Kurkukun Ƙaddara page 39

Kurkukun Ƙaddara page 39

Kurkukun Ƙaddara

 💋KURKUKUN ƘADDARA💋


39


Daga alƙamin Boss Bature writer Abban Sojoji❤


A heart touching story of prisoners💔


"but why ɗazu baki ci ba? Da haris ya yi maki magana"? A harzuƙe tace"Saboda bana jin yunwa a lokacin yanzu kuma ina jinta, meyasa ma ka tambayeni? bata jira yabata amsa ba, ta kuma cewa"To kai meya hana ka cin naman ɗazu"? Tayi tambayar tana jiran jin amsarshi, sai da ya ɗanyi jim before yace"saboda ke, na damu da halin da kika shiga, naji kince ba zaki ci abinci ba, shiyasa nima naƙi ci, saboda bana so ki ji yunwar ke kaɗai," sam bata ji ɗaɗin maganarshi ba, saima haushin shi data ƙara ji, muryarta ƙasa ƙasa tace"Nifa baka burgeni komai zaka Yi, ko son ganinka ma bana yi, wlh haushinka nake ji kamar in nannaushi fuskarka, ka 6ata mini rai sosai, Kana nuna ka damu dani wannan duk abanza ne, tun da baka iya nuna damuwarka akan deeja, da aka dawo da ita daren jiya, kowa yana tofa albarkacin bakinsa amma kai kaja baki kayi shiru amatsayinka na babba acikin mu, har haris ma yafi ka sanin yakamata," Tana kai ƙarshen maganar, ta fusge kwandon daga hannunshi ta miƙe, cikin duhu ta nufi table dinsu ta ɗauko fitila ɗaya ta kunnata, A saman dining Carpet ta zauna, Ta ajiye kwandon agabanta, ita kuma fitilar ta ajiyeta a gefe, Zuciyarta duk ba daɗi, ita kanta bada son ranta take gaya mashi magana ba, daurewa kawai take yi,


Daga inda yake a zuƙunne bakin gadon batool yana hangenta, jikin shi yayi mugun yin sanyi, duk sai yaji ya rasa kuzarinshi, tamkar ya fashe da kuka haka yake ji, baya son angel tana yin fushi da shi, hatta faɗan da take yi mashi baya so, dan ba yadda zai da ita ne, kasa jurewa yai ya yunƙura ya miƙe ya nufi saman dining carpet ɗin, Yana ƙarasawa ya zauna tare da lanƙwashe ƙafafuwanshi Yayi zaman cin tuwo kamar yadda tayi, Ya kasance suna fuskantar juna ita dashi, Ko kallo bai ishe ta ba, bakinta acunkushe da yankar naman data tura sai tauna take yi, duk in suka haɗa ido saita jefa mashi harara, bawan Allah miyan sai tsinkewa yake yi, 


yana so ya ɗauki naman yaci, sai dai ya kasa saboda gudun faɗan ta, Muryarshi arauna ce yace"pls angel, ki bari na ɗauka naci nima, koda fruit ɗinne, am serious yunwa nake ji" sai da ta kammala taunar naman dake abakinta tukunna tace"baka da ƙarfin da zaka ƙwata ne? Wai kai wani irin namiji ne? Mace kake marairaice ma fuska? duƙar da idanuwanshi ƙasa ya yi batare daya tanka mata ba, dogon tsoki taja, takai hannu ta ƙara ɗaukar yankan naman ta tura abaki tana ci, Sai da ya rage saura  biyu, tace mashi"in kaga dama ka ɗauka kaci," tayi maganar tana daukar fruits din ciki tana sha" muryarshi na rawa yace"bazan ci ba, saboda me zaki dinga yi mini faɗa? Nifa haka rayuwata take, ki ƙyale ni mana, bana jin daɗin yadda kike kushe ni," Ranshi amatuƙar 6ace ya miƙe, Ya juya ya nufi gadonshi ya haye ya kwanta, 


Sai bayan daya tafi, Jikinta yayi sanyi, daƙyar ta iya shan fruits ɗin, idanuwanta suka Cicciko tab kwalla,  yunƙura ta yi tare da miƙewa ta ɗan ranƙwafa ta ɗauki fitilar ahannu ɗaya, yayin da ɗayan hannun kuma ta ruƙe handle na kwandon, wurin gadon shi ta nufa, daga gefe ta ajiye fitilar tare da kwandon, idanuwanta na akan gefen fuskarshi, ya ƙanƙame pillow aƙirjinshi, jikin shi har wani kerma yake yi saboda tsabar 6acin ran da yake ciki, Zuciyarta ce ta dinga tunzurata akan kada ta kuskura tace zata lallashe shi ta ƙyale shi wata'kil yayi hankali, gani take ma idan taci gaba da lallashin shi zai ƙara lalacewa ne, ƙwara ta koya mishi hankali, jinjina kai ta ɗanyi alamar gamsuwa da shawarar da zuciyarta ta bata,


  "Idan kaga dama ka tashi ka ɗauki naman kaci, idan kuma baka ci ba, matsalarka ce" Takarasa maganar tare da watsa hannayenta, Irin bata damu din nan ba, wuce wa tayi zawa gaban table ta ƙara ɗauko wata fitilar ta kunna ta, kaitsaye ta nufi gadon deeja, domin ta yi mata yaji ƙi, tun ɗazu da safe take ta son taje wurinta amma damuwa ta hanata, zuciyarta tayi mata nauyi a ƙirjinta, shiyasa ta tagaza tashi daga saman gadon ta yi kwanciyarta,


Daga gefen gadon deeja ta zauna, tana haska fuskarta da fitilar hannunta, da alama tayi nisa acikin baccinta, har cikin zuciyarta taji daɗin yadda deeja ta samu sauƙi, don jiyan nan zuciyarta ba ƙaramar karaya tayi ba, harta fara fidda ran da zata rayu, sai gashi Allah ya taimake su, deeja ta wartsake, a hankali ta ɗaura yatsun hannunta saman fuskar deeja ta ɗan shafata, kafin ta soma karanto addu'o'i tana tottofa mata, 


  "Bazan tashe ki daga bacci ba My lovely sis, gobe in sha Allah, idan kika farka daga bacci zanzo in yi maki ya jiki, Allah ya ƙara maki Lafiya, "  janye hannunta tayi daga kan fuskar deeja ta mayar dashi saman sumar kanta, dake a hargitse duk ta yamutse babu gyara, aranta ta ayyana cewa, idan deeja ta samu lafiya sosai jikinta yae kyau zata gyara mata gashin kanta, ta kuma yi mata kalaba, kalar tasu azeeza, sauƙin ma ita gashin nata bai kai nasu tsayi da yawa ba, ya dai sauko har saman kafaɗarta, baƙi wulik, kamar na ɗiyar roba, Ta jima zaune tana kallon deeja, daga bisani ta miƙe hannunta ruƙe da fitilar tabi gadon kowannan su ta tottofesu da addu'o'i,  lokacin da ta dawo zata wuce gadonta, Sai da ta saci kallon shimfiɗar danish, Still bai ɗauki naman shi yaci ba, duk sai taji ba daɗi, Duk yinin yau baici komai ba, ko ruwa bata tunanin  yasha mutun sai kace aljani, anya kuwa zata biye mashi, kodai taje ta lallashe shi ya tashi yaci?


A ƙasan gadonta ta ajiye fitilar hannunta, wurin ya ɗanyi haske hada ƙarin ɗayar fitilar dake a kusa da gadon danish,


daga Gefen gadonta ta zauna tana kallon bayanshi, still babu alamun yayi bacci, yatsun ƙafarshi basu daina yin kerma ba, Zuciyar imani ce ta zo mata,  ta miƙe taku ɗaya biyu, ta zuƙunna abankin gadon shi, Cikin sanyin murya ta ambaci sunanshi"Danish" shiru bai amsa mata ba, 


   "Fushi kake yi da ni, saboda kawai na faɗi gaskiya," ta ɗanyi maganar tana hararar bayanshi,


   "Its ok komai ya wuce, bazan ƙara ba, pls ka tashi ka ci naman nan kasha fruit din idan ma baka Iya Ci da hannunka sai in baka abaki, ba wani abu bane, ni kawai bana so ne ka kwana da yunwa, dama ka faɗa mini cewa saboda ni ne baka Ci abinci ba, To yanzu ni naci kaima saika tashi kaci, ko ba haka ba My man"? Bakinta ƙumshe da dariya tayi maganar, babu alamun zai tanka mata, 


Cikin zolaya tace"dama ance mutun mai haƙuri bai iya zuciya ba, yau na tabbatar da hakan, danish yayi fushi da angelar shi," babu irin lallashin da bata yi mashi ba, amma yaƙi tanka mata a ƙarshe ranta ya 6aci a fusace tace"Kai ni fa ko daddyna bana zama in lallashe shi kamar yadda nake yi maka, don ma ka samu ina kula ka shine kake wani shamin ƙamshi, to shikenan, Nasan me zanyi, Zanje ne kawai in dura tagar nan ta cikin toilet, kome zai faru ya faru, " tana kai ƙarshen maganar, ta miƙe da sauri ta ɗauki fitilar dage ƙasa gefen gadonshi, Ta nufi sashen makewayinsu har ta kusa kaiwa bakin ƙopar shiga, Kamar walƙiya taganshi agabanta tsaye yana faman lumshe idanuwanshi, doguwar sumar kanshi duk ta yamutse,  Tsananin mamaki ne ya kamata, da sauri ta ɗan juya ta kalli gadon shi donta tabbatar idan shine dagaske, bata ga kowa ba, sai taga kamar 6acewa ya yi daga saman gadonshi ya faɗo gabanta, 


Kafin ta yi mashi magana ya riga ta cewa"zan ci shi kenan ko"? Ɗaga kai tayi alamar eh, ya ruko hannunta acikin nashi yaja ta suka koma Cikin ɗakin, a gefen gadonshi ya zauna, Suna fuskantar juna shi da angel, tana azaune saman nata gadon, ta tsareshi da ido tana jiranshi ya kammala Ci, kwandon Ya dauka ya ɗaura shi saman laps dinshi, A tsanake ya kai hannu ciki ya ɗauki yankan nama yana ci, Bayan ya gama taune shi duka, Ya ɗauki sauran 6allin apple data rage mashi yakai baki yana gatsa, jefi jefi yakan ɗan ɗago ya saci kallonta, Ko uwarsa Albarka yadda ta tsare shi da ido, 


  "Zaka sha ruwa"? Ɗaga mata kai yayi alamar eh, ta miƙe tsaye sai da tafara ɗaukar kwandon, Kafin ta nufi gadon batool, A ƙarƙashi ta tura kwandon ta ɗauko mishi robar ruwa guda ɗaya, Ta dawo ta miƙa mashi, yasa hannu ya kar6a ta koma saman gadonta ta kwanta tana facing ɗinshi, Buɗe murfin bottle ɗin yayi tare da kwafata abakin sa, kusan rabi ya sha, bayan ya gama shan ruwan, ya maida murfin bottle ɗin ya ajiye ta daga ƙasa, Sannan ya gyara kwanciyarshi, suna fuskantar juna, kallan ƙurulla suka shiga yi ma junansu, bakomai take tunawa ba, face yadda ya sha gabanta ɗazu saboda tace zata dura tagar nan, tarasa gane dalilin dayasa baison tasan komai dangane da kurkukun, Ta fahimci cewa danish yasan komai, shiyasa yake lalla6ata don kada ta gani taja musu wata matsalar, Abunda kuma bazai ta6a yiyiyuwa bane, 


Da wannan zancen zucin bacci yayi awon gaba da ita, shima danish ɗin tuni bacci ya ɗauke shi, 


A washe garin ranar, kafin kowa ya farka daga bacci, batool ce tafara tashi tana miƙa tare da Yin hamma, ta sauko daga saman gadonta, cikin sauri ta nufi toilet saboda wani irin fitsari daya matseta, Ya ɗaure mata mararta, hada ɗan gudunta wurin shiga toilet, batare data yi locking door din ba, hannayenta ta sanya wurin zame wandon jikinta ta zuƙunna tana Yin shi, bayan ta kammala ta kunna fanfo ta yi tsarki,  Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa tsaye tana gyara wandon Jikinta, kafin ta nufi ƙopar fita, harta miƙa hannu zata buɗe sai ga azeeza ta faɗo cikin toilet ɗin. jikinta sai kerma yake yi, batool tace"lafiyarki kuwa kika faɗo mini Cikin toilet ba neman excuse? Batare da azeeza ta kalli batool ba tace"ke dallah fitsari ne ya matse ni, ni ina nasan da mutun a ciki, " tana faɗin hakan ta wuce cikin toilet ɗin, girgiza kai batool tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta fito daga waje, taja mata ƙopar ta rufe, tana ƙoƙarin shiga cikin ɗakinsu, Tajiyo muryar azeeza daga Cikin toilet tana kwala mata kira na fitar hayyaci, da sauri ta koma ta nufi ƙopar toilet ɗin, Fitowa daga Ciki azeeza tayi idanuwanta azazzare hannunta dafe da saitin ƙirjinta tace"Batool, naga ɗigon jini a cikin toilet wurin magudaji ke ce kika zubda shi"? Wata irin mummunar faɗuwar gaba ce tazo ma batool, nan da nan walwalar fuskarta ta ɗauke, amatuƙar ruɗe tace"Bani bace, sai dai ko kece da kika shiga ciki yanzu, saboda ni har na fito banga wani ɗigon jini ba"aruɗe azeeza tace"Wlh bani bace, Ae ni yanzu na shiga, Ko tsugunnawa ban kaiga yi ba, naga jinin, hakan na nufin daga Jikin ki yake, " a tsiwace batool tace"Nifa bani bace na zubda shi ba, wlh bani bace" tuni hawaye sun wanke fuskarta, Azeeza ta fashe da kuka tana faɗin"Wlh kece, Ae ni ban kaiga yin fitsarin ba, Ki yadda ko karki yadda naki ne daga Jikin ki ya fito," shaƙo wuyan rigar azeeza batool tayi da hannunta biyu ta jijiigata, cikin shessheƙar kuka tace"You're lying to me azeeza, Kina so ki ƙala min sharri ne, Kiji tsoron Allah, ki faɗi gaskiya," Hankalinsu yayi matuƙar tashi, Kowa Ya haƙiƙance Yana ƙoƙarin kare kanshi, 


*Jinin wanene AZEEZA OR BATOOL ❓❓❓*


(Na ƙara maku yawan free pages, wadanda suke son shiga paid group, Suyi mini magana kaitsaye ta account dina, Zanyi musu sauƙi akwai facebook grp na wanda suka biya dana whatsapp)

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post