Kurkukun Ƙaddara page 69 Complete

Kurkukun Ƙaddara page 69 Complete

69 complete kurkukun Ƙaddara

 💋KURKUKUN ƘADDARA💋

69

By Boss Bature

ɗagowa ta yi da Rinannun idanuwanta akan fuskar Angel da ke kallonta, 

Miƙa mata pant ɗin dake a dunƙule cikin tafin hannunta ta yi tare da cewa 

"na baki shi kyauta Angel, dan Allah kada ki ce min baki so, inaso ku dinga tunawa dani acikin rayuwar ku, kodan saboda in samu masu yi min addu'a idan na mutu.

fashewa su kayi da matsanancin kuka, Hannu biyu angel ta sanya wurin kar6ar pant ɗin da unaiza ke miƙo mata, sosai ta matse shi acikin tafin hannunta muryarta na rawa tace"nah..na kar6a Unaiza, kuma zanyi amfani dashi, nagode sosai," Murmushi ne ya bayyana akan fuskar unaiza, 


"Inaso ku bayyana min irin ƙaunar da kuke yi min," Atare suka haɗa baki wurin furta"wlh bazamu iya misalta maki irin ƙaunar da mu ke yi maki ba, muna son ki ƴar uwarmu, bamu ta6a ƙin ki ba, muna fatan mu kasance atare da ke har ƙarshen rayuwar mu," 


 Dariyar farin ciki Unaiza ta saki, fararen haƙoranta kamar gonar auduga, Nan ta ke gaban su ya faɗi ganin Jinin dake gangarowa ta cikin ƙofofin hancinta, wata irin zufa ta fitar hayyaci ta soma tsastsafo mata, agigice suke kallonta sun kasa motsawa, ta tsakanin cinyoyinta jini ya shiga kurɗaɗowa, idanuwanta suka kaɗa jawur dasu, ta soma cizon la66anta, Da sauri Batul ta sanya hannu ta ruƙo ƙasan rigarta ta janye ta, Hankalinsu yai mugun tashi ganin yadda gabanta ya 6urma wurin ya jagwale sai uban rami, basu ta6a ganin tashin hankali irin na yau ba, gaban unaiza ya lalace, Da ƙarfi suka shiga ambaton “Inna lillahi wa inna ilayhir raji'un” tsabar fargabar abun da su ka gani yasa mutun huɗu daga cikin su suka sume nan take,


Angel ce ta yi ƙoƙarin biya mata, Kalmatusshahada ita da Deeja suka dinga maimaita mata, itama batul ta ɗauka atare suke karanto mata ita, A lokacin Allah ne ya nufi Unaiza zata furta kalmar nan saboda takai matakin ƙarshe, Harshenta yana dab da karyewa muryarta da wani irin sauti ta furta kalmar shahada, tana ƙarasawa murmushi ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta idanuwanta a buɗe kanta ya faɗa saman kafadar batul dake a kusa da ita, rai yayi halinsa.


Kullu nafsin za'ikatul maut, Rest in jannatul firddaus Unaiza rai yayi halin shi, munayi mata fatan dacewa.........." 


Alƙalamina ya girgiza, Bazan iya fayyace irin tashin hankalin da bayin Allahn nan su ka fuskanta ba, a wannan lokacin, Tun da su ke arayuwar su basu ta6a ganin gawar ɗan uwansu agabansu ba Sai yau da su ka ga gawar Unaiza, suman zaune su ka yi, hawayen ma sun daina shararowa kan fuskar su, Komai ya tsaya masu cak! zuciyarsu da tsananin fargaba take bugawa, Idanuwan su sun kaɗa jawur da su, mutuwar Unaiza ta girgiza su fiye da tunanin mai tunani, tsawon awanni babu wanda ya motsa a cikinsu, 


Muryar Angel babu sauti take karanto addu'ar da ake yiwa mamaci duk wasu addu'o'i da aka koya mata a islamiyyar su wanda su ka shafi mamaci sai da ta karanto su duk da bata acikin hayyacinta, ta dinga tottafa mata saman jikinta, haƙiƙa sun ji ɗacin da yafi na maɗaciya a cikin zuciyoyinsu, sunji raɗaɗi mara misaltuwa, Sunga tashin hankalin da basu ta6a ganin makamancin shi ba........"


Yayin da suke acikin toilet, Suna jimamin mutuwar Unaiza, basu san meke faruwa ba acikin ɗakin su, Tun bayan da suka ɗunguma zuwa toilet, Ya rage saura Azeeza da jamima dake rungume da majnoon cikin bargo, Azeeza ta zabga uban tagumi tana kallon bargon da suka lullu6e shi, Ashe Jikin shi ya fara bleeding, ta hanci da baki da ƙasan shi babu wanda Ya ankara a cikin su, tuni ya farka daga bacci, yana ta ƙoƙarin ƙwace kan shi daga ruƙon da jamimah tayi mashi amma ya kasa saboda rashin ƙwarin Jikin shi, gashi ita jamimar bacci ya ɗauke ta, Fashewa yai da matsanancin kuka yana faɗin "dodo zai cinye ni, Ku sake ni ku ƙyale ni, kaina ciwo ya ke yi min, jiki na zafi" a firgice azeeza ta farga da sautin kukan shi, tai saurin sanya hannu ta yaye bargon, karaf idanuwanta suka sauka akan Fatar jikin shi dake neman ɗaɗewa ta fashe, jikin shi ya kumbura, Ga jinin dake bin Cinyoyin shi, A gigice ta fasa wata irin razananniyar ƙara wadda tayi silar farfaɗowar Su batul suka dawo hayyacin su, A matuƙar ruɗe suke zazzare idanuwan su, kusan atare Deeja da Angel suka yunƙura cikin zafin nama suka watsa a guje zuwa cikin ɗakin su, shigar su keda wuya suka tarar da tashin hankalin daya kara gigitar dasu, Gaba ɗaya suka ci burki suna kallon shi, a lokacin Jamimah ta farka Jin ƙarar da azeeza ta fasa, tana buɗe idanuwanta taci karo da jinin majnoon da ya wanke fuskar shi, Nan take ta fashe da kuka tare da sakin shi ta miƙe zaune hannayen ta biyu asaman kanta, zuciyoyin su sun gama karaya sun riga sun fidda rai da rayuwar Majnoon, duba da yadda Jikin shi ya kumbura gwanin ban tsoro, ahaka ya dinga ambaton sunayen su yana neman taimako daga gare su don suzo su agaza mashi ko ya rage raɗaɗin da yake ji, A sukwane Angel ta faɗa saman gadon tsananin tsoro da firgici sun hana ta ta6a jikin shi, gudun kada fatar ta fashe, sunan Allah ta dinga ambato a cikin bakinta, Jamimah tana kuka tace "Majnoon kada ka tafi ka barni, dan Allah ka daina zubar da jini, ka daina kumbura jikin ka, bana son ganin ka haka,


 Muryar shi na rawa ya soma faɗin "Zafi jikina babu daɗi, dodo sun kashe ni, sun rabani da rayuwata, sun rabani da ƴan uwana......" wannan maganar da yayi ta yi matuƙar ta6a zuciyoyin su, Muryar Angel cikin shessheƙar kuka ta soma magana "Majnoon ka yi haƙuri, Allah yana atare da kai, shi zai kawo maka sauƙin abunda ke damunka, waɗanda suka cutar da kai kuma Zasu ɗanɗani kuɗar su ne Ranar gobe ƙiyama, domin kuwa duk wanda ya cuci wani Allah zai bi mashi haƙƙin shi, kai yaro ne ba ka mallaki hankalin ka ba, ga ta6in hankali dake damun ka, majnoon ba ka da zunubin kowa akan ka, Nayi maka farin ciki idan ka mutu, saboda itace hutu agare ka, Allah zaiji ƙanka ya tausaya maka, ya baka farin cikin da baka samu ba a gidan duniya........" kuka ne yaci ƙarfinta har ta kasa ƙarasa maganar, juriyace da ƙarfin hali yasa harta samu damar furta waɗannan kalaman, Idanuwanta akan fuskar shi data kumbura, Tayi jawur idanuwan shi duk sun gwale fatar su tayi jawur da ita,


"Majnoon don't die, ban gaji da ganin ka ba, ina matuƙar ƙaunarka, inaso mu cigaba da yin wasa atare muci abinci atare, Angel tace zata kai mu gidan su su bamu kayan wasan yara, dan Allah kada ka mutu kaji majnoon ɗina......" Jamimace take yi mashi magiya fuskarta jaga jaga da hawaye hada majina,


Magana ta ƙarshe da majnoon ya furta masu itace"Zan tafi kira na akeyi, naga wani mutun sanye da fararen kaya yana miƙo min hannun shi, yace min inzo gare shi zai sama min farin ciki, zan bi shi mu tafi, Angel jamimah azeeza......." bai kaiga ƙarasa maganar shi ba, Numfashinsa ya ɗauke, jikin shi ya saki, nan take rai yayi halin shi............"


Ya Allah kajiƙan waɗanan bayin naka! Da dukkan waɗanda suka rigamu gidan gaskiya, waɗanda su ke acikin irin wannan ukubar ta rayuwa, Ya Allah ka kawo musu ɗauki, Waɗanda su ka yi silar shigar su cikin wannan Masifar ya Allah ka tona asirin su, Ka kawo mana ƙarshen su, Kai kaɗaine zaka Iya dasu!.


Zuciyar Angel kusan bugawa tayi, a gefen majnoon ta sume, ba itaba hatta Azeeza da deeja  A nan ƙasa suka kwakkwanta, Kansu Na bala'en sara masu, Basu ta6a ganin baƙar rana irin ta yau ba.


Jamimah sai kuka take yi tana ambaton sunan shi, ita kaɗai ta rage mai motsi a cikin ɗakin nasu, batasan cewa ya mutu ba, muryarta har shaƙewa ta ke yi wurin ambaton sunan shi.


💔PRISONERS💔


Kafin wani Lokaci Giants su ka turo ƙopar ɗakin su, Uku daga cikin su masu kawo masu Abinci ne hannayensu ruƙe da trays, daga bayan su wasu Giant ɗinne Su huɗu hannuwan su ruƙe da gadaje guda biyu kalar wanda ake ɗaukar marasa lafiya, masu ɗauke da sunan Kurkukun ƙaddara, A tsakiyar ɗakin suka ajiye gadajen, Giant ɗaya ya nufi sashen toilet ɗinsu, Jim kaɗan ya fito hannun shi ɗauke da gawar Unaiza, a saman ɗaya daga cikin gadajen ya kwantar da ita, kafin ya nufi gadon majnoon Ya ɗauko gawar shi Ya ɗaurata a ɗayan gadon da ya rage, biyu suka ruke ɗaya, yayin da biyun suka ruƙe ɗayan gadon, A haka suka Ɗaga su tare da haurawa saman benen su ka fuce dasu........" 


(Next page gobe zan sa shi in sha Allah, Masu son shiga paid group na facebook Ga link Kuyi mata magana after kun biya zata sanyaku👇


https://www.facebook.com/manal.muhd?mibextid=ZbWKwL


waɗanda ke yin arewa book su yi following account ɗina, zasu dinga samun Littafin kurkukun ƙaddara hada abban sojoji, Ga link ku yi joining👇


https://arewabooks.t/chapter?id=6535288c429337735998e5aa


Masu son paid group na whatsapp 08103884440

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post