💋KURKUKUN ƘADDARA💋
E38
By boss Bature writer of Abban sojoji❤
"Dake nake magana" muryar haris ce ta kuma katse ta, batare data amsa mashi ba, ta yunƙura ta miƙe ta nufi gadonta, tana isa ta haye sama ta kwanta, koda suka haɗa ido da danish dake kishingiɗe saman gadon shi, harara ta watsa mashi, kafin ta juya mashi baya, lumshe idanuwanshi yayi, zuciyarshi duk ba daɗi, saboda ya gane dalilin dayasa ta harare shi, dole taji haushin shi, saboda rashin ta6uka komai, shi kuma aganinshi indai baida maganin abu to baida amfani ya tsoma baki, shiyasa yake yin shiru, Amma har ga Allah yana matuƙar damuwa dasu, Yana jin tausayin ƴan uwanshi, Yana matuƙar ƙaunarsu fiye da kan shi,
Rabi da kwatarsu tuni bacci Ya yi awon gaba dasu, mutun uku ne suka rage, Haris da tuni ya jima da komawa saman gadonshi, damuwar halin da deeja ke aciki ce ta hana shi runtsawa, Sai kuma Parveen da Yunwa ta addabe ta, ta lafe kwance saman gadonta sai juyi take yi, bayan ita kuma sai Angel wadda babu alamun zata runtsa, ita fa babban abunda ke damunta, irin takurawa rayuwarsu da ake yi, da kuma cutar dasu da ake yi, tana matuƙar jin tsoran tarasa wani acikinsu, tabbas zata ji raɗaɗin da yafi wanda taji a lokacin da ƙaddara ta rabata da daddynta, a yanzu tafi jinsu acikin zuciyarta fiye da kowa ma nata, yanzu bakomai yafi tsaya mata arai ba, face mutun shiddan nan da Deeja ta faɗa mata cewa ta gansu akanta, Shin su wanene su? Uban me suka aikata mata? Kodai su duka suka afka mata a lokaci ɗaya suka lalata rayuwarta? Innallahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma Ajirni fil musibati...... wani irin ɗaci take ji acikin zuciyarta, idanuwanta suka cuccuko tab da ƙwalla, ta tausaya ma rayuwarsu, Idan har suka cigaba da kasancewa acikin kurkukun nan tabbas kuwa wata rana za'a nemi koda gawawwakinsu ne arasa, Ita dai bata fatan tarasa ranta acikinsa, kodan saboda ta gano su wanene suka assasa ƙungiyar da kuma waɗanda suka sadaukar dasu, Wannan alƙawarine ta ɗaukarwa kanta, sai sun ɗanɗani kuɗarsu, sai sunyi danasanin haihuwarsu da uwarsu ta yi acikin duniyar nan!!! Acikin zancen zucin da take yi, kwata kwata bata sanya tsohuwa aciki ba, duk da itama taji haushin abunda tayi mata ayau, amma ta ajiyeta gefe ɗaya, saboda ba ita bace agabanta, masu ƙungiyar kurkukun ƙaddara sune agabanta, da kuma waɗanda suka yi sacrificing ɗinsu.
Lokacin da giants suka shigo kawo musu abinci, Mutun ɗaya ce ta Iya miƙewa, har zata tada su daga bacci, Haris yace ta ƙyalesu, taje ƙarƙashin gadon batool ta ɗauko kwandon da suke ajiye abinci, ta kwaso musu aciki, idan suka farka zasu Ci, ta amsa mashi da toh, Bayan ta ɗauko food basket ɗin taje gaban jerin farantan da giants suka sauke musu, Ta zuƙunna ta ajiye kwandon gefe, ta sanya hannu ta yaye jan ƙyallen dake akan farantin farko, Steak and onions ne, Yankan nama manya manya sunji albasa da kayan ƙamshi, Hannu tasa ta dinga ɗebowa tana zubawa cikin kwandon, duka ta kwashe, Ta kuma buɗe faranti na biyu dake ɗauke da Snacks tare da madaidaicin bowl Na kayan marmari ta kwashe komai ta ɗaura akan naman, Faranti na ƙarshe Bottles waters ne, Miƙewa tayi tare da sanya hannu biyu ta ɗauke kwandon, Yayi nauyi, A agaban gadonta ta ajiye shi, ta koma domin kwaso robobin ruwa, dake a jere saman faranti na ƙarshe, Ta ruƙo su a hannayenta, Bayan ta kammala giants dake a tsaye suka raƙwafa atare suka ɗauke farantan, Tare da kama hanya suka fuce daga Cikin ɗakin, Zama parveen tayi agaban gadonta, ta ɗago ta kalli haris dake kallonta tace"Ba yanzu zaka Ci ba? Yana daga kwance saman gadonshi, Yace mata"sai sun farka zai ci" tace"Nima in jira sai sun farka"? Ba don taso ba ta faɗi hakan, Girgiza mata kai yai alamar a'a kafin yace"zaki iya ci mana, kici iya cinki, sauran da kika rage sai muci, ae nasan duk haɗamarki ba zaki iya lamushe abincin duka ba, ko rabi ma ba zaki iya tadawa ba" murmushine ya bayyana akan fuskar Parveen, jin abunda yace, bata ƙara tanka mashi ba, takai hannu tana zakulo naman tana turawa abaki, Sai da taci iya cinta, ta haɗa da snacks ɗin duka, har saida cikinta yayi ƙato, tukunna ta dakata da ci tana faman shafa ciki, bottle water ta ɗauka ta buɗe tasha ruwan, Data kammala ta tura kwandon ƙarƙashin gadonta, Haris yace"Salon da anjima idan kinga muna cin namu, kice kema zaki ci," dariya ta ɗanyi har dimple ɗinta na saman chin ɗinta ya lotsa, komawa saman gadonta ta yi tare da hayewa, da niyar itama ta samu baccin ya ɗauke ta,
Basu suka tashi farkawa ba, sai da suka kwashe tsawon awanni suna bacci, daga bisani yunwa ta fara farkar dasu, ɗaya bayan ɗaya, kowa ya miƙe yana hamma, Haris yace suje su wanko bakinsu suzo suci abinci, Suka amsa mashi da toh, Kowa ya nufi toilet, bayan sun kammala wanke fuskokin suka zo suka zazzauna ya dauko musu kwandon abincin dake a karkashin gadon parveen, Ya ajiye musu atsakiyarsu, ba yadda baiyi da angel ba akan tazo taci abinci amma taƙiya saima ce mashi tayi ita bata jin yunwa su dai su ci, Komawa yayi bakin gadon danish a lokacin ya ɗan fara bacci, ya tada shi tare da cewa" ka taso mu ci abinci," danish yace"suje su ci baijin yunwa" lamarin yai mutuƙar ɗaurewa haris kai, su biyu sunce basu jin yunwa, Anya kuwa lafiya? Ko dai duk don saboda rashin lafiyar deeja ne yasa suka ƙi Cin abinci? A ƙarshe daya gaji dayi musu magana akan su taso sai ya ƙyale su, ya koma wurin dasu batool suke a zazzaune shima ya zauna, Suka tsoma hannayansu suna Cin abincin, Ba duka suka cinye ba, Sai da yace su rage ma Deeja idan ta farka, Sai kuma Angel da danish, Yankan nama shida shida suka ajiye ma kowannan su, Sai fruits, banda snacks duka suka cinye shi, Sun dai ajiye musu bottle water Biyu, bayan sun kammala suka ajiye musu nasu a karkashin gadon batool,
Wuraren marece, Deeja ta farka muryar ta a disashe take faɗin, Ruwa zata sha, ƙishi take ji, da sauri haris Yaje ya ɗauko robar ruwa cikin wanda suka ajiye musu, Ya koma gefen gadonta ya zauna yana kallonta a lokacin ta yaye bargunan da suka lullu6a mata, daƙyar ta yunƙura ta miƙe zaune ta ɗan jingina bayanta jikin bango, Yadda kasan fatalwa, tayi haske ga rama, ƙashin wuyanta duk ya fito 6aro 6aro jikin fatarta, Gashin kanta kuwa duk ya hargitse, Baiwar Allah daga gani ba ƙaramin Jiki taji ba.
"Sannu deeja ya jikin naki" ya yi maganar tare da buɗe murfin robar ruwan ya kwafa mata baki, Hannu bibbiyu tasa ta tallabe hannanyenshi dake a ruƙe da robar, saboda tsabar yadda take shan ruwa kana Iya jin sautin throat ɗinta kwat kwat! Har sai da yace mata tasha a hankali kada ta shaƙe, janye robar ta yi da hannunta alamar ta ƙoshi, Sai lokacin ta samu damar ƙare mashi kallo, su batool dake a zazzaune saman gadajensu suna yin fira, Ganin deeja ta farka yasa suka dawo bakin gadonta, wasu suka zauna wasu kuma suka tsaya atsaye, A hankali take binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, Ba ƙaramin daɗi taji ba, irin yadda suka nuna mata kulawa, sai dai a yayin da take kallonsu, wani irin tausayin kansu ne ya kamata, domin kuwa tasan ƙarshen su yana dab da zuwa, a yanzu bakowa tafi jimawa ba face waɗanda ba'a ta6a ɗauka acikinsu ba, musamman azeeza da tafi kowa rauni acikinsu, gata ƴar ƙarama duk da ba shekaru suka fita ba, amma babu alamun girma atattare da ita, saboda rashin tsawonta, idan suka miƙe tsaye ko kafaɗarsu bata kai ba, farat ɗaya ka kalleta sai ka yi hasashen shekararta Goma, saboda ƙarantar jikinta,
tana Cikin yin zancen zucin nan muryar batool ta katse ta da cewa"deeja me kike tunani muna ta yi maki magana tun ɗazu amma kin yi shiru baki ce komai ba, ina fata kina lapiya," ajiyar zuciya ta ɗan sauke, still idonta na akan azeeza data zauna gefen gadonta ita dasu Yasmin, haɗa baki suka yi wurin yi mata ya jiki ta amsa musu da cewa"Alhamdulillah Jiki da sauƙi, Naji daɗi sosai da irin kulawar da kuka bani, Ina matuƙar alfahari da ku ƴan uwana nakaina" Murmushi suka saki gaba ɗayansu, ta mayar da idonta kan haris dake kallonta, ta lura da irin damuwar da ya yi akanta,
"Lokacin da aka tafi dani, haris ya iya Cin abinci kuwa"? da zolaya tayi maganar, gaba ɗaya suka yi dariya, yasmin tace"ae tunda aka ɗauke ki, ya gaza samun natsuwa, idan ya kwanta saman gadonshi idanuwanshi na fuskantar ceilling sai ya ɗauki tsawon lokaci bai tashi ba, wata'ƙil hoton fuskarki yake gani" Harara haris ya watsa ma yasmin da tayi maganar,
Kafin yace "Abunda ta faɗa ba ƙarya bane, Na damu dake sosai, Ko bacci nake yi sai nayi mafarkin ki, Bani kaɗai ba Kowa ya damu dake" duƙar dakai deeja ta yi hawaye suka cicciko idanuwanta, muryar azeeza ce ta ratsa kunnan ta"Sister deeja pls don't cry, muna cikin farin cikin samun sauƙin ki, kada ki karya mana zuciyoyin mu," azeeza na rufe baki, deeja ta karasa kifa kanta saman gwiwowin ƙafarta, sosai ta fashe da kuka, Sai faman lallashinta suke yi, ita bakomai ne yafi damunta ba, face tuna cewa wata rana fa dole wani ya mutu a cikin su, gashi sun shaƙu da juna, Allah kaɗai yasan raɗaɗin da zasu ji aranar da suka rasa wani acikin su,
Haris ne yace dasu"kubarta ta huta, kowa yaje yayi wanka, zan kula da ita" kasa tafiya suka yi har saida ya maimaita musu maganar tukunna suka miƙe, azeeza hada bubbuga ƙafarta tana faɗin"wai shi yacika takura, yana ganin kamar yafi kowa girma, shine zai wani kore su" murmushi haris ya saki batare da ya mayar mata da martanin ba, bayan sun bar bakin gadon deeja, suka nufi toilets domin yin wanka, hannunshi ɗaya ya ɗaura asaman bayan deeja yana ɗan bubbuga shi cikin sigar lallashi yake yi mata magana"its ok my lovely sis, kukan ya isa haka, ki daina pls kina ƙara ma kanki ciwo, kuma kina sanya mu cikin damuwa" Sai lokacin deeja ta ɗago da idanuwanta sunyi jawur da su, yadda kasan na mashayin giya, kallon shi kawai take yi kamar yarda shima yake kallonta, matsawa yaɗan yi dab da ita, ya sanya hannunshi ya ruƙo arm ɗinta tare da janyo da ita, ta kwanto saman kafaɗarshi, lallashinta yaci gaba da yi har saida ta daina yin kukan, Cikin sanyin murya tace"Danish baizo ya duba jiki na ba, naga fuskar kowa amma banda tashi, meyasa"? Girgiza kai haris ya ɗanyi dama saida ranshi ya bashi cewar saita yi magana akan danish, Yaji haushi da takaicin irin halin ko'in kulan da danish yake nuna musu, duk da yasan yana yi badan baya ƙaunarsu ba ne, Amma aduk lokacin da basu jin daɗi zaiyi wuya yaja su ajiki, har ƙwara Azeeza, itama ɗin ya lura don yana mata kallon ƙaramar halitta ne shiyasa yake damuwa da ita sosai, muryar deeja ce ta kuma katse shi"haris naji ka yi shiru? Ko dai danish bai yi farin ciki da dawowata ba ne?"da sauri yace"A'a, Ke ce baki ganshi ba, danish ya damu dake, ko adaren jiya da angel tazo tada mu daga bacci, hada shi muka shigo cikin toilet ɗin," Deeja tace"Amma shi bai jani ajiki ba, kamar yadda kayi" runtse ido haris ya ɗanyi kafin ya buɗesu a hankali yace"ki yi haƙuri yanzu bacci yake yi, amma ina da tabbacin zuwa anjima idan ya farka zaizo da kanshi ya duba jikin ƴar uwarshi" ta6e baki ta ɗanyi tare da cewa"da kamar wuya" ruƙe hannunta haris yai acikin nashi yace"Akwai steak da muka ajiye maku tare da fruits in ɗauko maki ki ci" yayi mata maganar ne don ya kawar mata da zancen danish, ɗago da kanta ta ɗanyi daga saman kafaɗarshi tace"Anya zan iya ci, baki na babu daɗi, amma ina jin yunwa aciki na"
"Don't worry ur self xan taimaka maki ki ci shi" yakai karshen maganar, tare da miƙewa daga saman gadonta, Ya juya ya nufi gadon batool dake gefen na Danish, yana kwance sai baccin shi yake sha hankali kwance, guntun tsoki haris yaja ji yake kamar yaje saman gadonshi ya shaƙon wuyanshi, Bayan ya ɗauko kwandon ƙarƙarshen gadon batool, Ya juya ya koma gefen gadon deeja, a tsakankaninsu ya ɗaura basket ɗin, Deeja sai kallon shi take yi don ba ƙaramin burgeta yake yi ba, saboda irin yarda yake nuna damuwarshi akanta,
"Angel ta yi bacci ne"? Yace"I don't think so, Kinsan jiya ranta ya 6aci sosai, saboda tsohuwa tace bazata duba lafiyar jikin ki ba, har sai ta durƙusa agabanta ta roƙe ta, Inaga shiyasa ta lafe saman gado ta rufe ido, amma ba bacci take yi ba" juyawa deeja tayi tare da kallon gadon danish dana angel, duk suna kwance abunsu, kafin ta juyo da kanta tana fuskantar haris dake miƙo mata yankan Nama, buɗe baki tayi ya tura mata aciki, tasa hannu ta dafe tana Ci, sai da ta kammala taunewa tace"Haris, naji daɗin abunda angel tayi saboda Ni, farkon zuwanta prison din nan, Nayi tsammanin bata ƙaunata, duk da a lokacin Mune muka fara nuna mata ƙiyayya, Amma yanzu na gane kuskure na, domin kuwa angel tana matuƙar son mu sosai, kuma ita ɗin Alkhairi ce agare mu," jinjina kai haris ya ɗanyi, tare da cewa"Nima na fahimci hakan, yanzu dai ki maida hankali ki ƙarasa cinye naman kisha fruit ɗin sai ki kwanta, ki ƙara hutawa" murmushi tasakar mashi, shima ya mayar mata da martani, A tsanake yaci gaba da bata Naman tana ci, bayan ta kammala tasha fruit ɗin ta kwanta saman mattress ɗin, Ya lullu6a mata bargo ajikinta, baisan ya zai ƙare dasu angel ba idan suka farka suna Jin yunwa, ganin deeja tana Ci yasa ya ƙara yankan nama Shida Cikin nasu Ya haɗa mata, kuma duka ta cinye shi, wanda ya rage acikin kwandon yanka shida ne na mutun ɗaya sai dai su raba uku uku ita da danish, Sai apple guda ɗaya, ayaba biyu, ɗauke basket ɗin yae daga saman gadon deeja, Yaje ya tura shi ƙarƙashin gadon batool, A lokacin duk sun fito daga wanka, ba ƙaramin daɗin jikinsu suka Ji ba, a tsakiyar ɗakin nasu suka hallara, Hannah ce ta shirya musu wasan da zasu Yi,
Angel dake kwance sautin hayaniyarsu duk ya cika mata kunnuwanta, pillow ta sanya saman kanta ta toshe kunnuwanta, Ƙasa ƙasa take jin hayaniyar ta ɗan ragu, wani irin baccine yayi awon gaba da ita batare da ta shirya yin shi ba, su batool sunsha wasansu, har sai da dare yayi hasken ɗakin ya ɗauke sannan kowa ya koma saman gadonshi ya kwanta,
Batare da sun kunna fitilun ɗakinsu ba, yayi duhu sosai, Har time ɗin bacci bai ɗauke su ba, fira suka soma yi a tsakaninsu kowa yana daga kwance saman gadon shi, Batool ce ta fara cewa"kun lura da angel duk yinin yau bata sauko daga saman gadonta ba" Haris yace"Kije ki tada ta mana" muryarta ƙasa ƙasa tace"So kake in jama kaina, ae tun ɗazu naso inje in lallashe ta, amma fargaba ta hana ni, kasan halinta, zata iya sauke fushinta akaina"Hanna tace"nima abunda ya hanani tunkararta kenan, kada in sha mari" Gaba ɗaya suka tuntsire da dariya, Javed yace"gaskiya banji daɗin abunda tsohuwa ta sanyata tayi ba, kawai don ba yadda zamuyi ne shiyasa muka tursasa mata akan ta durƙusa mata" Haris yace"nifa Haushin tsohuwa nake ji, don me zata ce dole sai angel ta durƙusa mata tukunna zata duba lafiyar deejan mu? Kenan koda ace mutuwa za ta yi bata iya duba ta ba, in har angel bata bi umarnin taba, sai dai tarasa ranta?Anya kuwa tsohuwa tana son mu? Eve tace"nima nafara kokwanto akanta, ae bata ƙaunar mu, shiyasa ran nan naƙi gaishe da ita," eve na rufe baki hibba tace"kuma hada cewa wai angel ce babar mu, baku ji me tace ba ɗazu ba da muna a wurin toilets, " waɗanda basu sani ba, suka tambayeta me tsohuwa tace, Nan hibba ta kwashe maganganun da su ka yi da ita, ta sanar musu, aikuwa sunsha dariya, batool tace"oh shiyasa naji tace aje akira babar mu tazo ta ɗauki ƴar ta, tsohuwa ta iya zolaya, gashi yau ta fusata mana Mamanmu,' rubina tace"Abunda ta faɗa gaskiya ne, angel itace babar mu, saboda tafi kowa damuwa da mu, bazan ta6a manta irin wahalar da ku kasha ba, ita dake batool wurin yin jinyarmu lokacin da giants suka dawo damu, kun nuna mana ƙauna, muna matuƙar alfahari daku,' azeeza tace"Da Batool da angel sune zasu zama iyayen mu idan muka fita daga Cikin prison ɗin nan, zasu bamu kyakkyawar kulawa" eve tace"Nifa ina tsoran ranar da zamu fita, mutanan dake awajen kurkukun nan zasu Iya su cutar damu, ko su kashe mu ma," parveen tace"waya faɗa maki? Ba angel tace mana gidan daddynta zamu zauna ba, ina ruwan mu da wasu mutane, ae ba akansu zamu zauna ba, dangin angel ne zasu taimake mu"da ƙwarin gwiwa parveen tayi maganar, Haris dai sai dariya yake yi musu, jin irin wasiƙar jakin da suke saƙawa, wadda bazata ta6a zama gaskiya ba, azeeza tace"Na ƙosa Allah, zamu ji daɗin rayuwar mu, kowa zai sakata ya wala, muje inda muke so, ni dai kawai burina inga ga gidansu angel da kuma daddynta,"
"Amma fa ita kanta angel ɗin bata da tabbacin cewa daddyn nata yana araye koya mutu," acewar Batool, azeeza tace"Ae ko baya araye akwai auntynta aneelerh, da mommynta adama tace duk danginta ne kuma zasu ɗaukin nauyin ɗawainiya damu" sai lokacin javed ya tsoma baki, muryarshi da alamun bacci yace"pls, surutun ya isa haka, kun takura mana, dare fa yayi sosai, yakamata kowa yaja baki yayi shiru ku kwanta ku yi bacci, kun zauna kuna ta tsara shirme da shiririta, kuda fita daga Cikin kurkukun nan sai dai ata mafarki, amma badai zahiri ba" a ƙule ya ƙarasa maganar, shi kanshi javed ɗin da yayi maganar ba ƙaramin buri yake dashi ba akan su fita, kawai dai baison suna ƙwallafa rai ne, tun da babu ƙopar da zasu Iya guduwa acikin kurkukun, tun da javed yai musu magana babu wanda ya kuma cewa wani abu, tuni bacci ya fara ɗaukarsu, mutun ɗaya ce bata runtsa ba, Jira take suyi nisa dayin bacci ko ta samu ta lalla6a taje ƙarƙashin gadon batool ta ɗauko Yankan naman da aka ajiye masu danish ta cinye, dama ta ƙware wurin iya satar ragowar abinci,
lokacin da parveen ta tabbatar da cewar sun nutsa Cikin baccin su, Cikin sanɗa ta sauko daga saman gadonta, duk da duhun dake akwai hakan bai hanata gano inda gadon batool ya ke ba, daga gefen gadon ta zaƙunna tare da zura hannu cikin ƙarƙashin gadon ta janyo kwandon, har wani lumshe idanuwanta take yi tana shaƙar ƙamshin naman, tana yunƙurin tsoma hannu da niyar ta ɗauki tsoka ɗaya, kwatsam taji an damƙi wuyan rigarta ta baya, A matuƙar tsorace ta wage baki zata fasa ƙara, yayi saurin sanya tafin hannunshi ya toshe mata baki, ta yadda bazata iya yin ihun ba, Saboda tsabar tsoratar da tayi har saida ƴan hanjin Cikinta suka kaɗa, Jikinta sai kerma yake yi, shegen tsoro ne da ita, duk a tunaninta ɗaya daga Cikin aljanun da tsohuwa ta basu labarin akwaisu agidan kurkukun ne yazo ya damƙeta, zazzaro idanuwanta tayi waje, jikinta ya ɗau zafi,
Cool voice ɗinshi ce ta ratsa kunnanta"its me, me kike yi agaban gadon batool? Ko kinzo ne ki sace mana steak ɗin mu da aka ajiye mana ne? wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke jin muryar danish, Ta harzuƙa sosai ashe shine ya firgitar da ita, tayi matuƙar yin mamakin taya akai ya iya ganinta Cikin duhu? Kuma har yasan cewa tazo satar naman da aka ajiye musu ne, bayan basu da masaniyar sun ajiye musu,
"Am talking to u, ki amsa mini, dama har yanzu baki daina bin abincin mutane kina satar musu ba"? Yawu ta haɗiya, tare da sanya hannayenta ta zame mashi hannunshi daya toshe mata baki dashi" ta juyo tana fuskantar inda yake atsaye, duhu ya hana ta ganshi dakyau,
Muryarta kamar zata fashe da kuka tace"Ae zuwa nayi inga idan ya lalace, in zubda, tunda naga tun ɗazu da safe aka ajiye maku amma baku ci ba" muryarshi asake yace"A cikin Cikin ki zaki zubda shi ko?" shiru tayi bata bashi amsa mishi ba,
"Maza ki wuce kije ki kwanta, tunkafin in yi wurgi dake" tana ƙunƙuni ta juya tana laluban hanya harta gano gadonta ta haye ta kwanta, zuciyarta duk ajagule, taso ace tacinye naman duka, ita uwar haɗama, kuma ba yunwa take ji ba,
Bayan tafiyar parveen, danish ya duƙa inda ta ajiye kwandon, yana ƙoƙarin ruƙe handle ɗin yaji an damƙi hannunshi, har sai da ya ɗan ji bugun zuciya, duk da bai iya gane wacece ba, amma yaji aikin shi cewa ANGEL ce, itama parveen ɗazu daya Canko sunanta, saboda yasan halinta ne, Ya farka yana Jin yunwa, ɗazu yaji haris yana cewa arage musu nasu naman shiyasa ya yi tunanin akwai saura, wannan dalilin ne yasa shi saukowa daga saman gadon shi, ya nufi gadon batool donya duba yaga idan an rage musu nasu, Yana tunkaro bakin gadon yaji motsin mutun, nan take ranshi ya bashi cewar itace, dama halinta ne,
Kusan atare zuciyoyinsu ke bugawa, gashi dai basu ganin juna dakyau, saboda duhun da ya mamaye idanuwansu, muryarshi na ɗan rawa ya ambaci sunanta"Angel" Muryarta a kausashe tace"Ni ce, sai me? Idan ma yankan naman nan kazo ka ɗauka sai dai ka haƙura kabar mini saboda nafi ka jin yunwa " yadda tai maganar babu sassauci, dagaske yunwa take ji sosai, kamar ta cinye ƴan hanjin Cikinta, shima kuma yunwar yake ji, cikin sanyin murya yace"me zai hana mu ci atare, sai mu raba" kamar tana ganin shi tace"A'a, kawai dai ka haƙura kabar mini, saboda ba isata zaiyi ba"
(Mu haɗu Next page in Allah yakai mu da rai da lafiya, Waɗanda suke da ra'ayin Cigaba da karanta littafin part two, Su yi mini magana ta account ɗina, hada wanda ke da ƙaramar waya, akwai group na facebook da za'a sanyasu in suka biya)