin mutun ya rikiɗa ya koma dabba ba, duk da suna Jin labarin Matsafan dake rikiɗa suna canza halittar su,


Ja da baya halittar  nan tayi, Kafin Ya daka suka, Kaitsaye Ya faɗa kan Ƴa'ƴan malamin nan, Ya shiga yagar Naman Jikin su Yana ci, malamin na kuka yana ƙoƙarin ceton ran ƴa'ƴan shi da jini Ya wanke fuskokin su, Aikuwa nan take sauran Alhazawan guda biyar dake a kewaye da su, suka rikiɗa, gaba ɗayan su ka canza halittar su, Cikin lokaci ƙanƙani su ka handame malamin nan da ya'yan shi, 


In taƙaice maku zance, Sai da Suka cinye namansu tass, Ko ƙashi basu bari ba, Tukunna Suka rikiɗa a lokaci ɗaya suka koma Mutane, Bakin kowannan su, Da6a da6a da jini,


A hanzarce bodyguards ɗinnan suka zura hannayen su Cikin aljihunan wandunansu kowannansu ya  zaro Hanky mai girma. suka shiga goge masu jinin da ya 6ata bakunan su, Bayan sun kammala suka jefar da hanky ɗin Cikin ƙoramar dake a gabansu,


Batare da 6ata lokaci ba, suka koma Cikin motocin su, a guje suka bar cikin dajin 6aaat suka 6ace,


Jikin Taj na kerma Ya kalli Uzair wanda tuni ya jima da ƙamewa a tsaye kamar saƙago, Idanuwanshi sun firfito waje tamkar zasu faɗo ƙasa,Wani irin matsanancin tsoro ne ya ziyar shi zuciyoyin su, hankalin su ya tashi matuƙa,


A ruɗe Taj ya fisgi hannun Uzair suka Koma Cikin motar su, Aka rasa wanda zaiyi driving ɗin su, tsakanin su biyu, jikinsu duk yayi sanyi ga wata uwar zufa dake tsatstsafo masu, tamkar waɗanda aka tsamo su daga cikin ruwa sun haɗa uban gumi, daƙyar Taj ya iya tada motar, ya samu ya karya kwana da wani irin speed ya fusgi motar tamkar zasu tashi sama, Duk tsoro ya kama su ga tausayin malamin nan da ƴa'ƴanshi, abun ya yi matuƙar girgiza su,


A can gida kuwa, Sam bacci ya ƙaurace wa idanuwansu, Daga angel ɗin har aneelerh, Sun yi zugudum saman Gado, kowa da abunda yake ayyanawa a ran shi, Ganin har ƙarfe 12 ta buga amma ba su dawo ba,


"Aunty aneelerh, ni tsoro nake ji kada a ce wani abu ya faru da su daddy" Janyo ta Jikinta aneelerh ta yi Tare da  shafa sumar kanta tace"in sha Allah ba a bunda zai faru da su, zasu dawo ne nan bada jimawa ba, ni inaji a raina"

 "Allah bazan ƙara bari ya tafi ya barni ba, duk inda zai je ƙafata ƙafar shi, idan ba haka ba zan sa ce tayar motor shi kowa ya rasa" aɗan shagawa6e tayi maganar, tamkar zata fashe da kuka,

  Fashewa aneelerh tayi da dariya daƙyar ta tsagaita da yin dariyar tace"Idan ki ka sa ce tayar motar shi ae yana da ƙafafu ko suma zaki guntule su ne? Kuma in banda abun ki, idan kika sa ce tayar motar shi, ae a kwai ta Uzair zasu fita a cikin ta shi ne,"

  Tur6une fuska tayi, ba halin tace zata sa ce tayar motar uzair,


 (Mu hadu a Next page don jin yadda zata kaya, amma fa last posting bakuyi likin da comment ba, idan kana bakwa yi nima zan daina ne,)

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post