Kurkukun Ƙaddara page 51 Complete

Kurkukun Ƙaddara page 51 Complete

 💋KURKUKUN ƘADDARA💋


E51


Daga alƙalamin Hafsat Bature Boss✍️


Haƙiƙa Ta yi matuƙar jan hankalinsu, Kyakkyawar matashiyar budurwa, jawur da ita, Uniform ɗin dake Jikinta Style ɗin yasha banban da nasu, Ita nata gajeran skirt Launin Ja Ko laps ɗinta bai rufe ba, fararen tsala tsalan cinyoyinta sun bayyana a suffarsu kamar ba'indiya, daga sama Coat ce launin Ja, daga Ciki ƴar vest ce, Hannunta na Hagu na ruƙe da igiyar ƙatuwar backpack ɗin data rataya saman shoulder ɗinta.


yarinyar bata da ƙiba ko misƙala zarratin, sai dai wani abu dake da matuƙar jan hankali ajikinta, shi ne ƙirjinta, duk rashin ƙibarta ƙirjinta a cike suke fam, Boobs ɗinta tamkar zasu fasa rigar jikinta, tana da doguwar fuska, dara daran idanuwanta farare ƙal launin ocean blue, Jar sumar kanta anyi mata kitso guda biyu, bata da yawan gashi sai dai akwai tsayi, wutsiyoyin kitson sun sauko ta side by side na shoulders ɗinta, hancinta hada nose ring golden colour, earrings ɗinta na zallar gold ne, gefen wuyanta zanan tattoo ne na bindin ɗawisu, Launika daban daban, A bunka ga farar fata zanan yayi bala'en yi mata kyau, daga gani yarinyar ƴar gidan wani shege ce, mai ji da Naira, sai dai daga ganin fuskarta, ba ƙaramar wayayya bace, zai yi wuya tayi kunya a ido. 


Hankulansu Haris gaba ɗaya yana akanta, Har sai da taƙarasa saukowa daga saman benan, ta ɗan dakata da yin tafiyar tana faman wurwuga manyan idanuwanta akan fuskokinsu, Sauran Sabbin Prisoners ɗin dake a bayanta, Daga Cikinsu akwai wani matashin saurayi dogo twins ne shida ƴar uwarshi, wuyansu na sanye da sarƙar cross wanda ke nuni da addininsu, kyawawan gaske, Launin fatarsu kala ce mai tsada wadda ake kira da Chocolote, yadda kasan ɗan wrestling haka ƙirar Jikinshi take, ga wata irin haɗaɗɗiyar sumar kai, Curly har ta gaban goshin kanshi, Uniform dinsu jajayene, Bayansu Akwai wani Ƙaramin yawo da bazai wuci  shekara sha biyu ba, Albino ne (Zabiya) Hatta sumar kanshi Fara ce fat kamar hurhura, daga gani baida cikakken hankali don tunda suka faɗo ɗakin ya ke ta tsalle Yana dariya, Bayan su akwai wata Doguwar budurwa yadda kasan fatalwa, Bata da ƙiba ko kaɗan, sai tsawo tubarkalla kamar qugunta zai karye, duk tsayin Danish To ga wadda ta taka shi, gwanin ban tsoro tana tafiya kamar macijiya, launin wankan tarwaɗa ce ta ɗaure guntuwar sumar kanta da ribbom, 


Tashin sense, tsabar ruɗu Ya hana su angel cewa komai sai kallon kallo suke yi a tsakaninsu da sabbin prisoners da aka kawo musu, Aranta tace wannan karan Hada Jinsin Aljanu aka bankaɗo mana, Mun shiga ukun mu, Ashe Zaune bata ƙare ba,


Daga Cikin sabbin prisoners ɗin akwai wata ƴar ƙaramar yarinya da bazata wuci 10 years ba, Komai na jikinta sak irin na azeeza, banbancin shine ita azeeza tana da shekaru, girman jiki ke babu, Ita kuma wannan yarinya ce da gaske, Gata kyakkyawa itama, ga wani ƙato mai manyan kumatu, da mazannai, Namiji ne baƙi wulik, yana tafiya tsokokin Jikin shi na motsawa, hatta ƙirjinshi acike yake kamar na mace, tashin hankali akwai gwarama fa,


a hankali Danish Ya sanya hannayen shi biyu ya sauke azeeza daga saman wuyan shi, Ya ajiye ta ƙasa, Yanayin fuskar kowannan su Ya canza, Lokacin da Sabbin prisoners ɗin suka kammala shigowa ciki Su Goma sha takwas ne, Sanye Cikin Uniform jajaye kalar nasu Parveen, A jere suka tsaya cikin ɗakin kamar masu jiran abasu Umarni, Kallon kallo su ke ta yi a tsakanin su dasu Deeja, Kowa Yasha Jinin Jikin shi, A hankali suka soma Jin takun tafiyar mutun daga can saman stair ɗin, Da sauri Su angel suka kai idanuwansu kan Mai shigowa bakowa bace face*TSOHUWA ZAFREEN*cikin shigarta ta jajayen Kaya Ta rufe ko'ina na Jikinta, Idanuwanta kaɗai ne awaje, Yayin da hannayenta ke a ruke da sandar ta, daga bayanta Giants ne kusan su Uku, Gabza gabza, Masu ƙirar Samudawa, suna ƙarasa saukowa Cikin ɗakin, Da sauri Danish Yace masu Parveen su gaishe ta, Atare suka ɗan russina Cikin girmamawa suke gaishe ta, Wani abun mamaki Mutun ɗaya ce bata russina mata ba, Saboda ƙarfin hali irin na angel hada goya hannayenta saman ƙirjinta, Fuskarta babu annuri, don ta gane cewa itace tsohuwa zafreen, Ba ta yi tsammanin zata ankara da ita ba, Sai ji tayi tace"Ke baki Iya gaisuwa bane"? Cikin ƙarfin hali angel tace"Na iya, Ina kwana,"


 Al'ajabi ne ya kama Zafreen, Hankalin Danish kuwa idan yai dubu toh ya tashi, da ido yake yi ma angel magana akan ta duƙa ta gaishe da ita, amma ƴar tahalikar nan sai tayi kamar bata gan shi ba, hada ƙoƙarin ɗaure fuska idonta na kallon ƙasa,


Da kakkausar Murya Tsohuwa zafreen tace"Ki gaishe ni kamar yarda sauran ƴan uwanki suka yi mini" Cikin jin fargaba da ƙarfin hali angel tace"wuya na ke ciwo, bazan Iya russina kai na ba, amma ki gafarce ni" 


Tsabar mamaki yasa Idon kowa ya koma kan Angel, Hatta Giants dake a bayan Zafreen Acike suke da al'ajabin maganar Angel, Idan ka kalli fuskarta zaka ga ta ɗaure ta tamau, kuma babu alamun wuyan nata na ciwo, ita kanta amma a firgice take, saboda wani irin mugun tsora da take ji, kuma da gangan taƙi russina mata, Saboda ba ta yi  Niyya ba ne, don bata ga dalilin da zaisa ta ƙasƙantar da kanta wurin gaishe da tsohuwa Zafreen ba.


Jinjina kai tsohuwa zafreen tayi babu alamun ta fusata, Sai ma ta miƙa mata hannu don su gaisa, a ruɗe angel ta kalli tafin hannun zafreen dake a sanye cikin jar safa, Wani irin fagaba taji


"am happy to see your face, my granddaughter, Ƙwarin gwiwarki ya burge ni, tun da nake a duniyar nan ban ta6a ganin mahalukin da baya jin shakkar Yi min magana irin ki ba, ga ki ƙarama Kamar insa ƙafa in take" Jin wannan magana yasa angel taji hankalinta ya ɗan kwanta, har ta samun damar ɗaura hannunta acikin na tsohuwa tsaffin, Sosai ta ruƙe hannun angel acikin nata, Kafin daga bisani ta sakar mata hannunta, 


Cikin ƙasaita Ta Juya baya ta kalli Giants da ta zo dasu, Da hannu ta yi masu magana ba tare da ta furta musu a baki ba, Yatsu Biyar ta watsa musu sau biyu, Gaba ɗaya su angel suka shiga ruɗani sunyi tsammanin wani mugun abun zata yi musu sakamakon Abunda Angel tayi mata, Amma sai suka Giant Sun Kalli Sabbin prisoners da suka zo dasu, Da hannu Suka nuna mutun biyar na farko da suka fara shigowa, su ka yi musu alamar su tsaya a ɗakin, Sauran Goman Cikin su Da hannu su kayi musu alamar su wuce su tafi, A matuƙar ruɗe Su angel suke kallon su Cike da mamakin Ina za'a kai Mutun Goma da Giants suka ware? kenan an fasa ajiye su a ɗakin su? can kuma ta tuna da maganar da Batool ta ta6a faɗa mata na cewa Akwai wasu 6angarorin da prisoners suke rayuwa a gidan kurkukun basu ka ɗai bane, wata'ƙil can  za'a kai su.


A jere mutun Goman nan suka nufi saman Benan zasu koma, Christian ɗin nan Namiji Ya fasa wata irin ƙara da taja hankalinsu, da gudu yabi bayan waɗanda aka tafi dasu, Sai dai bai kai ga ƙarasawa ba, Giants suka Damƙo hannun shi, sosai idanuwanshi suke fitar da hawaye Yayin da yake miƙa hannu yana nuna ƴar uwarshi mace, Yana faɗin"My twin sister pls kada ku raba ni da ita, bazan iya rayuwa babu ita ba, " Fashewa da kuka ƴar uwar tashi ta yi kamar ranta zai fita, da gudu ta dawo ta faɗa jikinshi ta ƙanƙameta, Kamar zai maida ta Cikinsa, wani irin tausayin su ne ya kama su angel, azeeza tuni ta fara yi musu kuka saboda sun yi matuƙar ta6a mata zuciyarta, bayin Allah Kamanninsu sak iri ɗaya, Daga gani suna matuƙar ƙaunar junan su, saboda rashin Imani na Giants suka sa ƙarfi wurin raba su da juna, Su ka tasa ƙeyar macen gaba suka haura saman benan, Sai kuka take tana faɗin"My twin bro, Ka kula min da kan ka, Duk inda za'a kai ni zan dawo wurin ka," shima yana kuka yana kiran sunanta, Ahaka har aka fuce da ita" Bayan fitar su ɗakin yai tsit Ya rage Saura Su Angel da tsohuwa Zafreen sai mutun biyar da aka Bar musu cikin sabbin prisoners, Haƙika Tagwayen sunyi matuƙar ta6a Zuciyoyin su, Namijin sai share kwalla yake yi, idanuwanshi sun yi jawur dasu,  ga wata irin zufa dake tsastsafo mishi, Allah kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi, An raba shi da twin sister ɗinshi, Giant sun yi yankan ƙauna.


Gyaran murya tsohuwa zafreen ta yi musu kowa Ya shiga natsuwarshi, Cikin harshen turanci ta soma Yi musu magana


"Ina fata tsohuwa Tamira ta yi maku bayanin komai a dangane dani, ba sai na maimaita ba," Har suna haɗa baki wurin ce mata eh,


Jinjina kai tayi Yayin da take kallonsu ɗaya bayan ɗaya, kafin ta tsaida Tsoffin idanuwanta kan fuskar angel, 


"Sai dai ga dukkan alamu akwai waɗanda basu san wacece ni ba, Amma asannu zasu fahimta" 


Ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta kalli Sabbin prisoners da aka Bar musu tace"Ya rage naku, Ku zauna lafiya ko akasin hakan, Bata shafe ni ba, zan dinga zuwa akai akai ina duba ku, A koda yaushe ku kasance Cikin shiri" 


A hankali ta soma ja da baya Still idonta akan Angel, Kafin ta ɗauke su tare da juyawa ta nufi stairs ta haye, Giants su ka take musu baya, Suna jiyo datse ƙopar ɗakin, Nan fa kowannan su Ya shiga sauke ajiyar zuciya, don ba ƙaramin shakkarta suke ji ba, 


Sai lokacin su Haris suka samu damar yin magana


"Wannan wani irin rashin imani ne? Don me za'a raba shi da ƴar uwarshi? Bayan akwai sauran gadajen da kowannan su zai samu wurin kwana, Ni bansan me ke damun waɗannan mutanan ba, tsabar zalunci ne kawai" Haris ne yae magana yana mai jan tsoki, Azeeza tace ni wlh tausayi suka bani bayin Allah, hakanan an raba su"


Angel ta shiga ruɗani, Ita damuwarta ina za'a kai sauran toh? Ga kuma gadajen su A ajiye, Allah dai yasa ba wani mugun abun za'ayi musu ba, bakowa tafi jima tausayi ba face christian ɗin nan, Ya yi tsaye hawaye ta ko'ina akan fuskarsa.


Danish ne yai ƙoƙarin zuwa wurin shi Ya janyo shi tare da rungume shi yana lallashinsa, Cikin shessheƙar kuka yake faɗa mishi cewa ƴar uwarshi, tun da suka taso atare suke rayuwa komai atare suke yi, basu ta6a rabuwa ba, Amma yau An raba shi da ita," daƙyar Danish ya samu Ya lallashe shi, Har ya daina kukan, Tukunna Ya raba jikin su,


Tun da suka shigo ɗakin Yaron nan da aka bar musu zabiya, Sai tsalle Yake Yi yana dariya, babu wanda ya lura dashi saboda Halin da suka shiga, Ya haye saman gadajensu Yana ta ɗaukar fululluka yana watsar dasu ƙasa Hada bargunansu.


"Hey, y'all! my name is Unaiza, and i'm excited to get to know u all."


Da sauri suka kalli bakin mai magana, wata irin zazzaƙar murya mai cike da kwarkwasa da duniyanci, Bakowa bace face Ƴar madarar nan, da alama taji sunyi tsit basu tarbesu ba, Shiyasa tayi fara yi musu magana, ae daga ganinta wayayyiya ce, Murmushin yaƙe kowannansu ya sakar mata, Batare da sunce komai ba, ta kuma cewa


"It seems like we're not welcome at all" Jin wannan maganar yasa Danish Yin ƙoƙarin yi mata magana


"it's not like that, We welcome you with open arms. We are excited to have you here and look forward to getting to know you. You are highly welcome here"


 Fuskar shi ɗauke da murmushi ya ƙarasa maganar, Yana yi musu nuni da gadajen su, don su shugo ciki su zauna.


shu'umin murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, irin na tatattun ƴan iska, Ba zato ba tsammani, su angel suka ga ta nufi Danish Tana ƙarasawa gabanshi Ta sanya hannu biyu Tayi hugging ɗinshi ajikinta, Cikin harshen turancin dake nuni da ƙwarewar ta ta furta"Tayi matuƙar jin daɗin haɗuwa da shi, tana fata za'a kar6e su hannu bibbiyu," 


Ran angel ya 6aci da sauri ta nufi inda suke atsaye, Suma sauran suka bi bayanta, Tana ƙarasawa gabansu ta sanya hannu Ta ruƙo damtsen hannun Danish Ta janye shi daga Jikin yarinyar, ta dinga jefa mata harara, Amma ko ajikinta sai ma ta sakar mata ƙayataccen murmushi tare da miƙa mata hannu don su gaisa


"Hi, Am unaizah ƴar gidan daddy, can i know u"? Ta jefa ma angel tambayar, Yatsina fuska angel ta yi, Kamar bazata tanka mata ba, Sai kuma tace"My name is Unaisah, Amma daddyna Yana kira na Angel, shine sunan da kowa Yake kira na" Dariya su ka ga ta saki tare da cewa"Wow, sunan mu yae shige dana juna, banbancin kawai harafin ƙarshe ne, ina fata zamu zama abokai" Da hausa tayi maganar amma sai ka rantse da Allah da turanci tayi ta, Saboda Yadda take furta ta, daga gani baturiyace amma ta iya hausa ba laifi,'


Murmushin yaƙe angel ta sakar mata tare da cewa"why not, tun da zama ya haɗu mu wuri ɗaya" murmushi ta kuma saki tana kallon fuskokin su Tace Idan ba damu tana son su gabatar mata da kansu, batare da sun Yi mata musu ba, ɗaya bayan ɗaya Kowannan su Ya gabatar mata da kanshi, koda a kazo kan Danish Yana yi mata bayani dangane dashi har wani lumshe ido take yi tana kallonshi, ran angel ya gama 6aci gani take kamar an kawo musu annoba ne, saboda babu natsuwa atare da yarinyar,  bayan sun gama da kansu, Haris ya kalli sauran sabbin prisoners ɗin yace"saura ku ya rage ku faɗa mana sunayen ku, sannan muna son musan daga ina ku ke"_


Ƙaramar yarinyar nan ce ta fara Yi musu magana tace sunanta *JAMIMAH* Itama Prisoner ce a gidan kurkukun ta taso shekararta Goma cuf aduniya," Bayan Jamima Ta kammala gabatar musu da kanta, Wannan Doguwar mai zubin Taliyar indomi Ta faɗa musu cewa"ita Sunanta *SARAH* shekararta, Sha bakwai, Itama rainon kurkukun ƙaddara ce" Jinjina kai su kayi yayin da suka maida dubansu ga kirista ɗin nan suka ce mashi Ya faɗa musu wanene shi, Cikin sanyin murya yace musu Sunan shi*GABRIEL* twin sister ɗin shi kuma sunanta *GABRIELA* shekararsu goma sha bakwai," su angel sun yi mamakin jin shekarun su ashe duk Yara ne, Girman Jikine kawai, Naufal yace"rainon kurkukune ku ma Ko kuwa daga waje aka kawo ku"? Gabriel yace mishi bazai iya tuna komai dangane da rayuwarsu ta baya ba, shi dai kawai a bunda zai iya tunawa twins ne su, yana matuƙar ƙaunar ƴar uwarshi itama tana son shi, tare suka taso basu ta6a rabuwa ba"


 Maganar shi ta ɗaurewa Angel kai, ga dukkan alamu suma tagwayen ba rainon kurkuku bane, daga waje aka zo su, Saboda babu addini agidan kurkukun ƙaddara, Su kuma Akwai sarƙar cross a wuyansu, hakan na nufin An canza musu tunaninsu ne, 


Gaba ɗaya sun manta da mutun ɗaya daya rage basu su tambayi wanene shi ba, Kowa ya shafa'a da ɗan ta halikin nan, Sai da Parveen ta tuna da Abincinsu, Da sauri ta waiwaya baya don ta kalli Kayan abinci, Ras taji gaban ta ya faɗi ganin Mahaukacin yaron nan zuƙunne gaban faranti Ya ɗauki Chicken shawarma Yana turawa abaki, rabi na shiga rabi na zubewa ƙasa duk ya cakalkala ta, ga kuma Bargunansu daya wurgo ƙasa da fululluka, Da ƙarfi Ta ambaci"Innalallahi! " gaba ɗaya suka kalle ta, Ganin Tana kallon saitin dining carpet ɗinsu Yasa suma suka kalli wurin, Da gudun gaske parveen ta nufi yaron ta shaƙo wuyan rigarshi Ta wurgar dashi gefe ɗaya, Ya faɗi ƙasa kanshi ya bugu, Maimakon yayi kuka sai ya kama Dariya Yana Wuntsila ƙafafuwanshi, Rai a6ace Parveen ta shaƙo wuyanshi tana faɗin"Wanene kai?daga zuwa yau zaka fara Yi mana hauka? kana da hankali Kuwa....." bata kai ƙarshen maganar ba, sakamakon jin saukar Yawun daya watsa mata akan fuskarta, tsabar fusata yasa ta kikkifa mishi maru ka, ya dinga dariya ba ƙaƙƙautawa, daga gani jaki ne bai jin bugu.


Hankalinsu yae matuƙar tashi, saboda sun fahimci cewa Yaron yana da ta6in hankali, Mahaukaci ne aka kawo musu,  


"Parveen ki daina bugun shi, Baki ga yaro bane"? Azeeza ce tai mata magana, Rai a6ace tace"Babu ruwana da yaro ne, Ubanshi zanci, har ni zai watsa wa miyau a fuska"? Da alama ta fusata, Rigarshi ta damƙo ta goge miyan daya watsa mata a face ɗinta, duk da haka bata ƙyale shi ba, sai da ta sanya hannu ta dunguri kanshi, Kafin ta miƙe ta nufi toilet don ta wanke fuskarta, badajimawa ba Sai ga parveen ta dawo Cikin ɗakin fuskarta ɗauke da lemar ruwa, Sai Jifar yaron take yi da harara kamar ƙwayar idon zasu faɗo ƙasa.


Deeja tace"Mun shiga uku, tamu ta same mu, Yanzu haka zamu rayu da wannan Ta6a66an? Naufal yace"Bazamu zuba mishi ido ba, Dole mu koya mishi hankali," tsoki haris yaja batare daya ce komai ba, 


Danish ne yace da sauran"Idan kuna jin yunwa ga abinci nan, Idan zaku huta ga beds ɗinku nan, sannan......." bai ƙarasa ba yaɗan  kalli ƙopar shiga sashen toilet ɗinsu yace"Game buƙatar watsa ruwa ko yin wani uziri wannan ƙopar zaku bi, Anan toilets ɗin mu su ke" Yana magana hankalin shi na akan Matashiyar yarinyar nan, dake ta kallon shi tana faman cizon pink lips ɗinta, ran angel idan yai dubu ya 6aci, bakomai yafi ƙona mata rai ba face ganin yadda take kallon Danish tana cizon le6e, tarasa gane me hakan ke nufi, to ko dai halittarta ce ahaka? Ko kuwa wani sabon salon iskancin ne"? 


"Bana jin yunwa, I need to take bath, before in kwanta In huta" Ƴar gidan daddy ce tayi maganar tana ƙoƙarin sauke School bag ɗinta, Idon kowa na akanta, Miƙa ma Danish Backpack ɗin tai tare da cewa"Ka ajiye min ita, sannan ka raka ki toilet ɗin, bazan iya ganewa ba" Wani irin kallon harara angel take jefa ma Danish, duk yasha jinin jikin shi, Sam ya kasa kar6ar jakar Unaiza, Sai angel ce ta kar6e jakar tace"Zan ajiye maki ita, sannan zan raka ki toilet ɗin, idan ma kinaso har cuɗa maki baya zan Iya yi" Girgiza kai Unaiza tae tana fadin"No, bana so, ki dai ajiye min back pack ɗin, Shi sai ya raka ni toilet ɗin" mamaki ne ya kama angel, aranta tace"that's impossible, kinzo da bidi'a," Kar6ar jakar tayi daga hannun unaiza taje ta ajiye mata ita gefen donta mai ɗauke da no 16, juyowar da za ta yi, karaf idanuwanta suka sauka akan Unaiza da ke ƙoƙarin cire Coat ɗinta, Bakomai ne ya faɗar mata da gaba ba, face Ƙirjin Unaiza, Musamman da ta ƙarasa Cire rigar Hankalin Kowa Ya koma kansu, Kamar babu riga ajikinta saboda Yadda surar su ta bayyana ajikin vest din, Manya manya dasu kamar balan balan,  shatun nipples ɗin sun fito sosai, kamar zasu huda ta, gata yarinya amma tubarkalla, Allah yayita da boobs, "


Kwanciyar hankali ya ƙarewa angel, Kishi ne ya addabi zuciyarta, kodan hada ƙarin ita bata da su ne, Oho dai, 


Bayan Unaiza ta ɗebe Coat ɗin Ta miƙa ma Danish tace Ya ruƙe mata, Hannun shi na kerma ya ruƙeta, wani irin ƙamshi ne ke fita jikin coat ɗinta," hannayenta ta ɗaura saman gajeran skirt ɗinta, Waro ido angel tae baki a sake take kallon ikon Allah, Cire shi tae ya rage daga ita sai Short na mata, "


duk su naufal suna a tsaye suna kallon ikon Allah, Miƙe ma Danish Skirt ɗin ta yi"Ka ajiye min su" Kafin yai yunƙurin kar6ar skirt ɗin angel tai saurin komawa wurinsu ta sanya hannu ta kar6i skirt din ta kuma ƙwaci coat ɗin dake a hannun Danish, Fuskarta a ɗaure ta nufi akwatinsu ta sanya mata su a ciki, Kafin ta dawo ta tsaya agefen Danish, 


"Muje ka raka ni toile ɗin" ta yi maganar tana ƙoƙarin ruƙo hannunshi, Angel tae saurin ka6e mata hannun"Ni zan raka ki," Bata jira amsar da unaiza zata bata ba, Taja hannunta, ta wuce da ita zuwa sashen toilet ɗinsu, sai bayan da suka shige, azeeza da parveen suka kalli juna, Alamar mamaki, sufa sunga abunda basu ta6a ganin irin shi ba, tun da ko tsohuwa nata azube suke kamar silifas, Cikinsu kuwa ba wadda ta ke da su irin na ƴar gidan daddy, har ƙwara waɗan da suka fara manyanta, Sune ya fara fito mawa, amma ita ko wannan ƴar shilan ƙirjinta sunfi ƙarfin jikinta da shekarunta. 


"Gabriel, banji kace komai ba"? Danish ne yae mishi magana ganin yayi tsaye bai motsa ba shi da sauran ƴan uwan nashi, Cikin sanyin murya yace"Inaso na kwanta, saboda kaina ciwo yake yi min" Nuna mashi gadonshi danish yae da hannu, Yace mashi thanks kafin Ya nufi gadon, Sai da ya fara cire coat ɗinsa, Ya ɗaura ta gefe, Sannan ya haye gadon ya kwanta,


Kallon Jamima su kayi ƴar ƙaramar yarinyar nan, parveen ta raya aranta cewa"Wannan dai rainonta zamuyi da alama" Haris ne yace da ita"Kefa? Zaki kwanta ko xaki ci abinci" Ta6e baki ta ɗanyi kafin tace"Yunwa nake ji," Deeja tace"amma ke kike yin wanka da kanki"? Ɗaga mata kai tayi"Eh, inayi yanzu, amma sai ana cuta min bayana saboda hannu na bai kai wa" Murmushine ya bayyana akan fuskokinsu, don ba ƙaramin burgesu tayi ba, gata ƴar kyakkyawa da ita, Hibba tace"idan ma kinaso har wankan sai muyi maki," dariya tasaki tare da sanya tafin hannayenta ta rufe fuskarta, alamar taji kunya.


Ruƙo hannunta Haris yae acikin nashi yace"muje muci abinci ko"? Tace mishi eh, " mubeen yace"to itafa Wannan bamu ji ra'ayinta ba, " yae maganar yana nuna Sarah dake atsaye Ta ruƙe qugu, Yatsina fuska Ta ɗanyi can kuma saita ƙaƙaro murmushi tace"Nima bana Jin yunwa, zan kwanta na huta ne" tae maganar tare da juya ta nufi gadajensu, Ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, a sukwane Ta juyo ta kalle su Deeja tace"wai a ina zata kwanta ne"? 


Nan take su ka fahimci cewa Ta raino gadon ne, Wato yayi mata ƙanƙanta, Hannah tace"Acan inda kuka Baro, a  saman Ina ki ke kwana ne"? ta6e baki Sarah ta yi Ba tare da ta bata amsa ba, Ta maida idonta kan gadon, Ta curo bargon saman shi, Ta shimfiɗashi a ƙasa, ta ɗauko pillow ta jefa, Kafin ta cire coat ɗin Jikinta ta ɗaura a ƙasa, Ta faɗa sama gadon ta kwanta.


A bunda ya faru bayan Angel ta raka ƴar gidan daddy toilet, suna shiga ciki taja burki ta tsaya Tana faman zazzare blue eyes ɗinta haɗi da yatsina fuska, Angel tace"Ni xan Koma, ayi wanka lafiya" har zata juya muryar Unaiza ta dakatar da ita


"Nifa ban fahimta ba, Ina bathtub yake ne? tana nufin (kwamin wanka) Wannan wani irin toilet ne kamar na Marasa galihu" Tsabar mamaki yasa angel sakin baki kamar sakarya tana kallonta, Daƙyar ta iya buɗe baki tace"ba mu da bathtub, Iya a bunda idonki suka gane maki acikin toilet din su muke dasu, Ga Shower nan, Sai kuma bokiti, can kuma Soso ne da sabulu," aruɗe unaiza tace"that's Impossible, ae ni bana sharing soson wanka, Kuma bana wanka in ba a cikin bathtub ba, I can't stay here i wanna go home, cos daddy ba haka Ya kwatanta min school ɗin ba, Yace min fa komai irin na Gidan mu ne, but why naga banbanci"? tamkar zata fashe da kuka tayi maganar, har saida gaban angel ya faɗi jin abunda tace, Wato ita duk a tunaninta School ce aka kawota batasan cewa Prison bane, To me hakan ke nufi? Kodai mahaifinta ne ya yi mata ƙarya kan cewa za'a kawo ta makaranta! Tashin hankali Sai lokacin angel ta tuna da irin uniform ɗinta na gayu, dama ta yi mamakin ganinta da haɗaɗɗun takalma ƴan ƙwaras ƙwaras, Ga gajeran skirt na gayu, Ga kuma ƙatuwar School bag Ta goyo, Tabɗijancan, In dai a bunda take hasashe ya tabbata to kuwa Iyayenta sun Cuce ta, Mamaki Ya hana angel cewa komai, taya akai basu gusar mata da hankalinta ba? Kamar yarda aka yi ma Gabriel? Ko kuwa sihirin ne bai kama Jikinta ba?


ta yi zurfi acikin tunaninta muryar unaiza ta katse ta"Pls talk to me! Ni ban fahimci komai ba, game da school din nan," tashin hankali ne Ya bayyana ƙarara akan fuskar angel, miryarta na ɗan rawa tace da unaiza"wacece ke? Dama ke ba rainon Kurkuku bace"? Waro ido tae tare da maimaita sunan prison da angel ta faɗi, Ba don ta fahimci me hakan ke nufi ba, 


"Ban fahimce ki ba, Naji kince prison, Nifa daddyna yace dani xai sanya ni a  high school Na south korea, saboda inason kallon drama ɗin su komai nasu yana ƙayatar dani, Daddyna yana yi min komai nake so, shi ne Da kanshi, Ya sama min admission a school ɗin nan, a gida aka kawo min uniform na sanya ajiki na......" unaiza bata ƙarasa maganarta ba, Angel ta ɗaura hannunta akai,! Irin ta shiga ukun nan, fito wa ta yi daga Cikin toilet ɗin Ta tsaya daga waje tana ambaton"Innallahi wa'inna ilaihirraji'un"! da sauri ƴar gidan daddy ta biyo bayan angel, baiwar Allah duk ta ruɗe ta rasa gane me angel ke nufi,


"Pls tell me the truth Ko ba school bane nan ɗin? I ave to know" wani irin kallon tausayi angel ke binta dashi, muryarta kamar ta mashayin giya tace"Zaki iya tuna Ta ina aka kawo ki Nan" girgiza kai tayi"I can't remember, Ni dai nasan time da masu aikin gidan mu, suka taimaka min nayi wanka na sanya uniform da daddyna ya bani, so bayan nan sun rakoni zuwa wurin da motocin bodyguards ɗina su ke, sun buɗe min mota, Na shiga Ciki na zauna, ina ta farin ciki, duk na qagara  mu ƙarasa Airport sai bacci ya ɗauke ni, daga nan ban ƙara tuna komai ba, sai dai na ganni Acikin School ɗin nan tare da sauran students din da muka zo da su" Tana magana tana yatsina fuska daga gani ɗabi'arta ce yin hakan,


Jinjina kai angel tae yayin da take kallonta, haƙika ta yi mamakin da basu canza mata tunaninta ba, tun da har ta iya faɗin yadda aka kawota Cikinsu, tabbas kowanene Ubanta ba ƙaramin Mugu bane, Azzalumi, Wato shi wayau yayi mata ya fake da cewa za'a kaita Sk don ta yi karatu batasan cewa Sadaukar da ita ya yi ba zuwa Gidan Kurkukun ƙaddara, don biyan wata buƙata tashi, Rayuwarta abun tausayi baiwar Allah, Sai da aka gama sangartata, Daga gani an gama jiyar da ita duk wani daɗi na duniyar nan kafin aka tsamota daga aljannar duniya aka kawota gidan kurkukun ƙaddara,


Ganin irin kallon da angel take binta dashi ne yasa tace"Pls Ke nake jira ki bani amsa," A ƙagare tayi maganar,


"Ya sunan mahaifinki? Kuma wanene shi"? Muryarta A disashe tace"Ae ni bansan real name nashi ba, na dai san ana kiran shi Jan wuya..." bata ƙarasa maganar ba angel ta katse ta da cewa"Ba ki ta6a zuwa school bane? Da wani suna kike amfani"? Ta bata amsa da cewa"ni tunda na taso ban ta6a zuwa school ba, daddyna bayaso ina shan wahala, A gida ake koya min karatu, yanzu ma don na kwallafa raine akan inason zuwa south korea karatu shine yace zai sani...." 


Jinjina kai angel tae kafin tace"Amma awace ƙasa ku ke zaune duk da naji kina magana da yare biyu, hausa da turanci so na kasa gane wani jinsi kike"


Wannan karan tamkar zata fashe mata da kuka ta yi maganar don ta gaji da tsayuwa, 


"My dad is from Nigeria and my mom is from England. I've never been to Nigeria, and I don't know my dad's hometown or his job, Ni da Mommyna ne kawai muke rayuwa a england sai ƴan Aikin gidan mu, amma yana yawan zuwa kawo min ziyara daga Nigeria"


Hankalin angel ya ƙara tashi, daƙyar tace mata yanzu kiyi haƙuri kiyi wankan idan kin kammala zanyi maki bayanin komai" Girgiza kai tayi"ae bazan iya wanka awannan toilet din ba, saboda ba irin na gidanmu bane, ni nasaba acikin bathtub nake yi, kuma masu aikin gidan mu ne suke taimaka min wurin yin wankan" 


Kallon ta kawai angel ke yi, Iya cutuwa dai an Cuci yarinyar nan, tama rasa taya zata fahimtar da ita cewa Nan kurkuku ne, ba high school ta ƙasar korea ba? Zaiyi wuya ta fahimce ta, babbar matsalar irinsu Suna da ƙarancin imani, sannan basu da tawakkali, Tana iya ta faɗa mata azo asamu matsala, Ya za tayi da ita? 


Yayin da su Angel suke a sashen toilet dinsu ita da ƴar gidan daddy, Su kuma can ɗaki suna fama da wannan mahaukacin Yaron, abunda ya faru Suna ƙoƙarin zuwa suci abinci, Eve tace dasu,


"Wai nikam Ina Yaron nan yake ne"?  Kafin wani ya buɗe baki ya bata amsa suka Ji ƙarar karyewar wani abu acikin kunnuwansu, Agigice suka kai idanuwansu wurin da suka Jiyo sautin ƙarar, ransu yae mutuƙar 6aci ganin  Irin uwar 6arnar da Yaron yayi musu, Gaba ɗaya Ya kado da cake ɗinsu ƙasa, Table ɗin Ya 6alle, Cake ɗin ya ƙundumo kasa Ya tarwatse, hakan bai ishe shi ba, sai da ya hau saman Cake ɗin Ya dinga duma hannuwanshi aciki Yana Kwaso shi Yana turawa abakinsa, duk ya 6ata uniform ɗin jikin shi da cake ɗin, A ƙarshe ma sai ya hau saman Cake ɗin ya dinga burgima yana dariya, a fusace parveen ta nufi inda yake, Haris da Danish suna ta ƙoƙarin dakatar da ita akan kada ta buge shi, amma ina ko waiwayon su bata yi ba, wata irin damƙa takai ma wuyan rigar shi, ta ɗago dashi ta daddage ta buga kanshi a ƙasa, azabar zafi yasa shi fashewa da kuka mai tsiwar gaske, tana huci tace"Shege ashe kana jin bugu, ae nayi tunanin kurma ne kai" Sautin kukan yaron ne ya karaɗe kunnuwansu angel dake a sashen toilet ɗinsu, da gudu suka nufi ɗakin suna shugowa suka ci burki suna kallon Yaron dake ta kuka, Hatta gabriel dake kwance yana bacci shi da Sarah sai da suka farka saboda sautin kukan fitinannan Yaron, An rasa me lallashin shi acikin su, haushin shi suke Ji, Ya baƙanta musu rai, duk irin yadda suka ƙwalla fa ransu ga son cin cake ɗin nan ya tarwatsa komai, Farin Cikinsu Ya gushe, Har ga Allah basu Ji daɗin zuwan prisoners ɗin nan ba, Saboda mutun biyun nan dake acikinsu, Mahaukacin yaron nan da Angel ta sanyawa suna Majnun saboda Yaƙi faɗa musu sunanshi, Sai kuma Unaiza ƴar gidan daddy, A ranar Bayan Danish ya lallashi Yaron Yaje dashi toilet ya wanke mishi Jikin shi Da uniform ɗinshi da ya 6ata da cake, Ya shanya su saman igiyar toilet ɗinsu, ya ɗauko bargo Ya ƙudundune shi ajiki yakai shi Daki ya kwantar dashi saman gadon shi, Cikin ƙanƙani lokaci bacci yayi awon gaba dashi, Hankalinsu har ya kwanta, ashe ƙura bata lafa ba, Sun gama shan wahalar gyara ɗakin nasu da ya 6ata musu ya hargitsa komai, Suna ƙoƙarin zama su huta, Unaiza tace musu Yunwa take ji, Suka ce mata Ga abinci can saman dining carpet ɗinsu taje taci, Saboda damuwa ma yasa babu wanda ya waiwayi abinci acikin su, Sai wannan ƙaramar yarinyar jamimah Ita kaɗai ta zauna tana ci.


(Masu so karanta middle Step book 2 whatsapp suyi min magana 08103884440 masu son facebook paid group Ga link ku danna shi za kaiku ga wadda zaku yi ma msgana👇


https://www.facebook.com/manal.muhd?mibextid=ZbWKw

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post