MIJIN MAGE🐿️
(kuliyya).
The king 👑 and queen 🔥
Prodly with my first novel 🥰
Littafi daki ƙunshi da
***Makirchi***
***Zalunci****
***Munafurchi***
***Yaudara*****
***Chin Amana***
***Jahilchi********
***Zumunchi*****
***Soyayyya*****
***Riqon addini**
***Nishaɗi*******
Story and Writing
by
Narnah kanwar soja 🥰
Facebook page"Narnah kanwar soja"
Wattspt number
08101235739*
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
بسم الله الرحمن الرحيم
Before I begin to write anything .
Ina son in Fara da godiya ga Allah subhanahu wata'ala mai kowa mai komai, da ya bamu tsawon rai da lafiya har muke bauta mai…..🙏🙏
D'aukaka da aminci su tabbata ga wanda a kayi duniya da lahira domin shi, d'an gatan Allah masoyin Allah Sallallahu alaihi Wasallama 💖.
Hakin mallaka:ban yarda wani ko wata suyi Amfani da wani sashi na wanan littafin ba,ba tare da izini na ba..
Wanan shine littafina na farko Ina fatan zakuyi hak'uri da duk wani kuskure da kuka yi karo da shi..
Ina mai rok'on ALLAH subhanahu Wata a'la Kamar yanda ya bani iko da damar farawa lapiya yasa na Gama lapiya, ALLAH yasa mu amfana da abunda nazo dashi.
GODIYA: Ina godiya ga Auntie's nawa da suka bani shawarwari da gudumumawa a garani
Abokiya ce,kuma uwa ce Amreesh babban yarinya ke ta musanmance a gareni, Allah ya barmu tare..
Godiya Mai tarin yawa gareki k'anwata ta gari mhiz Shatourh 💝💝
Much love to you all ♥️💝.
First page
*********" Abun bauta ya ƙara tsawon kwana
Abun bauta ya ƙara girma da d'aukaka
Sa gabanka inda kaso namiji uban mazaje
Fari mai farin aniyya.
Mai farar zuciya, mai farar doki,
Ginshiƙin dutse,kowa yayi karo dakai shi ka faɗi,
Hadarin ƙasa maganin mai kabido, Gaba salamun baya salamun,
takawarka lapiya Dan sarki jikan sarki!!
Hadari sa gabanka inda ka ke so!!,
Zakin fama kowa yaja dakai zaici k'asa!!!
A ganka abar ka Yarimah Mai jiran gado,kaje lapiya ka dawo lapiya
Duk wanan kirarin wasu laftan-laftan mutane ne ke masa kirari,
Kai idan ka gansu ka rantse samudawane,ga wasu zabga-zabgan dorinoni (bulalar fata) riqe a hannun su,
ga fuskan Nan babu alamar Wasa ko murmurshi.
(lokachin da Idanuna sukayi arbah da wanan zabga zabgan bulallar ce wa nayi na fasa d'auko wanan labarin duk da cewa nimah fa kanwar soja ce🤣).
Kwari da baka abun Harbin namun daji ga masu zuwa farauta,
Aman Kash anan kam Ana jiran ɗan Adam da zai kawo wah Yarima Hari ne a farauci ransa.
A bayan wanan mazajen duniyar A kwai wasu kyawawan Mata cikin shigar Al'adarsu na zani da kallabi da rigar da tayi daban da kayansu, kowacce na d'auke da kwando Nan gaba da yasha kayan Alatu na ado .
A bayan wanan dandazon niii Naga wasu bayi sun zube suna ta jirah kirari!! Abundai abun burgewa.
(ganin hakan nimah na bi sahu Kar naji bulalla a bayana🤣)j
Download littafin Mijin Mage comple Document domin cigaba da karatantawa.
Kada ku manta kuyi comment da share