Kurman Baƙi Page 6 complete

Kurman Baƙi Page 6 complete

HUGUMA

 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 06

*****Kamar kowacce rana da zata karba girki,duk sanda ka ganta tana gyare gyare zaka tsammaci wata tafiya me nisa saleem din yayi yake shirin dawowa. Kusan komai na dakin sai ta tabashi,wani ta canza masa guri wani ta gogeshi wani ta sauyashi gaba daya. Kafin azahar sai ta tabbata komai na dakin ya sauya daga ainihin yadda saleem ya fita ya barshi.


               Sha daya na rana ta fito daga dakin bayan ta gama kintsashi. Qofar ta murda ta bude ta fito parlor dinta hannunta riqe da qaramin towel da tayi goge goge dashi.


             Alhassan da alhussain ne zaune sun sanya tv a gaba,sun wani nutsu har abun yaso nata dariya. Ta jima bataga yatan dake masifar son kallon cartoon ba irinsu 


"Yadda kuka nutsu kuna wannan kallon,kada ku yarda anjima nazo karban hadda naci gyaranku". Yare suka dago kai suka kalleta suna dariya,alhussain ne ya fara cewa


"Ni ko yanzu ma mommy ki karba Allah na shirya"


"Nima din ai na shirya yaro" alhassan ya fada. Take 'yar musu ta barke a tsakaninsu. Gaba tayi ta barsu a gurin,don irin wanann qananun rigingimun nasu a rana har bata iya riga adadin sau nawa sukeyi,saidai fadan baya nisa ake watsewa,shi yasa ba kasafai ta fiya damun kanta da rabo ba.


             Gaban fridge dinta ta qarasa,ta saka hannu ta bude tana ciro wata doguwar gora me kyau,sai ta azata saman Fridge tana kallon agogo da dan mamaki a fuskarta. Tun dazun take mamakin rashin jin motsin saleem,duk da bata son zurafafawa kanta da tunanin abinda ya hanashi shigowa dubasu tunda hakan ba sabonsa bane,tanata son kiransa ko tabi ba'asin jinsa shurun amma zuciyarta tana kwabarta. Batason abun rigima da fitina,ko kuma taje ta gano ko ta jiyo abinda zai motsa kishin da taketa qoqarin ganin ta mallaki zuciyarta a kansa.


               Sai da yadan huce sannan ta bude gorar,take qamshin kanunfari da sauran kayan qamshi suka cika gurin. Tun kafin takai bakinta yawunta ya tsinke,ingantaccen tsumi ne data zauna ta dafashi da kanta jiya da sanannun saqe saqi da danginsu rake mazarqwaila harma da zuma a ciki. Cup daya ta cikashi dashi ta fara sha a hankali. Idonta ta lumshe tana jin dadinsa har saman harshenta,sai data shanye a nutse sannan ta kife cup din wanda yayi dai dai da kwada sallamar Zainab,sannan kai tsaye ta danno cikin parlor din.


               Hannu ruqayya ta sanya ta dauke gorar tsumin nata tana qoqarin maidawa fridge,duk da ba wani abu bane don Zainab din ta gani ba,koda ta gani tasan ba lallai ta fahimci meye ba,to amma ita din mutum ce da ba komai take bari idanun kishiyarta yakai kai ba (hakan ba laifi bane,yana da kyau ki iya takunki wajen kishiya,ba komai kike bari tana sani naki ba,koda kuwa me kyau ne,akwai abubuwan da sukan zama tamkar wani sirri ne naki,kuma makaminki da kike naki yaqin cikin gidan tsakaninki da mijinki,barin kishiya tasan da wannan sirrin ko makamin tamkar wargazawa kanki da kanki shiri ne). Tuni idanunta suka kai din,tunda itan tana cikin jerin sahun matan da komai kayi suna da buqatar sani ko gani,amma tunaninta sai ya tafi ga wani abun daban


"Ana nan ana fama da coca-cola" ta fadi qasa qasa. Bata damu da kallon da ta bita dashi ba,ta gyara zaman tsumin ta maida fridge dinta ta rufe tana amsa sallamar tata


"Aron mopper zaki ban yara sun karya min tawa" ta fada tana riqe hannu a qugu. Sau tari tana mamakin Zainab har ba iyaka,duka yara biyu amma idan kaga barnar da ake a sashen nata zaka dauka wasu gayyar yara gareta. Duk tsananin baqin kishinta kuma bata kunyar aron abu daga hannun kishiya?,wani abu guda daya tal da ruqayya zata iya bugar qirji tace bata taba yi ba(zubda kaine aron abu a wajen kishiya,muddin ba wai ta kama bane ko ba yadda zakiyi,komai da kikasan zaku buqata keda yara siya ki ajjiye,gwara ke a ara a hannunki).


             Waiwayowa tayi ga alhassan ta sanyashi shiga store ya dauko mata,saidai sanda ta maido dubanta ga zainab din sai ta sameta tana sana'ar tata wato sanya ido. A duk sanda wani uzuri ya kaita ga shigowa sassan nata to ba zata taba fita ba sai ta yiwa parlor din nata kallon tsaf!,in sha Allah duk abinda ta gani sabo ko baqo sai tayi qoqarin siyan makamancinsa. Abun tun yana bawa ruqayya mamaki har ma sai ya koma bata dariya.


"Nikam daddynsu lafiya na jishi shuru bai leqo ba?" Tambayar da tayiwa Zainab mugun dadi,sai ta waiwayo tana sakin murmushi


"Angoncinne ya motsa,don da qyar na lallabashi ya fita sallar asuba saboda jiya bamu samu isashen bacci ba ni dashi duka,saboda tsabar duniya ta masa dadi harda wani guntun zazzabin shagwaba" Girma sosai maganar ta yiwa ruqayya,takai idanunta da sauri kan alhassan da alhussain iftee dama baccinta takeyi saman kujera. Allah ya taimaketa hankulansu gaba daya ya tafi kan cartoon din sosai,da alama kunnuwansu basuyi wannan baqin jin ba,sai ta daga ido ta maida dubanta ga zainab. 


            Idanun zainab din fes kan fuskar ruqayyan tanason ganin bacin ran da ta qiyasta zata gani din,saidai ga mamakinta murmushi ruqayyan ta saki bayan ta tako zuwa sashen da take don ta kaucewa kunnuwan yaran jin abinda bai shafesu ba


"Ayyah,kayya kiyi masa sannu,ai ban sani ba,bai kamata ace har wannan lokacin ba'a shiga an dubashi ba,amma ina nan shigowa na duba angon naki,irin wannan dattijon amarci ga shekaru ga kuma bar muku sudi?,da kin sani ai aikomin kikayi dasu haneefan,kinga ni lokacin nawa amarcin duk girman gidan nan daga shi sai ni,baccin shekara ma sai muyi babu me tashinmu".  Baki Zainab din ta tabe,maimakon ran ruqayyan ya baci sai tata zuciyar ta soma motsawa


"Ah ai kunsha bacci,shi yasa tsabar bacci aka dauka juya ya auro"


"Sai kuma ga mazaje har guda biyu sun wanke sunan ummansu daga juya zuwa uwar maza ba" ta maida mata amsar tana tsuntsira dariya abinta hankali kwance.


             Baki yasan abinda zai furta saidai kuma bashi da masaniyar amsar da za'a bashi. Maganar ta sake tunzura Zainab din,sai ta juya tana ficewa a gurin


"Ki bar mopper din a wajenki idan kin gama" ruqayyan ta sake fadi,saidai ko waiwayowa zainab batayi ba ta qara gaba. K'aramar dariya ruqayya ta saki,kwata kwata wautar zainab take gani,idan tasan halittar ta saurin fushi,tunzura da rashin iya cinye bacin rai,to ya kamata ta kiyaye shiga ko faro maganganun da amsarsu ba zasu mata dadi ba,ta dinga kame kanta da hana kanta da kanta shiga hurumin da bai shafeta ba,ke da aka yiwa tambayar me gida kurum saiki zaqe?,bayan kinsan zuciya da fuskarki duka basu da baiwar iya shanye bacin rai da maida komai ba komai ba


"Kadanma kika gani,na fiki iya iskanci" ruqayya ta fada tana komawa ciki.


          Kitchen kawai ta shige abinta,ta canza shawarar shiga dubashi din,a maimakon hakan sai ta jawo wayarta ta tura masa tex tana masa sannu da jiki. Yana fahimtar ta qwarai,tasan ko iya tex din ya wadatar. Data tabbatar ya shiga saita bude fridge ta ciro lafiyayyen kifi mara wadatar qaya ta kwara masa ruwan zafi sannan ta fara aikin sarrafashi. 


              Nau'in kifin da saleem yafiso ne,kuma ita din bata taba rabo dashi koda wanda ya siyo ya qare,tana siya da kudinta ta zuba a fridge din. Jin dadin hakan ya sanya duk sanda yazo yaga ta zuba din zai biyata kudinta harma wasu lokutan ya qara mata. Abun na masa dadi qwarai,saboda na gefin Zainab sau tari saidai yaga an zubda a shara ya lalace,don ba damuwa ta fiyayi da kunna Fridge din kayan miya ba kwata kwata,ko ta kwashe ta bayar kyauta don kawai tayi bajinta.


              Kafin ta gama aikin ta kira qanwarta 


"Kizo ku tafi dasu alhassan su kwana gobe sauka idan jikin abbansu yayi sauqi na samu fitowa saimu dawo tare,tun jiya dama na tambayar musu" ba jimawa ta iso gidan,saita sakar mata gyaran kitchen din,ita kuma ta wuce bedroom dinta.


            Wankanta wani abune da bata wasa dashi,kowanne lungu da saqo da tasan maboyar datti ce sai tabi ta qalqale,ramin cibiya,qasan mama duk da tana da baiwar tsayayyun mama,matse matsin mazaunai,matse matsin cinyoyi,bayan kunne harma da cikin kunnen da qasan mara.

               Cikin mintuna talatin ta fito fes cikin doguwar rigar atamfa chocolate color din fatartan nan tayi luf cikin qamshi da cream masu taushi,daurin dankwalin kuma ya zauna mata sosai a kanta.  Sai da tayi sallar azahar sannan ta dawo parlor din.


              A falo ta samu anata daru da iftee tace itama sai taje,da farko sai ta qyaleta tanata saka turaren wuta a burner tare da jona humidifier dinta,har ta gama bata bar kukan ba yarinyar,duk da ba'a jima da dawowa da ita gidan daga yaye ba, dole ta hada mata kala dayan itama ta bisu din.


                  Kitchen ta wuce,ta ciro dafaffiyar budurwar kazarta da tasha hadin saqe saqi,kazar da take dafata da hannunta da ingatantattun saqe saqi da kayan da suke bawa jiki garkuwa da lafiya su kuma magance ciwon sanyi. Dan dumamata tayi kadan sannan ta zauna a nutse ta fara ci hankali kwance saboda sashen nata ya dauki shuru. Minti goma sha biyar ta gama,sai ta wuce da kwanon kitchen,ta koma dakinta tayi brush sannan ta dawo ta sake mulke jikinta da turaren da ba kasafai take amfani da shi ba idan ba lokacin kwanciya bacci ba saboda yadda saleem din ke matuqar sonsa. 


              Bata yafa komai ba sai wani dan siririn gyale da yafi kama da mayafin yara wanda ya dace da atamfar jikinta ta fito daga sashen nata ta ratsa babban falonsu da yaron dake musu aike aike cikin gidan tuni ya gama tsaftaceshi ya wuce sabgar gabansa,ta doshi qofar falon sashen zainab din.


              Tun bata qarasa ba take jiyo ifce ifcen haneefa da khalil,da alama ma fada sukeyi,don tana jiyo muryar uwar tana kwarara musu tsawa wanda sauran kadan ta barke da ashar,tana tuna cewa saleem din yana gidanne da tuntuni ta hadasu data maguzawa,tunda a cewarta ta lura sunfi ganeta.


               Duk da tayi sallama ba wanda ya jiyota,sun kacame da dambe. Ta sanya qafarta da hanzari don ta isa ta rabasu,saudai tayi kyakkyawan Katarin taka wani abu me danqo. Koda ta dube sai taga ashe tea ne aka watsar har ya fara kama gurin ya soma bushewa. Tsigar jikinta ta zuba,ta janye qafarta tana takata saman carfet din falon saidai a nan ma qasa ta cabo a qasan qafartata. Dubanta ta maida ga tafin qafartata kafin ta dago kai saleem da hayaniyar ta isheshi har ta tayat dashi a bacci ya fito a dakin.


              Dif sukayi kowanne na neman gurin buya,sai suka fara qoqarin barin parlor din. Bai lura da ita ba saboda baiyi tsammanin shigowarta ba,saidai sassanyan qamshin da ya gauraye parlor din yake shiga masa hanci ya sanyashi wara idanunsa a parlor din. Qamshine da a jikin mutum guda ya sanshi,qamshine da duk sanda ya jishi ya tabbatar zai samu wani irin tarairaya da soyayya me girma,qamshin dake nuni da zai shiga wata duniya me cike da tarin nutsuwa.


             Ido suka hada daidai da fitowar Zainab daga kitchen wadda ke mamakin me ya sanya haneefa da Kahlil din nutsuwa lokaci guda?.


               Sarai ruqayya ta ganta amma ko da ido bata nuna mata hakan ba,sai tafi maida hankalinta ga saleem din.


"Zuwa nayi na tafi da ango,ban sani ba ko angoncin daka balle jiya ya hanaka gane hanya shi yasa har yanzu baka samu shigowa ba" ta fada a tausashe tana murmushi. Hannu yasa ya shafi sumar kansa,har yanzu baya jinsa ya koma dai dai,kuma har yanzun idan ya tuna jiyan ya kasa nutsuwa haka siddan ya koma haka,ba abinda zai iya dorarwa me shauqin da zaice yayi matuqar qayatar dashi da zai tsaya masa a rai,face wasu irin abubuwa da hancinsa ya shaqa. Idanunsa sun rufe ya zurfafa hancinsa cikin jikinta,abinda dama ba kasafai ya fiya yi ba,wannan din wani sirrinsa ne da ba mahaluqin da ya sani,ruqayyan kadai yake iya yiwa hakan,saboda yasan duk inda zai cusa hancinsa AMINCI zai tarar da marabta me kyau. Gaba daya zainab din ma a tsarinta ire iren wadan nan abubuwan bata lokaci ne,gwara a dinga tafiya zuwa ga babbar headquarter din gaba daya. 


"Banajin dadi ne" ya fada shima cikin narkewar da baima san yayita ba,kawai wani farinciki yaji yana saukar masa tamkar mutumin dake tsakiyar kogo me duhu masu agaji suka riskeshi don fiddashi hakanan yaji.


"Ya salam" ta fada tana nuna zallar alhini a fuskarta tana kuma takowa da sassarfa zuwa kujerar da ya zauna din a kai,yanayin yadda take takun ya bawa qirjinta damar motsawa,wanda ya ciko yayi fam saboda baiwar aqirji da take dashi,uwa uba kuma tana using push off brazier don bahaushe yace idan kana da kyau ka qara da wanka. Ita kanta tana alfahari da baiwar beast da hips da Allah ya bata,ita din baqace ko ace wankan tarwada,zainab ta fita fari da tsahon gashi sosai,farin da a baya yaso ya zame.mata tarnaqi kuma kalmar da akaso ayita cusguna mata da ita. Bata taba mance lokacin auren zainab,zuciyarta ce kadai ta rage bata buga ba,amma hawan jini kashi kashi ta yishi. Hasken fata da tsahon gashi tayi imani kawai zainab ta fita,saidai ita kuma Allah sai ya qareta ta bangarorin da take da tabbas ta yiwa zainab rata me tarin yawan da bazata lissafu ba.


              A hannun kujerar da yake kai ta zauna tana duban fuskarsa


"Habba amma ya kamata na sani ko?" Ta fadi a shagwabe tana tura baki gaba. Murmushi ya saki yana kauda idanunsa saboda ta fara tadoshi sosai


"Am sorry" ya fada a taqaice saboda tsaiwar Zainab a wajen wadda kamar zata fashe


"Alright,muje na qarasa wannan jinyar gaskiya,wannan amarci an cishi yadda ya dace,har ruwan dumi zan maka na gasaka da kyau,kaga nima sai naji dadin diban nawa tsumammen uwargidancin" ta qarasa maganar tana kashe masa ido daya hadi da cije lip's dinsa na qasa abinda ya sanya tsigar jikinsa zubawa.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post