Kurman Baƙi Page 10

Kurman Baƙi Page 10

 https://chat.whatsapp.com/EKyzZCUEGyRAEGGAnTHmGF

*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 10

               Hankali kwance cikin nutsuwar ta ta macen da tasan kanta ta tura kanta cikin gidan bakinta dauke da sallama. Sai da tayi sallama sau biyu kafin a amsa. Daga can cikin daya daga cikin dakunan dake hannun hagunka.


"Da alama umma bata nan" ta fadi qasa qasa ta wucewa dakin da take jiyo ana amsa mata sallamar.


            Labulen ta dage tana sake jaddada sallamarta. Ido hudu sukayi da matashiyar dake zaune saman abun salla. Sanye take da hijab har qasa,baka ganin komai sai fuskarta da tayi wani haske dauuuu,irin hasken da kana masa kallon farko zaka san cewa ba natural haske bane. Hannunta da yanayin hasken fatarsa yasha banban da hasken fatar fuskarta na riqe da carbi tana ja daya bayan daya,bakinta yana motsawa mis mis da alamun wani abun take karantawa


"Iskancin banza,ashe kina ciki kina jina naketa kwada sallama" ta fadi tana dan jifanta da harara hadi da zare takalminta ta shigo dakin gaba daya tana cewa


"Yo wannan basai a shigo ayi muku sata bama?" Tayi maganar tana zama gefan kujerar guda daya dake dakin idonta akan matar.


               Hannunta ta dora saman bakinta alamar tayi shuru,sannan taci gaba da jan carbinta. Sasakai ruqayya tayi tana binta da kallo,sai kuma taja tsaki ta maida dubanta ga dakin.


                Kayan ado ne jere sama madubin,mayuka kala kala da turaruka,harda kwalabe da gwangwanayen supplement kala daban daban.


              Kan supplement din hankalinta yakai,ta miqa hannu daga inda take ta dauki wata zungureriyar kwalba dake dauke da syrup a ciki. 


                Tun a rubutun farko ta fahimci maganin qara qiba ne,saita daga kai tana kallo fuskar matar dake zaune akan sallah. Tabbas,ta qara qiba qiba data jima tana mamakin ya akayi wasila siririya da ake tsokanarta da sunayen tsokana kala kala saboda rashin qiba lokaci guda tayi irin wanna qibar?. Mamaki ya hanata magana,saita mayar da kwalbar ta ajjiye dai dai sanda idonta ya gano mata wani tablet din dake nuna whitening yakeyi. Kai ta sake jinjinawa tana maido dubanta ga wasilar,dai dai nan ta shafa hannunta akan fuskarta da alama ta gama.


"Ke kuwa me kika zauna yi har rana tana shirin faduwa bakiyi sallar la'asar ba?"


"Haba ni da nake da tarin buqatu?,ta yaya zan bari sallar ta kufecemin? la'asar dinta liman yana sallamewa ina sallame tawa,wannan wani wuridi aka bani nakeyi"


"Wuridi ko addu'a"


"Duk daya ne ai" ta amsa mata tana ninke sallayarta


"Addu'ar ce idan anayi ba'a amsa sallama?,nidai a iya sanina salla ce kawai ya haramta idan anayinta ayi magana" Ruqayya ta sake jifanta da tambayar


"Ke wannan ba irin addu'ar da kika sani bace,wannan ta neman miji ce,yazo ayi aure nima na ganni a dakina na huta kamar kowacce mace" ta fadi tana zare hijabin jikinta t wurgar gefe,hakan ya sake bayyanawa ruqayya qibar da ta tsammata daga wasilar,saidai ashe hijabi ma ya rufe wani abun.


               Kasa shuru ruqayya tayi tana duban wasilan tace


"Yanzu wasila wannan wacce irin qiba ce haka da uban fari da fuskarki tayi?,ga kunnenki duk kin bula kin cikashi da barima?" Gefen ruqayyan ta zauna tana daukar wayarta


"Ba zaki gane bane,ke don kina dakinki asirinki a rufe,yanzun rayuwar sai da updating sai kina gyara,idon mazan a bude yake,saisu rainaka ko kiga wanda baikai ajinka ba yazo yace kai yakeso saboda rainin hankali"


"Yanzu qibar da farinma kenan yayinsu akeyi"


"Ke,qwarai kuwa,mace 'yar duma duma ai duniya ce,farar mace kuma itace alkyabbar mata,lantarkin gida,ajebo kalar hutu,sadakinsu ma daban yake,hakanan sunfi shiga" hangame baki tayi tana kallon yadda wasilan ke magana da confidence. Tare sukayi yammatanci da wasila,tunda can tana da surutu da rawar kai,amma yanxun kamar an qara mata da wasu sabbin halayen


"Indai hakane kice mu da bamu samu mashinshini ba"


"Da kenan,sanda kukayi aure ai duniya a kwance take,shekara bakwai zuwa takwas baya fa,kema ba yadda banyi ki goge baqar fatar nan ba kikaqi,ai gashinan kina zaune kina ji kina gani mijinki yaje ya dauko farar,wadda ma bata fiki komai ba" dariya wasilan ta bata yadda take nuna jin zafi da jin haushinta duk sanda akayi zancan zainab


"Wai tsaya,kin manta bleaching haramunne?"


"To ya za'a yi?,neman wanda zamu shige daga ciki kawai mukeyi?" 


"Tabdijan,wasila?,a haka?,kina abinda Allah bayaso amma ke kina neman ya dubeki?shaidanne fa yayi alqawari da kansa Allah ya fada mana cikin suratun nisa'i aya ta dari da sha tara,cikin alqawarin da yayi yace zan sanyasu su dinga canza halittar Allah,cikin canza halittar Allah wadan nan abubuwan suna daga cikinsu,kisha magani ki qara qiba,kisha magani don ki sirance bayan qibar ba matsala take kawowa ga lafiyarki ba,ki shafa mai kiyi haske ko ki shafa mai don kiyi baqi duk da mu an jarabci mutanenmu da son suyi haske ne kawai,duk da ana samu cikin turawa da yahudawa masu maida fatarsu baqaqe,duk me ya kaiki wannan wasila?"


"Ina zuwa" ta fadi tana dagawa ruqayya hannu sakamakon kiran da ya shigo wayarta.


              Da kallo ruqayya ke binta da shi har ta gama amsa wayar tana gatsine gatsine hadi da amsa maganarsa da qyar. Wayar ta wulla gefe tana jan siririn tsaki


"Sirikin namu ne?" Ta tambayeta tana ciro tata wayar daga jaka ta kirayi shukra taji yaushe zasu iso


"Wa?,Allah ya kiyaye,sulaiman ne fa" tsayawa ruqayya tayi da abinda takeyi tana duban wasila cike da mamaki


"Sulaiman dinne abun Allah ya kiyaye?,badai sulaiman wanda yazo duba umma sanda aka kwantar da ita a asibiti ba"


"Shine,amma ke kinga mijin aure a nan?" Ta jefawa ruqayya tambayar tana kallonta


"Ni kuwa naga mijin aure nagartacce ma,me sulaiman ya rasa?" Baki wasila ta tabe tana jawo carbinta ta saka a yatsarta ta fara ja tana cewa


"Abubuwa da yawa mana,haba ruqayya kamar makauniya?,yana da rufin asirinsa yana da hali me kyau,amma gaskiya kamar bai qarasa irin mijin da nakeson aure ba" Mamaki ya qarasa kashe ruqayya


"Amma yanzu bake na samu kina wasu wuridai ba duk akan Allah ya kawo miki miji kiyi aure ki huta ba?"


"Eh amma mijin ai ba kowanne iri ba,irin sulaiman ina dasu sun kusa hudu,amma wanda yadanfi hakan rufin asiri nake nema,bance saimai shahararren kudi ba,amma ina laifin miji kamar naki saleem din,ke ba motar hawa gareki ba yanzu ke da kishiyarki?" Kasa cewa komai ruqayya tayi mamaki yana ci gaba da kamata


"Kuma ma dazu dazu na dawo daga gurin wani bawan Allah,yayimin istihara ya gayamin aure na da isma'il babu alkhairi a cikinsa sam sam,mijina yana nan zuwa,dan kasuwa ne a kantin kwari,kinga kuwa ta yaya zan tsaya ina dagawa kaina hankali akan wanda nasan ba mijina bane"


"Shi din Allah ne da har zai fadi abu ki yarda?"


"Amma istihara ai ba qarya bace"


"Wacce irin istihara yayi miki?"


"Normal istihara da aka saba,carbi ya ajjiyemin yace na zabi daya,da na dauka na miqa masa ya karba na wasu mintuna sai yayi min bayani,babu qasa a wajen bare dai kice min duba ne" wasila ta fadi cikin gamsuwarta da abun.


              Cike da takaici ruqayya ke girgiza kai tana duban wasila


"Wai duk yawon islamiyyar da muka dinga yi ina naki karatun yayi wasila?,dama haka annabi ya koyar da istihara?,suna fakewa da duba suna canza masa suna da istihara?,wallahi sai sunyi shari'a da annabi,ba wani wanda zai maka istikhara kai zakayi abarka da kanka,bayan kinyi sallar raka'a biyu zaki karanta


*_Allahumma inni astakhiruka bi'ilmika,wa'astaqdiruka bi qudratika,wa'as'aluka min fadlil azeem,fa'innaka taqdiru wala'aqdir,wa ta'alam wala a'alam,wa'anta allamul guyub,Allahumma in kunta ta'alam anna hazal amra(saiki fadi buqatarki)kairul lee,fi diny wamu'ashy wa'aqibatu amry,fayassirhu ly summa barikhly ly fihi,wa'inkunta ta'alam anna hazal amra(saiki fadin abun),sharrully fi diny wamu'ashy wa'aqibatu amry fasrifhu anni,wasrifny anhu,waqduriliyal khairu haisu khana,summa ardini bihi) annabi yace ba wanda ya taba istikhara irin wannan bayan yaji ya gamsu da abun ya zartar da shi,daga baya kuma abun ya zame masa nadama,idan kayita kayi shawara da mutane nagartattu guda biyu akansa sannan ka zartar" .


              Kai wasila ta kawar tadan mele baki sannan ta dawo da dubanta ga ruqayya


"Na gode da tunasarwa,amma na jima ina yin wannan ai,sannan shi kansa abinda ke faruwa jifana akayi,mutum kusan biyar suna gayamin asirin akayimin don kada na auru,ina da magauta da yawa da maqiya,duk wanda naje gurinsa cewa yakeyi a gaba aka sakoni" 


"Babu wanda yasan gaibu sai Allah,amma asiri gaskiya ne yana kuma iya kama mutum,saidai bisa amincewar Allah ne,ba wanda ya isa ya cutar dakai sai Allah yaga dama,akwai kuma ayoyi daga alqur'ani da tsafatattun hanyoyin warware sihiri da kuma kare kai daga sake kamuwa dashi,kamar cikin suratul a'araf......"


"Duk fa inayinsu amma.....hmmmm" sarai ruqayya ta fahimci me takeson cewa,sai ta gyara zama


"Eh bata karbu ba kikeson cewa?,ko kin dade kinayi ba nasara ko?,to bari kiji wani abu da baki sani ba,ita kanta addu'a tana da qa'idojin yinta da amsata.....indai zakiji a ranki addu'arki bata karbu ba to kin wargazata,indai zakiyi......"


"Kinga rubutamin addu'o'in saina hada dasu" ta fada tana zaro biro da memo ta miqa mata,sannan ta miqe tana fidda kayan jikinta.


"An kusa kiran sallah,akwai hayaqin da zanyi kada lokaci ya wuce,ina zuwa" ta fada tana daura zanin fallen atamfa tana fita a gaggauce daga dakin.


            Da kallo kawai ruqayya ta bita dashi,saita girgiza kanta takaici yana kamata,cikin qasa da minti biyu qaurin hayaqi ya risketa a nan inda ta barta a zaune.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post