Kurman Baƙi Page 15 by Huguma

Kurman Baƙi Page 15 by Huguma


KURMAN BAƘI_⚫⚫⚫


*HUGUMA*


PAGE 15


https://chat.whatsapp.com/KHGP5vnV6yg6X9CpkQcf39*_Assalamualaikum warahmatullah_*


*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*


*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_*

____________________________
Tana kitchen taji ya sake shigowa


"Ki dauko mayafi muje mu kaita" waiwayowa tayi ta kalleshi,sai kuma ta kauda kai. Wani abune ke mata yawo a zuciya,ba zata taba manta wannan ranar ba,ranar da banda kiyayewar Allah babu abinda zai hana ta rasa ranta a abinda Zainab din tayi mata,bayan ta rasa ranta harma ta rasa ran abinda yake cikinta


"Kuje kawai saikun dawo,zan zauna da yaran tunda dai ba za'a barsu haka gida ba kowa ba" ido ya zuba mata na wasu sakanni,har zaiyi magana sai kuma ya fasa ya juya ya fice.


              Koda ta gama kintsa kitchen din alhassan ta aika ya kirayi su haneefa suka dawo sashenta,sannan ta saka alhassan din ya kulle sashen zainab din,don yafi haneefa nutsuwa da hankali,sau tari banda tsaho da ta fishi zaka dauka shine babban.


              Falon ta dawo ta zauna lokaci lokaci tana duba wayarta,yaran suna kallon carton,saidai bari bari da su haneefa din keta sanyata,ba'a samu sauqin abun ba sai da khalil yayi bacci.


                Dole ta saka ya qure ac dinsa saboda yanayin da jikinta ke bayarwa da ya soma dumame motar. Yawun takaici kawai yake hadiyewa,ya rasa me Zainab ke buqata a rayuwa da zai sanya ta canza halinta. Wasu lokuta yakanji kunyar ace ita din matarsa ce,abinda bai taba ji ba dangane da ruqayya duk da sunfi dadewa da ita nesa ba kusa ba akan zainab din.


              Wani kuka take kwazara mishi babu dadin amo bare dadin sauraro,ita a haka dole kukan da zai taba ransa yaja hankalinsa,abinda bata sani ba zallar takaici ne ya qumeshi.


"Wallahi na sake yarda da gaske asiri yana tasiri a kanka,na rantse da Allah ko kaffara bazanyi ba inda ruqayya ke wannan kukan da tuni ka rasa inda zaka tsoma ranka,amma ba komai akwai Allah"


"Ba zaki rusuna ba kenan ki saita kanki ba"


"Me nayin da har zan rusuna?,saboda kawai idan ba'a sonka idan ka fada ruwa ma sai ace ka tayar da qura?,kuma ko meye ya sameni ai ta sanadinka ne,duk inayine don na gyara kaina na samawarwa kaina 'yanci kamar yadda ruqayya ke dashi,don bana son kaucewa hanya nabi malamai".  


"Anzo gurin" ya fada a ransa,cikin zuciyarsa yana fatan ace shiriyarta ce tazo,sai ya sassauta tuqinsa yana duban titi


"Ai baki kama hanya ba sam zainab,ke din ba makauniya bace amma ta wani fannin kinfi makaho makanta,ta yaya kike tunanin zaki kamo ruqayya a haka?,bayan kinfi kowa sanin abubuwan da takeyi wadanda suka kaita matsayin da kike hange?, duk da ina iyakacin bakin qoqari na na yin adalci a tsakaninku?" Kamar ta banka masa ashariya haka taji,ita da yayi mata misali ko kwatance da ruqayya gwara ya sakata a daki ya lallasata tayi dumamen jikinta


"Wanne abu takeyi banda zallar kissa da munafunci da bin malaman tsubbu duk don ta mallakeka?,idanunka ya rufe ka kasa ganin gaskiya?,ni da kullum nake fadi tashin gyara maka shimfidarka amma qoqarina a banza yake kullum". Kai ya girgiza


"Zaki bawa Allah tabbaci ranar qiyama akan qazafin bin malamai zainab,ki kiyaye harshenki daga fadar abinda baki da yaqini akai" kuka ta fashe masa dashi


"Ehnnn,an tabo shalelenka ba?,muddin kana irin wannan akan ruqayya wallahi zaman lafiya tsakanina da ita har abada" ko ya waiwaya ya kalleta bai sakeyi ba,ya sani Zainab tayi nisan da bazata taba jin kira ba sai wani ikon Allahn.


             Sun samu sunga likita,amma yawan gudawar da takeyi yasa likitan yace zata kwana anan a saka mata drip,gudun kada suje gida cikin dare abun yayi worsening.


              Sosai ta sharbe masa tana ci gaba da koke kokenta da babu abinda suke qarawa saleem sai takaici. Don tuni likita ya gaya masa ya dinga sakata tana kiyaye shan magani barkatai


"Magungunan nan basu da wata qa'ida ko doka,duk maganin da za'a shashi ba bisa qa'ida ba dole yayi illa" tuni saleem din ya fahimci maganin meye,ba zata daina halinta ba kenan duk da tarin gargadin da yayi mata?.


             Bai iso dakin da suka batan ba sai daya kira hajiyayye qanwar mahaifiyarta akan tazo ta kwana da ita sannan ya wuce dakin. Tanajin sallamarsa ta sharbe magashiyyan. Baibi ta kanta ba tsabar takaici,yaja kujera ya zauna kawai yana danna wayarshi.


             Ba dadewa hajiyayye ta iso,ya miqe yana bata gurin zama 


"Da kayi zamanka abinka" hajiyayye tace


"Ah dama ke nake jira,tafiya zanyi ni" ido zainab din ta bude da sauri,taci alwashin yau kwanan asibitin zaiyi,shine abinda zatayi kawai wanda zai quntata ran ruqayya. Yunqurin amai ta fara yi na qarya,shi da hajiyayyen dukka suka qaraso,saidai babu wani abu data fitar don tuni aman gasken ya fidda komai daga cikinta


"Idan na fita zan tsaya na yiwa nurses din magana,ko alluran tsaida amai din suzo suyi mata" ya fadi yana matsawa gurin saman kanta


"Sai da safe zan sake shigowa,banajima zamu kai azahar bamu koma gida ba,Allah ya sawwaqe " ya fada yana fiddo kudi daga aljihunsa ya ajjiye gefan kanta cikin qoqarin danne bacin ransa kada duniya ta fahimci halin da suke ciki


"Yanzu ko tausayin halin da nake ciki bakayi tafiya zakayi?" Ta fada da qarfi don hajiyayye taji harda matso hawaye


"Banda abinki zamansa a nan ai bazaiyiwu ba,kuma me zaiyi miki shi da bashi ke cire ciwo ba?,jeka abinka gida,Allah ya bamu alkhairi"


"Sai da safe" ya fadi yana ficewa.


            Kaman jira takeyi ya fitan ta miqe ta zauna sosai har cannula din hannunta na qoqarin gocewa


"Banso kikayi magana ba, wallahi hajiyayye na fara gajiya da rashin adalcinsa,qiri qiri mutumin nan kiga abinda yakeyi,na rantse miki da Allah yau inda ruqayya ce zatayi kwanan asibiti bazai iya tafiya ya barta ba" kai kawai hajiyayye dake cire hijabinta ta daga ta kalli Zainab. Duk da tasan wasu abubuwan amma sai tayi kaman bata sani ba ta hanyar tambayarta


"Saboda me?"


"Saboda wani irin mahaukacin kula da yakeyi da ita da wani kulawa da na tabbatar ba ta domin Allah bace"


"Ke ya akayi kikasan bata Allah bace zainab?" Hajiyayye ta fada tana jawo kujera dab da gadon Zainab din saboda su biyu ne a dakin,donma daya patient din tayi bacci abinta tuntuni,kuma abun mamakin ita kadaice babu dan jinya. Sake jan kujerar tayi baya kadan saboda yanayin da jikin zainab din ke bayarwa taci gaba da kallonta daga nesa nesa


"Yo hajiyayye aiba irin wannan soyayyar a yanzu a wajen mazan wannan zamanin,kana gyara ma ya ka cika dasu bare baka gyara,nifa kullum cikin fuskantar matsala nakeyi da saleem,kyara gwasalewa,komai nayi banyi dai dai ba,komai nayi baya nuna wani jib dadi ko kuma wai na burgeshi,ni kuma a iya sanina macen da bata gyara HQ dinta ita ke fuskantar wannan matsalar,macen dake gyara take kulawa baji ba gani ai tafi qarfin ayi mata irin wannan tijarar,to ita ba wani gyara da takeyi matar nan,idan kuwa ba asiri ba banga ta yadda zata mallaki saleem ba"


"A tunaninki?" Hajiyayye data gama sauraron soki burutsun zainab ta fadi tana dubanta


"Hakane mana" zainab ta amsa mata kai tsaye


"Sam sam" ta sake maida mata tana zama sosai idanunta cikin nata


"Mun sani mafi rinjayen abinda ake kira da aure wannan abunne,to amma shi kansa baya tasiri baya kuma qayatarwa gami da jan hankalin d'a namiji saikin mallaki wasu abubuwan,tsafta,ladabi biyayya iya magana tattalin miji da tarairaya duka ina kika barosu?,ina kika baro iya girki?,ado da gayu?"


"Duk basukai wannan muhimmanci ba hajiyayye,indai sune ke riqe maka miji me yasa saleem ya auroni idan ka cire matsalar haihuwa?,ita kanta haihuwar ba damun wani namijin tayi ba indai zai samu wannan gurin da kyau" ta fada tana qoqarin maida kanta ta kwanta,don kwata kwata maganganun hajiyayye basu samu matsugunni a ranta ba.


              Ta dade da sanin Zainab da kafiya da kafirin taurin kai,musu kuwa ba abinda yafi mata shi sauqi,tunda har bata da intention na ta fahimcetan to ba fahimtarta zatayi ba,zata batawa kanta baki ne,don haka tace


"Gaskiya ne,hakane,amma akwai gaskiya daya da zan gaya miki,don Allah ki dinga qoqarin amfani da turare,sannan kodon zirga zirgar da kake wuni kanayi wankanki ki maidashi sau biyu"


"Ke hajiyayye kin ganni nan,saleem bai taba cewa wani abu ba,turare kuwa mu ko munsa ko bamu saka ba mun wanku fes daga gurin kakanninmu,jikinmu baya komai in gaya miki,ki qyaleni na huta"


"Hakka" tace da ita kawai tana tura kujerarta baya,ta dauki wayarta ta soma chart abinda.(hajiyayyen bazawara ce, mijinta ne ya rasu ya barta bata taba haihuwa ba,shekarunta kuma duka duka basu wuce arba'in da biyu ba).


              Idanunta ta rufe saidai maimakon tayi nazarin maganganun hajiyayye a'ah,asarar da zata tafka ta maganinta take qiyastawa indai shegen likitan nan ya riqeta bai sallameta ba a gobe


"Aikuwa koda tsiya koda tsiya tsiya dai an sallameni gobe" ta fada tana muskutawa hadi da gyara kwanciyarta.


"Me kika ce?" Hajiyayye ta daga kanta tana tambayarta


"Ba dake nake ba" ta amsa mata don bata taba zaton zancan zucin da takeyi ya fito fili ba. Itama bata sake tambayarta ba ta maida kanta ga abinda takeyi.


********Dogon tsaki taja tana gallawa wayar ta data dauki ruri a karo na babu adadi harara


"Kinsan fa ni banason irin wannan abun,waye yake kiranki da baki daga ba bare ki kawo masa uzuri?" Umma dake zaune a gefanta tana cin tuwon dare ta fada


"Isma'il ne umma"


"To ki daga mana?"


"Haba umma,dame zanji don Allah?,da takaicin shegen yaron nan da na aika ya siyomin indomie yaje ya zauna koda nacin kiran wayarsa?" Side hannunta data gama cin tuwon umma ta farayi tana cewa


"Duk dai ke kika jawowa kanki,inda tuwonki kikaci da ba yanzu bakinki alaikum ba,ba wanda yaji bare ya gani"


"Allah ya sawwaqe,tuwon masara aisaidai a bawa gawata" ta fada tana kyabe baki tare da gyara zamanta tana ci gaba da hada sabbin syrup da supplements din gyaran jiki dana qiba data siyo jiya. Gefe kuma ga mayukan saka hasken fata suma data yiwa roba guda. 


            Dai dai nan yaron ya kwado sallama ya shigo hannunsa da baqar leda


"Kaci uwarka surajo,inda kasan dadewa zakayi uban me yasa ka karbarmin aike?"


"Banason lamarin zagin iyaye na gaya miki malama" umma ta fada tana kwada mata harara


"Layine a wajne wallahi da qyar akazo kaina"


"To kinji ma" umman ta fada ta yunqura tana miqewa da kwanonta ta nufi kitchen.


               Jakar umma ta jawo ta zuge,daga can umman ta jiyo qarar zuge jakar


"A'ah fa,ni ba zaki talautani a daren nan ba,na baki kudin indomie me kuma kike nema?"


"Pepsi zai siyomin don Allah,sai kuma ashirin din dana masa alqawari,zan biyaki bashi na ansa" ta fada tana ciro kudin da sauri ta miqawa surajo din tana masa inkiyar yayi sauri ya fita.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post