Cuta ta Ɗau Cuta Page 37 by Bilyn Abdull ce
Health College

Cuta ta Ɗau Cuta Page 37 by Bilyn Abdull ce

 

Littafan Bilyn Abdull

*_Typing📲_*

   *_CUTA TA ƊAU CUTA_*

             _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na talatin da bakwai

__________


*_WAI KINA SHIRIN WUCEWA NE BAKI KARANTA BA😨._*



*_TO MAZA DAWO BAYA KI DUBA. IN BA HAKA BA ZA'AYI BABU KE NE_*



*_INA KUKE MASOYAN ZAFAFA BIYAR DAMA WANDA BAZU TAƁA SIYA BA SAI DAI SU KARANTA A HANYA_*.


*_MAZA KU MARMATSO KU MALLAKI NAKU DAN GAB JIRGIN YAKE DA BARIN ƘASA. MA'ANA GAB ZAFAFAN SUKE DA FARA SAKAR MUKU ZAFAFAN LITTATAFAN SU NA SABUWAR SHEKARAR 2024_*


*_KAR KUYI MAMAKI IDAN NACE MUKU TAFIYAR FA TA BANBANTA DA BAYA. SABODA SALON NA DABANNE, NA KUMA MUSAMMAN NE_*.



*_TSUTSAR NAMA....!!_*

          _(Bilyn Abdull)_



*_AMEENATU_*

         _(Mamu gee)_



*_KWANKWASON JIMINA...._*

         _(Mss xoxo)_



*_GUDUN ƘADDARA_*

         _(Safiyya Huguma)_



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥


___________



........A kujera ya zube yana cigaba da mata dariya tsokana. Itako ta koma gefe ta zauna ta zabga tagumi kamar zata fasa kuka. Yatsa yasa yana ɗan cakularta taƙi kulashi, ya zame ɗan kwalinta ya ja mata gashi, nan ma taƙi ko motsi, ita a dole dai tayi fushi. Dariyarsa ya danne da ƙyar, ganin bazata kulashin ba ya fizgota ta faɗo jikinsa. Ƙankameta yay yana dariya da sakar mata kisses tako ina. Tun tana ture masa kai da zizzilewa harta nutsu luff a jikinsa suka koma dariyar tare. Daka gansu kasan suna cikin farin ciki da matuƙar ƙaunar juna...


     Washe gari yana dawowa daga massalaci sallar asuba a kitchen ya sameta tana ƙoƙarin haɗa masa breakfast. Rungumeta yay ta baya da sakar mata sumba a gefen wuya yana faɗin, “Good morning Baddo am”.

    Idanunta ta lumshe tare da sakin murmushi tana kai hannunta ta shafo kansa duk a lokaci guda. Sai kuma cikin sauƙaƙa murya a hankali ta furta, “Morning Hamman Baɗɗo. Ina fatan ka tashi cikin ƙoshin lafiya da yalwatuwar nutsuwa”.

        “In dai kina gefena akowane dare tashi da waɗanan abubuwan biyu, haɗe da farin ciki tamkar wajibi ne a gareni Baɗɗo am. ALLAH yay miki albarka ke dai, ya wadata zuciyarki kema da farin ciki ke da zuri'arki baki ɗaya. ALLAH ya ƙara min sonki, ya bani ikon ƙyautata miki da yi miki adalci a rayu. ALLAH ya haneni ƙuntata miki koda da mummunar kalma ne”.

      Wasu hawaye ne a hankali suka silalo a kumatun Khadijah. Soyayyar mijinta na ƙara ratsa mata ɓargo da zuciya. Ji take, inama duk mata su kasance kamar ita a gidajen aurensu. Da tabbas an samu farin ciki da wadatar zuci harma da ƙauna da farin ciki mara iyaka. Tayi imanin da mata da yawa sun daina shirka a domin maza....

         “Uhm-uhm ni bana son kuka Baɗɗo, idan ba hakaba nima zan tayaki”.

    Da ƙyar ta iya haɗiye kukan, yayinda shi kuma yake share mata hawayen. Cikin son canja yanayin nasu ya buɗe tukunyar dake kan wuta yana faɗin, “Mi surukar Mamy ke dafa wa mijinta?”.

      Hannunsa ta ɗan bige kaɗan tana hararsa, ba shiri ya saki murfin tukunyar. Baki ya tura mata, ita kuma ta hararesa da faɗin, “Sirrine babu mai gani sai a kwano.” bakin ya sake turawa irin nayi fushin nan. Ta masa gwalo da faɗin, “Oho dai bazaka gani ba. Tafi wanka ma an yafe taya hiran”.

      “Ni naki nake so”.

    Ya faɗa yana ƙara ɓata fuska.

Cikin marairaicewa ta ce, “ALLAH Hamma rigimarka yawa gareta. Yaushe na gama aikin nan akaje wani wanka”.

      “Oho, nidai koma yaya ne ke zakiyi. Shiyyasa ma yanzu a office an fara cewa yanzu ina latti kuma duk kece baki saurin shirya ni”.

     “Kai Hamma ALLAH babu ƙyau sharri”.

    “Gaskiya dai”. 

Ya faɗa yana ja mata hanci da sakin murmushi. Itama sai ta saki dariya. Haka suka cigaba da aikin tare cikin nishaɗi. Bayan sun kammala ya jata part ɗinsa sukai wanka tare suka shirya tsaff sannan suka fito sukai karin. Sashin Mamy suka je dan tare zasu fita, zai maidata ganin likita. Tun cikar satinta guda yay mata magana game da inplan na jikinta. Sai ta sanar masa ai Baba da kansa yasa Mama da Ni'ima suka kaita asibiti aka cire tun bayan warware matsalarta da Dafeeq. Ya gamsu da hakan, amma dai ya kaita asibiti bisa shawarar Mamy. Doctor ya dubasu su duka ya kuma ɗaurasu akan magunguna da fatan ALLAH yasa iyakar wahalarce tazo. Tom yau sune cikar kwanakin da yace su sake komawa.

       Sun samu doctor ma na jiran zuwansu. Komai an musu shi cikin girmamawa da kulawa. Dan ba shi uban ginsamin ba hatta ita kanta Hajiya sama Hajiya ƙasa ake kiranta. Basu ci awa ɗaya ba cikakke suka fito. Shi suka fara ajiyewa a office ita kuma Awwal ya wuto da ita gida. Kai tsaye sashen Mamy ta wuce, dan tasan tana can cikin kaɗaici dan ma akwai masu aiki...


__________★


        Komai ya gama hargitsewa musamman a ɓangaren Kainaat da gaba ɗaya kanta ya gagara gane yanda abubuwan suke ma tafiya. Dan duk wanda tasan nada alaƙa dasu Nadwa ta nemesa a waya. Amsa ɗaya ce su basu san ina suke ba. Bama su san sun bar gari ba. Sannan nan fa Adamawa garin mahaifin Nadwa ne kawai. Mahaifiyarta ba ƴar nan ɗin bace, hasalima su basu san ƴar ina bace ba. Wasu suce Jos, wasu Lagos babu dai matsayar kamawa, itama kuma shaida ce akan hakan, sai dai ita sukan gaya mata Lagos da Jos ne garin su Mom, amma abin ALLAH ita bata taɓa binsu taje, su kuma bawani taron biki sukai taga danginsu ba tunda Nadwa dai har yanzu bata taɓa aure ba, ita kaɗai kuma suka haifa.

         Da ƙyar Dafeeq yake danne dariyarsa yana lallaɓata da faɗin ta kwantar da hankalinta. Sai dai kuma bayan sun buɗe takarda sun duba abinda ke ciki labarin ya canja salo, dan kuwa dai yanke jiki Kainaat tai ta faɗi a sume. Anan kam duk da Dafeeq na jin ransa fes shirinsa ya gama cika a kanta sai da yaji bazai iya guduwa ya barta ba kamar yanda ya tsara. Hankali tashe ya ɗaga waya domin kiran Doctor Giɗaɗo. Sai dai me, Number switch off. Cigaba yay da nema, amma dai still amsa ɗaya ce switch off ɗin dai. Da farko bai kawo komai a ransa ba ya jajibeta suka wuce asibitin su Dr Giɗaɗon. An musu tarba ta gaggawa saboda halin da Kainaat ɗin ke ciki. Dafeeq bai samu nutsuwa ba har sai da yaji ance ta farfaɗo tana ma barci. A lokacine ya nufi office ɗin Doctor Giɗaɗo. Sai dai ya samu a rufe, wata Nurse ke sanar masa ai duk yau ma Doctor Giɗaɗo bai shigo asibitin ba. Zuciyarsa taso ɗan shiga ruɗani, amma sai wani sashe ya gargaɗesa akan ba hakan bane.


      Kwanakin Hajiya Kainaat biyu a asibitin aka sallamesu. Sai dai har yanzu babu Doctor Giɗaɗo babu labarinsa. Tun Dafeeq na ɗaukar al'amarin wasa har lissafinsa ya fara canjawa. Gashi bai san ainahin gidan su Doctor Giɗaɗo ɗin ba, sai gidansa kawai ya sani, yaje ya samu kuma a rufe wai sunyi tafiya masu gidan. Yata bin Nurses na asibitin su sanar masa ko Dr Giɗaɗon nada wani gidan bayan wannan sun ƙi, da ga ƙarshe wani ke sanar masa Doctor Giɗaɗo fa ainahinsa baɗan Adanawa bane, kuma zaune yake shi kaɗai babu matarsa. Hasalima ba ɗan Nigeria bane. Ɗan Cameroon ne. Neman faɗi Dafeeq yayi, amma ya daure ransa da ƙyar suka bar asibitin zuwa gida a napep.

      Sun iso kowa da abinda yake tattaunawa a ransa, sai kuma mi, suka sami ƙofar gida danƙare da kayayyakinsu duk an fiddosu waje. Sai mai gadin makwabta ne ke sanar musu ai aikin wanda suka sayi gidan ne. Sannan kuma wani yazo ya bada saƙo a bama Dafeeq. Baibi takan saƙon ba hankalinsa ya karkata ga Kainaat dake tambayar ina sauran motocinta biyu. Da mamaki maigadin ya bata amsa da ai ƴar uwar nan tata da wanda ya bada wannan saƙon a bama mijinta ne suka ɗaukesu suka wuce. Neman yanke jiki ta faɗi tayi dan tasan dai Nadwa ce kowa ya sani matsayin ƴar uwarta, nan ma sai da Dafeeq ya riƙeta. Ganin mutane sun fara taruwa Dafeeq ya lallaɓata akan tazo suje gidan da ya zauna da Khadijah dan shi ya kasa fahimtar komai. Bata da zaɓin daya wuce binsa, dan wlhy jitake kamar kanta zai fashe...


       Sosai gidan yay kura, dan ba zama ake ba. Shi kansa yayi kusan wata biyu ma bai zo ba. Da dai yakan zagayo ya ɗauki kayan Khadijah yana shin shina wani lokacin harda hawaye. Sai dai wannan abin daya tasa gaba akan dukiyar nan ta Kainaat ta ɗauke hankalinsa kwana biyu. Kuka sosai Kainaat keyi na tashin hankali. Babu abinda ke juya mata a rai da ƙwaƙwalwa kamar batun wai Abaan ɗinta yayi aure sati ɗaya kenan daya wuce.    

      Yanda take kukan ne ya sake hasala Dafeeq, a kausashe ya ce, “Wai minene kuma?!”. Cikin suɓutar baki tana ƙara fashewa da wani sabon kukan ta ce, “Yayi aure fa, kana ji wai ni Nadwa ke faɗama Abaan yayi aure”.

        Wani harara ya wulla mata zuciyarsa na tafarfasa. Sai dai yay dauriyar yimata banza ya ɗauke kansa kawai. Sai ma warware babbar envelope ɗin da maigadin nan ya bashi yake. Wayace a ciki, wayar da shi da kansa ya bama Doctor Giɗaɗo akan suna waya. Baima san sanda yay saurin shiga wayar ba, kamar an saita da video ya fara cin karo. Nadwa da Doctor Giɗaɗo da Mom suka bayyana. Wani shegen zabura da ya maido hankalin Kainaat kansa yayi. Ƙoƙarin miƙewa yake ya fita Kainaat ta warce wayar ta danna play.

      “K miye haka?!!”.

  Ya faɗa cikin daka tsawa. Ko kallonsa batayi ba ta maida hankali akan videon. Dan abu na farko da mutanen uku suka fara shine dariya a tare. Kafin Doctor Giɗaɗo ya ɗaga hannu ya ce, “Hy Dafeeq mijin Kainaat. Oh Hajiya Kainaat.” sai kuma suka kwashe da dariya. Sai da sukai mai isarsu sannan ya cigaba da faɗin, “Nasan zakuyi mamaki, matuƙar mamaki. Amma karku damu. Dafeeq kai tsuntsune mai wayo. Sannan ALLAH ya baka kwanya sosai. Sai dai matsalarka ɗaya ce baka da ilimi. Ƙarancin iliminka yasa ko kayi lissafi yake wargajewa batare daka farga ba. Zan fayyace farkon alaƙarmu saboda ko ita Hajjajun taka zata gani dan saƙon ya isheta. Hajiya Kainaat kamar yanda kika sani nasan Nadwa da mamarta ne a dalilinki kamar yanda na sanki a dalilin Alhaji Abaan. Mun ƙulla alaƙa mai ƙarfi tsakanina da Nadwa da jimawa lokacin kina tare da Abaan, sai dai mun rabu daga baya sakamakon wasu matsaloli. Tunda muka rabu bamu sake ganin juna ba sai randa aka kawoki asibiti, a dalilin gano kina da shigar ciki na nema number Alhaji Abaan domin na sanar masa. Sai dai yanda ya karɓi batun cikin naki yaban mamaki. Ina tsaka da taraddadi sai ga Nadwa. A wajenta nake jin ai kun rabu, yaron daya kawoki shine mijinki yanzu. Nasha mamaki, amma sai wani zancenta ya shafe min mamakin nawa. Ta nema mu ƙulla dil, in har na taimaka mata muka mallaki dukiyarki to lallai ko zata auran. Humm naji daɗi kamar zan mutu, dan ina son babyn nan”. Ya wani shafa ƙirjin Nadwa yana dariya da kashe ido duk da kuwa mahaifiyarta na wajen ko'a jikinsa balle ita. Cike da shaƙiyanci ya cigaba da faɗin, “Mun sami nasarar hakan, bayan ta amshe takardu da komai naki cikin siyasa sai kuma ga mijinki, shima yazo min da barazana, wai yaji duk abinda muka tattauna da Nadwa a office dan haka in ban bashi haɗin kai ba zai yimin miye-miye so soki burutsunsa na ƙuruciya dai da rashin ilimi. Niko na zarmashi ya shiga, nama nuna masa tsaronsa nake ji. Shine ya bani duk wani point dazan iya cimma gaci. Ada munyi niyyar barinki da motocinki da gidan da kuke ciki, sai muka fahimci ai ke da shi CUTA CE TA ƊAU CUTA. kawai mukazo suma mukai packaging nasu. A yanzu dai ki sanar masa ya daina wahal da kansa. Dan ni da matata Nadwa da Mom namu bama ma ƙasar, har abada kuma bazaku sake ganinmu ba byeeee”. Ya wani warwatsa yatsu kamar ɗan daudu. 

         Dariya Mom da Nadwa suka sanya. Sai kuma can suka tsagaita. Mom ta fara magana, “Humm Kainaat Kainaat. Nasan zaki shiga mamaki, sai dai ki sani ba abun mamaki bane dan kece kika jama kanki. Kina da son zuciya, yanda na riƙeki a rayuwa ban taɓa tunanin zaki saka mana da mugun hali ba. Ke kin samu dukiya tsakaninmu dake sai dai kiɗan tsakura mana ko. Ƙyauta 500k bata taɓa haɗamu ba duk wahalar da mukai miki a rayuwa. Har ƙasar waje na kaiki karatu saboda ƴata, amma da kika samu mijin nunama Sa'a sai kika maidamu wawaye ni da ita. Sai abinda kikai ɗan niyyar sammana. To dama binki muke sannu a hankali har zuwa gaɓar data dace. Gashi mun kai, karma ki wahalar da kanki a neman mu. Yanzu haka mun sayar da kaf kaddaririnki har company ɗin, mun tsallake ƙasa, saboda lawyer ɗin da duk wani mai motsin kirki a companyn dama mune muka haɗaki da su. Ki taya ƙawarki murna sunyi aure da Doctor kuma, nima zan sami wani mai jini a jikan nai wuff da shi kamar yanda kikayi da wannan yaron Dafeeq yake ko mima oho muku. Dama ita bariki alalan gero ce, wanda bai iyaba saita kwaɓe masa. Tun barowarki gidan Alhaji Abaan muke fakon dukiyar nan, sai zuwan yaron nan ya sauƙaƙa mana aiki. Muna masa godiya, ga ladan aiki nan mun bar masa ya rage zafi 500k ne babu yawa.” itama tai mata wani salo tana kashe ido ɗaya.........✍️



*_WAI KINA SHIRIN WUCEWA NE BAKI KARANTA BA😨._*



*_TO MAZA DAWO BAYA KI DUBA. IN BA HAKA BA ZA'AYI BABU KE NE_*



*_INA KUKE MASOYAN ZAFAFA BIYAR DAMA WANDA BAZU TAƁA SIYA BA SAI DAI SU KARANTA A HANYA_*.


*_MAZA KU MARMATSO KU MALLAKI NAKU DAN GAB JIRGIN YAKE DA BARIN ƘASA. MA'ANA GAB ZAFAFAN SUKE DA FARA SAKAR MUKU ZAFAFAN LITTATAFAN SU NA SABUWAR SHEKARAR 2024_*


*_KAR KUYI MAMAKI IDAN NACE MUKU TAFIYAR FA TA BANBANTA DA BAYA. SABODA SALON NA DABANNE, NA KUMA MUSAMMAN NE_*.



*_TSUTSAR NAMA....!!_*

          _(Bilyn Abdull)_



*_AMEENATU_*

         _(Mamu gee)_



*_KWANKWASON JIMINA...._*

         _(Mss xoxo)_



*_GUDUN ƘADDARA_*

         _(Safiyya Huguma)_



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE

ALLAH ka gafartama iyayenmu 

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post