Jikar Iya page 7&8 Complete

Jikar Iya page 7&8 Complete

Jikar Iya 7 & 8

🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️

      *JIKAR IYA*

🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️

   Mallakin 

     Teemerh Cool🖊️

       08161316781

Bismillahi ramanin rahim.

*Dan Allah kuyi hkr akan jiya baku samu post ba, account nane na whatsapp akayi banned nasa, kuma har yanzu basu buɗemun ba, inason kumun uziri na gode da kulawa, da wanda suka ƙirani danjin dalilin rashin post ɗin duk ina godiya da kulawa* Teemerh cool ce🖊️

*🦅MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*🦅

Page 7️⃣🆒8️⃣

_____Nan jama'ar wajen suka bisu da kallo, kowa da abun da yake saƙawa a cikin ransa, Indo kuwa ƙara fashewa ta yi da wani kuka, wanda yaja hankalin mutanen wajen, Iya ce ta hankaɗe Iya Ladi da faɗin " ai kinga ɗanki yana shirin mana sharri harda tara mutane, akan yana tuhumarmu a kan abun da bamu san dashi ba," ta ƙarashe maganar tana ɗan ƙwalla.

Duk da haka Bafada baiyi ƙasa a gwiwa ba ya ce "duk jama'a nan babu wanda ya ga abun da Ɗan Lami ya bada labari akai," nan fa mutane suka fara sun kuyar da kai wasu na faɗin"wannan sharri da mai ya yi kama, marainiyar Allah zai mata sharri, ai hakki ma bazai barsa ba" a faɗar Hadi yana ƙwalla.

Nan Indo ta zuba masa Ido ta na faɗin "ai wlh kar kaga ka faɗi haka wai zan ƙyaleka, dan wlh sai na gasa maka aya a tafin hannunka," abun da ta faɗa kenan a cikin zuciyarta.

Duk mutanen wajen sai yabon su suke yi, kowa na cewa mutanen kirki anyi musu sharri, hakanne yasa ran mai gari ya ɓaci tare da faɗin "yanzu ni zaka zo ka faɗawa labarin kanzon ƙurange" a faɗar mai gari, nan ya juya ya kalli Bafada ya ce "a yanke masa hukuncin da ya dace dashi," nan ya amsa da faɗin "anyi an gama ranka ya daɗe.

Shela ya yi akan gobe da safe za'a ayiwa Ɗan Lami bulala ɗari biyu, a ƙofar mai gari.

Jama'a dai babu mai ce uffan ciki harda Mahaifiyar Jummai Amarya, da ita ma tana tsoro ta ce uffan Indo ta ce "mata za'a saketa, dan batason abun da zai rabata da mai gari, sannan kuma ita Indo ka ce zaka ja da ita to ka janyowa ruwan dafa kanka ne.

"Tashi mu tafi" tayi maganar tana mike tare da riko hannun Indo ta na faɗin " da wanda ya bada wannan labarin da wanda ya idar, sannan da mutanen da suke tare anan suna jirar a tozartamu, duk sai Allah ya ɗeɗeta ku, sannan kuma ba zamu yafe ba, kun dunga ganin bala'i tunda kuka taɓa marainiyar Allah" tayi maganar tana kuka tare da jan hannun Indo suka yi waje.

Nan fa jama'ar wajen suka fara hawaye tare da surewa akan wani bala'ine zai tun ƙarosu yanzu.

Ita kuwa Iya Ladi cewa tayi "Allah dai yasa nawa bala'in in zai sameni ba rabani zaiyi da Malam ba" tayi maganar tana sakin kuka, nan mata wajen suka fara dubanta fa faɗin "aike da sauki yanzu, tunda kinci duniyarki da tsinke Iya," cewar Larai da shirin tashi.

"Au haka kika ce Larai bari mijinki yazo zai sameni ai".

"Iya Ladi ai kema yanzu kinsa babu abun da ya kamaceki irin istigifari, tare da neman gafarar wanda ki ka ɓatawa, sai kuma a jira ƙira daga mai sama" a faɗar Kanwar Larai.


Duk za ku yi bayani dan Uban ku, bari mazajen ku su zo.


Haka dai daƙyar Iya Ladi ta samu ta tashi, tana shiga gida ta huce ban ɗaki, zawonne yaci gaba da fito mata, tana ta kai kawo da fargaban abun da Iya ta faɗa, dan batasan ko jikar tata ta shafa mata ba, " ai kuwa inda ta shafa mata kam sai na Iya yafi zafi, tunda ita kaka ce kuma babba ce, kaga na babba abun sai yafi ci" a faɗar Iya Ladi ta na ajiye butar da ta fito a bayi, riƙe kugu tayi tana sauke ajiyar zuciya.


Indo tunda ta je gida ta saka ƙafa ta fita, dan za ta je ta samu abokanenta ayi sabon shiri.


Iya kuwa abinci ta ɗaura musu tana daga zaune ta na kunna radio, nan ta ƙara gyara zamanta tare da mai da hankalinta ga radio, sallamar da akayi ne ya dawo da hankalinta zuwa gamai sallamar.


"Ya akayi kamun sallama ka tsaya mun akai zangangan kamar wani sanda, kato kamar ka baka iya tsayawa daga wajene sai ka faɗo gidan mata" ta yi maganar tana sireshi da idanu.


"Ina wuni Hajiya Iya, Allah huci zuciyarki Tsohuwa mai ran ƙarfe," ya yi maganar yana mata dariya.


"Ta Allah ba ta ka ba, tunda raina ba'a hannuna yake ba, ja'irin yaro au kaima ka kawo kai kenan?, kaga ka fara tara gashin hammata" Iya tayi maganar tana riƙe haɓa.


"Wai ina hatsabibiyar yarinyar nan take, dan naji labarin abun da ta aikata a gidan mai gari" ya yi maganar yana zama a gefen Iya.


"La'ila'a illah daman haka munafurcin Ƴar Iya ya yi nisa, daman nasani munafurcin kune kai da uwarka ya tashi, shine ta aikoka ta kara jin karin bayani ko, to ka ƙwashi tsintsiyar ƙafarka ficemun daga gani" tayi maganar tana ƙara daga radiota tasa a kunne, tare da turo baki gaba, kamar zai faɗi kasa.


" Kuma wlh ina nan zuwa gidan zan sameta, duk sai na nuna muku iyaƙar ku" tayi maganar tana ƙara manna radio a kunnenta.


"Allah baki hakuri ba sai kinje gidanmu ba, dan bama bukatarki, dan kwanan nan muma ba'a kawo mana biredin balle kije kici" ya ƙarasa maganar cikin zolaya.


"Ubanka ma ya yi ƙaɗan ya ciyar dani ai tunda ina da Yara a burni, sannan kuma kasan yarana biyu ne acan, banda uwarka da batada rabon arziki tayi zamanta anan ƙauyen ta liƙewa Ubanku, ai da yanzu ita ma tayi aure a can" ta ƙarashe maganar tana mikewa tsaye, shima ganin kamar ran Iya ya ɓaci ne yasa shi miƙewa tsaye.


Hanyar waje tayi masa nuni da hannu tana faɗin "ga ta inda ka shigo, kazo ka tayarmun da hankalina, sannan ni zakayiwa gori, dan Ubanka ya taɓa aiko mana da wata busheshiyar buroɗi, to wlh sai na koma gidan yarana da suke birni, nida nake da Yara a Kano ta dabo tunbin giwa yaro ko damai kazo anfika" tayi maganar tana hanƙaɗasa waje, sai da takaisa ga ƙofar gidan sannan ta rufo kofar tana ta sababi.


Tana komawa ta zari mayafinta, har zata fita sai ta tuna ta ɗaura girki, dawo wa tayi taje ta buɗe abincin nan taga shin ƙafar ta kusan sosewa, dan haka ta ɗibi ruwa kusan kofi uku ta zuba aciki.


"Yauwa nasan har na dawo bazai ƙarasa ba, in girki ne kuma ai in anzo wajen mu an tashi, dan haka nakeso Indo ta tsaya ta koyi girki yadda ya dace" ta yi maganar tana jan kofarta, " koda yake ma basai ta koya ba, dan ita a birni zatayi aure, ina zuwa zan zaɓa mata wanda ya dace da ita a can, dan gidanta duk ma'aikata za'a zuba" maganar da take tayi kenan har ta manta ma inda zata yi.


"Iya ina zuwa haka da yamman nan" cewar Fatu ƙanwar Sule da yazo gidanta.


Fashewa tayi da kuka tare da ƙara mayafinta akan fuskarta, tana share ƙwallan karya.


" Iya daga tambaya sai kuka, mai ya faru" Fatu tayi mata tambayar.


"Ƴar nan daman gidanku zanje tsaɓar ɓacin rai yasa na manta gidan, gaba zamuyi ko baya?" Iya ta jefawa Fatu tambayar.


Suna zuwa daidai gidan Iya ta ɓaɗa dan ta riga Fatu ma shiga gidan tare da fashewa da matsanci kuka, kai ka ce Indo ce ta mutu.


Jin kukan Iya kowa ya fito daga ɗaki, duk sunyi carko carko dan jiran jin mai ya faru.


"Iya mai ya faru? ko mutuwa a kayi ne?" cewar Ƴar Iya.


"Ai gwara ma ace Mutuwa akayi akan wannan bakin cikin, kamar ni yau za'aci mutuncina, kuma wai jikana" ta kara sakin wani kuka wanda kowa ya kasa gane mai take nufi.


"Iya ki mana bayani dan Bamusan mai kike nufi ba" Ƴar Iya ta jefa mata tambayar.


"A she ke Ƴar Iya har yanzu baki bar wannan ɗaki kancin ki ba, daman haka duk cikin yara na kece mara ganewa, kullum Malam yana magana akan asarar kuɗin da yake biya na maƙarantarki, amma gashi har yanzu daƙi kancin bai ƙyale ki ba, ko da ɗiwawu kike jin magana ne, bakiji abun da na faɗa ba" Iya ta ƙarashe maganar tana neman waje ta zauna, ita kuwa Ƴar Iya kamar ta buɗe ƙasa ta shiga tsabar kunya, da yadda Iya ta kunyata ta a gaban Yaranta harda jikarta ɗaya.......
Wannan littafin na kuɗi ne, ki biya kuɗinki ki karanta shine mutuncinki, ban yadda a fitar mun da littafi ba dan kin siya, duk wata mace mai aji bazata karanta littafin sata ba, ki mallaki naki akan naira 300 kacal post kwana biyar a sati, special 500 post kullum , 9048703453 Fatima Muhammad Aliyu opay bank sai ki turo shedar biyan kuɗinki ta wannan number 08161316781, in kuma kati ne MTN,  AIRTEL,9MOBILE, duk ina using dashi, sai a turo hoton Katin, na gode sosai.


TEEMERH COOL🖊

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post