Kurman Baƙi Page 11

Kurman Baƙi Page 11

 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫


*HUGUMA*


PAGE 11

https://www.mkdatasarvices.com.ng

*MK DATA SERVICES* _ake magana_👇🏽👇🏽👇🏽


*_INA MASU SARIN DATA,BIYAN BILL KO SUBSCRIPTION KO MASU SIYAN DATA DIN MA KADAI DON AMFANIN KANSU?_*


*_TO KU MARMATSO KU BANKI ARON HANKULANKU DON KADA AYI BABU KU!!_*


*_GA WANI SASSAUQAN WEBSITE DON SIYEN DATA CIKIN FARASHI ME SAUQI DA RANGWAME_*

https://www.mkdatasarvices.com.ng

_Ga me neman qarin bayani ko magana dasu kai tsaye sai ya tuntubesu ta wannan number wayar_


08038258489*ARAHA SAUQI DA RANGWAME KAMAR AN BAKA A KYAUTA*🫰🏾🫰🏾  

              Tana saka kanta a tsakar gidan umma tayi sallama


"A'ah,baqi mukayi?" Umman ta fada cikin fara'a. Tun asali ita din macace me kirki da qoqarin zumunci,saidai ubangiji ya jarabceta da dabi'ar son 'ya'ya. Irin matan nan ne da basa iya boye soyayyar yaransu,wannan ya sanya abubuwa da yawa da yaran zasu aikata ba kasafai suke iya tsawatar musu akai ko su hanasu ba.


"Sannu da zuwa umma" ruqayya ta fada tana murmushi,a ranta tana jin dadi me yiwuwa umman yanzu data shigo ta taras da uban qauri hayaqin turaren ta yiwa wasila fada,iya zallar qaurin ta isa ta sanya ka samu matsala idan kana da cutar asma


"Tun yaushe kika zo?,munyi sabani naje barka 'yar hannatu ce ta haihu" ruqayya na qaramar dariya taja kujerar 'yar tsugunno ta zauna kusa da umma da ita ta zauna saman kujerar bayan ta fidda mayafinta ta rataye jikin igiya


"Ahhhh,umma hannatu ce yanzu da jika?,lallai rayuwa tana gudu" 


"Uhmm,kedai bari kawai,shi yasa yanzu gaba daya hankalina ha koma kan 'yar uwarku,ta samu itama tabar gidan nan,kada na mutu banga aurenta ba" umman ta fada cikin karyewar murya. Gyara zamanta ruqayya tayi


"Umma kada ki damu,muddin kina mata addu'a akwai lokaci shi aure kaman haihuwa yake muddin yazo sai anyishi ba abinda zai canza,lokacinta ne kawai itama baiyi ba" baki umman tadan tabe kadan fuskarta fal alhini


"Uhmmm,mutanene yanzu sun zama abinda suka zama,baka takawa mutum ba baka barar masa ba amma sai ya saka ka a gaba sai yaga bayanka,nidai tunda nake ban tana jifan dan wani da ko Allah wadai ba,amma ni tawa diyar ita kenam qwaya daya an hanata ta motsa" cira kai ruqayya tayi tana kallon umman,alamu dukka sun nuna itama ta yarda da cewa jifa aka yiwa wasila,itama nata idanun sun rufe da tarin kura kurai da dabi'u da ya kamata wasilan ta fara gyarawa saboda ta samu tsakaninta da ubangijinta yayi kyau ta yadda addu'arta zatafi shiga. Sau tari mune sila na rashin karbuwar addu'o'inmu,amma saimu danganta sanadin ga wani ko wata.


"Don Allah umma kada ki saka wannan a ranki,hadisi ne guda daga ma'aiki cewa,idan da dukka mutanen duniya zasu taru don su cutar da kai,ba zasu iya cutar da kai ba sai abinda Allah ya rubuta a gareka,hakanan idan da dukkansu zasu taru don su amfanar da kai basu isa su amfanar da kai ba sai abinda Allah ya rubuta a gareka zai sameka"


"Uhmm,kedai Allah ya rufa asiri kawai,ina kishiyar tawa da masu gidan nawa?" Kamar jira suke umman tayi tambayar sai ga sallamarsu,suna gaba yusra na bayansu.


            Da gudu suka qarasa shigowa kamar wadanda suka shekara basu ga mamar tasu ba. A jikinta suka zube iftee ta haye cinyarta


"Ku dagani hakanan ku gaida umma" ruqayya ta fada bayan duk sun gama ifce ifcen.


              Daya bayan suka durqusa suka gaidata har ifteehal da take qarama. Umman ta amsa tana shafa kawunansu sannan tace


"Allah ya nuna mana yaran wasila haka,da tuni itama nata yaran sunkai haka"


"Lokaci dai umma" ruqayya ta fada tana wucewa bakin famfo don yin alwala.


               Tana fitowa ta ji umman na magana da waseelar,waseelan tana sake mata bayanin abinda malamin ya gaya mata


"Wallahi umma da kin barni na tambayeshi,ya gayamin su waye da waye,na rantse da Allah duk randa aurena ya tashi kaf sai na tambayi sunansu,sai naci(ta dura ashar),kuma wallahi wallahi ba wanda zai moreni,ba wanda zaici arziqina,kada ma daga baya kice ai ya wuce na yiwa wance kaza na yiwa wance kaza,arziqin mijina nawa ne saike sai 'ya'yana da wanda naga dama" ta fada tana shanye ragowar rubutun dake cikin leda ta jefa ledar cikin kurfetunsu na girki


"Ki barsu da mugun nufinsu,duk wanda yayi na gari kansa ai ko?". Sake cika da mamaki ruqayya tayi,gaba daya wasilan ta sake canzawa,duk wasu halaye da ruqayya tasan wasila dasu ta ninko wasu a kai wasu kima ta sauyasu gaba daya. 


               Tana salla amma mamaki ya gaza barin kanta,ita wasila dake wannan zancan har ma tasan me kudi zata aura kenan da take zancan ba wanda zaici arziqinta. Kafin ta gama sallar wasila ta shigo dakin,ta nade saman katifarta tanata amsa waya,ko muryarta ma ba'a ji iya ji sosai saboda tsabar sanabe da langwashe murya. Waiwayawa kadan tayi ta kalleta sai kuma ta dauke kai tana ci gaba da lazuminta tana sauraron kusur kusur din wasila saboda bata iya jin muryarta sosai. A gaban umma ta fara wayar,sai daga bisani ta tashi,tana mamakin yadda take iya zance tsaf da saurayi a waya a gaban umman ko yayyenta,ba tun yau ba ta saba hakan dabi'arta ce.


                Dai dai sanda ta shafa addu'a wasilan ta saki siririyar qara


"Da gaske don Allah?.....wow......bari na shirya" ta fadi tana katse wayar gami da saukowa daga katifar


"Ki tayani murna 'yar uwa, iphon 13promax yanzun nan za'a kawomin ita" wasila ta fadi tana bude wardrobe dinta tana zubo da kayan ciki qasa.


"Toooo.......isma'il dinne?" Waiwayowa wasila tayi ta zabga mata harara


"A'ah sulaiman ba isma'il ba,kina da abun haushi wallahi.....wannan wani guy ne irin type dina wallahi" ajjiye carbin hannunta ruqayya tayi ta tallafe habarta


"A'ah,amma yanzu kk ce baki samu wanda kikeso ba ko saboda jifanki akeyi" rigar atamfar ta zaro ta dawo gefan gadon ta zauna tana kallon ruqayya


"Inason mutumin nan ruqayya,amma na masa maganar ya fito yakai sau goma har yanzu shuru,malamai biyu sun gayamin jifan da akeyimin ne yake hanashi turowa,shima yana shafarsa" kai tadan gyada


"Kuma kin tabbatar yana sonki kema?"


"Sosai,ke kinga hidimar da yakeyimin ne?,kuma inda baya sona ai da tuni ya tafi,wata nawa muna tare,munfi shekara fa". Shuru ta sakeyi tana nazari,duk da ita da wasilan tamkar ciki daya suka fito haka suka tashi,kuma ko yanzun dukansu suna iya yiwa juna katsalandan akan abinda ya shafi rayuwar daya,saidai zuciya da kuma shaidan batasan ta fiya challenging wasilan.


"Au,bari na gayawa umma ta tura wani yaron ma ya siyo masa lemo" wasila ta fadi tana fita da sauri a dakin.


              Minti daya kacal ta soma jin muryar umman tana magana


"Bazaiyiwu ba,tunda kinsan ko kin karba Bashir sai ya saka an maida masa,bayan uban fadan dazai hada ni dake yayi mana" 


"Don Allah umma ki manta da yaa Bashir,shi wallahi ya fiya tsanani,waini qaramar yarinya ce da zatayi abinda bai kamata ba?,nasan fa abinda nakeyi da hankalina,waya me tsada kamar wannan ina gani umma kice kada a kawo?, gaskiya kiyi haquri umma,yaa bashir dai tunda ba'a gidan nan yake ba sai naso ma zaisan wacce irin wayace a hannu na".


"Nidai ba ruwana na gaya miki"


"Haba umma,haba umma" wasila ta fadi tana buga qafarta,sannan kuma rai a bace ta dawo dakin.


"Wasila" ruqayya ta kira sunanta


"Inajinki" ta amsa mata tana zama gefan gadon


"Abinda ya bashir fa yayi dai dai ne,sannan dadewa da saurayi da kuma yi miki hidima ba shine tabbacin ingancin halaye da dabu'unsa ba,hakanan ba shine tabbacin yana sonki ba,babu soyayyar data wuce mutum ya aiko gidanku ayi maganar aure tsakaninki da shi"


"To amma meye hadin waccar matsalar da wannan,kawai sai ace kyautar wayar ma ba za'a karba ba,komai an maka izini kamar dan qaramin yaro?"


"Kudin iphone 13ya isa fa ya kawo kudin aurenki harda sadaki fa wasila,mutuncinki suke kare miki" juyawa tayi kawai ta kwanta rub da ciki ba tare data sake cewa da ruqayya komai ba,sai qananun gunaguni data ci gaba da yi,kana ta jawo wayarta tahau yin waya.


            Tata wayarce itama tahau tsuwwa,koda ta duba sai taga saleem ne. A nutse ta daga tana daidaita muryarta tamkar budurwar da zatayi magana da saurayinta da suke sharafin ganiyar soyayya


"Habibee,hala munyi dare ko?,ayi mana afuwa umma dince ban samu ba sai dana jirata"


"Kada ki dami habibtee,nima ina komawa na fito,zan qaraso saimu dawo tare,da motarki kika fita?"


"Eh da ita ne"


"To sai na qaraso"


"Allah ya kawomin kai lafiya"


"Ameen habibtee" ya amsa mata.


            Ajiye wayar tayi tana fita gurin umma,ta sameta tsakiyar su iftee ta sakasu a gaba suna cin alkubus da miyar ganye,sunata zuba mata surutu tana biye musu.


               Sake gaisawa sukayi a nutse sannan suka shiga hirar duniya wadda kusan duka ta zumunci ne. Akwai zumunci sosai tsakanin mahaifiyar ruqayya da umman data kasance qanwa ga mahaifiyar ruqayya. Suna tsaka da hira kiran saleem din ya shigo wayarta, saita duba tana cewa da alhassan


"Duba ko abbanku ne a waje,yace zai qaraso mu wuce gida tare"


"Asshsha,kya barshi a waje,jeki shigo dashi mana"umman ta fadi,sai ruqayyan ta miqe ta fice.


            Tare suka shigo tana zolayarsa,yayi kyau cikin yadin voyel fari qal yana zuba qamshi


"Kodai kodai anya kuwa?" Murmushi ne ma ya qwace mishi,ita ta tafi dashi saboda daurin data lanqwasa kanta,fararen idanunta kuma sun fito tarwai a hasken qwan lantarkin da ya haske gidan gaba daya amma ita tsokanarsa take qoqarin yi


"Kodai me?"


"Zance kaje ka biyo ta nan" ta fadi tana qaramar dariya me jan hankali saboda sautin da take bayarwa ma daban yake. Hakanan ita kanta ta saba,idan tana tare da saleem komai nata yakan canza,takan rikide daga ainihin ruqayyanta zuwa habibtee dinsa.


              Sosai umma ta tarbeshi,don kafin su iso ma ta masa shimfidar dadduma. Hira sukayi kadaran kadaham,don yafi sakewa da ita ma akan maama mahaifiyar ruqayya. Wasila ta saka ta zubo masa alkubus,amna kuma baici ba yace ya qoshi,don ba kasafai yakecin abinci a wani guri ba muddin girkin ruqayya ne. Ko kadan bayason yayi missing girkinta,gurin hajiya mahaifiyarsa kawai yake iya karbar abinci yaci indai tayi masa tayi ranar girkin ruqayyan.


                 Koda zasu tafi umman ta juye masa abincin

"Ku tafi dashi ruqaiya" umman ta fadi. A gurguje ruqayya ta leqa don yiwa wasila da bata sake ganin gilmawarta ba sallama,saidai bata cikin dakin,bata kawo komai ranta ba ta fita suka wuce.      

*HUGUMA*👑

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post