Jikar Iya Episode 19-20 Complete

Jikar Iya Episode 19-20 Complete

 

Teema Cool Hausa Novels

🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️

      *JIKAR IYA*

🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️🙎‍♀️

    Mallakin 

      Teemerh Cool🖊️

           08161316781

*🦅MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*🦅

Bismillahi ramanin rahim

Pages1️⃣9️⃣🆒2️⃣0️⃣

*Banyi edit ba kuyi hkr*

*LONDON*

____Tashi ya yi yana ta famar haɗa kayansa, bai mata magana ba tayi masa magana yafi a irga amma babu amsa, nan ta samu gu taa zauna tana ta famar taunar cigam nata har ya gama haɗa kayansa.

Hanyan fita ya nufa hannunsa ɗauke da akwatina biyu yana jansu, gabansa ta shiga tare da tsare masa hanya da hannayenta, " haba baby ina zaka je ba tare dani ba, sannan baka faɗamun ba, in  laifi namaka dan Allah kayi hkr baz....." wani mari ya sakarmata hagu da dama tare da hanƙaɗeta gefe, nan ta zube a wajen hannunta rike da kuncin nata da yasha mari, fuskarta take ta nuna kasancewarta fara ce, kuka ta saka dan ƙaran tashin mota da taji, tashi tayi da gudu ta leƙa ta window, hangosa tayi ya fita da motar a ɗari da hamsin, ƙara fashewa tayi da kuka inda ta ɗauki wayarta ta lalubi number Sa'eed da ƙyar, sai da ta masa ƙira uku tunna ya ɗauka, nan ma Sallama kawai ya mata daga nan bai ƙara magana ba, ko amsa sallamar ma bata iya yi ba sai kuka take yi, jin tana kuka sai hankalin Sa'eed ya tashi akan ko wani abune ya samu Zohaib, magana yake mata amma ta kasa tsayar da kukan nata, ransa ne ya ƙara ɓaci daman shi ba burgesa take ba sannan kuma yanzu ta ƙirasa tana masa kuka ta kasa faɗa masa komai, cikin tsawa ya ce mata " wai ba za ki faɗamun abun da ya faru da Zohaib ba, sai kuka ki ke mun, ki faɗamun mutuwa ya yi ne?" ya ƙarashe magana cikin rauni, dan jikinsa ya yi sanyi.

"Zohaib ne ya ƙwashe komai nasa ya fita cikin fusata, ina tambayarsa sai marin da ya zabgamun a maimakon ya bani amsa, sannan kuma yana driving ne cikin ganganci " bayan takai zancen ne ya ƙara fashewa da sabon kuka kamar sabuwar amarya.

Jin ba mutuwa abokin nasa ya yi ba yasa shi sauke ajiyar zuciya, sannan ya bata hakuri tare da faɗin su haɗu a airport, motarsa ya ɗauka shima ya yi can itama haka yake a ɓangarenta airport ɗin ta nufa.

Zaune yake ya kwantar da kansa akan hannayensa, inda yake jirar bizansa ya fito, jin an dafasa ne ya dawo dashi daga tunanin da ya tafi, juyawa ya yi da sauri dan ganin waye ne, Sa'eed ne yake koƙarin zama daga gefensa, bayan ya zauna ne yake faɗin "why Zohaib za ka yi haka, sannan in laifi aka maka ni mai na maka da zaka tafi gida ba tare da ka sanar mun ba, asalima ni kayiwa laifi, amma kuma yanzu ka ke ƙara yin wani laifin babu komai, yanzu nasan matsayina a wajenka, yana kaiwa nan ya miƙe da niyar zai tafi, riƙe hannunsa Zohaib ya yi tare da kai gwiwoyinsa kasa yana faɗin "please my Sa'eed karkayi fushi dani, nima bansan zanyi tafiyarnan ba sai da na tashi naji banason zaman nan ɗin, hankalina duk ya yi gida wannan ne yasa na taho nan, amma kayi hakuri bazan ƙara ba" ya ƙarashe maganar yana haɗe hannayensa biyu.Tausayin abokin nasa ya shiga yi tare da tunanin ba lafiya ba gaskiya, dan yadda Zohaib ya tsani Nigeria, ɗagasa ya yi sama tare da rungumarsa, wani hawayene mai zafi ta samu damar gangarowa daga fuskarsu, inda suke rufe idanunsu tare dan bawa wannan hawayen damar gangarowa, inda Zohaib ya buɗe idaanusa tare da saukewa akan Amrish da ta iso wajen, zame jinsa ya yi a jikin Sa'eed tare da faɗin " ki barnan, mai yasa ki ke bina " yana kaiwa nan ya bata mari hagu da dama, yana yunkurin ƙara mata sai Sa'eed ya yo saurin rike masa hannu, inda ita kuma Amrish ta dafe kumatunta, tare da faɗiwa kan gwiwarta tana kuka tana faɗin "wlh Zohaib ko za ka kasheni bazan daina binka ba, sannan kuma bazan iya rayuwa babu kai ba, kaine rayuwata" ta ƙarashe maganar cikin sheshsheƙar kuka."Au baza ki iya rayuwa babu ni ba, Amrish na sakeki saki ɗaya, Amrish na sakeki saki biyu, Amrish na sakeki saki Ukk......" bakinsa Sa'eed ya rufe masa, inda duk jama'ar dake kai komo a airport suke zagaye dasu, wasu kuma na musu video dan abun ya basu mamaki yadda akayi saki uku dukka a airport, abunne ya bawa Sa'eed haushi yadda ake musu video ɗin, ganin an fara haramar shiga cikin jirgin yasa Sa'eed tura Zohaib akan ya tafi, dan yadda yake a fusace yake kuma jikinsa sai rawa yake dan ransa ya ɓaci baya iya controk ɗin kansa.Shiga ya yi ransa a ɓace dan kamar ya ƙara dawowa ya ƙarya Amrish zaifi farin ciki, amma Sa'eed bazai barsa ba, da haka ya shiga har jirginsu ya tashi zuwa Nigeria.


Ita kuwa Amrish tana ganin jirgin ya tashi ta mike daga durkushen da take, hannunta ta ɗaga sama tana ihu tana faɗin "Wayyo Allahna Baby Zohaib karka tafi ka barni" kuka take yi kamar wacce aka aikowa da sakon mutuwar uwarta.
Ai kuwa mutane basu tsaya da video ba, dan abun fa ƙara basu arɓashi yadda aka mata wannan mummunar sakin amma kuma bata hakura ba, take ƙara nuna tana butar kusantuwarsa a tare dashi, wasu na faɗin in suka yi update ɗin wannan zasu samu followers sosai.Yadda ta ƙara zufewa akan gwiwoyinta ne tana ɗanɗaga hannu sama, kamar wata mai shirin firewa sama.
Hannunta Sa'eed ya kama tare da jansu har sai da yakaita ga gaban motarsa, buɗewa ya yi tare da hanƙaɗata cikin motar, rufewa ya yi tare da jan motar da a guje, shi ba abun da ya ɓata masa rai irin wannan video da aka musu, amma bayan wannan sai abun da yake damun abokinsa, amma sakin da aka yimata bai damesa ba, duk da ba abune mai dadi ba.Yana kaiwa izuwa gidan Zohaib ya yi parking inda ya ce mata ta sauka, sai da tayi kusan minti biyar dakyar ta iya jan ƙafarta ta fita, inda shi kuma ya bawa driver gidan key mota biyu dana Amrish dana Zohaib akan yaje airport ya ɗauko motocin.

Tana sauka yaja motarsa ba tare da ya mata magana ba.Alhaji Abubakar yana zuwa garin ya yi gidan Iya, amma bai sameta ba, nan yaje gidan ƴar Iya inda ita ma bai sameta ba, sai mummunar labari da ya samu akan ƴar Iya, nan ya wuce Police station ɗin inda yana zuwa aikuwa suka rikesa, tare da sakin ƴar Iya akan tunda kisan namiji suka yi.Zohaib ya dawo  Nigeria lafiya qlau, inda ya ƙira abokinsa Taufiq ya ɗaukesa, inda suna hanya zuwa wani mai mashin ya shiga gabansu, sai da suka kusan yin accident ma, Allah ne ya kiyaye, Taufiq ne ya fito ransa a ɓace, inda ya yi kan mai adedetar yana ta famar faɗa, shi kuwa mai adaidaitar sai hakuri yake basa amma ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba.


"Wani kalan ƙafirine kai? ana haɗaka da Allah baka ji, ka ganka wai kai masifaffe kafi ka damu mutane da babbami," cewar Iya dake cikin mashin ɗin.


"Kinga tsohuwa ni....."kafin ya ƙarasa maganar dai ya hango Zohaib ya fito yana magana akan yazo su tafi ya ƙyale wayannan ƴan wahala, daga gani wai yinwa yake ji shiyasa ya shiga gabansu.


Nan Indo taji zafin abun da kunnenta ya jiyo mata, inda kuma a cikin a daidaitar ta hango kayan gyara a wani ɗan jarka da taka buɗesa, aciki da abubuwa da dama wanda take ganin zaiyi mata aiki.Nan ta fito inda ta kalli Zohaib kallon sama da ƙasa sannan ta ce "aini anan banga arziki ba, tunda banga yana zuba a ƙasa ba, ko ɗan gidan ƙaruna ne nan bamu asani ba, sai mu masa barka da ya dawo duniyar, kai da ka ke cin abincin banga shinkafa ta maka tsiro ajiki ba, tsabar cinta kaga abun da sauki, dan da zakaje garin mu da kaga masu cin abinci, banda ma Kisan kai muka aikata mai zaisa muzo wannan garin da bakwa ganin mutumcin mutane" jin ta ambaci kisan kai ya tabbatar wa da Zohaib kallon da yake mata na mahaukaciya ce, hakan yasa ta ya yi kokarin shiga motarsu, bayan sun shiga ne ƴar Iya ta yi saurin zuwa kusa da motar ta ajiye musu wasu ƙarafuna, sannan ta dawo da baya ta zura hannunta a ƙwalbatin dake bakib titi, jarƙar da ta gani a ciki ta ɗauko, dan cikinsa ya cika da ƙwata ɗauka tayi ta musu jifa a glass ɗin gaban motar, inda sai da ya fasa glasa ɗin sannan ya fashe, sai akan fuskar Zohaib da yake daga zaune a gaban motar.....


Da gudu ta shiga cikin mashin ɗin inda mai adaidaitan ya yi saurin jan, Iya kuwa daman daga cikin mashin ɗin ta bawa Taufiq amsa, dan ƙafarta sai famar ciwo yake mata wannan dalilin ne yasa bata fita ba, sannan batasan abun da Indo ta aikata ba.


Taufiq ne ya yi kokarin ɗiban motar a milion amma sai yaji wani abu ya tsayar da shi, nan ransa a ɓace ya fito dan duba menene, sai yaga abun da aka saka kuma tayar tayi faci, sannan kuma ga babu mai gyara a layin dan unguwar na manya ne, yawanci inda ake musu gyara sai waje n wane da wane.


Zohaib in ransa ya yi dubu to yau ya ɓaci, dan tunda yake bai taɓa ma kusantar wannan abun ba, dan bazai iya baka ma sunan abun ba, kasa magana ya yi kasancer har fuskarsa ya taɓa, Taufiq ne ya dawo cikin motar inda ya mikawa Zohaib tissue, gogewa ya shiga yi sannan ya samu ya fita daga motar, Taufiq ne ya bisa da Rufaida Table Water inda yake wanke fuskarsa da kuma sauran jikinsa, ransa ne a ɓace dan shi yasan mai yake ji a zuciyarsa, sai da ya gama ƙarar da ruwan amna shi duk da haka ƙenƙemin kansa yake.


"Na ratse kama da Allah bazan bar wannan yarinyar ba, ko ƴar Uban waye a garin nan sai nasa annemota kuma na hukuntata, ni zata shafawa diasease water, Taufiq mai sunan abun ne?" ya yi maganar yana yatsina fuska kamar wanda abun yana cikin bakinsa.


"Ai ba ƴar uban kowa bace sai ƴar talakawa, ƴar wahala ƴar masiyata, ni ina zansan sunan abun maybe Blackwater suke cewa ko" cewar Taufiq yana ƙoƙarin kiran waya.


Abokinsa da gidansu yaka area nan ya ƙira a waya cikin minti biyar sai gashi da mota, nan suka shiga.Mai mashin yakai Iya da Jikarta gidan Alhaji Abubakar dake unguwar Nasarawa, inda ya shigar dasu har ciki, mai mashin ɗinne zai fito sai sukaci karo da su Zohaib za su shigo, baya ya yi inda su Iya da jikarta suke tsaye da kayansu a gabansu, ganin wannan yarinyar a cikin gidansu yasa Zohaib buɗe motar tun kafin ayi parking..........
*LAST FREE PAGES**TO JAMA'A KUNSAN DAI HALIN  HAJIYA KAMALA, SANNAN KUMA GA ABUN DA JIKAR IYA TAYI WA ZOHAIB, SANNAN KUMA GA ALHAJI ABUBAKAR A HANNUN ƳAN SANDA, SANNAN KUMA KARKU MANTA DA ISAR KAN DA IYA SUKA AIKATA DA JIKARTA, SANNAN KUMA YA KUKE GANIN ZAMAN IYA ZAI KASANCE A BIRNI, SANNAN KUMA YA BATUN SAKIN DA ZOHAIB YA YIWA AMRISH, SHIN AMRISH ZATA AMINCE DA WANNAN KADDARAR KI KUMA WANI MATAKI ZATA ƊAUKA, SANNAN KUMA AKWAI SAURAN LABARIN DAN GANE DA ƘAUYE, DAN ABUN DA INDO TA AIKATA KAFIN FASA AUREN ƳAR MAI GARI, DA KUMA HATSANIYAR DAKE TSAKANINSU DA INDO, DUK KU KASANCE DANI TEEMERH COOL AKAN NAIRA ƊARI UKU KACAL, KU BIYA ƘUDI KU KARANTA SHINE ƘAUNAR DA ZAKU NANUMUN, NA GODE*Wannan littafin na kuɗi ne, ki biya kuɗinki ki karanta shine mutuncinki, ban yadda a fitar mun da littafi ba dan kin siya, duk wata mace mai aji bazata karanta littafin sata ba, ki mallaki naki akan naira 300 kacal post kwana biyar a sati, special 500 post kullum , 9048703453 Fatima Muhammad Aliyu opay bank sai ki turo shedar biyan kuɗinki ta wannan number 08161316781, in kuma kati ne MTN,  AIRTEL,9MOBILE, duk ina using dashi, sai a turo hoton Katin, na gode sosai.


TEEMERH COOL🖊

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post