Jawaheera Complete Page 4

Jawaheera Complete Page 4

 

Hausa novels complete

☘️🍀☘️🍀☘️🍀☘️🍀

   

         *JAWAHEER* 


☘️🍀☘️🍀☘️🍀☘️🍀 *NA* 

 NUSAIBA ALKAMAWA


   PROFICIENT WRITER'S ASSOCIATION


 *Tare Da* 


 SAYYADA Barrister


MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

 *Part 4* 

________Jawad na niyyar tashi Dady ya tsayar dashi da faɗin," akwai maganar da xamuyi da kai , gyara zama Jawad yayi sosai ya maida hankalinsa wajan mahaifinsa.


"cikin nutsuwa da dadtako dady yace my son akwai waliman buɗe asibitinka bana son walimar tadau lokaci,kuma naji daɗi da zakayi aiki agidanka Nigeria baka ga kuɗin da ake baka ba kaxaɓi nan ƙwarai naji dadi sosai.


"murna ce takama Jawad yace dadi ina da kishin kasata ko da nafara aiki a asibitin cen SBD bankammala karatuna ba Shiyasa naxaɓi abinda zai debin kewa shiyasa ina gamawa nataho kasata Nigeria SBD nabasu tawa gudummawar, godiya yayiwa mahaifinsa tare da addu'oi.


"Dady yafurta da "amen" yace kaga saika faɗawa abokanan arziki  "to dady insha Allah" mikewa yayi cike da nutsuwa yayi musu saida safe Allah yakaimu suka furta atare.


_____Dakinshi yashiga yana mai godiya ga Allah daya bashi iyaye nagari. jawad yana fita dady yadauko wayarshi yakira number Alhaji Abdullahi basu dade da haɗuwa ba Amman sunyi sabo sosai kamar waƴanda sukayi shekaru maiyawa suna tare alhaji ABDULLAHI na kwance akan gadonshi yayin da ammi kemasa tausa, wayar shi ce tadau ruri yadauka tare dayin sallama bayan sun gaisa alhaji Abdallah

Yace ya yaran nawa?


"suna lpy daman Jawad yadawo jiya shine nace Bara na faɗa maka to kuma inaso na hadamai walima bude asibiti ne "murmushi Abba yayi yace amma naji dadi shine baka sanar dani dawowar  my son din nawa da wuri sai yanxu kasan fa bantaba ganinsa ba Amman gaskiya baka kyauta minba ace babban ɗana yadawo amma 

Saiyanxu zaka sanar dani? calm down alhaji abinda jibi xakazo kaganshi yauwa katawo da ƴaƴan nawa gabaki ɗaya dan susan juna karsuje suhaɗu ahanya kowa yahuce dan uwanshi baisani ba  muji kunya.


"aikuwa dai alhaji," kaga ranar juma'a ne  karfe shidda Allah yakaimu amen.


Kashe wayar sukayi Abba yajuyo ya kalli Ammy yace kinga wai yaron alhaji  adamu harya dawo

Daga u.k yagama karatunshi  to yanxu dai jibi xamuje dukanmu harke gobe xamuje dake idan Allah yakaimu asiyo musu kaya, yacemin yana da ƴa mace Kinga sai asiyo musu iri daya da mama!  shima jawad din  sai ayi musu iri ɗaya da  imran da abeed.

" aikuwa dai Alhaji sai afadawa yaran zuwa unguwar.


"Washe gari jawaheera da asuba natashi dayake muna da lecture bayan 

nayi sallar asuba kitchen na nufa naha da musu break fast nazo najera musu akan dining bayan nagama sannan nakoma dakina nafara shirin tafiya  makaranta bayan nashirya nafito parlour wajan dining nanu fa nafara break fast ina gamawa nanufi dakin Abba dan gaidashi Nocking kofa nayi muryar Abba naji yace yes come in shigowa nayi da sallama abakinta.


"Amsawa yayi"


 Na tsugunna Abba ina kwana "lafiya lau mamana kintashi lpy?" lafiya klau Abba wajen da Ammy take na kalla Ammy ina kwana "lpy lau yakika tashi?" lpy klau ammy, sallamar yaya Imran mukaji muka amsa,shigowa yayi yatsugunna yafara gaida Abba sannan yagaida ammy , nima jawaheer gaida sa nayi "ya amsa".


"mikewa nayi zan tashi Abba yace "tsaya mama na daman akwai wani aminina to yagayya cemu taron bude asibitin danshi shine yace muje daku duka dan yasanku gobe in Allah yakaimu karfe shidda.


"Allah yakaimu Abba suka amsa Dukansu mikewa jawaheera nayi nace Abba natafi ammy natafi "to saikin dawo mamana cewan Abba" fita nayi nakoma dakina nadauko bag dina nafito baba audu yakaini skul ina sauka nashiga ajinmu naga jahan  hartazo, zama nayi akusa da jahan bamu fito ba daga lacture dinba sai karfe sha biyu kowa kagani kasan agajiye yake muna tafe da ita da jahan.


Jahan tace jawaheer daman Daddy ne xaiwa yaya Jawad walimar bude asibitinshi dan Allah kizo ina gayyartaki.


"jawaheer nace yaushe ne walimar "gobe ne" cewan jahan karfe nawa jahan tace haba jawaheer besty aike yar gidace tunsafe zakizo inda halima kwana xaki.


"Jawaheer nace  kinsan kuma mena tuna jahan besty?"a'a besty cewar jahan, Abba na yace xamu tafi unguwa karfe shida kuma yace dole damu xa'aje  unguwar, tafaɗa tana mejim dadi aranta da Allah yasa batanan xaayi SBD ta tsani yayan jahan din nan, dama ta tambaya ne SBD jahan kardaji haushi ko babu fita unguwa zata ƙirƙirar wa jahan fitan.


"ɓata rai jahan nayi tace kardai kicemin baxa kixo ba tafaɗa cikin haɗe fuska," murmushi jawaheer nayi indai mun dawo da wuri xanxo na kwana inkuma bamu dawo ba da wuri shikkenan nafaɗa SBD karta zargeni.


"Allah yasa kudawo da wuri amen,sallama mukayi kowa yashiga motanshi muka nufi gida.


___________Abangaren su Abbansu jawaheer , jawaheera bamu dade da fitaba suma sukafito sukayi break fast suka shirya sai super market sukaje suka xabo wani arnen shadda mai tsadan gaske akalla kudinsa xaikai nera dubu ɗari biyu  kuma yadi goma suka siya su biyu saikuma wani lace wanda akalla kudinsa xaikai nera dubu ɗari suka dauka su biyu kuma duk siyayyar ashagon ,S.B.Maisallah sukayi dake  kwari suna gama siyayyar direct wajen kai dinki suka nufa Wanda shine yake musu dinki ya iya dinki na maza da mata bayan isarsu wajan aka tare su da mutumci aka basu wajen zama.


"bayan alhaji Abdallah yafito da kayan ne telan yace wa Alhaji wannan kayan mutun nawa za a dinkawa Alhaji Abdallah yace mutum biyu xaka dinkawa dinki mai kyau nandai yayi masa bayani yace masa gobe xaizo yakarba wajen karfe takwas shikkenan alhaji ciro kudi yayi wajan dubu dari da hamsin yabashi yace ga kudin dinki

Godiya yayita zuba mai yana washe baki sallama sukayi suka tafi akan cewa karfe takwas xasuxo karɓa.


"Abangaren jawaheera kuma ina shiga parlour naga babu kowa dakina nashiga naje na kwanta nafara baccin gajiya ban  tafarka ba sai wajan la' asara mikewa nai na faɗa  toilet nayi brush dama ina hutun Sallah  ne,ko abinci ma banci ba babban parlour nafito naga Ammy da Abba a parlour cewa nayi ammy yaushe kika dawo ina kikaje nadawo naga bakwanan? inda kika aikeni naje.


"Abba yace donta tambayeki kike fadawa mama na haka unguwa mukaje kinji mama!to Abba fatan kundawo lpy? "lpy klau mamana xauna kici abinci" to jawo abinci nayi naxu bawa kaita Ammi kinsan waida jahan tagaiya ceni taron da za ayi agidansu shine nace mata muma unguwa xamuje.


_____ aikuwa gwara dakika fada mata haka don kuwa muma fita xamuyi muna xaune muna hira wajan karfe shidda saiga Abeed yadawo daga islamiya dagudu yazo ya rungume Abba Abba "yace my son kadawo" eh Abba na dawo to sannu da zuwa mama!! jeki ciremai uniform to Abba mikewa jawaheera nayi nakama hannunshi inamai cewa shine bakamun oyoyo ba Abba kawai kayiwa  ko Ammy baka ganiba ballanta mani," dariya Abeed yayi yace wllh namantane ai baka manta da dadyn ba nafaɗa ina masa hararar wasa, "eh aunty daidai lokacin da nake cire masa kaya  nayi masa wanka Sannan nasaka masa kayan gida nace kuma yaro gobe xanje unguwa kuma bandakai xamuje, kuka yafara yana cewa yaya jawah nidai sainaje dariya nayi nace kai dawasa nake maka daman kai ragone .


Dariya yayi yace ai aunty dani xa aje ko "eh xanje dakai shikkenan?


______Washegari  alhaji Abdallah da wuri yatashi yanufi wajan tela yana zuwa yagama dinkin dayake anbashi kudi ishashshe karba yayi yayi masa godiya yanufi gidan abokin nashi.


"Abangaren Jawad kuma da wuri yafara shirye_ shiryen wajan da za ai walimar shikuma alhaji Abdallah yana zuwa haraban gidan yacire na imran dana jawaheer waya yadauko yakira alhaji adam yace gani akofar gidanka dayake Alhaji Abdallah

Yasan gidan nashi kawai dai baitaɓa shiga gidan bane ba .


Alhaji Adam cikin mamaki yace dagaske to kaidai fito kagani mana ,fitowa yayi kuwa  hango motar shi yayi yanufi wajan,cike da murna yatari aminin nasa gaisawa suka fara yi Alhaji Abdallah yabude murfin motarshi ya miƙawa Alhaji Adam kayayyakin ,"karba yayi da mamaki yace wannan na meye Alhaji ?"


"murmushi yayi yace alfarma nake nema awajenka inaso Jawad ɗana yasa Wannan yau sonake suyi iri ɗaya da Imran shikuma Wannan sonake ƴata tasa itama suyi iri ɗaya da mama! murmushi alhaji adam yayi yace yanxu Alhaji harda wannan hidimar Allah yasaka da alheri kadaina min Godiya ai ƴaƴana nayiwa bawani ba.


"haka ne cewar Alhaji Adam toni Bara natafi sai anjima zamuzo.


"Aini naxata ma zama xakai muyi shirye_ shiryen dakai a'a Alhaji sai anjima zamuzo to shikkenan Allah yakawo ku lfy sallama sukayi alhaji Abdallah Yakama hanyar gida shikuma Alhaji Abdallah a parlour yashiga yakirawo mamy yanuna mata kayan da Alhaji Abdallah yakawo itama sosai tayi murna nan danan kuwa yakirawo su Jawad din.


_____Shikuwa Jawad tunda yau yatashi yakejin jikinshi wani iri Amman SBD kar iyayen shi sukula da halin da yake ciki su shiga damuwa yasa baya nunawa, karar wayarshi yaji dagawa yayi daga dayan ɓangaren yaji ance kaxo parlourn dadynka,ammy tana fadar haka takashe wayar.


"Tashi yayi yanufi parlour sallama yayi suka amsa masa Sannan yanemi guri yaxauna yace dady gani kallonshi dady yayi da fara'a afuskarsa mikawa Jawad leda yayi yace ga wannan kayan abbankune Alhaji Abdallah aminina bakusanshi Amman yace xaixo ,yabaku  wannan ne yace yana son kusaka ataron mikawa jahan itama nata yayi godiya suka yi masa suka mike.


Jawad baiji dadi ba SBD yagama tama abinda zai saka ataron Amman Wannan mutumin yayi masa cikas.


Bangaren Abba kuwa

 yana isa gida


Comments and share it

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post