Jawaheera Complete Page 5


Health College

Jawaheera Complete Page 5

 🍀☘️🍀☘️🍀☘️☘️☘️


            *JAWAHEERA* 


☘️🍀☘️🍀☘️🍀☘️🍀









 *PART* 5



Littafin haɗaka ne 




          Daga su 

        

NUSAIBA ALKAMAWA

       

PROFICIENT WRITER'S ASSOCIATION


          Da 


SAYYADA ( Barrister)


MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION





______Yasa aka kira masa jawaheera Shi kuwa imran sai yadawo daga gurin aiki sai yabashi nashi,aikuwa ba adadeba sai ga jawaheer tashigo bakinta dauke da sallama karasa shiga tayi taxauna ta gaishe da Abba ,amsawa yayi sannan ya mika mata kayan  yace dadynku alhaji adam ne yaɗinka muku kuda Imran, yafaɗi haka ne SBD yakarawa abokin nasa kima a idon ƴaƴansa bude ledan kayan tayi mai tambarin Maisallah shop,wani tsadadden lace tagani!batasan Lokacin da tace wow! Ba ,Amman Abba wanann lace din gaskiya yayi kyau Abba kuma rigar dai_dai nice   yakyauta angode masa Allah yasaka masa da mafificin alkhairi.


"Amen Abba ya faɗa, "mikewa tayi tace Abba Bara nashiga ciki to mama Abba yafaɗa! "tana fita ammy ta kalle shi da alamun tambaya akan fuskarta, murmushi yayi mata yace ai daman násan zaki tambaya kinsan abinda yasa nace Alhaji Adam ne yasiya musu ?saboda sukara daukar sa da muhimmanci, murmushi ammy tayi tace nagane yanxu.


* *JAWAD**


Shikuwa Jawad yana shiga daki zama yayi ya ajjiye kayan,shifa tunda dady yayi masa maganar abokinshi yaji yana son ganinsa tare da yaranshi kodan yasamu kanne,tashi yayi yace afara shirye _shiryen decorations dayake a inda za ayi walimar babu wani nisa tsakanin su da gidansu sosai wajan karfe biyar abokan Jawad suka fara zuwa gidansu SBD tare xasu tafi da Jawad hira sukai tayi acikin hirar ne Shabbir" yace gaskiya Jawad baka kyautawa asiya gaba daya ma kasata a Black list inta kiraka ma bata samu wllh bakaga yadda tadamu ba .


"Tsaki jawad yayi  yace kaga mutum wai meyasa kadamu da asiyah ne malam idan sonta kake kafaɗa Ni me bada sadakine,"rufamin asiri karnaje Madam Dina taji wannan Labarin kasanfa tana da  kishi kuma wannan big girl din ai sai dai kai dariya sauran abokanansa sukayi.


" Jawad yatashi yanufi bedroom yaje yakara yin wanka yana fitowa ya nufi wajan mudubinsa Saida yagama  shafa tsadadden mansa sannan yagyra kwantancen gashin shi aikuwa yayi kyau sai sheƙi yake ,dauko shaddar da Abba yabashi yayi yabude tsadaddiyar shaddar,  yaga dinkin shaddar yayi masa kyau sosai ,saka kayan kayan yayi (mukuwa writers Saida muka tsorata ganin irin azababben kyau da yayi.)


Gaskiya Jawad ba ƙaramin kyakkyawa bane ba ,turarukansa ya feffesa Sannan yafito yana baza wani daddadan kamshi.


"Aikuwa abokanan sa  suna ganin yafito suka saki baki da hanci suna kallon shi saboda tsabar haduwar dayayi sai suka raina kwalliyar su, duk da suma sun kure adaka ,yo namiji ma ya kalleshi yaji ya birgeshi inafa gakuwa mace ? " murmushi yayi musu yace, sai kutashi mutafi mana karmuje ayita,jiranmu tashi sukayi suka tafi.


 *JAWAHEERA* 


Abangaren su jawaheer kuwa abba yace kowa yatashi ya shirya daman kuma ya imran yadawo.


"Jawaheer ma anshiga wanka tana gamawa ta wuce wajan mirror tagama shafe_shafenta sannan tafara tsantsarawa kanta light makeup dauko lace dinta tayi taxura tayi ɗauri sannan tadauko mayafinta da jaka da takalmi kai masha Allah wato reader's jawaheer ba karamar kyakkyawa bace ba faɗan kyawunta sai mu kwana muna typing bamu gama ba ,Amman dai ku hasasota,  parlour tafito taga Abba har yashirya dashi da ya Imran suma sunyi matuƙar yin kyau ,ohh my jawaheer baby kinyi matukar kyau u looking lake takeaway Bara na dauke ki ahoto Wannan kwalliyar baza tatafi abanxa ba .


" murmushi tayi tace to yaya Imran, muna cikin haka ne saiga Ammi ma tafito da autanta abeed suma kuwa sunyi kyau dama ammy badai kyau ba dan kusan duk ita mukayi ,Abba yace kunga imran ku kyale pictures din nan haka kuxo mutafi,fita sukayi abba yabude motar yashiga suda ammy da abeed.


"Ammy tace batare da mu xakuje ba, Imran kushiga motarka kuje aciki saikuna binmu abaya,"kai ammy batare da ku xamu ba jawaheer tafaɗa cike da shagwaɓa." eh haka nace cewar ammy.


"Haka nan jawaheera tashiga motar ya Imran suka nufi wajan taron suna isa sukayi parking suka fito duk atare, abba yace kutsaya nakira dadyn naku ,fito da wayarshi yayi yace gasunan aharaban wajan,Dady da Mamy ne suka fito harda jahan suna karasowa jahan ta wani zaro ido itama jawaheer ido ta zaro waje.


Dagudu suka rungume juna dama kune baƙin da zamuyi jawaheer besty ? gaskiya nayi murna ,cewar jahan."Nima mamakin da nakeyi kenan jahan besty ashe nan zamuzo,dady ne yakatse musu zancen nasu ta hanyar cewa,dama kunsan junane? murmushi jahan tayi tace la dady itace fa besty na da nake baka labarin ta ,"auho itace kenan jawaheer tace Dady ina yini yataro?dady ya amsa cike da mutuntaka shima nan dai sukaita gaishe_ gaishe, sannan suka shiga ciki kallone yadawo kansu bare ma jawaheer da ta haskaka wajen shima ubangayyar yana juyawa suka haɗa ido biyu da jawaheer mai yakawo wannan yarinyar nan yafaɗa azuciyarsa Amman afili sai ya galla mata harara,itama kuwa jawaheer din ta mayar masa da murguɗa masa baki,cike da mamakinta yayi mata kallon xakixo hannu nane mara kunya kawai, samun guri tayi suka zauna da aminiyar Tata wanda sukayi anko cas abinsu,shima ya imran wajan da Jawad yake, dady yakaishi suka gaisa Sannan yazauna suna mamakin kayan nasu daya xamanto iri ɗaya .


____Shagali aka fara aka kawo wa kowa abinci wanda a plate din abinci kala biyar akai fried rice paper chicken Irish sai alala, da dambu ,kowa yaci ya koshi har cake aka yanka banda rabon abubuwa da akayi .



______Anyi shagali lpy antashi lpy kowa yakoma gida abokanan Jawad kuma waƴansu sun tafi wasu kuma basu tafi ba shidai Imran har sun dan saba da Jawad suna ta hira tare da abokanansa dayake imran akwai Surutu, ɗaya daga cikin abokanan yake cewa yana son jawaheer shifa yaga matar aure dama gidansu an matsa masa cewa yafito da matar aure shidai Jawad baice komai ba, shi hasalima haushin hirar tasu yakeji musamman ma akan mara kunyar nan,   haka dai sukaita hirar su wanda Imran bai nuna kanwar sa bace ba .


_____Su Abba dama suntafi gidansu Jahan cen nahango Abba tare da dady suna hirarsu ta abokanai ammy nagefen Abba ,Mamy nagefen Dady jahan da jawaheer suna ƙasa akan carpet zama Jawad yayi wanda suka shigo yanxu yagaida Abba cike da girmamawa shima Imran yagaida su dady,suka amsa cike da kaunar yaran azuciyar su.


" suna gama gaisawar dady yayi gyaran murya yace násan zakuyi mamakin inda muka hadu Allah ne yahada mu da Alhaji Abdallah kunsan yana siyar da atamfofi Nima kuma tunda ba sana'a ɗaya nake ba ina hadawa da kasuwanci to dai anan dai muka hadu,har muka ƙulla aminintaka.


 "murmushi sukayi abba ne yacewa jawaheer ashe daman Jahan ƴatace bansani ba inajin labarin ta daman bantaɓa ganinta ba saidai najita abakin mama, jawaheer tace la Abba kuma jahan budurwar yaya imran ce rannan datazo gidanmu suka hadu,tafaɗa cike da taɓargaza yarinta fal akanta,sunkuyar da kai Jahan tayi tsananin kunya duk ta mamaye ta jitake da alokacin kasa zata tsage to tabbas saita shiga ciki.


"shikuma Imran gallamata harara yayi,Shikuwa gogon ko kallon inda take baiyi ba shikanshi ma asunkuye yake  Amman yana mamakin Irin wautarta.


"Dariya Abba  yayi yace ashe suruka tace ƴartawa murmushi su Dady sukayi suma sukace Amman munji  dadin Wannan Maganar kutashi muyi salla saimu dawo cewan Dady mikewa sukayi sukayo alwala sukayi salla suna dawowa suma daman su mamy sun idar da salla.


 _______Yace to mufa tafiya zamuyi dan naga dare yayi cewar Abba , Dady yace tun yanxu kubari sai dan anjima mana bamu da wani nisa , murmushi Abba yayi yace

Ai gwara mutafi kam.


"Jahan tace Amman dai Abba anan zakubar jawaheer besty ta kwana kaga gobe Saturday ranar Sunday sai ta dawo,tambayeta idan tanaso ta kwanan .



"Dady yace gaskiya Alhaji yakamata ƴartawa ta kwana," to shikkenan babu damuwa mutafi,tashi ammi tayi suka fita wajan parking space dukansu Daman suka rakasu harda Jawad din mota suka shiga shima Imran din motarshi yashiga daman shi abeed harya fara bacci tare suka shiga mota da Imran sukuma Abba Suda ammy tada motar sukayi kirar c.r.v sunata dagawa juna hannu komawa cikin parlour sukayi dukansu suka zauna .


"Dady yace gobe Jawad ka kwashi kannan naka kakaisu shopping to Dady ya amsawa mahaifinsa amma azuciyar shi bayason fita da wanann yarinyar,Jahan tace Dady Bara mushiga ciki dan bacci nakeji daddy yace tun yanxu xakuyi bacci eh Dady to shikkenan Saida safenku to Allah yakaimu suka haɗa baki wajan faɗa.


_____ daki suka nufa shima Jawad yace wa Dady Bara yaje ya kwanta dan yagaji ,"mukadai zaku bari kenan muma bari mutashi Saida safe Allah yakaimu Dady ,fita yayi yanufi dakin sa.

Yana zuwa toilet yanufa yaje yawatsa ruwa Sannan ya fito daure da towel a kugunsa ,jallabiya yaxura sanna yakwanta wayarshi yaji tana ruri dubawa yayi yaga  rufaida afuskar wayar kauda fuskarshi yayi daga kallon wayan gajiya yayi dajin ringing din wayar daukan wayar yayi dan yasan indai baidagaba baxata hakura da kiraba, yakara akunne sallama tamai ya amsa shuru tayi nawani dan lokaci Sannan tace jawad wai meyasa kakemin wulakanci ne kodan kaga ina inasonka ne yasa kakemin haka jawad kaso mai sonka dan Allah wllh bazan iya Rayuwa babu kaiba dan Allah kasoni pls wllh ina sonka shiru yayi mata nawani lokaci Sannan kamar bayason yin Maganar yace mata rufaida nibance bana sonki ba kawai dai nibansan takura kekuma kincika takura.


" wllh bakaji yadda nakeji acikin zuciyata ba jinake indai ban aure kaba zan iya rasa rayuwata dan Allah Dr Jawad kasoni ko da ɗan kadanne tausayi tabashi yace mata ya isa haka rufaida," to kakarbi soyayyartawa dan Allah koda kadanne wataran zakaji kana sona shiru yayi mata shifa harta isheshi da zance to naji kidaina kukan Saida safe to Allah yakaimu i love U ,ya katse wayar batare da yayi mata martaniba.


Ita kuwa farin ciki ne ya mamaye ta SBD basu taɓa magana ba irin haka tsawon shekarun da take bibiyarsa.


____Abangaren su jawaheer suna shiga suka hau kangado kayan barci jahan tadauko musu suka xira Sannan suka kwanta karar wayar Jahan sukaji dauka jawaheer tayi taga ansa sweetheart 💋 jawaheera ta mika mata wayar tace ga sahibinki nan ,wanene keeefa yaya Imran ne inajin idan ba yaudarar mu akeba.


" dariya tayi tace ahaba Ni na isa na yaudare ku saidai ku kuyaudareni harya huta kenan maimakon yayi barcinsa tunda yau munhadu to ai yau din bakuyi hira sosai ba ko uhmmn besty.


___Daga wayar tayi tace hello Dear Naam kanwata yakike lpy klau yakaje gida lpy wllh kinsan bantaɓa tunanin Dady shine aminin Abba ba abin mamaki uhmn wllh kuwa Nima dai haka nagani kuma shine dakika ganni bakiyimin magn ba sosai murmushi tayi tace wllh kunyar su Abba nakeji shiyasa ma banma magana sosai ba kagama jawaheer akusa dani batayi bacci ba, Ohk bata wayar to mika mata wayar tayi tace gashi.


" amsa tayi tace hello yaya na'am haryanxu bakiyi bacci ba .


"eh yaya aikaima bakayi ba karike min kawata kaki bari muyi hira dariya yayi yace aimu Bama bacci da wuri sai mungama shan love dinmu tukunna muke baccin ahakan ma Bama son rabuwa da juna dariya tayi tace saikace super glue dariya yayi yace aimunfi super glue keni nama manta ambani sako sakonme kuma yayana, wani ne yace abashi number ki shine nace saina tambayeki sai damuna yake ,waishi da gaske yake auren ki yakeso yayi.


" Ita dai  jawaheera shiru tayi tarasa abin faɗa SBD tunawa da habeeb da tayi to nidai xanbashi number taki Saida safe Allah yakaimu mikawa Jahan wayar tayi suka cigaba da hirar su itadai jawaheer kwanciyarta tayi sukuwa su Jahan sundade suna waya sannan suka kashe wayar.


Washegari da asuba tashi sukayi salla tukunna suka koma bacci ba jawaheer ta farkaba sai wajan karfe goma tana tashi tayi wanka tana fitowa saiga Jahan tashigo dakin ita tariga jawaheer tashi yauwa zo kiban kaya nasa yauwa harkin tashi eh saidai kidauki abaya tunda kindanfini jiki zai matseki ki bude kixabi wacce xatayi miki to budewa tayi ta dauki wata dark blue 💙🔵 tasa tagyara gashinta dayake jawaheer akwai tsayin gashi batada cikar gashi sosai sai tsayi har baya yake saukowa dan ya wuce kafaɗarta ribom tasaka blue colour ta daure gashin tayi rolling din mayafinta masu karatu xo kuga yadda jawaheer ta hadu kamar wata balarabiya a larabawan tafi wata kyau Jahan sakar baki tayi tana kallon tsattsan kyau duk da itama ba bayaba.





Share and comment it.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post