Kurkukun Ƙaddara episode 44 Complete

Kurkukun Ƙaddara episode 44 Complete

Kurkukun Ƙaddara

 💋KURKUKUN ƘADDARA💋


PRISONER'S STORY


E44


Daga alƙalamin Boss Bature writer of Abban sojoji❤


muryarta ashaƙe ta ƙarasa maganar, ita kanta batasan menene ma'anar budurci ba, tadai san kalmar acikin kanta, azeeza ta janyota ajikinta ta rungumeta tare da zagayo da hannayenta saman bayanta, tana ɗan bubbugashi,  Hankalinsu Haris yai matukar tashi jin abunda tace har suna haɗa baki wurin maimaita kalmar budurci, basu ta6a ji ba sai abakinta, Amma sai suka ɗauka cewa wurin bugunta ne Ya ta6a wani organ na jikinta, Shi take kira da budurci, nan fa suka harzuƙu, Naufal Ya shaƙo wuyan rigar Danish Ya ɗago dashi Yana huci yace"ka faɗa mana uban me kayi mata?  Taya akai ka gane mata budurcinta? Saboda baƙin hali irin naka"!  bawan Allah ya rasa ya zaiyi, hayaniyar su ba ƙaramin tafasa zuciyarshi take yi ba, Ga wani irin zafi da jikinshi ya ɗauka, haris ne ya lura da yadda yake lumshe idanuwanshi, Da sauri ya ƙarasa gabansu Ya ruƙo hannun naufal ya janye shi daga jikinshi, wani irin jiri ne ya kwashi danish Ya tafi xai faɗi ƙasa sai dai bai kaiga ƙarasawa ba, haris Ya tallaboshi da hannu biyu, ya ruƙo shi zuwa saman jikinshi, Ya rungume shi sosai, yana ambaton sunanshi, duk da ƙarnin Jinin da ke a jikinshi hakan baisa haris Ya guji ta6a shi ba, kallonsu mubben yai tare da cewa"Pls ku taimaka mini, mu kai shi daki" Turo baki Javed, Naufal kuma ya juya mishi ƙeya, mubeen Ya ɗaga kai ya kalli ceilling ɗin toilet, alamar bazasu ta6a shi ba, 


"Ka bani mamaki haris, Kafi kowa nuna  6acin rai akan abunda Danish yayi mana, amma sai gashi yanzu nema ka ke yi ka taimake shi" Rai a6ace naufal yai maganar,


Fuskar haris ɗauke da matsananciyar damuwa yace"bazan iya jure ganin shi acikin mawuyacin hali ba, Shi ɗan uwanmu ne, tabbas yayi mana kuskure amma abunda nake so ku fahimta, koda ace danish Bai miƙa ma giant batool ba, to xasu ɗaukota ne da kansu, don su tafi da ita, baida za6ine," 


Sunyi mamakin canzawar da haris yai lokaci ɗaya, duk dan sunsan irin ƙaunar dake a tsakanin shi da Danish, dole yaji tausayin shi a halin dayake ciki,


Ganin sunƙi taimaka shi yasa shi yin fushi, Yaja danish shi kaɗai ya shiga dashi cikin ɗaki ya kwantar dashi saman gadon shi, idonshi biyu sai dai jikin nashi ne ba ƙwari,


Shigowa cikin ɗakin Hanna da deeja su kayi angel tana a goye bayan hannah, Ta rurruƙeta da hannu biyu. A saman gadonta hanna ta kwantar da ita, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, a can ƙasan zuciyarta wani irin ƙunci ne ya cunkushe mata, danish yaga tsiraicinta, Babu sauran kwanciyar hankali, yanzu shikenan zai dinga ganinta tsirara koda ace da kaya ajikinta, tuna wannan yasa ta ƙara fashewa da wani sabon kukan, gaba ɗaya hankalinsu Ya dawo kanta, baiwar Allah bakinta duk ciwo amma ahaka take riskar kuka,


"Dan Allah angel ki daina kuka, Kiyi haƙuri, Ki faɗa mana me danish yayi maki? Hibbe ce tai mata magana, duk sun shiga damuwa, Azeeza tace"ina matuƙar jin tausayin angel, taji jiki ba kaɗan ba, danish bai kyauta mana ba Allah," Kowa yana tofa albarkacin bakinsa, danish dai duk yana sauraronsu ya lumshe idanuwanshi yayin da hannayen shi biyu ya rungume pillow dasu,


 sai da Angel ta gama shan kukanta mai isarta, tukunna tace musu ita fa bashi bane Yayi silar halin da tashiga ba, hasalima taimakon ta yayi a jiyan nan, a dole ta ƙirƙiro ƙarya ta fada musu cewa, Ta fita hayyacinta ne Saboda ɗauke batool da akayi shine ta fada toilet ta ɗauki bokitin nan na ƙarfe ta bubbuge jikinta dashi, da ta galabaita shine ta faɗi ta sume cikin toilet ɗin, ta faɗa musu hakan ne badan tana so ta kare shi ba, face don ta kwantar musu da hankalinsu, 


Gaba ɗaya sunyi amanna da abunda ta fada musu, har suka ɗanyi danasanin maganganun da suka gaya mishi duk da haushin sa da suke ji, Duk wannan abunda dake faruwa babu wanda ya ankara da sabbin gadajen da aka sanya musu acikin dakinsu, Har sai da suka fara Jin yunwa, Parveen tana hamma tare da kai hannu ta shafa cikinta ta soma ambaton Yunwa take ji,


Tana rufe baki Danish yace "An kawo mana breakfast tun ɗazu da safe, time da kuna bacci," batare daya buɗe idanuwanshi ba, yayi maganar,


 Atare suka Juya baya don suka ga In dagaske ne an kawo musu abinci, duk da sun cewa danish baya ƙarya.....  


Kaitsaye idanuwansu suka sauka akan sabbin gadajen da aka jera a cikin ɗakin nasu, gaba ɗaya suka zazzare idanuwansu saboda tsabar mamaki duk suka bi suka ruɗe, Sun saki baki suna kallon Ikon Allah saboda ba su yi tsammanin zasu yi arba da wani baƙon abu a cikin ɗakin su ba, da mamaki akan fuskar parveen Tace"Kuna ganin abunda nake gani kuwa? ko dai idanuwana ne suke nuna min ba dai dai ba"? Azeeza tace"Ae duk mun gani sabbin gadaje ne har kusan goma sha biyar tare da Akwatuna Biyu, ko a ina aka same su"? Danish ne ya basu amsa da cewa Ɗazu da safe kuna bacci giants suka kawo su, akwai ma kayan amfani da aka sanya mana a toilets" deeja tace"hakan na nufin zamu kar6i baƙuncin wasu prisoners ɗin"? Tai tambayar fuskarta babu walwala, domin kuwa ba abun farin ciki bane agare su, da duk wani mai hankali ba zai so wani bawa ya ɗanɗani irin rayuwar ƙuncin da suke yi ba.


"Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un! Ni dai har ga Allah bana farin ciki da zuwan waɗannan Sabbin prisoners ɗin, Saboda bana so suma su ɗanɗani irin rayuwar da muke Yi acikin kurkukun nan" Deeja ce tai maganar, Haris yace"ni kaina bana son mu ƙara yawa, muna fama da kanmu xa'a ƙaro mana wani ciwon kan" hibba tace" ni babban baƙin ciki na, Mu da muke fatan wata rana mubar kurkukun nan, sai gashi ana ƙoƙarin kawo mana wasu har mutum goma sha biyar zamu ƙara cunkushewa, tashin hankali kuma zai ƙaru"  hannah tace mu je mu duba gadajen ni sunyi mini kyau, Dama mu ma a canza mana sababbin," wani kallon harara deeja tai mata "Wato ke ta gado kike yi, to Allah yasa acanza miki gadon kiyi ta zama cikin prison ɗin, mu kuma Allah ya bamu sa'ar fita daga cikinsa" hanna tana ƴar dariya tace ba amin ba, Aniyarki tabi ki," 


Agaban gadajen suka tsaitsaya cirko cirko suna ƙare musu kallo, Sabbi gal dasu sunyi matuƙar yin kyau, Azeeza da parveen hada ƙoƙarin hawa saman wasu daga Cikinsu suna faɗin Bari su ɗana kafin baƙi su ƙaraso, azeeza tace ita yau ma asaman sabon gado xata kwana, suma sauran su ka ce duk anan zasu kwana su sha lagwada,


sai da suka gama kallon gadajen kafin suka koma kan akwatunan suna kallonsu tare da Floor laps ɗin da aka ajiye musu, ba ƙaramin daɗi suka ji ba, dama fitilun dake gare su sunyi kaɗan, Idan dare yayi sai dai mutun yai ta yawo da fitila zuwa toilet, amma yanzu sun yanke shawarar zasu ɗauki ƙananun fitilun guda uku, su ajiye su a kowani toilet, don su sawwaƙawa kansu.


a cikinsu an rasa wanda zai buɗe boxes ɗin nan, duk sunyi tsammanin Ba mallakin su bane, na sabbin prisoners ne da za'a kawo shiyasa basu ta6a su ba, saima suka kawar dasu zuwa bakin gadajen, bayan sun gama da ɗaki, eve tace"su je su duba toilets suga sabbin kayan da aka sanya musu, Parveen ta bubbuga ƙafa tare da cewa"Mu fara Cin abinci tukunna idan ku ba ku jin yunwa ni ina ji" sai da ta yi maganar suka tuna da cikinsu, hankalinsu gaba ɗaya yana akan Kayan da aka kawo musu,


Atare suka nufi dining carpet ɗinsu suka zazzauna, Kowa ya natsu zasu fara Cin abinci,


Duk wannan abun dake faruwa angel da danish suna kishingiɗe saman gadajensu, sun Juyawa juna baya babu mai fuskantar wani,  kowa da abunda yake saƙawa acikin zuciyarshi, ita dai damuwarta batool ɗinta, ko awani hali take ciki? Fatanta Allah yasa maganar da danish ya faɗa mata akan furen nan ta zama gaskiya,


Bayan su parveeen sun kammala Cin abinci. Sauran da suka rage ma angel da danish, Haris yace su je su ɗauko kwandon batool a kwashe musu nasu aciki, Nan fa duk jikinsu yae sanyi tunawa da batool ɗinsu, duk da dama tana acikin ransu ba yadda za su yi ne, tsakaninsu da ita addu'a ce kawai.


Hanna ce taje ta ɗauko kwandon batool dake a kusa da gadon danish Kifin da suka ajiye mishi tun jiya duk ya bushe jikinshi, hada ƴar rabin gwandar da baici ba, nuna musu kwandon tai tare da cewa"Fried fish din ma ya lalace  bari naje na zubar dashi, in wanko basket din sai asanya musu abincin aciki....." tunkan ta ƙarasa maganar parveen tai wuf ta sanya hannu ta kar6e kwandon tana faɗin"Inji wa yace maki ya lalace, bani nan ki gani, yanzu nan zan sanya shi a hanya..." Murmushi suka saki gaba ɗayan su yayin da suke kallonta, A ƙasa ta zuƙunna ta ajiye kwandon tare da kai hannu Ciki tana tatta6a Jikin kifin, azeeza tace"amma parveen baki da hankali, tun jiya fa yake a buɗe cututtuka duk sun hau jikin shi a haka zaki ce? Salon Cikin ki ya 6aci," Harara parveen ta watsa mata tare da cewa"Bai shafe ki ba ae cikina ne ba na ki ba" duk yadda suka so su hanata Cin fried fish din nan taƙi ji, tai kunnan uwar shegu dasu, Zama tayi na musamman tacinye shi tass bayan ta gama da kanta taje toilet ta wanko kwandon tass ta shigo dashi Cikin ɗakin ta miƙa ma Hanna kwandon, tasa hannu ta kar6a ta zuƙunna gaban farantin da niyar ta ɗibar musu wanda suka rage musu, Muryar Angel ta dakatar da ita,


"Kada ki haɗa mini abinci dashi, Ki ware mini nawa daban" idanuwanta arufe tai maganar, batare data motsa daga kwancen da take asaman gadonta ba, Haris yace ki ɗibar mata nata ki je ki taimaka mata taci, Ni kuma zan kaima Danish nashi, ta amsa mashi da toh,


Kafin marece yayi saida suka shiga cikin kowani toilet suka dudduba sabbin kayan da aka sanya musu, bakomai yafi burgesu ba face Hair gel kodan sabo da gashin kansu, sun samu na gyara shi, basu fara amfani dasu aranar ba, saboda sunfi so sai angel ta samu sauƙi ta taimaka masu wurin gyarawa.


A daren ranar Saman Sababbin gadajen nan kowannansu ya kwanta, in ka cire mutun biyun nan, Angel da kuma danish suna asaman gadajen su, jiki duk ba daɗi da ga ita har shi, ko wanka sun kasa tashi su yi, room ɗinsu yayi wani irin haske tamkar da rana saboda sabbin fitilun nan da suka kunna hasken su ya gauraye ko'ina gwanin ban sha'awa, Cikin nishaɗi suke ta wasa da pillows, Idan wannan ya jefa ma wannan sai shima yaɗauko pillow Ya jefa ma na kusa dashi, yadda kasan basu da wata damuwa bayin Allah, Angel tana jiyo hayaniyar su suna yin fira bayan sun gama wasa da pillown deeja tace"Nifa gani nake kamar zamu dawwama acikin kurkukun nan, tunda ga wasu ma za'a ƙaro mana" Parveen tace"ai kwara su zo suma su ɗanɗani irin zaman da muke yi, su ji in akwai daɗi," Azeeza tace muguwa parveen yanzu har wasu kike yi ma fatan suyi irin rayuwar da muke yi"? Parveen tana dariya tace"Nifa na faɗi hakanne kodan mu samu a ƙyale mu adaina ɗaukarmu mu tsaffin prisoners, su kuma sabbin sai acigaba da ɗaukarsu, Kunga mun hutu ko ba haka ba,'


Murmushi angel ta ɗan saki, yayin da idanuwanta suke fuskantar ceilling, ta ɗan ɗaga murya tana faɗin"parveen maganar da ki kayi sam ba ta yi mini daɗi ba bai kamata kina yi musu mummunan fata ba, tun kafin zuwansu ma, Ni tausayinsu ma nake ji, su da basu san komai ba, wlh ko maƙiyina bana yi mishi fatan shiga wannan kurkukun ƙaddarar, ballanta su da za'a kawo mana, musamman in ya kasance daga waje za'a kawo su, Ba ƴan asalin cikin kurkukun bane"


 jin wannan magnar ta angel yasa parveen tace"patient Ashe baki yi bacci ba, da ace nasan idonki biyu da ban furtata ba," dariya su kayi gaba ɗayansu, Angel tace"Oh, wato ni sarkin yin wa'azi ko? Kiji tsoron Allah parveen, Nidai komai na faɗi inayi ne don in taimaka muku wurin gyara rayuwarku," hanna tace"ai kina ƙoƙari kuma muna jin dadi sosai, muna fatan Allah yabarmu tare dake har bada, har mu shiga aljanna," murmushi angel ta ɗan saki, tare da yunƙurawa ta miƙe zaune saman gadonta ta jingina bayanta jikin bango, ta wutsiyar idonta take satar kallon danish, Ya rungume pillow sai bacci yake yi, aranta tace shi ko tsamin jikinshi baiji, " can kuma ta ta6e baki tana faɗin to ni meye ruwana dashi, " ta ambaci hakan tare da jan tsoki, Muryar Javed ta jiyo daga inda take fuskantarsu Yana ta yi musu faɗa akan su yi musu shiru sun hanasu runtsawa, su kuma sun dage sai zuba suke yi kamar kanyar da bata da daɗi, 


kasa kunne ta yi tana sauraron firar da suke Yi, sai taji akan gidan daddynta su ke magana, lamarin ya ɗan bata mamaki, jin parveen tana faɗin ai wlh idan suka gudu daga Cikin kurkukun suka koma gidansu angel ita acikin kitchen zata dinga kwana, ko dan ta dinga dafa abunda take so" 


Sakin baki angel tai tana sauraron ikon Allah, aranta tace wato ita parveen burinta na duniya shine abinci, taci abinci bata gajiya, mai iya rainonta sai manomi, amma wannan in baka da ƙarfin jari saita naƙasa ka," bata kammala zancen zucin nata ba, ta jiyo muryar azeeza tana faɗin"Ni dai ba ruwana da wani abinci, Idan Allah yasa muka bar kurkukun nan muka koma gidansu angel, A ɗakin daddynta zan dinga kwanta, nima ya rungumeni kamar yadda yake yi ma angel suna kwana tare," Haris yace"Sannu uwar son banza, menene alaƙarki dashi da har xaki kwana a ɗakinshi Ya rungume ki," zum6ura baki tae ashagwa6e ta bashi amsa da cewa"Ae ta faɗa mana cewa, Daddynta yana son ƴa'ƴa, Kaga kenan muma zamu zama kamar angel awurinshi" naufal yace"Kuna yaudarar kan ku dayawa, ku ɗan sarara mana, kada wata rana zuciyarku ta karaya, a garin sanyawa rai abunda bazai ta6a yiyuwa ba," 


Kafin wani ya kuma cewa wani abu angel tace"Inji wa ya faɗa maka cewa bazai ta6a yiwuwa ba? Ƙarancin imanin ku shine zaisa mu dawwama acikin kurkukun nan, bai kamata kuna sage musu gwiwa ba, Idan Allah yaso a yau ɗin nan zamu iya barin kurkukun nan wannan ba abun mamaki bane, amma nasan zaiyi wuya ku yarda da maganata har sai ranar da Allah yasa muka ku6uta inda rai da lafiya, tukunna zaku tuna da wannan maganar dana faɗa maku!!!"


(Mu haɗu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya)

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post