YANDA ZAKI HADA DILKA DA KANKI

YANDA ZAKI HADA DILKA DA KANKI

Dilka

Sharadin shine ayi Sharing domin yan uwa su amfana πŸ””πŸ””πŸ””

An fi sanin mutanen Barno wurin amfani da garin dilke don gyaran jiki.

Hakan ne ya sanya a wannan makon muka kawo muku yadda ake hada dilke.

Yawanci ana amfani da garin dilke ne wurin gyara wa ‘yan matan da suke shirin zama amare jiki, akan yi hakan ne kafin a yi bikinsu.

Akwai hanyoyi da dama da ake hada dilka;

↬Akwai na dankali da na gyada.

Shafa dilke a jiki na taimakawa wajen cire fatar da ba ta da amfani a jikinmu kuma yakan s fata ta yi laushi da santsi da kuma kyalli.

Abubuwan bukata:

Gyada πŸ₯œ da πŸ₯ƒ man zaitun da ☕ ruwa.

Hadi: A nika danyar gyada tare da bawonta, sannan a wanke ta da ruwa, daga nan zuba ta a matsami, sannan a soya ta da mai kadan har sai ta canza launi zuwa ruwan kasa.

Yadda za a shafa:

A tafasa ruwan zafi, sannan sai a kwaba garin dilke da mai kadan har sai hadin ya yi kauri.

Bayan hakan, a jika fatar jiki da ruwan dumi kafin a fara shafawa da tafin hannu. Bayan an gama dirza dilke a fata an cire dattin fata, sai a wanke da ruwan dumi.

A bar jiki ya bushe kafin a shafa man shafawa.

MALLAKAR MIJI CIKIN SAUKI*

■ GYARAN JIKINMU TA KO INA YADDA ZAKI DINGA KYALLI, SANTSI, KAMSHI, MAGANIN KURAJE ■

♜SABULUN KURAJE♜

• Asef soap

• Pharmaderlm soap

• Kanwa

• Jar dilka

• Zuma

• Lemon tsami

Ki goga sabulun kowanne guda uku, sannan ki zuba kanwarki dakakkiya cikin karamin cokali, kinkwaba dilka da ruwan zafi cikin cokali cin abinci daya ki zuba a ciki, ki matse lemon tsami daya a Kai kisa Zuma cokali biyar ki hada ki kwaba sosai, ki lailaya sai ki dinga shafawa a fuskarki kamar ya rage minti biyar kafin ki shiga wanka, Indan kin shiga wanka sai ki kuma wanke fuskarki da sabulun kamar uku ko Dama da haka.

☛SABULUN FIDDA TABO☚

Ko Zuma Zaki Iya shafawa idan Zaki kwanta bacci sai da safe ki wanke da ruwan dumi.

⇛Misscoroline soap

⇛Shary soap

⇛Aloevera soap

⇛Garin alkama

⇛Zuma

⇛Kanwa kadan

⇛Lemon tsami Bari 1/1

Sai ki goga su ki hada ki zuba Zuma a ciki da lemon tsami da kanwarki ki kwaba, ki dinga shafawa fuskarki minti biyar kafin ki shiga wanka, idan kuma zakiyi wanka dashi Zaki dinga wanke fuskarki.


❮SA MAIGIDA BITA ZAI-ZAI❯

Idan kina yin haka dole maigida yaga kinyi kyau fiye da ko yaushe jikinki da fatar fuskar ki zata yi haske.

︽ Lalle

︽ Kwanduwar kwai ³

︽ Manja cokali ³

︽ Kur-kur

sai Ku kwaba su guri daya Ku shafe jikinku zuwa awa guda, sai Ku yi wanka da ruwa zalla in dai kyan fata ne sai dai agani a jikinku, kowa zaiyi sha'awar ki.


⟪GYARAN FATA DA JIKI HADIN SABILU⟫

Dole maigida ko saurayi yai tabinki zai-zai to yaga kin yi kyau. ke dai yi wanka da

SABULUN BITA ZAI-ZAI

Dudu osun

Dettol

Sabulun Ghana

Garin zogale

Farar albasa

Sai Ku hade su guri daya Ku kirba su a turmi ki mulmula Ku rinka wanke fuska zaku ga yadda fuskarku zata yi kyau.

BITA ZAI-ZAI

Sunan hadin kenan idan dai kana yin wannan hadin zaki sha mamaki za kibani labarin amfani hadin tabbas idan amarya tayi wannan hadin zata kidima ango har yakasa gane ta sai yayi da gaske ke dai yi mugani domin gyaran jiki.

- Ayaba

- Lemon tsami

- Tataciyar madara

- Kwai uku

zaku sami ayaba mai kyau Ku bare Ku matse da hannun ko Ku markada yi laushi sai Ku zuba tataciyar madara Ku fasa kwai kamar uku amma farin zaku zuba sai Ku matse lemon tsami Ku gauraya shi Ku shafa a jikin Ku ya sami kamar tsayin ¹ daya sai kuyi wanka da ruwan zafi, idan har kuka lazimci yin haka ba magana.

___________________________________

  SABULUN GYARA FATA

Idan har kina San gyaran fata kina iya wannan hadin domin gyaran jiki, fatar ki zata yi kyau sosai.

Sabulun sel

Sabulun salo

Lalle

Zuma

Garin darbejiya

Sabulun premier

Kurkum

Sabulun zaitun

Dudu osun.

Dettol

Zaki daka sabulun duka ki zuba a mazu Bi ki zuba lalle da majigi a Kai da zuma da kur-kur ki juya shi sossai garin darbejiya kuma ganyen Zaki samun ki shanya ki daka ki tankade ki hada akan sabulun ki saka ruwa kadan ki juya yadda zai hade jikinsa Zaki ga yadda fatarki zata canja sirrin kyau.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post